← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 31 OF 40

Chapter.....33

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Na Sadaukar Da Wannan Chapter Ga Yar Uwa A Harkar Rubutu HADIZA SALISU SHARIF. Wacce Tarigamu Gidan Gaskiya Ya ALLAH Ka Karɓi Bakwancinta Ka Kyautata Tamu In Tazo. 🙏


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Baba Bukar Yace, "Gashinan Zaune." Yana Mai Nuna Dady. Kafin Yaɗora Da Cewa, "Saboda ALLAH da Ya Nuna Musu Darajar mu Da Suna Ƙin Zumunchin?" Kowa Falon Yaɗauka "Lalle Laifin Dady ne." Yayinda Dady Ke Aikin Bada Haƙuri Dan Shi Sun Gama Masa Komai Irin Wannan Zuwan Bazata da Sukayi Masa, Duk-da Kuwa Yana Cikeda Mamakin Irin Wannan Zuwan Nasu na Ban Mamaki. Shima dai Ya Nuradeen Shiru Yayi yaɗan Sunkui da Kansa ƙasa yana Murmushi dan Yasan Shi Mai LAIFI ne, Baya Tuna Rabonsa Da Zuwa Adamawar dan ko A Wancan Lokacin Marigayiya Khaleesat ce Mai Ƙokarin Tilas ta Masa Suje. Anan Kuma Saida Yaji Wani da Ya Tuno da Yar Uwar Tasa da Babu Garin ALLAH da Zaizo Yawaye Yawuce Batareda Yatuno da Ita ba, Wanda Yanaji Har Tashi Mutuwar tazo bazai Taɓa Mantawa da Mutuwarta ba.


Cikin Dubara Yasanya Hannunsa Yana Mai ɗauke Hawayen da ke Zobo Masa Kafin Yaɗan ɗago Kansa Yana Kai Kallonsa Ga Wani Ƙatoton Tangamemen Hotonsu dake Maƙale Aɗakin.

Sunfito Sosai Kamar Zakayi Magana Su Amsa Ma. Dady ne Zaune Gefensa Na Dama Momy ce Zaune Yayinda Ya Nuradeen ɗin Ke Gefen sa Na Hagu Shima Ita Kuwa Khaleesat Tana Gefen Momy Taɗan Rumgumota Dukkanin Su Suna Murmushi. Anɗauki Foton ne Sanda Yasamu Aiki A Legos.

Falon Yayi tsit! Bakajin Komai Sai Ƙarar Cukulla dake tashi Dattijan dai Kowane Sai Aikin Ba Cikinsa Hakke Yakeyi. Ya Nuradeen Ya Yunƙura da Nufin Fita Baba Bukar Yadawo dashi Yace, "Maza Zauna, Ina Kuma Zakaje?" "A'a Da Zanɗanje ne Harku Kammallah Wai." Ya Nuradeen Yafaɗa Cikin Girmamawa. Baba Tanko Yamiƙo Masa Flet Tareda Cewa, "Kaima Zuba Abinci Kaci, Kana Gudun mu Haka Ina Za'a Shaƙu?" Dole Ya Nuradeen Yayi Yanda Suka ce ɗin Kuwa Yasoma Cin Abincin Shima. Dan Dama Yunwar Yakeji Tunda Shima bai daɗe da Sauka Gidan Ba.


**********


Turus Tayi Ganin Baƙin da Ke Wajen Dr ne Kawai Ta Iya Shaidawa Kasancewar Shi Ta Sanshi, Saidai Baba Tanko ma Taba Ma Ranta Cewa Mahaifin Khaleesat Ne tun daga Yanda Taga Suke Ɗibar Kama dan Haka taja burki Jikinta Na Tsuma.


Dai-dai Lokacin Abdul-wahab Yashigo Gidan Bayansa Abubakar ne Sannan Yusuf Yashigo Shima. Duk Sukayi Cirko-Cirko Kukan Khaleesat Na Tsuma Zuciyoyin Su Musamman ma Sahibin Nata(Abdul-wahab) Da Yakejin Kukan Nata Tamkar Dalma Ake ɗiga Masa Ajiki Saboda Yanda Yakijin Damuwar Kuka Nata da Bayaso.

Dr ne Yaɗago Kai Yana Kallon Su Cikin Son Tantance Halinda Abdul-wahab Ke Ciki Kan Kukan da Khaleesat Keyi, Yaɗan Sauke Ajiyar Zuciya Kana Yace, "Tau Ai Zamu Iya Tafiya Ko?" Kafin Yajuyo Gurin Su Innarmu Yana Mata Ƙarin Bayani Cewa, "Innarmu Yaune Ranar da Nake Ce Maku Zan Warware Muku ƘULLALLEN ƘULLI Akan MUTUWAR Khaleesat Saidai Yanzun Zamuje Canne Gidan Nasu Ayi ta Gaban Kowa."

Kaitsaye Suka Miƙe Harda Baba Tanimu da Haryanzu Khaleesat take Maƙale dashi. Saidai Yanzun Tadaina Kukan Ajiyar Zuciya ce Kurum Takeyi Akai-Akai. Haka Suka Fice Aka Rufe Gidan Su Innarmu da Khaleesat Mmn Walida Dr Baba Tanimu Suka Shiga Mota Abdul-wahab, Abubakar da Yusuf Kuwa Suka Shiga Cikin Kk Napep ɗin Yusuf ɗin.


Gasunan-Gasunan Har Cikin Shiyyarsu Khaleesat Yayinda Sukayi Parkinq Suka Soma Firfitowa, Khaleesat Itace da Fitowa Lokacin Ba Kowa A Layin Nasu Tsit-tsit.

Dan Haka Basu Samu Yaron da Zai Musu Iso Cikin gidan ba sai Kawai Baba Tanimu Yajagorance Su Zuwa Cikin Gidan.


Dam! Dam!! Dam!! Shine Sautin da Zukatan Su Momy Sukayi Sanda Idanuwansu Sukayi Musu Arba da Su Baba Tanimu Tareda Khaleesat. Baba Tanimu duk Yana Hankalce dasu Yayi Murmushi Kawai Kafin Yakara Rangaɗa Sallama Cikin Fara'a Yajawo Hannun Khaleesat Gamida Cewa, "Zo ki Zauna Nan ɗiyata." Anan fa Aka Shiga Kallon-Kallo Tsakanin Momy, Dady Ya Nuradeen dakuma Matarsa Aunty Shahuda, Sukam Su Baba Bukar da Baba Tanko Da Baba Manu Murmushi Kawai Sukeyi Kasancewar Damar Suna Sane da Komai.

Muyyudim kuwa Yasheƙo da gudu yaɗale Jikin Khaleesat Yana Oyoyo Momy na(In baku manta ba itaɗin mutunniyar sa ce.) ga Khaleesat ɗinma Haka Lamarin Ya Kasance Duk Ilahirin Jikinta Rawa Yakeyi Yayin da Take Wasu Hawaye Suka Ɓalle Mata Tamkar Anbuɗa Famfo. Kafin Su Ankara Kuwa Ihun Momy Kawai Sukaji Tafaɗi Sume Dole Sukayi Kanta da Hanzarinta Suna Masu Ƙokarin Shafa Mata Ruwa, Yayinda Haryanzun Dady da Ya Nuradeen Harma da Aunty Shahuda Sukayi Mutuwar Zaune Wuta Ta ɗauke Musu Ɗif Suka Kasa Tantance wace Irin Duniya ta Suke Anasu Sanin dai Ba'a Taɓa Mutuwa Aka dawo ba Kuma Lalle In ma Ba Yaudarar Kansu Sukayi ba Khaleesat ce Suka Gani Tareda Su Baba Tanimu da Kuma Yan Gidan su Abdul-wahab Tau Meke Shirin Faruwa Kenan? Tambayar da Suka Kasa Amsawa Kansu Kenan.

Sukuwa Innarmu Daƙyar da Taimakon Dr Suka Samu Momy ta dai-dai ta Inbanda Zabure-Zaburen ba'abunda Takeyi. Tana Faɗin, "Shikenan Ita Ma Ta Mutu dan dai Inba DUNIYAR MATATTU BA. Ba Yanda Za'ayi Ta Koma Ganin Khaleesat ɗinta Wadda Takeda Tabbacin Cewa Ta MUTU. "Tau Meke Shirin Faruwa danine?". Tafurta Hakan A Fili. Baba Tanimu Yayi Murmushi Yana Cewa, "Ba Abinda Zai Faru dake Sai Alkairi dan Haka Ki Nutsu Kiji Abinda Ke Faruwa Ko ya Farun Khaleesat dai bata MUTU ba Tana nan Raye."


Wayyanan Sune Kalamai Mafi Razani da Girma Ga Su Momy Harma Su Dady da Ayanzu Wutar su data ɗauke ta Dawo, Inbada Gumi Ba Abinda Dady keyi Kamar Ba Muna Cikin Lokacin Sanyi ba. Dole Baba Bukar Yamiƙe Ya Kunna Fanka Tasoma Bama Dady Iska. Ya Nuradeen Kuwa da Aunty Shahuda Suka Kafe Khaleesat da Idanu Ko Ƙyaftawa basayi.

Momy Tamiƙe Zata Fice Falon da Gudunta Su Innarmu Sukayi Hanzarin Riƙota Suka dawo da Ita Cikin Falon, Momy Ta Fara Sarewa Cewa da Mafarki ne Takeyi, Tafara Yarda Cewa Wanda Abun dai Yana Son Zama Gaske. Tau Amma Ai A gidan su Take. Dady Yadafe Kansa da Ke Shirin Tarwatsewa Gida Biyu Haka Shima Ya Nuradeen Yayi Yayinda Aunty Shahuda Take Kuka Wiwiwi Cikin Wani Irin RUƊANI Da Ta Matsu Ya Ƙare Ta Mastu Ace Da Ita Tafarka Daga Baccin da takeyi dan Wannan Abun Babu Ko Tantama MAFARKI NE kawai Irin Na da Daɗin Bacci. Yo Inba Bacci Ba Waya Taɓa Ganin Mutum Ya MUTU kuma Yadawo Ko Acikin Fina-Finai da Littafai da Suka Kasance Rayuwar Ƙarya Indai Akace Mutum Ya Mutu Tau Shikenan Fa Ya Mutu Balle Kuma Duniyar Tasu ta Gaskiya.

Kai Haka dai Sukayi ta Fama da Tashin Hankali Wanda In Zamu Ƙai Yaushe Bazamu Iya Bayanne Adadinsa ba Wanda Kuma Babu Wani Rubutu da Zai Iya Bayyane sa Harma Ya Misalta Irin RUƊANIN Da Suke Ciki Harma da Iface-Ifacensu. Saidai Kawai Abarwa Mai Karatu da Ƙyiyasta Irin Hargitsin da Su Momy Suke Ciki. Sun Kasa Yarda da Kalamin da Su Baba Tanimu ke ta Nanata Masu Cewa, "KHALEESAT BA MUTUWA TAYIBA KHALEESAT TANA RAYE Illai Kawai Akwai ƘULLALLEN ƘULLI Da In Suka Nutsu Za'a Warware Musu Tau Amma Sun Kasa Samun Nutsuwar Sun Nemi Nutsuwar Sun Rasa. Haka Akai Ta Fama da su Acikin Falon Kafin Aka Samu Suka Natsa Saboda Faɗan da Baba Tanimu Yatasa Gaba Yanayi Musu Kasancewar sa Mutun Mai Zafi da Faɗa Shiyyasa ma duk Familyn Nasu Sunfi Shakkarsa. Cewa Yakeyi, "Karku Maida Mu Ƙananu Mana Ai Kunsan dai Bazaiyu Tsofai-tsofai Damu Muzo Gurin Da Maganar Banza Ai Bazai Yu Bane." Khaleesat dai Sai Kuka Take Mai Matuƙar Tsuma Zuciya Takuma Rasa Wa zata Tunkara Acikinsu Momy, Dady ko kuma Ya Nuradeen? Kawai Sai Ta Sami Kanta A tsakiyar Falon Tana Cigaba da Rera Kuka Tamkar Ranta Zai Fita. Hakan Yasa Falon Yayi Tsit! Inbabda Kukan Nata Ba'abunda Kakeji.


Taɗago Kanta Ta Kalli Momy Taga Yadda Duk Momyn Tafita Hayyacinta Tayi Wata Irin Rama Mai Ban Tausayi Kamar Ba Momynta Da Ta Sani Mai Matuƙar Jiki da Ƙwalisa Ba Kai Lalle Tayi Yawo Da Hankalin Iyayen ta Mafi Soyuwa Agareta Wanyanda Nan Duniya Takeji Bata da Kamar Su tau Amma Yazatayi Ita Kanta Ba Laifin ta Bane SONEE SILAR KOMAI. Sannu A Hankali ta Rarrafa Izuwa ga Jikin Momy Tafaɗa Tana Cigabada Kukanta Cikin Kukan Tace, "Momy Kuyafemin Natuba Nabi ALLAH Nabiku. Wallahi duk Abinda Yafaru, Yafarune Bisaga SILAR SO Wanda Nabari Ya Rinjayi Zuciyata Har Yazama Nakasa Tafiyar dashi Yazamana Shine Ke Jagoranci na Har'izuwa Sanda Ya Makantar da Idanuna Ga Manta Muhimmancinku da Irin Fifikon da Kuke dashi Akan Wanda Na Aikata Hakan Ta sanadin Na Rayu dashi, Saidai Nasani Rayuwa taredashi Gareni Dolene Inba Hakaba Nina Nasani Mutuwa Ta Wajaba Gareni domin dai Nasani Walwala da Kwanciyar Hankali Zasuyi Bankwana Dani." taɗan Sarara Cikin Ƙunar Zuciya da Ta Ruhi Kafin Taɗora da Bayanin da A yanzun take Ganin Bata da Mafitar da Tawuce Yinsa Kodan Irin Fa'idar da take Hangowa Tattare da Bayanin Ko Bayan Hakan Ma Ai Akace "Ranar Wanka Ba'a Ɓoyon Cibi." dan Haka Ta Kalli Dady Gamida Cewa, "Dady Kaima Ina Neman Yafiyarka, ALLAH Shine Shaidata Nayi Iya Ƙokarina Na Fahimtar da Ku A Hakan A Irin YARE Mai Sauki Saidai Kun Kasa Fahimtar sa Shiyyasa Muka ZAƁI Fito Muku Ta Wannan YAREN Domin Muna da Tabbacin Zai Nuna Maku Zahirin Abinda Kuke Son Aikatawa BAIDACE BA."

Taufa Wasa Farin Girki Kallo Kuma Yakoma Sama Akace Shaho yaɗau Giwa. Gabaki ɗaya Mutanen dake Cikin Falon In Kacire Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Dakuma Almajirin Gidan Su Khaleesat ɗin Watau Sani tau Sauran Kam Duka Sunkasa Fahimtar Wannan Zaurancen Na Khaleesat domin Kuwa ko Su Baba Tanimu Wani Suka Sani Wanin Basu Sani Ba.


My Readers Wai Ya'ake Ciki ne? Meke Shirin Faruwa Ko Kuma Yafaru Wanda Ba Kowa Yasani Ba? Muje Tare da Ku A Fage Na Gaba Domin Jin Warwarar Lamarin
Tareda Alkalamin 👇


Fa'IK ✍
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 31 · 0% Book details