← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 27 OF 40

Chapter.....29

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Sai Kawai Yakama Auntyn Tasu Yarike Sosai! Yana karanto duk Adu'ar da tazo Bakinsa Yana tofa Mata, Kafin Ya'ankara Ta zube A Sume.

Tashin Hankali Wanda Ba'a Samaka Rana Cikin Wata Irin Kuwa da Ƙaraji Yake Kira "Aunty!!!!!" yadurƙushe gabanta Yana Cigabada Cewa, "Duk Tafiya Zakuyi Ku Barni ne?" Dai-dai Lokacin Al'umma Suka Hankalta da Abinda Ke Faruwa Na take Kuma Suka Kawo ɗauki.

Aka Tallabi Maman Walida Saman ɗan Gadon tura marassa Lafiya Zuwa Imerginycy Room Domin Bata taimakon Gaggawa. Dai-dai Lokacin ne Kuma Abubakar Yajuyo Yana ƙarewa Cincirindon Mutanen dake Gurin Kallo Ga Mamakinsa Kuma Sai Yaga Abdul-wahab ne Cikinsu Shima Cikin Tashin Hankali Akan Halinda Maman Walida Tashiga. gefen sa Kuma Khaleesat ce Itama dai Hankali Tashe. Dubawa Yasakeyi Domin Ƙara gasgata Abinda Idanunsa Ke Gane Masa Shin Mafalki Yakeyi Ko dai Shima Haukar Ce Ta Raɓeshi? A wanna Lokacin ne Abdul-wahab Yamatso Kusada Shi Yana Cewa, "Auta Kaga Abinda Nake Gayama Ku ko? Kaga Ƙaryar dai ce Khaleesat ɗita Bata Mutu ba ko? Ina Fatar Kai kam zaka Nutsu Ka Fahimce ni Ba Kamar Yadda Su Innarmu da Maman Walida Suka Kasa Fahimta ta ta ba."

Wata Irin Hajijiya ce ke Neman kai Abubakar Ƙasa, Amma Sai Yayi Hanzarin dafe Bango Sa'anan Yalalubi Kujera Yazauna Lokaci ɗaya kuma Yasa duka Hannayen sa Biyu yadafe Kansa Yana Mai Ƙokarin Karanto "Innalillahi Wa Inna Ilaaihi Raju'un!!!"
Kalmar da Yaketa Nanatawa Kenan Babu ji Ba gani Yana ji Duk duniyar na Juya Masa.

Innarmu Kuwa Tunda Suka Baro ɗakin Suka Biyo Maman Walida da tayiwa ɗakin Fitar bindiga.

Cikinta yaƙulle tamau Kafin Kuma Wata Irin Guduwa Mai Matuƙar Sauri ta Tasoma mata Dole Tadinga Kai Kawo tsakanin ɗaki da Toilet tana Fyace Majina da Gyafen Zanen ta Tareda Ƙara Tabbatarwa Kanta A Yau Wata Annoba Tafarmusu Sukam Sai Yanda ALLAH Yayi dasu Kawai.

Acikin Wannan Halin ne taɗaga ƙafarta dakyar Tafito zuwa inda tun ɗazun takejin Hayaniyar.

Kai tsaye gurin Abubakar ta Nufa tadafashi Tareda Cewar, "Auta Meke Shirin Faruwa Damu ne?".

Dai-dai Lokacin Itama Khaleesat ta matso tana Kuka Tadurƙushe Gaban Innarmu Tareda Cewa, "Innarmu Ku Nutsu ku Saurare ni Wallahi Ban MUTU ba Akasine Aka Samu...." Innarmu tai Maza takoma Gefe tana kallon Khaleesat ɗin Yayinda Shima Abubakar Yaɗago A Firgice Yana Kallon ta Yana Kuma Ƙokarin tattaro dukkan Wata Jarumta tasa domin Karya Fece da Gudu Shima.


Itama Innarmu Sai Kallon Khaleesat Takeyi ba ko kyaftawa. Tana Kuma Tambayar kanta Dama Haka FATALWA Take? Amma taji Ance FATALWA nada Siffa Mai Ban Tsoro Kuma Ita Bataga Haka ga Khaleesat ɗin ba?


Ita kuwa Khaleesat Kukan ta Yatsananta, Yinsa Takeyi Kamar Ranta Zai Fita Saboda yanda taga Mutane Na Tsoro da ƙyamarta.


Abdul-wahab yaƙaraso Gurinta Yana Cewa, "Khaleesat Kidaina Kuka Koda Kowa zai guje ki ni Ina Tareda ke! Ba MUTUWA Kikayi kika dawo ba ko fin Hakan kikayi bazan taɓa gudun ki ba." tajuyo tana Cewa, "Yawwa Abdul-wahab Ni Nasani Ko Kowa Yakasa Fahimta ta Kai Zaka Fahimceni Kuma Koda Kowa ya gujeni Kai Bazaka Gujeni ba."


Tahaɗa Hannayen ta guri ɗaya tacigaba da Cewa, "Dan ALLAH Innarmu Ku Nutsu ku Saurare ni Wallahi Wallahi Nice Ba MUTUWA Nayi ba."


Kalaman da Khaleesat keyi Kenan Wayanda Suka ɗan Fara Samarmawa Innarmu da Wata ƴar nutusuwar da Suka rasa tun a ɗazun, Suka Kuma jefa Su Innarmu Cikin Nazari da Tunanin Yakamata su Natsu su Saurareta.

A wannan Lokacin ne kuma Likitan da ke Duba Maman Walida Yafito Yana Ƙokarin Cire Facemaks ɗinsa, Gurin Su Abubakar ɗin Yazo Yace, "Kune Yan Uwan Waccan patien ɗin Tamu Ko?" Abubakar Yaɗago kansa dake Matuƙar Sara Masa Kamar zai Rabe Biyu Saboda Halin Ruɗanin da Suke Ciki Yace, "Eh Mune."

Likitan Yace, "Yawwa Mun Samu Yar Uwar taku ta farfaɗo, Tashiga Firgici ne Wanda Yasa daba dan Suman Tayi ba, tau Zata Iya Samun Bugun Zuciya Na Nan take. Tau Kuma Sai ALLAH Yagajarta Mata Wahlar ta Yatsaya A Suman Yanzun Ma Komai Ya dai-dai ta Zuwa Anjima Idan taɗan Ƙara Samun Hutun Ƙwalƙwalwa da Na Jiki Zaku Ganta tadawo Sumul."


"Tau Likita Zamu Iya Shiga Muganta Yanzun?" Abdul-wahab Ya watso Masa Wannan Tambayar

Batareda La'akari da Waye Yayi Masa Tambayar ba Yace, "A'a 4Now Tana Buƙatar Hutun ƙwalƙwalwa Dana Jiki Kamar Yadda Na sanar Daku, dan Haka Akwai ɓukatar Kubarta ɗin Zuwa Anjima."


"Tau yayi Likita Muna Godiya! ALLAH yayiwa Rayuwa Albarka." Innarmu ce Mai Wanna Jawabin.


"Ameen." Likitan ya'amsa Harya Wuce Kuma Sai Yadawo Yana ƙare Musu Kallo Cikin Mamaki Yace, "A'a Wannan Ba Patien ɗinmu Bane da Ba Lafiya?" Yayi Maganar da Kallon Abdul-wahab.

Abubakar Yace, "Shine."


Likitan Yayi Saurin Kama Hannun Abdul-wahab Da Tun Faruwar Lamarin Ketsiyaya Jini Saboda Fisge ƙarin Ruwan Da Akeyi Masan da Yayi Ba Bisa Ƙa'ida Ba.


Yace, "Wannan Ai haɗari ne Yazaku Barshi Yataso Cikin Irin Wannan Halinne?" yana Wannan Maganar Yana Ƙokarin danne Hannun na Abdul-wahab da Plaster Kafin Yajashi Suka Nufi ɗakin da Aka Kwantar Abdul-wahab ɗin. Innarmu Tabibayansu Tana Faɗin, "Yaro Ai Mu Muna Cikin RUƊANI. wanda Ko A Rayuwar Mafarki Bantaɓa Ganin Irin sa Ba." Bai Saurari Abunda Innarmu Take Sanar dashi Ba Sai da Yadangana Abdul-wahab da Gadon sa Yaga Ya dai-dai Ta Komai, Sannan Yajuyo Yana Cewa, "Inna Kudaina Barin Irin Hakan Na Faruwa Yakamata Inkunga Irin Hakan Kuyi Ƙokarin Sanardamu Dan Mu Ɗauki Mataki da Wuri."

Innarmu Tafahimci Sukaɗaine Suka San Ruɗanin da Suke Ciki Kuma Su Kaɗaine Suka San Halinda Suke Ciki Dan Haka Babu Wani Bayani tsayayye da Zatayi Masa dan Haka sai tazaɓi Amfani da Wayyanan Kalmomin Da Zasu Sanyaya Zuciyar Likitan Itama Kuma Su Hutar da Ita. Wayyanan Kalaman Kuwa Sune. "DAN ALLAH LIKITA AYI HAKURI INSHA'ALLAH ZAMU KULA!!!" daganan ta Lalubi Buta dan Komawa Toilet.

Kallo ɗaya Likitan Yayiwa Khaleesat Kamar bai santaba Kamar Kuma ba Komai A tsakanin su Yajuya Yafice daga ɗakin.

Ita kuwa Khaleesat Sai ta Nemi Kujera taxauna tana mai Ci Gaba da Fuskantar Abin Ƙaunarta Cikin Wani Irin Bugun Zuciya da Zallar DAMUWAR da Tayiwa Zuciyarta Kane-Kane. Tana ƙara jin Cewa Komai ma Yafaru SONEE SILLAR SA! Da Taimakon Iyayensu da Suka Kasa gano Girman Soyayyar dake Tsakanin su da Masoyin ta Abdul-wahab.


**********


Tsakar Dare Suka Sauka A Ƙasar ta Maleshiya gama Lokacin Agogon Ƙasar ke Nuna Ƙarfe 2 Nadare Dai-dai.


Tafe Suke A Matuƙar gajiye Musamman ma dai Maman Asharaf da Yakasance Wannan Shine Karo na Farko A Rayuwar ta da Tashigo Jirgi da Nufin Barin Ƙasar Nigeria, Kasancewar Shi Dr Jabir Sunsha Fita Zuwa Yin Wasu Kwasa-kwasai Akan Abinda Yadangaci Cututtuka.


Shine ke Janye da Akwatinsu da Sauran Yan Shirginsu Yayinda Maman Asharaf ke Saɓe da Asharaf ɗin A Kafaɗarta Wanda Tuni Yayi Bacci. Taxi Yake Ƙokarin Tarar Musu Cikin Sa'a Kuwa Yasamar Musu Shatar Mai Tax ɗin da Zai Saukesu Har Masaukinsu. Kyawon Ƙasar da Tsarin ta Suka Sa Maman Asharaf ta daina jin gajiyar da take ji ɗazun, tabaza na mujiya tana Kallon Farar fata daketa kai Kawo A Ƙasar Kamar ba Dare ba Kowanensu Jibge da Coat. Ga dogayen binaye da Kuma Shuke-Shuken da Sukayiwa Titunan ƙawanya.


Dai-dai Wasu Flat ɗin Gidaje da Korayen Ganye Suka Mamaye Gurin, Mai taxi ɗinsu Yayi Parkinq. Suna fitowa, Wani Irin Sanyi Yabuso su Wanda Sai da Maman Asharaf Taƙamƙame Jikinta Tana mai daɗa Shakar Iskar Mai Tafe da Kamshin Shuke-Shuken Itace Kala-kala da Sukayi wa Wurin dabaibayi. A ranta Tana ƙara tasbihi ga ALLAH Mai Falala Harma da Ni'imomi daban-daban, Lalle Maganar Nan ta Bahaushe Gaskiya ce, 'ALLAH ɗaya gari banbam' dan itakam taga zahirin Hakan.

Dr Jabir Sallamar mai taxi Yayi Kafin Suka nufi Cikin Flat ɗin Kaitsaye Hawa Na Biyu Suka Nufa Bayan Sunkawo Wata ƙofa Suka Tsaya Dr Jabir Yafitar da Wani Samfurin key Mai Kama da Takarda Yaɗan Manna A Ƙofar Sai gata Ta buɗe.


"Aljannar duniya!" Abinda Maman Asharaf Tace Kenan Sanda Suka kutsa Kai Cikin Gidan. Faɗar Irin Tsarin Gidan da Kuma Kyanshi Sai Ya cinye Mana yan Shafuka Namu dan Haka mai Karatu Nabarka da Wannan Hasafin Amma dai Falo ne ƙato da yake ɗauke da ɗakuna daban-daban Sumaɗin Kuma Cikin tsari akayi Su.


Tsakiyar sa Wani Lallausan Carpet ne ke malale A gurin da kuma wasu Zafafan Kujeru da Suka fi Kama da Na gidan Sarauta suke Zagaye A Falon. Ga Kyakykyawan Center table ɗin Glass dake Gurin, Shima Sai ƙyalli Yake. Ko'ina Na Falon Sai Hasken Gluf Keta Fita.


Faɗar Abinda Ke Zuciyar Maman Asharaf Gameda Risƙan Kanta A matsayin Wacce Zata Kasance Ma Mallakiyar Gidan Na Yan Shekarun da Gwammanti taɗaukar Ma Su Dr. Jabir Su Ƙara Ilimi Akan Wani Ciwo da Ya ɓulla kwana nan, Ba'a Bune Mai yuwa Cikin ɗan ƙanƙanin Lokaci ba. Ilai dai kawai Harta fara Ƙissima Irin gyran da Zata dinga yiwa Gidan.


Wani Murmushi Yasubuce Mata batareda tasan Cewa Dr Jabir Na hankalce da ita ba. Sai da Taji Yace, "Baƙauya Kawai!l."

Tayi hanzarin dubansa tana Dariya Kafin tace, "Naji dai, Ai da Kaine Ni Kila ma Fin Hakan Zakayi." Yakama Bakinsa yana Cewa, "Nine Ma Zaki ce Wa Haka? Lalle ma Yarinyar nan, Nifa Nama Lura Kwana nan Wani Reni Yashiga Tsakanin mu Fa? Kodai dan...." Sauran Zancen Yaraɗa Mata A Kunne.


Me Zatayi Inba Dariya ba Tareda Rufe Fuskarta Cikin Matsanaiciyar Kunyar da Zancen Nasa Yasaukar Mata Kafin taɗora da Cewa, "Nidai Wallahi Bance Ba."


"Ba Waninan Ai Nagane ki Kuma Wallahi In....." Maman Asharaf Tayi Wani Irin Sufa ta Rufe Masa Baki tana Cewa, "Dan ALLAH Kabar Zancenan, Wai Kai Kam Meyasa Baka gane Ka Girma Yanzun?" Yadanna Mata Cizo A Hannun Nata Tayi Saurin Janyewa Tana Kukan Shagwaba.


Yakanne Mata Ido ɗaya Yace, "Meye Girma....?" Maman Asharaf Ta Taresa Wurin Cewa, "Nidai dan ALLAH Gajiya Nakeji Muje Kanuna min gurin, Inɗan Samu Inwatsa Ruwa Inyi Sallah In Sama mana Abinda Zamuci Ko Kai duk Baka Buƙatar Wannan?"

Yasaƙalo ta Tareda Karɓe Asharaf ɗinda ke kwance Kan Kafaɗarta tun ɗazun Batareda Yasan Wainar da'ake Toyawa ba. Yana mai Cewa, "A'a Nima Ina Buƙata Uwargida Ran gida."


Tau Dr Jabir da Maman Asharaf Asha Soyayya LAFIYA!


Anan Kuma Zan Nisa Masu Karatu Muje daku Gaba Tareda Alkalamin


FA'IK.
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 27 · 0% Book details