← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 40

Chapter.....4

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

A.......
Maimaikon Pages 123, Zankoma Da Yin Amfani Da Chapter.👌


Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


Typing.....💻


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. 07039676994

Bissmillahi Rahmanin Raheem


Abdul-wahab Duk Sai Yarasa Nutsuwar Sa Amma, Da Yayi Wani Tunani, Kawai Sai Yamaze Yayi Mirsisi Dan Kar Yabada Da Kansa. Dan Haka Da Kuzarinsa Yabude Kular Dake Gabansa Yadibo Mal-Malar Tuwo Leda Biyu Yasaka A Flet Kafin Yazuba Bushashiyar Miyar Goro Da Wadatu Da Man Shanu Sai Kyalli Take, Yasoma Aikawa Cikinsa (Dama Can Shi Baya Wasa Da Ci😜)

ππππππππ

Cikin Kwana Ukku, Abdul-wahab Yakamu Da Wata Irin Zazzafar Soyyayar Da Baisan Ya'akayi Tayi Tasiri Akansa Ba. Ikram Gaba Daya Tabi Ta Mamaye Zuciya Da Ruhinsa Harma Da Tunanin Sa. Saboda Acikin Kowane Lokaci Cikin Kiransa Take Karramsa Takeyi Do Kowane Abu Da Yazamo Mallakinta, Kuma Komai Nata Soyyaya Yake Nuna Masa, Ayyukanta, Kalamanta, Gangar Jikinta, Ruhinta, Kai Har Idununta Idan Ya Kallah Ba'a Bunda Yake Hangowa Face Tsantsar Kauna Da Soyyaya. Tau Shikuwa Waye Shi da Zai iya Watsi da Wannan Masoyiya? Dan Haka dae Tuni Abdul-wahab Yakarbi Tayin Da Khaleesat Tayi Masa (Kamar Yadda Momynta Ke Kiranta) Suka Antaya Duniyar Masoya Suke Ci Gaba Da Lulawa.

Azumi Dae Yangangara Har Yakawo Gangara Dan Yauma Kowa Kagani Da Dan Radionsa Yana Saurare Yaji Me Sarkin Musulmi Zaice Akan Ganin Wata? Dan Haka dae Yau Muna Sa Ran Daren Sallah ne, Mata Dai Mussamman ma 'Yan Mata Tuni Aka Baxama Ana Kitso Da Lallen Sallah, Wasun Ma Har Andawo Gida Anfara Shirye-Shiryen Abincin Sallah Gobe.

Khaleesat Na Cikinsu Dan Ansha Lalle Yazauna Radau! A Yan Hannayenta Da Santala-Santalan Kafafunta Abinka Ga Farar Macce Sai Kyalli Take, Ga Kitso Anzubo Wasu Gaba Wasu Kuma Baya, Sai Kai Komo Take A Tsakar Gidan Nasu Domin Taya Momy Girki. Lokaci-Lokaci Tana Duba Wayar Momynta Dan Sunyi Da Abdul-wahab Zai Kirata. Shikuwa Abdul-wahab Yana Can Gida Wanka Ake Sha Bayan Andau Gayu Aka Fito Tsakar Gida Ana Daura Agogo Innarmu Dake Ta Kai kawo Tsakanin Dakinta Da Madafi(kitchin) Dan Tana So Ta kammallah Miyarta, Da Gari Ya waye Tuwon Laushinta Kawai Zata Tuka. Ta kalli Abdul-wahab Din Tace, "Kai Kuma Wannan Gayu Haka Sai Ina? Ko Duk Zumudin Sallarne Ka Kasa Bari Sai Gobe?" Yayi Dariya Kafin Yasa Hannun Yadauki Tsunkin Naman Miyar Da Inna Ta soya Yajefa A Baki Yace, "Kai Innarmu Wane Gayu ne Nayi? In Yusuf Yaji Kina Fadar Haka Ai Sai Yace Yafasa Baya Son In Rake Sa Gurin Budurwar Tasa."

"Oh Tau Can Kuka Nufa Kenan?"
Innarmu Ta tambayeshi Tana Kokarin juya Miyarta Kafin Ta debo Ta Dan Dana Danji Komai Yaji. Kafin Tace, "Sai Nake Jin kamar Miyar Nan Gishiri Yaso Yin Yawa Fa?" Abdul-wahab Yadan Tara Hannun Sa Yana Cewa "Dan Sammin Inji." Wanda Yayi Dae-dae Da Shigowar Yusuf Gidan Idonsa Yakai Kan Abdul-wahab din dake Ta Ayikin kwadai, Yayi Dariya Yace, "Innarmu Sarkin Kwadayin Nan Na Nan ya Hanaki Aiki ko?" Kafin Innarmu Tai Magana Abdul Yayi karaf Yace, "Eh Din Ya Ranka?" Innarmu Tace, " Ya Ransa ko?...." "Innarmu Raina Fari Sol." Yusuf Yafadi Hakan Yana Mai Kokarin Zama Kan Wata Kujera Dake Tsakar Gidan Abdul-wahab Yayi Maza Yace, "Kaga Dan ALLAH Karka Zauna, Tashi Zakayi Mutafi Yanzu Inkuka Fara Zance Kaida Innarmu Muda Tafiya Sai Safe."

Dai Dai Lokacin Shima Abubakar yafito Daga Cikin Toilet Yayo Wanka Yace, "Kajimin Ya Abdul Tunda Kai ka Cika Cikinka Shi Baxaka Barshi Yacika Nashin Ba?" Kafin Yakalli Yusuf "Kaga? Ya Yusuf Bari Inzubo Mana Abinci Muci In Yaso Ko'ina Zakuje Sai Kuje. Kai da ma Za'ayi wa Rakiyar Baka Sauri Sai Shi?" Kafin Abdul-wahab Yace, Wani Abu, Innarmu Tarigasa Cewa, "Yawwa Dan Auta Na ALLAH Ma Albarka Zo Kazubo Maku Abincin Namanzo." Innarmu Takarasa Maganar Cikin Sigar Zolaya. Gaba dai Sukayi Dariya Banda Abdul-wahab Da Yayi Fuska Yana Cin Magani "Nidae Innarmu Nagano Abbakar Dinnan Yamana Farrakau Dole in Tashi Tsaye." Gaba Dai Sai Da Suka Bushe Da Dariya Kafin Innarmu Tace, "Ba Wani Farrakau Da yayimin Illah Gaskiya Da Yafi Ka so Kuma Yafika Aiki Da Ita..." "Cau! Innarmu Telan Ne Mai Gaskiya? Lalle ma Innarmu, Ko Yanzun Kinsan Iyakar Adadin Wayanda Gobe Zasuyi Sallah Ba Dinki Saboda Rashin Gaskiyar Tela?"

"Tau Nidae Nasan Bada Dan Autana, Dan Tun Da Watan Azumi Yakama Kwana Gashi Bayayi, Kuma Ban Taba Jin Wani Ya Sallamo Masa Cewa Yasaba Alkawali Sai Dai Yace Yazo Yakarbi Dinkinsa."

"Gaya Masa Dae Innarmu, Ai ba Duka Aka taru Aka Zam Daya ba."
Yusuf Ne Mai Wannan Maganar Yana Kokarin Kai Cokalin Da yaciko Abinci Abakinsa. Abdul-wahab Yahararesa Yace, "Dan ALLAH Malam Yi Kagama Mutahi Dare Keyi Safiya Ba, Tunda Nidae Nagano Gidannan Kun Hade min Baki." Innarmu Ta Kalli Su Yusuf Tareda Cewa, "Kuyi A Hankali Har KU kammallah In Yagaji Da jira Yatafiyarsa." Kafin Tamikawa Abdul-wahab Wayarta Tana Cewa, "Kamomin Gidan Radio Naji Ko Sarki Yafara Sanarwar Ganin Watan," Yamikawa Innarmu Wayar Bayan Yakamo Mata Tareda Mikewa Suka Nufi Hanyar Fita Shida Yusuf Suna Yiwa Innarmu Sallamar Suntafi Sai Sundawo. Abubakar Yace, "Yusuf Kajira Akawo Mana Kunun Ayar Mana." Yusuf Kamar Zai Tsaya Abdul-wahab Yafisge Sa Da Sauri "Ai Wallahi Baka Isa Ka Tsaida mu Ba Kasha Kunun In mundawo." Suka Fice Ana ta Dariya.

Abubakar Yamike Yana wanke Hannunsa, Dan Dae Sukam Innarmu Ta Sabar Musu Cin Abinci Da Hannun Dan Haka Ko kadan Basa Jin Dadin Ci Da Cokali Yana Mai Cewa, "Innarmu Nifa Nafara Zargin Rakiyar Nan Ya Abdul ne Za'ayi wa Kawai Dai Ya Layance Mana ne."

"Fita Batunsa Ai Tuni Na hango Jirginsa Kawai Na Zura Masa Idone Inga Iya Gudun Ruwansa."

"ALLAH Yahadashi Da Tagari, Bari Ni inkoma Shagonnan Akwai Kayan Da Zan Kamallah Masu Su Zasu Zo Su Karba Dama Nadawo In Dan Watsa Ruwane." Innarmu Tace, "ALLAH bada Sa'a, Aci Gaba Da tsare Gaskiya Dan Autana Banda hadaMa Azo Ancinye Kuddin Mutane Kuma Dunkunan Su Yamaka Yawa baka Gama Na Wasu Ba, Ka karbi Kudin Na Wasun. Saba Alkawali Ba Dadi." "Innarmu Ai in Nayi Haka Tamkar Cin Amana ne Ga Tarbiyar Da Kika Bamu. Duk Abinda Zanyi Nakan Yi Iya Abunda Nasan Zan iya Kuma Baza'a Ga Rashin Gaskiya ta ba. Shiyyyasa Ma Tun Wata Yanada Kwana Ashirin Nadaena Karbar Dinki Dan Ma Wannan Karon Abubuwan Sunzo Mutane Ba Kudi Da Ai Tun Goma Zan Rufe Tau Amma Saboda Rashin Kudi A Hannun Jama'a Wasun Sai Yanzu Ma Suke Samu Suna Kawowa."

"Rashin Kudi Kam A kasarnan Ai Yazama Jiki Saidai Muyi Ta Adu'a."

"Shine Kawai Fa Abinyi." Abubakar Yafadi Hakan Yana Kokarin Fita Daga Gidan Kafin Kuma Yadawo Yana Cewa "Yawwa, Namanta Innarmu Nagama Dinkunan Maman Walida (Auntynsu Aisha Suke Cewa Haka Dan Diyar ta Biyu Hakane Sunanta) Harma Daxun Naje Tasha Na Tura Mata Abubuwa ne Sukamin Yawa Bansamu Na Kirata ba Inji Ko Sakon Yazo." "Eh Sakon Yazo, Dan Takira Ni Dazun Tacemin Ma Ukku Ga Sallah Zasu Zo Dan Za'ayi Bukin Wata Abokiyar Karatunta Da Sukayi Makaranta Atare."

"Eyyah Tau ALLAH Yakaimu Lokacin, Ni Naje Innarmu."

"ALLAH bada Sa'a Auta Yakuma Bada Halal."

Yafice Yana Cewa 'Allahumma Ameen Innarmu. ALLAH Barmana Ke."

Tau Su Abdul-wahab Fa Iyayen Soyyaya? Bari Muji!👂

*******

Tunda Suka Fita Yusuf Sai Tsokanarsa Yake "Mutumina Khaleesat Ta Tafi Da Zuciyarka Da Yawa Fa? Ko Ni Da muka Jima Da Fa'iza Bamu Kaiku Sharbar Soyyaya Ba." Abdul-wahab yacije lebensa Nakasa Yana Cewa, "Naku Wasa ne." Yusuf Yakama Haba Kamar Mace, Cikin Mugun Mamaki Yace, "ALLAH Mutumena?" "Sosaima ko Ku Me Ma Kuka Sani A Son?" Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Kokarin Danne Dariyar Da Tazo Masa. "Aikuwa Dae. Tau ALLAH Samu A Danshin KU." Yusuf Yafadi Hakan Yana Fanshe Mamakin Da yakeji Na Abokin Nasa.

"Ameen" Abdul-wahab Yafadi Hakan Batareda Yabawa Maganar muhimmanci ba.

Yusuf Yace, "Dama Fa Naji Ance KU Ustaxzanann Baku Iya Son A...." "Kaga Mal Nidae Karka Cikani Da Tawilinka Da baya Karewa, Ina Zamu Fara Zuwa? Kasiyowa Fa'izar Mayafin Da Takalmin Da Kace?" "Nope Bansiya Ba Gaskiya, Yau Banyi Aiki Sosai ba Wallahi, Kasan Azumin Daren Sallah Sannan Gashi Kuma Umma Tayi Ta Aikena Cefane Sai Nadawo Tace Tamanta Ba'a Siyo Wannan Ba Ga Zubaida Uwar Iyayi Harda Zuga Umma Inbasu Kudi Zasuyi Zobo." "Kajika Tau Da can Wazai Musu Inba Kai ba. Muje Kasuwar, Akwai Yan Kudi Hannuna Inkuma Basu Ishemu ba Na Sato Atm Din Abubakar Sai Mushiga Account dinsa Muyi Masa Ta'anati Kasan Wannan Watan Su Kakarsu ce Tasamun Kudi."
Gaba Dae Suka Farke Da Shewa Suna Cafkewa Irin Na Gayu Nan. Kafin Yusuf Yace, "Hooooo Abokina Kana Cinye wa Wallahi, Amma Naso Mu Fara Biyawa Muyi Aski."


"Mubar Askinnan Kawai Sai Mun Dawo Dan Nasan Yanzun Shagon T Boy Baya kalluwa Dan Taron Jama'a." "Oh Right Never Damuwa." Yusuf Yafadi Haka Suna Bushewa Da Dariya Dan Wannan Shine Turancinsu In Suna Jin Shakiyanci. Kaitsaye Kasuwar Kanawa Sukaje, Bayan Sun Gama Shan Wahla Da Gow slow Da Suka Iske Wurin. Damma Karshe Dae Dole Wuri Suka Samu Sukayi Parking Din Kk Napep Dinsu, Suka Taka Da kafafunsu Saboda Cincinrodon Al'Umma Wani Kan Wani Mussamman Ma dae Yan Mata Da Ayanzu Ake Fitowa Karasa Siyayyar Da Ba'a Samu Anyi Ba. Su Abdul-wahab Suka Shiga Jerin Mutane Domin Siyayya Yayinda Yasuf Ya Darje Yazabawa Fa'izarsa Takalmi Da jakkarsu Tareda Sarka Da Yan Kune Harma Da Mayafi Masu Dan Karen Kyau. Lamarin Da Yabawa Abdul-wahab Sha'awa Shima Yashiga Tsintar Tasa Sahibar Kayan Da yake Ganin Sun Dace Da'ita Kai Ba Ita Kadai Ba Harda Innarmu Tasamu Nata Rabon Suma Sukayi Sayi Boxes Da Singilet Dakuma Takalmi Anan Kam Harda Abubakar Aka Siyawa Dan Kudin Nasu Basu Ishesu Ba Dan Haka Dole Dae Saida Suka Shiga Acc Din Abubakar din Sai Dai Basu Diba Da Yawa ba. Dan ma Sai Da Aka Zo Siyen Boxes Dinne Suka Bada Atm Aka Cire A Account din Abubakar. Abubakar Dae Na Dinki Sai Ganin Yayi Yan Banki Sun Masa Alart Na Cirar Kudi Da Akayi Account Dinsa, Da Yaduba Sai Bai Damuba Dan Yasan Ya Abdul-wahab ne. Kuma Shida Abinsa Duk Na Abdul-wahab ne. Acikinsu Babu Mai Yiwa Wani Iyaka Da Abin Hannunsa Dan Komai Nasu A hade Yake. Wannan ma Kuma Yana Daga Cikin Tarbiyar Da Innarmu Tarenesu Da Ita. (Uwa Tagari Itake Samarda Al'Umma Tagari. Dan Haka Kalubale Garemu Iyaye Mata🙏)

**********

Karfe Daya Nadare Suka Baro Kasuwar Kanawa, Inda Suna Kan Hanya Muhawara Ta Barke. Yusuf Yace Gurin Sahibar sa Za'a Fara Zuwa Abdul-wahab Yaja Tunga Kan Shima Gurin Tasa Za'a Fara Zuwa.

Karshe Dae Dole Yusuf Yayi Nasara, Bayan Sun Tsaya Sun Kalli Uzurin Shi Yusuf Din Cewa Iyayen Fa'izarsa Suna da Tsanani Ko Yanzun Ma Babu Dole Abarta Tafito Sai ma Dai Taci Albarkacin Yau Take Daren Sallah. Dan Tuni Sarkin Musulmi Yayi Sanarwar Anga Wata Insha'allah Gobe Daya Ga Watan Shawall. Da Zuwan Su Da ganawa Da Fa'izar Bai Wuce Minty Ashirin Ba Suka Mata Sallama Bayan Taciko Musu Leda Da Soyen Nama Miyar Sallah Da Kunun Zaki. Suka Nufi Gidan Su Khaleesat Kira Daya Tadaga Dama Takagara Abdul-wahab Yakira tan Kai! Jima Nakeyi Kamar Nayi Tsuntsuwa Inje Gareshi Jiya daene Bamu Hadu ba, Amma Sai Nake Ji Kamar Munyi Wani Lokaci Mai Tsawo Bamu Ga Juna ba. "ALLAH Yasani Abdul-wahab Yatafi Da Zuciyata." Bayan Na Ajiye Wayar Momy Dake Gaban katuwar Roba Tana Motsa kullun Wake Sai Hamma takeyi, Tacemin "Abdul din Yaxo ne?" Nadubeta Ina Murmushi Nace, "Eh Yazo, Momy Duk Naga Kamar Kin Gaji. Nace Maki Momy Ai Shinkafa Da Miya Itace Ba Wahla Miyarmu Kawai Zamuyi Da safe Shinkafarmu Kawai Zamuyi Kince A'a Ke Sai kinyi Wani Abincin Yan Garinku Na Al'adarku Gashi Ya......"

Momy Ta Rarumo Takalmi Tana Jefata Dashi Tana Cewa, "Gidanku! Abincin Al'adarmu Yake Da Wahlar? Kawai Dai Ke Dan Baki Saba Dashi Bane Bari Nayi Abincin Kici Kiji Bazaki Kara Son Wani In Ba Shi ba ja'ira. Ko Dadynku Haka mukai Dashi Amma Yanzu Shi da Kansa Yabugo Waya Ayimasa Irin Abincin Garinmu Gobe Da Sunfito Sallar Idi Zai kamo Hanya."
Na Nufi Daki Bayan Nasamu Nasarar Kaucewa Takalminda Momy tajefo Ni Dashi Ina Fadin, "Hum'um ALLAH sa Zan Iya Cin Wanna Abun Da Haryanzun Nakasa Gane Ya'ake Hadasa." Nadubi Kaina Sama Da Kasa! Siket Da Riga ne Yan Kanty Nake Sanye Dasu, Sunbi Jikina Sunyi Das Sai Kaina Da Yasha Kitson Sallah, Na Dora Hullar Yorubawa Akaina Najanyo Hijabi Nasa Dan Na kula Abdul Dina Nason Yaga Nasa Hijab. Wit Leaps Nadan Murzawa Labbana Suka Kara Sheki Kafin Nadan Murza Hoda Afuskata Nadan Mutsutsuka Turare Daga Can Barandarmu Naji Momy Nacewa, "Ai kina Wannan Feleken Harsu Tafi."

"Momy Gani Fitowa."
Nafadi Hakan Dae dae Sanda Nake Bakin Kofar Dakinmu Ina Zura Takalmi Nawuce Momy Tana Cewa, "Karfa Ki Dade Khaleesat Kizo Nayi Abinnan Gabanki Inkika Iya Zaimiki Anfani Nan Gaba." Nafita Inacewa, "Tau Momy." Araina Kuwa Nace "Zan Iya Indinga Yiwa Abdull Dina." Nakasa Boye Fara'ar Fuskata Sanda Hasken Farin Gluf Din Bakin Garkar(Kofar) Gidanmu Yahasko min Fuskar Abdul-wahab Dina Mai Cike Da Annuri Na'isa Gabansa Da Wannan Fara'ar Shima Dai Murmushi ne A Fuskar Tasa Yajima Yana Kallona Kafin Ya Sauke Ajiyar Zuciya Yace, "Baby Na Sannu Da Gida."
Na Zunburi Baki Kamar Karamar Yarinya Tareda Cewa, "Nifa Fushi Nake, Saboda ALLAH Tun Karfe Tara Nake Dubin Kazo Amma Sai Yanzu Harna Fidda Tsamani." "Ayimin Hakuri Gimbiyata Nima din Badan Naso Haka Bane Kasuwar Kanawa Mukaje Kuma Kinsan Yau Garin Da Kwai Cinkoso." Kafin Nace Wani Abu Sai Ga Yusuf Yafito Daga Cikin Kk Napep Yakaraso Garemu Yana Goge Bakinsa Da Kyalle Yana Cewa, "Sahibar mu Sannu Da Gida. Ayi Hakuri Munyi Laifi ko?" Nace "Ba Wanin Nan Ai Duk Bakinku Daya."


"Tuba Muke Ni Nayi Laifin Dan Ni Na janye Maki Mutumin nace Sai Nasiyowa Fa'iza Ta Kayan Kwalliya. Nasan Ai Kuma baxaku So Nima Na Rasa Tawa Soyyayar ba Tunda Kan Sharafinta kuke Ko?" Nadan Harareshi Cikin Sigar Wasa, "Tau Ni Mezance? Tunda Duk Ka lauyeni, Ai Wallahi Kaikam matarka ko, Tashiga Ukku Da Dadin Baki." Duk muka Kyalkyale Dariya Yusuf Yace, "Ke! Ni Duk Dadin Bakina Ai bankai Gwarzon Naki ba Daxun Fa Cewa Yayi soyyayar mu Ba....." Abdul-wahab Yayi Saurin Dafe Masa Baki Yana Cewa, "Aku Sarkin Magana Kaidai Ba Damar Ayi Sirri Da Kai?" Duk muna Dariya Nace, "Yanzun Habibi Na Niza Kayi wa Sirri?"

"Ah Tau Nima dae Shi Nagani." Yusuf Yafadi Hakan Yana Yarfar da Hannayensa.

Abdul-wahab Yahararesa Kafin Yaturesa "Dan ALLAH Malam Koma Cikin Kk Napep Dinka Duk Kabi Kacika mu Da Surutu Ka hanani Inga Na Da Tawa babyn Bayan Kai Da Mukaje Nabaka Guri." Muna Ci Gaba da Dariyar Nishadi Yusuf Yace, "Kinji Ba?" Abdul-wahab Yayi Saurin Juyowa Yana Kallon na Tareda Dafe Bakin sa Yace, "Au..." Bi Ma'ana Dae Yayi Azarbabi Da Yawa Wanda Yawuce Ka'idarsa. Banda Dariya ba Abunda Muke. Bayan mun Dan Natsa Yusuf Na kk Napep Yana latse-latse Acikin Wayarsa Ga Alama Kuma Chat Yake Dan Sai Murmushi Yakeyi, Mukuwa Muna Nan Sai Batu Muke Wanda Mafi Yawancinsa Nice Ke Jan Ragamar Labarin Dan Abdul Dina Ba gwanin Surutu Dinnan bane Sosai Mussamman ma Dae in muna Tare. Hannun na Yakallah Wanda Yayi Shar Da Zanen Fulawa, Yace, "Babyna Kinyi Kyau Kamar Nasaceki Na Gudu Dake Wannan Lallen Jinake Kamar Incire Hannayen Inje Da Abuna Gida Duk Motsin da Zanyi Sai Na kallesu." "Habibi Mekake Sauri Inda Rai Da Lafiya Ai Watarana Nidin Takace Sai Yanda Kaso Zakayi Dani." Yayi Murmushi, "Are you sure?" Yafada Cikin Wata Irin Murya Mai Cike Da mayen So. Nagirgiza Kai ma'ana Dae "Yes." Yace, "Kenan Dai Zaki Dinga min Irin Wannan Lallen?"

"Sosaima ko Sai Wanda Kazaba Kake So Habibi Na."

"Wow! Gaskiya Nacika Da Zumudin Ganin Wannan Lokacin." Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Cikeda Wani Irin Shaukin So!

"Oh Afuwan Bari Dan ALLAH Nakawo Maku Ruwa Tun Daxu Na Saka Ku Gaba Da Surutu." "Kinga Ni kuwa Surutunan Yafiyemin Duk Wani Abu Da Zaki Kawomin.". "Duk-da Haka Babyna Idan Ga Ruwan Ai Sai Surutun Yafi Armashi Ko?" Nakarasa Maganar Cikin Zolaya. Abdul-wahab Yayi Dariya Yana Cewa, "Kinganki ko? Da Aikin Jarida Kawai Kika Karanta, Saboda na Tabbata Za'ayi Hazikar Yar Jarida Kuma Yar Baiwa." Cikin Farinciki Nace, "ALLAH ko?" "Sosaima." Yafadi Hakan Yana Mai Girgiza Kansa Dan Bani Tabbaci." Najuya Inafadin "Kaga, Infa ba Zuwa Nayi Ba Bazamu Taba Gajiya Da....." Yayi Saurin Cewa,"Kinga karbi Kayanan Kiwuce Dasu Ciki." Najuyo Nakarbi Ledar Ina Fadin, "ALLAH sa Ba Wahlar Da kanka Kayi ba dae Dan Ni dai Gaskiya Bai....."

"Shiiiiiii!" Nayi Shiru Saboda Hakan Din Da Yayi min Kafin Yadora Da Cewa, "Dan Miji Yayi wa Matarsa Abunda Yake Ganin Yadece Shikenan Kuma Sai Yakoma Wahla?" Kafin Yagirgiza Kai Yace, "Abunda Kawai Zakimin Ki Burgeni Ki Karba Da Hannun Biyu Sa'anan Kiyimin Adu'ar ALLAH Ya sanyawa Nemana Albarka Ta Yanda Zanci Gaba Da Dawainiyah Da Innarmu Dakuma KE Harma Da 'Yan Yaramu Da Zamu Samu Nan Gaba Insha'allah." Maganarsa Takarshe Tabani Kunya Dan Haka Sai Narufe Fuskata Da Hijabi Na Nufi Cikin Gida Dan Kawo Musu Abin Tabawa.
.


Tau Raedars Kafin Khaleesat Tadawo Bari Nima Na Dan Sarara Insamu Abin Kaiwa Baka.😜

Zansake Dawo Maku A Chapter Ta Tagaba. Labarin Dae Haryanzun Ba'a Soma Ba, Batutuwa Na Gaba.
🚶🚶🚶🚶🚶🚶
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: 💞 SONEEE....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 2 · 0% Book details