← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 37 OF 40

Chapter.....38

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Duk Wannan Abun da ke Faruwa Dr Jabir Yana Sane Yana da Labari, Saboda Kullum Muna Waya Dashi, Daganan Nagaya Masa Cewa, Ga Khaleesat Nakawo Asibiti Harsun Gana da Su Abdul-wahab Meye Plan Nagaba? Yacemin Yanzu In Zauna da Khaleesat Ita ce Zatamin Bayani Sun Riga da Sun Tsara Komai.

Daganan dai Na Keɓe da Khaleesat ɗin Nake Gayama ta Yanda Mukayi Da Dr. Jabir Tace, "Tabbas Hakane, Plan Na Gaba Yanzun Shine Kamar Yadda Suka Tsara Zata Koma Gida Ta Gayamasu Gaskiya Tasan Izuwa Yanzun Iyayen ta Sunyi NADAMA Kuma Tabbas Zasu Bata da Ga Wanda Takeso. Najima Cikin Nazari Kafin Nace Mata "Ba Haka Za'ayi ba." A Wannan Lokacin Taɗago Kanta Take Kallona da Alamar Buƙatar Ƙarin Bayani daga Gareni Nikuma na Musƙuta Cikin Murmushi Kafin Nace, "Yanda Za'ayi Shine Nasan Kuna da Family Kuma Baza'a Rasa Wanda Iyayen ki Suke Ganin Girma da Mutumci su ba Dan Haka Su Zamu Sama Sai Muje Tare Dasu dan Ƙara Wayar wa Da Su Iyayen Naki Kai Harma da Na Abdul-wahab ɗin." Cikin Murmushi Tacemin, "Tabbas Hakane, Tau Amma Tayaya? Haɗasu Ba Abune Mai Sauki Ba, Bayaga Haka Nida Zan Bayyana A Matsayin FATALWA Garesu Tayaya Kake Ganin Aikin Zaiyu Gareni?"

Nima dai Murmushin Nayi Nace, "Kibar Komai A Hannuna Abunda Nake Buƙata Kawai A Gurinki Yanzun Zaki Sanar dani Inda Dangin Naku Suke Sai Inje In Samu Su." Tazaro Ido "Wallahi duk Suna da Nisa Familyn Dady Suna Adamawa Momy kuwa Kogi."

"Badamuwa Zanje, Amma Tunda Suna da Nisa Zanje ga Na Dadynki."

Khaleesat Ta Kalleni Cikin Mamakin Irin Wannan Sadaukar wa Da Mukeyi Akan ta Nida ABOKINA Nace, "Karki Damu YIWA KAINE Hakanan Dr Jabir Yana da Wata Irin Daraja Gareni Ina Iyayin Komai domin Farincikinsa Kamar Yadda Nake da Yaƙinin Shima Zai Iya." Khaleesat tasauke Ajiyar Zuciya Tareda Cewa, "Hakane, ALLAH Yabar So da Yarda. Nima kuma Ina Godiya gareku ALLAH yabiya ku da gidan Aljannah bisaga Wannan Taimakon Naku Gareni."

Naɗan Kurɓa Lemun dake Gabana Kafin Nace, "Allahumma ameen Khaleesat Kema Kuma ALLAH Yanuna Burin Nan Naki Yacika."

Cikin ɗan Murmushi da Kuma Kinya Tace, "Ameen."

Nace, "Yanzun Saiki Bani Cikakken Adereshi Inda Familyn Dady Yake Hakanan Ki Bani Number Wani Wanda Zan Dinga Waya Dashi Har In Isa Wurin Nasu."

Tabani Number Baba Tanimu Tareda Gayamin Shine Babban Wa a Familyn Nasu Dady.

Daganan Nikuma Nasa Rana Naje Har Adamawa Bayan Na Kimtsa A hotel ɗinda Nasauka.

Bayan An Sauko daga Masallacin Jumu'a. Na Nufi Family House ɗin Nasu Dady da Taimakon Wayar da Mukeyi da Baba Tanimu.

Nasamu Tarba Mai Kyau Agurin Sa Daganan Kuma Nakoro Masa Bayanin Abinda Ke Tafe Dani Yayi Mamaki Sosai Yayinda Nikuma Naduƙufa Fahimtar dashi Cikin Taimakon ALLAH Yafahimci ni daganan Kuma Yasa dani da Sauran Dattijan Gidan Suma Nayi Masu Bagani Kamar Yadda Nayi Masa daganan Muka Aje Ranar da Zasu Zo Bayan Sun Kira Dady Sun Samu Tabbacin Ranar da Yake Gida Batareda Sun Nuna Masa Cewar Zasu zo Ba. Bayan Nadawo Nakira Khaleesat Nasanar Mata da Yanda Akayi Kasancewar Dama Nagayama Su Innarmu Suje da Ita Can Gida Har'izuwa Sanda Abubuwan da Nake Tsarawa su Dai-dai ta In Zaku Tuna Innarmu Munyi daku Haka Ranar da Aka Sallame ku Ko?" Yaƙare Maganar da Kallon Sashen Da Innarmu Take.

Cikin Sanyin Jiki Innarmu Tagirgiza Kai Tareda Cewa, "Hakane."

Shikuwa Dr. Faisal Yaɗora, "Bayan Su Baba Tanimu Sun IsoYake Sanar dani Gasu Sun Sauka Tasha dama Kuma Tun Suna Kan Hanya Muke Waya Dasu. Dan Haka Naɗauki Motata Naje Naɗauko Su Bayan Mun'ajiye Su Baba Bukar Nan Sai Muka Wuce da Baba Tanimu Kan Cewar Zamuje ne Muzo da Khaleesat da Kuma Iyayen Abdul-wahab Harma dashi Kanshi Abdul-wahab ɗin." Yaɗan Numfasa Yana Mai Nazarta Foskokin Mazauna Falon Kafin Yaɗora Da Cewa, "Kunji duk Yanda Abubuwa Suka Kasance Idan Har Munyi Maku Ba dai-dai ba Dan Girman ALLAH Amadadin Abokina Ina Mai Baku Haƙuri, Mudai Munyi Abunda Muke Ganin Da Khaleesat Taje Yawon Duniya Tau Gara Mu Ɓullo ta Wannan Hanyar tunda Wancan Ta zama dan Yiwa Su Dady Bayani Bai zama Dole Su Fahimta ba. Bugu da Ƙari dai MUTUWAR Khaleesat ɗin dai Yanuna Maku Abinda Zai Faru dan Gashi Shi Abdul-wahab Yasamu taɓin Hankali Sannan Ku Kanku Kunshiga Tashin Hankalin da Ba Sai An Tsaya Yin Bayani Ba. Dan Haka kuyi Tunani Idan Wannan Mutuwar ta Kasance Ta Ƙarya Tasa Irin Haka Yafaru Tau Sanda Kuka Dage Kan Aura Mata Wanda Ku kuke Muradi Koda Bata Gudu Ba Tau Intaje da Baƙinciki Zata Zauna Gidansa In Kuma Hakan Baiyuba Wataƙil Suci Gaba da Mu'amala da Junan Su Ita da Abdul-wahab Tunda Suna Son Juna, da Dai Sauran Wasu Dalilai Daban-daban da Ban Lissafo ba Wayanda Wasun Tunanina da Naku Yasani Wasun Kuwa Sai Sun Faru Sannan Zamu Sani Adawo Ana Tunanin da Ba'ayi Ba da Hakan Bazata Faruba. Dan Haka A Shawarce Ina......" Baba Tanimu Yaɗaga wa Dr. Faisal Hannu Kafin Yasoma Cewa, "Yi Shirunka Ko A Iya Haka Kuma Ai Kariga da Kabada Bayanin da duk Mai Hankali Zai Iya Ganewa. Kai Kuma Mustapha." Yajuyo Gurin Dady Da Yaketa Sharɓa Zufa Kamar Ba Lokacin Sanyi ba. Baba Tanimu Yacigaba da Cewa, "Yanzun Hukunci Yarage Gareka Duk-da Nayi Mamaki da Samun Ka da Wannan Ra'ayi Batareda Mun Sani Ba Wai dan Mutum Baya da KUƊI Bai Isa Ya'auri ɗiyarka ba Dan Bayada Kuɗin da Zai Jiyarda ita daɗi. Shin Ko Kasan Da Auren Wasu Masu Kuɗin gara Auren Talaka Wanda Yake da Kyakykyawar Zuciya. Nawa ne Suka Aurin Mai Kuɗin Amma Sai ka ga Matar Wani Talakan Tafi ta Mai Kuɗin Wadata Saboda Hali Ba ɗaya ba. Yakamata Kagane Bawai Kuɗin Bane A'a daga HALINE Koda Yana da Kuɗɗin indai Baida Hali Mai Kyau tau Bazai Wadatar da Ita Ba Hakanan koda Talaka Ne Indai Yana da Hali Mai Kyau Sai Kaga Yarka Ta Samu Kula Mai Kyau Hakanan Tana Yuwa Kuma Asamu Mai Kuɗin Kuma A Sameshi da Hali Mai Kyau Na Kula da Iyali dan Haka Ba Yanda Bata Iya Kasancewa. Amma dai Abinda yafi Kamata Muyi La'akari dashi Shine Shin Wanda Zan Ba Yata Yana da Sana'ar yi? Yana da Hali Mai Kyau? Yana da Addini? Idan Kasamu Wayyanan Sun Wadatar Sai Ka Haƙura da Sauran dan Ba Wanda Zaka Sama Ɗari Bisa Ɗari. Bayaga haka Jikina Yana Bani Wannan Ba Tunanin NAMIJI Bane. kawai Kabi Shawarar Matarka ne Kurum.

Gashi Mu ko ɗai Rana Baka Taɓa Sanar da Mu Wannan Lamarin ba Ko dan Baka ɗauke Mu Yanda Muka ɗauke bane Saboda Kana ganin Kaine Kayi Boko Ka Goge Ka Waye, Muko Bamu San Komai ba Inba Noma da Kiwo ba Sai Kuma Zama Massalaci Ko?" Dady Yayi Maza Yagirgiza Kansa, "Wallahi Bahaka Bane Yaya Ku Gafarceni Dan ALLAH Kawai dai Ni Banyi Tunanin Wannan Matsalar Girman ta Yakai Haka Bane Shiyyasa Ban Faɗa Maku Ba."

"Tau Ai Gashi Takaika ga Zubda Hawaye Ko?" Baba Tanko Yafada Yana Mai Kallon Dady.

Muje Zuwa Readers Man Kaina Na Hayaƙi Wallahi 😫

Tareda Alkalamin

FA'IK. ✍🏼
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 37 · 0% Book details