Chapter.....9
So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Mallakar 👇
Fa'IK ✍️
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.
FADAKARWA.
Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.
Bissmillahi Rahmanin Raheem
Haka Yayi Ta Nanata Kalmar Har Sanda Yasami Nasarar Dai-daita Bugun Zuciyarsa Kafin Yashiga Shawarar Shin Yaƙarasa Inda Suke Ko Ya Komawarsa Gida Kawai?
"Gara Dae Kaje Karkayi Saurin Yanke Hukunci." Abunda Wani Ɓangare Na Zuciyarsa Kenan Ke Sanar Masa. Dan Haka Sai Ya Tunkari Motar Kai Tsaye Yana Musu Sallama Alhaji Saminu Na Masa Wani Malalacin Kallo Ya'amsa Sallamar Tasa Dan Dukda Bai Taɓa Ganin Abdul-Wahab Ɗin Ba Jikinshi Yabashi Cewa Wannan Shine. Hirarmu Muke Cikin Kwanciyar Hankali Ina Ta Dariya Saboda Labarin Da Alhaji Saminu Ke Bani.
Shine Fa Abinda Abdul-Wahab Yagani Yafita Hayyacinsa. Ba Yabo Ba Fallasa Naɗago Kaina Ina Kallon Abdul-Wahab Da Yaja Gefe Yatsaya Yana Jiran Infito Nalumshe Idanuna Kafin Nasake Buɗesu Ina Kallon Alhaji Saminu Saboda Nasan Yana Son Wannan Salon Kafin Na Motsa Laɓɓana Cewar, "Baby Bari Naje Naji Da Wacce Yazo?"
"Shine Abdul-Wahab Ko?" Alhaji Saminu Ya Tambaya Cikin Nuna Abdul-Wahab Ɗin Ba Kowa Bane.
Nataɓe Baki Gamida Cewa, "Shine."
Shima Bakin Yataɓe Yace, "Ina Jiranki Ina Fatar dae Bazaki Daɗe Ba ko Swetina?" Yaƙarasa Maganar Cikin Wani Irin Salo Na Jan Hankali Nace, "Sha Kurumin Ka Yanzun Nan Zandawo Ina So Ne Na Rabu Da Kwallon Mangwaro In Huta Da Ƙuda." Ina Gama Faɗar Hakan Na Ɓalle Murfin Motar Na Fito Na nufi Inda Abdul-Wahab Yake Tsaye Yana Jirana. Banda Kallona Ba Abinda Abdul-wahab Yakeyi Nace, "Sannu da Zuwa."
Bai Amsa Sannun Da Nakeyimasa Ba Face Cewar Da Yayi, "Khaleesat Bai kamata Kina Sauraren Irin Wayyancan Mutanen Ba Mayaudara ne Kuma...... " Naɗaga Masa Hannu "Muyi Maganar Da Takawo Ka Dan Wannan Bai Shafeka Ba." Cikin mugun Mamaki Abdul-wahab Yace, "Mekike Nufi Khaleesat Nifa Ban ma Gane Kanki Ba Zuwa Nayi Fa Muji Yanda Zamu Ɓullowa Al'amarin mu A Yanzun Nashirya Aurenki Koda Su Innarmu Basu Amince Ba Dan.... " "Daga Baya Kenan Wannan Ba Khaleesat Ɗinda Ka Sani Bace, Nima kuma A yanzun Nagano Kuskuren da Natashi Afkawa Sai dai Ina Godiya Ga ALLAH da yaganar dani Tun Wuri."
"Bangane mekike Nufi Ba Khaleesat?" Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Cikin Wani birkicewar Tunani. Nikam Ko Ajikina Nace, "Abin da Nake Nufi A Yanzun Bana Sonka Nakuma Gano Wancan Yafi Dacewa dani Dan Haka Ina Mai Sanar Dakai daga Yau Bani Ba kai! Ina Fatar Yanzun Kagane Menake Nufi?" Jikin Abdul-wahab Yaɗau Kyarma Idanunsa Suka Kaɗa Sukai Jazir Kamar Gauta
"Nagane ALLAH Yahaɗa Kowa Da Rabon Sa. " Abinda Kawae Abdul-wahab Ya Iya Cewa. Tau Mai Ma Zaice? Koda Yana Da Abin Cewar Bayada Dama Dan Kuwa kwalkwalwarsa Ta Kulle Tamau! Khaleesat Ta Shayarda Shi Mugun Mamaki Bai Taɓa Zaton Khaleesat Ɗinsa Da Yake Wuni da Kwana Da Tunanin Ƙaunarta Zata Iya Yi Masa Hakaba.
"Ameen." Kawae Nace Kafin Najuya Na Koma Cikin Motar Alhaji Saminu Muka Ci Gaba da Hirarmu Cikin Nishadi Harda Kyalkylewa Da Dariya.
Ina Kallon Abdul-wahab Ta Gilashin Motar Sanda Yazo Wucewa Sai Wani Tangaɗi Yake Na Kalli Alhaji Saminu Shima Kallo Na Yayi Dan Haka Sai Na Taɓe Baki Kawae.
Shima Alhaji Saminu Hakan Yayi Cikin Jin Daɗin Yadda yaga Nayima Abdul-wahab Wulakanci Kafin Yazakuɗa Cikin Karsashi Yace, "Baby Kimin Wani promise Mana?"
"Uhummm." Nafaɗi Hakan Ina Mai Kallonsa Da Wani Irin Salo Mai Tafiyar da Zuciyar Masoyi.
Abunda Yake ƙara Ƙaunata Kenan Acikin Zuciyarsa Yace, "Ke Babbar Yarinya ce Bai Kamata kina Kula Kowane Irin Kilaki ba Musamman Irin Wayyanan Ƙananun Yaran ma."
"Yanzun Kuma Andaina Dama Ai Wannnan Yafarune Kafin In Haɗu Da Alhaji Saminu Ai ko?" Naƙarasa Maganar Ina Kashe Masa Ido Irin Na Yan Bariki Ɗinnan Yalumshe Ido Alamun Dae Saƙon Nawa Yakai Harcikin Zuciyar sa Kafin Yace, "Hakane Tawan."
Wai Abdul-wahab Fa?
Ikon ALLAH Ne Kawai Yakaishi Gida Domin dai Inba Da Muryar Khaleesat Ba'abinda Ke Amsa Kuwa Acikin Kwakwalwar Kansa.
Yaci Sa'a Babu kowa A tsakar Gidan Daga Innarmu har Abubakar ɗin ba wanda Yadawo yazube kan Katifarsu Yana mai fitar da Wani Irin Wahlallen Numfashi "DAN HAKA DAGA YAU INA MAI SANAR DA KAI BANIIII BAKAIII!!!!! "
Muryar Dake Ta maimaita kanta Kenan Acikin kunnawa Abdul-wahab Hawaye Wasu na korar Wasu A Fuskarsa Cikin Rawar Murya Yace,"Babu Shakka Haƙƙenki Ne Ki Bibiyata Innarmu Babu Shakka Nayi Wasa da Rayuwata Kaicona!!!" Kafin Yarushe Da Wani Irin Gurshuƙeƙen Kuka. Kamar Wani Ɗan Ƙaramin Yaro Ko Wata Macce.
Yinin Ranar Haka Yayishi Sukuku Kamar Wanda Bashi da Lakka! Innarmu dai na kule Saidai Batace Komai ba Hakama Abubakar.
Yayin Da Acikin Zuciyar Abdul-wahab Yake ta Tufka da warwarar Sabuwar Rayuwar Da Zai Fara Na Mantawa Da Khaleesat Da Duk Wani Abu da yadanganceta Yamaida Hankalinsa kan Karatunsa Kamar Yadda Innarmu taso Yayi tunda Farko, Tau Saidai Yayi Fargar Jaje Dandai Yamaida Hankali Ga Yan tsirarun Jarrabawa Da Suka Rage Masa Amma Suka Kasa Hanasa Faɗuwa dan dai Sakamako Na fitowa Yafito Da Wani Irin Tashin Hankali Ga Abdul-wahab ga ma duk Wani Masoyinsa Dan dae Yazube Warwars Da Tarin Carry over Wayanda Suka Sababba Akayi Withdrawalce Dinsa A makaranta. Watau Dai An koreshi A Skull. Saboda Jp Ɗinsa Yagaza Tsallake Yanda Ake Bukata.
Tashin Hankali Wanda Ba'a Sama Ka Rana. Duk yanda zan misalta Tashin Hankali Da Tsananin Damuwar Da Abdul-wahab yake Ciki Bazai Wadatar Ka gane ba mai karatu. Shikaɗaine Yasan Ya yakeji Saida Yagayama Su Innarmu da Abubakar Sannan Suma Sukabi Yarima Shan Kiɗa Wajan tayashi Shiga Damuwa Mussaman ma dai Innarmu Da Ta kwallafa Ranta Ga Karatun Kuma Take Fatar Suyi Nasara Akansa Tau Ga Abinda Abdul-wahab Yayi kuma Shi Yace SONE SILAR KOMAI!
kundai Ji Mafari da Tushen Lamarin ko da kuma Asalin Wayyannan Taurarin ko?
Tau muje Zuwa!!!
MUN DAWO LABARIN.
Innarmu Ta Sauke Wata Kakkarfar Ajiyar Zuciya Kafin Ta Soma Da Cewa, "Yanzun dai ai kagane Abinda Nake maku Nuni ko? Ka kuma gane abinda Yasa Nake Tsaye tsayin Daka Dan Rayuwarku Ta inganta ko? Kuma Yanzun Katabbatarda Babu Wata Rayuwar da Zata inganta sai da Ilmi? Yanzun Kun Fahimta da hakan Ko Sai Duniyar taci gaba da koya maku Darasinta?
Yakamata Kagane Abdul-wahab Ina yin Komai Domin ku ne ba wai Dan kaina ba. Danni Yanzu saidai nai Fatar gamawa da duniya Lafiya Amma Duk Kature Wannan Kawatsa min Ƙasa A Ido Gashinan Yanzun Wa gari Ya Waya?"
"Niya Innarmu. Innarmu Na'aikata Babban Kuskure Kuma Nayi Nadama Dan ALLAH Kiyafemin Ko Nasamu Naga Haske A Rayuwata." Abdul-wahab ke wannan Maganar Cikin Rawar Murya. Innarmu Tasoma Shafa Kansa itama Cikin Tata Rawar Muryar Tace, "Nayafe maka Kai Ku dukanku Nayafe Maku Ni Ban taɓa ƙullatarku ba Sai dai Nayi Hushi daku dan ku Gane Abinda Kukayi Badai Bane. Amma bawai dan Hakan Na Nufin Har A Raina Inajin Haushin ku bane. ALLAH yamaku Albarka.!!" Gabaki Ɗaya Suka Rumgume Innarmu Suna masu Sauke Ajiyar Zuciya Yayinda itama Innarmu ke cigaba da Shafar Kansu Cikeda Soyayyar Da Akasan kowace Uwa nada Akan 'ƴayanta.
Gefe Ɗaya Tana Mai Cigaba da nusar dasu Akan Su kula da Halin Rayuwa.
Innarmu dae Anhuce😅
********
Nacaɓa Ado Kamar wacce zataje gasar Kyau Sai kai da kawowa nake Daga Ɗakina Zuwa tsakar Gida Inata Zuba Kamshi Tareda Tauna Cimgam yana Kas! Kas! Inbanda kallona ba Abinda Momy keyi Hardai tagaji ta sa Baki Takirani Zuwa Ɗakinta.
Na'isa Ɗakin Nata Wayata A kunne Ina mai Dariya Ƙasa-Ƙasa Tareda Cewa, "Alhaji Lamarinka Azimunne, Nifa Tunɗazu Na Shirya Kai Kawai Nake Jira?..... ALLAH?..... Kai Amma ko danaji daɗi..... Ok Tau Sai Ka iso..... Nagodeeee. " wayannan Zantukkan Su nake tayi Kamar ba ina gaban Momy ba kuma ko Ajikina.
Abinda Nalura dashi Kuma Gabaɗai Jikin Momy Yayi Sanyi Da irin Wannan Sabon Hali da natsiro Dashi A yan Lukkutannan Tun Abun na bata Sha'awa Haryadawo Bata Tsoro
"Gidan Ubanwa Zakuje?"
Momy ke Wannan Tambayar Cikin tsawa Da Ɓacin Rai.
Na Zunburi Baki Cikin Shagwaba Gamida Cewa, "Momy Ba Fa Kowa bane nake waya dashi ba face Alhaji Saminu ku..... " "Eh Ai Nasani Shi Alhaji Saminu Ubanki ne? Wallahi Khaleesat ki kayayeni Da wannan sabon Iskanci dakika tsiro da Shi idan kika kaini maƙura Gamuwar mu dake bazata Kyau ba."
Haryanzun dae da Salon Shagwabar Nasakecewa, "Momy Bafa Komai ne ba Alhaji Saminu yace min Zaizo Zamuje....."
"Rufemin Baki Shasha Ba'inda Zakuje ni wannan Feleƙen Naku Yafara isata Bari Anjima Insa kati Zankira Mahaifin Naku Yaimaza yazo ayiwa Abun Tufkar Hanci."
Najuya Afusace ina Faɗin, "Ni Wallahi Momy Sai Naje Haka ka.... " Momy Tafisgoni Da Karfi "Khaleesat ina Magana kina Magana? Nashiga Ukku Ni Ɗiyar Alhaji Bola. Khaleesat Yaushe kika iya irin Wannan Rashin Kunya Haka?". Nidai Bance mata Uffan ba Kawae Nayi Shiru ne Ina Zumbure-zumbure. Abinda Nalura ya bala'in Ɗagawa Momy Hankali Dan Ba Ɗabi'ata Bace Wannnan.
Namike da Nufin komawa ta ɗakina Momy tasake Fisgoni Tana Huci Da Faɗin "Dawo Nan Ba inda Zakije Bani Wayar Nan. " Nace, "Momy Nifa ba fita zan ba Ɗa... "
"Nace Kibani Wayar ko? " Momy tafadi Hakan Cikin Tsawa tana mai mika Hannunta gareni Nufin Inbata Wayar. Ganin bazan bata ba yasa ta sanya Hannu Tafisge Wayar Kafin ta Zaunar dani Nan kusa Da Ita. Taci Gaba Da Juya Ƙullunta Da Zatayi Ƙosan Gobe Dashi. Hakanan Bakinta Baiyi Shiru Ba kan Canjin Da tagani Tareda ni Sai Faɗa take kamar zata Ari Baki Tayi Hausa Takoma Yarenta.
Wani Zagin Intamin Shi Sai Na Kunshe Baki Saboda Dariya. Dole Firar Danaso Fita Ranar Bata Yuwuba Saboda Momy Takasa Ta Tsare. Haka dae Alhaji Saminu Yayi ta jira da Aike Harya gaji Ya Tafi.
**********
Tau tunda Safe Momy Nagama Lazimi Ba Wanda Takira Sai Dady Dama can kuma shine Mutum Nafarko Dasuke fara waya duk Safiya ta ALLAH Mafi Yawa kuma Shine mai Kiranta dan Yaji Lafiyar Gida Tau Yaudae Takasa Hakurin Yakira Itace Takirashi Harma Yana Tambayarta Lafiya? Cikin Ɗacin Rai Tace Masa, "Ina Fa Lafiya Alhajin Nan Na Son Sauyawa Yarinyarnan Hali? Duk Tabi Ta Susuce A kanshi?" Mustapha Yanumfasa Dan Shi Duk Baiji Wata Matsala Anan Ba dan Haka Yakara tambayarta da Cewa "Kamar Yaya? Nifa Bangane Inda Zancen Naki Yadosa ba?"
"Alhaji Zancen Wayar Bazai Gamsar Ba Inaga kawai Ka Samu Lokaci Acikin Satinan Kashigo Inaga Abin Zaifi." Alhaji Mustapha Daga Can Inda yake Kishingiɗe Kan Gadonsa Ya musƙuta Kafin Yace, "Babu Damuwa Zanyi Ƙokari Inga Nazo ina Khaleesat ɗin Tana Lafiya?" Saida Momy Takyaɓe Baki Alamun Dae Tanajin Haushin Khaleesat ɗin tata kafin tace, "Tana Nan Lafiya lau. "
"Masha'allah Badai Wata Matsala ko?" dady ke Tambayar Momy Hakan.
Momy ta'amsa "Babu Bayan Wannan dana gayama."
"Tau Shikenan Zanyi Ƙoƙarin Inzo Ina Khaleesat ɗin In tana kusa Bata Wayar Muyi Magana. "
Momy Sai da Aka Harareni Kafin A mikamin Wayar Na'amsa Ina niyyar Miƙewa inbar Ɗakin Ta bugamin Tsawa "Dawo Nan Munafuka Ina Zakije?" Dole Bashiri Nadawo Na Zauna. daga can Dady Najinmu A Ransa yace 'Yawo Sarkin Rigima.".........
Masu Karatu Muje daku Shafi Na Gaba Domin jin yaxata Kaya Rigima dae tayi Ƙamari Tsakaninta da Yar lelenta Khaleesat.
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻
❤❤SONEEE ....💕💕
(Silar Komai.)