← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 35 OF 40

Chapter.....36

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Maimakon Inmiƙe ɗin Kamar Yadda Yabuƙata Sai Na Gyara Zamana Gamida Cewa, "Ai Bamu Gama Maganar ba Ko? Zaɓi Kabani In Bazan Iya Yanke Hukunci Yanzun ba Inje Har Inyi Shawara da Zuciyata." Naɗanyi Shiru Ina Mai Ci Gaba da Yawo Da Idanuna A Harabar da Muke Zaune Kafin Nadawo da Kallona Gareshi Shima ɗin Ni Yatsura Wa Mayun Idanun Sa Masu Matuƙar Kwarjini Wanda Kwarjinin Nasu Yataimaka Wajen Kasa Ci Gaba da Kallonsa Da Nayi Niyyar Yi Sai Kawai Na Ruzunar da Nawa Idon Ƙasa Gameda Cewa, "Shi Ruwan Kashe Gobara Ba'a Tsayawa La'akari da Kyaunsa Ko Akasinsa Kawai dai Amfani Za'ayi dashi dan Kashe Gobarar Dan Haka Na'amince daga Yau Zanfara Aiwatar da Nawa Shirin Duk Yanda Nayi Zan Ma Bayani."

"Da kyau Ta Abdul-wahab Ina Miki Fatar Nasara." Yafaɗi Hakan tareda Yimin ɗan Tafi Na Ƙarfafawa.

Tau Daganan Kuma Muka Miƙe Bayan Yasallami Masu Gurin Akan Abubuwan da Muka Ci, Yashiga Wasu Shagona dake Cikin Plus Center ɗin Yayiwa Iyalansa Shopin dangin Su Makilin da Su Brush Kayan Tea Dakuma Kayan Makulashe Harda Nima Sai da Yayiwa Nawa Shopin ɗin Yafito Hannayen sa Rike da Manya-manya Ledoji dake ɗauke da Tambarin Shagon da Yashiga Yasameni Ina Jingine da Motar sa da Yayi parkinq ɗinta A Wajen Harabar.

Yabuɗe Gidan Baya Yasaka Ledojin Sannan Muka Shiga Gidan Gaba Muka Soma Tafiya. Da Fari Motar Tsit Tayi Inbada Muryar Mai Labarai Da Yakamo A Radion Motarsa Bakajin Komai. Daga Bisani Kuma Muka ɗora Hirar Tamu Wacce Mafi Yawanta Muna Tattauna wa ne Akan Yanda Plan ɗinmu Zaije Batareda Ansamu Akasi ba.

Gamunan-gamunan Hargida Yayi Parkinq Nafito Kamin Yamiƙo min Ɗayan Ledar Tareda Cewa, "Ki Gaida Su Momy Ban Shiga Nagaishe su Ba Yau Nayi lattin Komawa Gida Nakuma San Hukunci na Nacan Najirana." Murmushi Nayi Ina Faɗin, "Ai Gara hakan, Sabida Kuɗinne Sai da Hakan dan Bakwa da Tabbas." Yace, "Lalala Lalle Yarinyar Nan Kinyi Baki yanzu Saboda ALLAH Macce Batafi Namiji Rashin Tabbas ba?" Nace, "Uhummm Kadai Faɗane Kawai Amma Ni Nasan Munfiku Tabbas." Dariya Yayi Yana Mai Shafa Sumar Kansa Kafin Ya tayarda Motar sa Yana Cewa, "Shikenan Ai, MAUDU'I Nan Yana da Girma gashi Ba Lokaci Amma Tabbas Sai Na Samu Lokaci Nahaɗu da ƊAN JARIDAR NAN ABDULLAHI IBRAHIM SOKOTO Su Saida Mana Fili A Radion su Dan Mu Tattauna Wannan Matsalar dani dake dashi A Kuma Buɗe Layi Jama'a Sukira Muji Su Waye da Nasara."

Nima Cikin Dariya Nace, "Tau ALLAH Yabaka Iko Amma Ni Nasan Zaku Faɗi Warwas Ne." Yaja Motarsa Yana Ta Dariya Tareda Faɗin "Baki da Dama Ni Kinga Tafiya ta Karki Sa Amini Hukunci Mai Yawa."

Yabarni Nan Tsaye Ina Bin Motarsa da Kallo Nima Kuma Dariyar Nakeyi Hakanan Zuciyata Na Ƙara Gayamin Cewa Ba Mutum Mai daɗin Sha'ani Yakuma San Darajar ɗan Adam Kamar Dr Jabir.

Ni Ina Masa Mummuna Kallo Ashe Yashigo Rayuwata Ne Kawai dan Yataimake ni, Sai Nake Tambayar Kaina Ko Ina Yasamu Irin Wannan Hazaƙa Shida Yakaranci Fannin Likitanci? Kila Kuma ABOKIN Nasa ɗan Jarida Abdullahi ibrahim Sokoto Yafaɗa Masa Irin Wannan Idaeyar. Gama Ni Ma'abociya Sauraren Shirye-shiryen Sa Ne Musamman Shirin sa Na 'LAMBUN MASOYA' Inajin Yanda Yake Warware wa Masoya Matsalolinsu Sosai. Hakanan Wani Lokacin Nikanji Shi Yace Yasadaukar da Wannan Waƙar Ga Abokin sa Likita Bokan Turai (Watau Dr Jabir)Ina Cikin wannan Karatun Wasiƙar Jaki Har Dady Yafito Zuwa Massallaci Zaiyi Sallar Magarib Yana Mai Riƙe da Hannun Muyiddim Zasu Masallaci Tare.

Nayi Hanzarin Rusuna Wa Ina Gayar Dashi Ya'amsa Cikin Fara'a Wacce Banyi Tsammani ba, dan Nazata Zaimin Faɗa Ne, Amma Sai Yacemi,
"Kun Dawo? "
Nace, "Eh."
Yace, "Ok Shi Jabir ɗin Yawuce ko? Ai Yakirani Yace min Zakuje ne Ki zaɓo Wasu daga Kayakin da Za'a Samaki Cikin Lefe Sbda Yafi Son Yasiyo Maki Zaɓinki."

Nace, "Eh Hakane Dady."

Yajuya Yana Faɗin "Tau Ai Saiki Hanzarta Shiga Gida Ki Samu Kiyi Sallah." Da Faɗin Haka Yaja Hannun Muyiddim da Nufin Suje Masallaci Tare Amma Sai Muyyudim Ya taɓure Ba'inda Zashi Yaggani da Ledar Kayan Kwaɗayi. Dady Yasake Hannunsa Yawuce Abunsa Gamida Cewa, "Kai Kasani Sarkin Kwaɗayi." Yabarmu Muna Ta Dariya.

Tunda Nashiga Gidan Nakuma Fitar wa da Muyiddim da Bisket da Chocolat ɗinda Ke Cikin Ledar Nabashi. Sai Nashiga Nima Haramar Sallah. Bayan Na Kammallah Kuwa Nafito na ɗebi Abinci Na Nufi ɗakina dan Nasan Innace Bazan Fito ba Momy Zata Zargi Wani Abin.

Abincin Kuwa Banbi Ta Kansa ba Sai Da Naɗauko Biro da Memo Na Tsara duk Yadda Nake Bukatar Abubuwan Suje Batareda Ansamu Cikas! ba. Sa'annan Nazauna Cikin Farinciki da Kuma Gamsuwa Kan Yadda Natsara Abubuwan.

Ina Gama Cin Abinci Kuwa Aka Ci Sa'a Sani(Almajirin gidamu)Yazo Karɓar Abincin sa Nai Maza Nafito Tsakar gidan Ina Cewa "Sani Kashigo?" Yace "Eh Aunty." Bayan Na ɗauko Masa Abincin Nasa Nace, "Ina So Muyi Magana da Kai Sani In ka gama Cin Abinci Kasameni Ɗakina."

Cikin Matuƙar Mamaki Hakan Yace, "Magana Kuma?" dan Bamu Taɓa Ƴar Haka dashi ba Komai Za'ayi Tsakar gida ne.

Ganin Hakan Yasa Nace, "Kai Karka damu Bafa Wani Abu Bane ba, In ma Baka Nutsu da Muje ɗakin ba Bari Muyi Maganar A Harabar Gida."

Yace, "Aha Zamu Iya Maganar Kawai Yanzun dan Banan Zanci Abincin ba Sai Naje Makaranta."
Nace, "Tau Yayi Jirani A tsakar Gidan Ina Zuwa." Kafin Na Nufi ɗakina

"Bari Nayiwa Su Momy Sai da Safe Kafin Kifito." Sani Yafaɗi Hakan Yana Mai Nufar Ɗakin Nasu Momy.

Ledar da Muka Dawo da Ita Na buɗe Nadebo Sabulai Na Wanka da Na Wanki da Mayukan Shafawa da Turaren Nazubo su A leda Nafito. Dai-dai Lokacin da Sani Shima Yafito Zuciyarsa Cikeda Saƙe-Saƙe Yabiyo Bayana Harzuwa Sanda Muka Samu Wuri daga Cikin Harabar Gidan Namu Na Zauna Ina Mai Kallon Sani Da Yayi Tsaye Yana Kallo na Cikin Maɗaukakin Mamaki, Saboda Irin Wannan duguwar Hulɗar Bata Taɓa Shiga Tsakanin mu ba. Duk Hulɗar da Zamuyi Mukan Yita Ne Idan Aiki Yahaɗa mu Kamar Inyazo Taya mu Aiki Nan Gida Ko kuma Muna Wurinda Momy Ke Saye da Sai Suwanta.

Nadubeshi Yana Tsayen Nace, "Zauna Mana." Ba Musu Yazauna Naci Gaba da Magana "Sani Wani Taimako Nake So Ka yimin Basai Na Tsaya Yima Bayanin Aure na da Ake Kusa da Yinsa Ba Nasan Kasani Kuma Kasan da Irin Matsalolin da Nake Fuskanta da Su Momy Kan Su Bani Wanda Nake So Amma Sunƙi Sudai Sai Na Auri Zaɓin Su Duk-da Kuwa Irin Bayanin da Nake Tayi Musu Da Magiya Saidai Sun Kasa Fahimta ta Dan Haka Na Yanke Shawarar Ɓullo Musu Ta Wata Hanyar da Nake Kyautata Zaton Zasu Fahimta Insha'allah Wannan Kuwa Ita ce 'Zanyi MUTUWAR Ƙarya Aje Abinneni Tau Ina Son Bayan Mutane Sun Watse Kuje Kaida Wayansu Amintattakunka Ku TONO NI Kuɗaukeni Zuwa Wani Wuri Da Nan Gaba Zanbaka Adireshin Sa." Tunda Na Fara Wannan Maganar Sani Yake Kallon Na Cikin Mamakin da Yafi Wanda Yake Ciki A tun ɗazun Dan Saida Ya Firgita Sosai.


Zan ɗan Numfasa Muje daku A Page Na Gaba.
Tareda Alkalamin 👇

FA'IK. ✍🏼
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 35 · 0% Book details