Chapter.....24
So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Mallakar 👇
Fa'IK ✍
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.
FADAKARWA.
Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.
Bissmillahi Rahmanin Raheem
Gefen gado tasameshi A zaune Yana Aikin duba Wasu takardu da Yake Shirye-shiryen Tafiya ta dalilinsu Daga shi Sai Gajeren Wando Da Yar Singlet Fara ƙal! Jikinsa Fari tas Shima Sai Walwali Yakeyi Kamar Ka lashe Saboda Fari da Taushin sa Yaɗago dara-daran Idanunsa Masu Yiwa Ƴan Mata Kwarjini Yazuba su Gareta cikin Wata irin tarin Ƙauna! Ta kula dashi Sosai Amma duk Yanda Farinciki Hakan Yataso Mata Sai ta tuna daga gobe fa Farinciki Raba dedensa Zasuyi da Wata Matar duk Sai taji Baƙinciki yamaye Gurbinsa Yanzu ma Hakan ce tafaru harta ɗebo Fara'a Tana Tuno wa sai Kawai ta gimtse Fuskarta Shima Yasan Abinda Yasa hakan dan Haka Cikin Sigar Lallashi Yawatasar da Takardun Yanufo ta Gamida Cewa, "Sai ni Mijin Ummu Asharaf kuma ɗan lelenta Abin daɗin da kuek Girkawa ne Aka ɗebomin Inyi Tastin?"
Yasa Hannunsa Yakarɓi Farantin Yadauki Donoth din Bakinsa Yana Tauna Hankali dai-dai lokacin wayarsa dake Gefe ta Soma Neman Ceto kamar Bazai ɗauka ba Amma ganin Number Dadynsu Khaleesat ne yasa Yayi Hanzarin ɗauka daga Can Dady ke kwararo Masa Bayanin Abinda Yafaru Kai! Ai Babu Shiri yamiƙe Yana "Subhanallah! Ganin Nan Zuwa Yanzun Dady!" yakashe Wayar Cikin Hanzari Yasoma Jawo Jallabiya Yasaka bai ko Saka dogon Wando ba!
Maman Asharaf Cikin Mamaki tariƙosa dan kamar Ma yamanta da ita Acikin Ɗakin Tace, "Menene Yafaru Baban Asharaf?"
"Wallahi Khaleesat ce Akace Ba Lafiya Sosai Kuma Harma Suna Asibitin Mu..." yana mai Ƙokarin Ficewa daga ɗakin Yake Faɗar hakan.
Cikin Ƙokarin danne Abunda Yataso mata Tace, "Ai Ka tsaya Kasa Complet Kaya Amma Kafita Haka?"
Ji Yakeyi Kamar ya Faskara Ma Maman Asharaf Mari Amma Me Ya tuna Sai Kawai Yanufi Drowar Kayansa Yana Ƙokarin Zaro Riga da Wando Na Adidas.
Cikin Hanzari yasanya Kayan Kafin yaɗebi wayoyinsa da makullin Motar sa Tareda ficewa yana Cewa, "Maman Asharaf naje Sai na dawo!"
"ALLAH Yatsare!" Can Cikin makwashinta tai Maganar Wacce Ma Bana Tunani Shi Uban gayyar Yaji Maganar tata wanda Ko yajin ma Bana Tunanin Yadamu da Jin balle Aje ga yakula Yanda Maganar tazo.
Sannu A Hankali ta Sulale ta zauna Kafin Tasanya Hannunta Biyu ta dafe Kantan Dai-dai Lokacin da Wasu Irin Hawaye Masu Zafin Gaske Suka Soma Sharafto Akan dan damalin Fuskarta Yayinda Tarin Tambayoyi Birjik Suka Soma Kara Kaina Acikin Zuciyarta Cewa Anya kuwa zata iya Jurar Irin Wannan Zumuɗin Na Dr Jabir? Shin ma Kuwa zata Iya Karawa da Amaryar Irin Wannan Masifaffen So da Dr Jabir keyi Mata wanda baya iya ɓoye shi ko Gaban Waye? Anya Ba Sallama Zata Nema Takoma Gidansu ba? Tau Inba Haka ba Fa Akwai Yuwar Ciwon Zuciya Zai Sheƙata Barzahu Matuƙar Amaryar ta'iso Gidan Kuma Dr Jabir ɗin yaci Gaba da nuna Haka.
Balle Kuma Ba tasan Halin Amaryar ba Wacece ita? Kila ba Mutumniyar Kirki Bace Su taru ita Dr Jabir Su Saka mata Ciwon Zuciya Koma Zuciyarta Ta Buga Lokaci ɗaya! Ta Mutu Murus Kuma su Basuda Asara! Kai Bazai yu ba.
Tau in Bazai yu ba Mezai yu? Wannan Tambayar Taƙarshe Samun Amsarta yayi mata Wahla wanda hakan Yasauya Akalar Kukan Nata daga ZUBAR HAWAYE zuwa Kuka Sosai Mai Sauti Tana mai Nadamar Kasancewarta Matar Dr Jabir Watakil da Irin Hakan duk bai Faru da ita ba.
Tajima Tana Kukan Kafin Taji Anzauna gefenta Gamida Rumgume Kafaɗarta tace, "Ya'isa Hakanan Kinji? Nabarki kiyi Kukane Saboda Shima ɗin Rahamane ga bawa A sanda Yake Cikin Matsi hakanan Yana Rage Nauyin Baƙinciki da Zuciya take kunshe dashi So Ina Fatar Kin Samu releaf?"
Maman Asharaf takasa Magana Sai Ajiyar Zuciya Takeyi.
Cikin ɗacin Rai Sajida Ta Numfasa Kana Tace, "Har muna Yabon Kin Warware Kin Manta Komai Sannan Kuma Zaki zo Yanzun Ki Ɓata rawarki da tsalle?...."
Cikin rishin Kuka Maman Asharaf ta Tari Numfashinta gamida Cewa, "Haba Sajida taya zan Juri Wannan Kinaga fa Muna Cikin Magana Cikin Salama Dadyn Amaryar nan Yakira shi Cewa Batada Lafiya Suna Asibiti Inkika ga Yanda Yaburkice Yana wani Rawar Ƙafa Ko Umma Ce Sai Haka Da Nayi Masa Maganar ya natsu Yashirya Kamar Zai Kifamun Mari tau A hakan Tun Kafin Tashigo fa Kenan? Kiyi Tunanin idam Tashi go Wane Irin Cin Kashi ne Zasuyi min Shi da Ita? Yanzun ma A Nashin kaɗai yana ƙare Balle Ga Nashin ga Nata? Gaskiya bazan iya jura ba Wallahi Bazan Iyaba Kawai Yasak......." Kuka Yaci Ƙarfinta Yayinda Sajida Ta toshe Bakinta Tareda Cewa, "Ko Kusa kidaina Irin Wannan Maganar Ko Sa Tunanin ki Akanta Maman Asharaf! Wanna ba hanya bace mai ɓullar dake ba Bakuma Shine Sulotion ɗin problem ɗin ba Kingane? Yanzun Kuma keda ya Jabeer MUTU KA RABA Takalmin kaza dan haka ki daina jin rauni Acikin Zuciyarki.
Dan Haka Nafison Kisamu Compedience Kizauna Sosai! Kiji A ranki Cewa kece da gida duk wadda Zata zo Bayanki Zatabi Ko babu Aure Keda Yaya Jabir Yan Uwan Juna ne JINI ƊAYA kuwa Ai Yawuce Wasa!
Ire-iren Wayyanan Tunanin Yakamata Kiyi Wanda Sune Zasu ƙarfafi Gwaiwar ki Bawai Wayanda Zasu Sa Ki Sare ba Ina Fatar Kin Fahimce ni Maman Asharaf?"
Sannu A Hankali Maman Asharaf ta girgiza kai Cikin Gamsuwa da Shawarar da ƴar uwarta ta Bata.
Fahimtar Hakan da Sajida tayi yasa ta ɗora da Cewa, "Yawwa Tawan dan Haka Tashi kije ki wanke Fuskarki Kizo ki Sake ɗanɗasa kwalliyarki Ta yanda ba wanda zai gane Abinda Yafaru Ki kuma Manta da Komai Ki maida Komai ba Komai ba."
Cikin ƙwarin gwaiwa da Kuma Karsashi Maman Asharaf tamiƙe Zuwa toilet ɗin dake cikin ɗakin Na Dr Jabir ɗin Tana Wankin Fuskarta Zuciyarta Naƙara tuna mata Shawarar Ƙanwar Mijinta Wanda Ko A Iya kulawarsu gareta kaɗai A yaci Ace Tasamu FARAGA Akan Baƙincikin KISHIN Da ke Ruruwa A Zuciyarta dan Nawa ne Ma Suka samu Kulawar Irin Tata? Dangin Miji Basa sonsu Hakanan Kuma zasu Sa shi yaƙaro Mata Kishiya dan ƙara cin Zarafinta Amma A Hakan ta Hakure tau Ina ga ita ba Ahaka yazo mata ba?
Ire-iren Tunanin da Shawarar Sajida Suka Asassawa Maman Asharaf Kenan Wanda hakan yaƙara Ƙarfafa mata gwaiwar dawowa cikin walwalarta Kamar dai komai Bai Faru ba.
Abinda Yasa taji Babu Shakkah Kasamu Wanda Zai Tallafeka Yakuma Agajeka da Shawarwari Nagartattu A Sanda kake Cikin Halin Damuwa Ba ƙaramar Rahma bace Ga BAWA dan haka sai ta Ƙara yiwa ALLAH godiya Tareda ƙara Rokon sa juriya da kuma Hakuri Akan Lamarin KISHIN Mijin ta.
*********
Daga sanda Suka Shigo da ita Asibiti Aka ɗora ta kan gado Aka turata Zuwa Emagyncy Room Basu Sake Sanin halinda take ciki ba, hakanan su Kansu Basu Sake Sanin Halinda Zukatansu Suke Ciki ba.
Sudai Kawai Gasunanne Zube A Ƙatoton Reception ɗin Asibitin. Momy dai takasa Zama Abinda Yakaita ƙofa Yadawo da Ita Cikin Falon.
Mami Iyabo ce Mai Tausarta da Lallashinta Yayin da Dady Yayi Tawakkali Yazauna Aɗaya daga kujerun dake jere gurin hakanan Bakinsa bai Futa da Faɗar duk wata Adu'a da ya sani ba ta Neman Samun Sauƙi ga Wanda Musiba ta Faɗama. Shikuwa Ya Nuradeen Jingine kawai Yake A bango yarumgume Duka Hannayensa Biyu A Ƙirji Yana Aikin Kallon Mutanen dake kai kawo A gurin bawai dan Hankalinsa Na kansu ba!
Awowi Biyu Suke Shuɗe A Haka Kafin daga can Aka Buɗe Ƙofar ɗakin da Aka Shiga da Khaleesat ɗin Dr Jabir Yafito Duk Yahaɗa gumi.
A Lokaci ɗaya duk Suka nufeshi da Tambayar "Yaya Ta tashi?" Tambayar da Yakasa Amsa Musu Illai Kawai Yakaɗai kansa Yawuce Yana mai Share Hawaye da duk Yanda yayi Ƙokarin karsu Zubomasa Sai da Suka Zobo! Wannan Yasa Duk Suka ƙara Firgita Ciki Kuwa Harda Dady da Ada Yayi ɗan Ƙarfin Halin Nuna Juriya.
Wanda Kuma Hakan Yasa Suka Shiga Turereniyar juna dan ganin Ƙowanensu Yashiga Acikin ɗakinda Khaleesat ɗin Take Adai-dai Lokacin Idanuwansu Sukayi Musu MUGUN GANI Wanda Har'abada Bazasu Taɓa Mancewa da Irin Wannan ganin Harma da RANAR da Sukayi Wannan Ganin ba!
Khaleesat Kwance Samɓal! Likitan dake Kanta yajawo Farin Zane Gamida Rufeta tundaga Ƙasa Har Saman Fuskarta ruf! Kafin Shima Yaɗauke kwallar da taru A idonsa na tausayin Wannan Family! Ya dafa Kafaɗar Ya Nuradeen Tareda Cewa, "Am Sorry!" da Hanzari kuma yafice ɗakin dan Ba Shakkah Shima Zai iya tayasu Kuka in ya Tsaya.
Wutace ta ɗaukewa Momy Cikin Firgici Take Tambayar Dady "Dadynsu Meyafaru da Ita? Eh dan ALLAH Kumin Bayani Mene ne?" Dady Yasharce Hawaye da Rabon Yayisu A Rayuwar sa Harya mance Yace da Momy, "Kullu Nafsin Za'iƙatu Mauti!!! Khaleesat Ta RASU ALLAH da yabamu Ita ya Amshi Abinsa dan Haka Muyi H......" Ina Momy bata gama jin Abinda Ya'am bata ba Ta Nufi Gadon da Gawar Khaleesat ɗin ke kwance Ta Rumgume ta Tana ihun, "Wayyo ALLAH Nashiga Ukku! Khaleesat Karki Mutu Ki Barni Ku Biyu ɗaine ALLAH Yabani.
Jama'a Ku taimakeni Karta Mutu!!!!" Babu Shakkah Izuwa Yanzun Kowa Yasan Momy Tafita Hayyacinta Kuma daga Cikin su Ankasa Mai ƙwarin gwaiwar da Zaizo Yakamata Ya Lallasheta Ko yadakatar da ita daga Girgiza GAWAR datakeyi.
Ya Nuradeen Haɗe kai da bango Yayi tayi Yana ƙwala kansa ga Bangon Yana Kuka Mai Cin Rai da ban Tausayi ga duk Wani kunne da ke Saurarensa dan Kai Kasan da jin Irin Wannan muryar Na Kuka tau Abun Yakaine.
Ɗakin Yaruɗe Yashiga Wani Irin Ruɗu da Ruɗani Dama Mami Iyabo ce Mai ƙwarin Zuciyar Lallashin Itama Yanzun ta Nemi ƙwarin tarasa Musamman idan Taɗago kai tayi Tozali da Gawar Khaleesat ce Acan, Khaleesat Amarya! Amaryar da ɗazu-ɗazu Suka dinga yiwa liƙin Kuɗi Suna Cashewa Cikin Nishaɗi Kai Lalle ALLAH ALLAH NE kuma Shiɗin Buwayi ne Gagara Misali.
Tau Dadyn ma dai Ba Kuka Yakeyi ba Kuma Shi Ba Wani Ihu Yakeyi ba Kawai dai Gashinanne Wuta ta ɗauke masa yarasa Nayi!
Ya Tuno ɗazu ne fa Yake mata Raha Akan Yan tsallen da Tasa Kan Cewa Irin Wannan Tsulun Haka? Bakya Tsoron Faɗuwa Ikram?" Khaleesat Tayi Murmushi Tace, "Dady Wane irin faɗuwa Ai Har Wayanda ma Suka Fisu Ina Sawa." duk Sukayi Dariya.
Zuwan Wannan Tunanin Acikin ƙwaƙwar Dady Yaƙara Tayar masa da Hankali Wanda Sai da Yayi da Gaske Kafin Yasamu Yafi Ƙarfin Zuciyarsa Yasoma Anbatar Innalillahi Wa Innah Ilaihi Raaju'un! Da Ƙarfi!
Tirkashi!!!!
Tashin Hankali Wanda Ba'a Samasa Masa Rana! Masu Karatu Muje Zuwa danjin Yazata Kaya....... Nidai Nayi Gaba.........
Tareda Alkalamin
FA'IK.
[9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪🏻J.A.W 💪🏻
❤❤SONEEE ....💕💕
(Silar Komai.)