← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 40

Chapter.....21

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Gwaggo Halima Tana Zaune Tsakar Gida Nama Take Yankawa Safiyya Na Rike Mata Suka Ga Mutum Yafaɗo Musu Acikin gida Kamar Wacce Aka Cillo Haka ta zube Gaban Gwaggo Halima tana ta Rusar Kuka Kamar Ranta Zaya Fita.

Gwaggo Halima da Safiyyah Sai da Suka Firgita Gwaggo Halima Tadubeta cikin firgici tareda Cewa, "Asiya Wannan wane irin Hauka ne kuma? Ki Faɗo ma Mutane gida A irin Wannan Yanayin?" Gwaggo Halima tayi shiru tana mai ci gaba da Kallon Maman Ashraf ɗin.

Dama tayi Tunanin hakan zai Faru tunda taji Cewa Ankai Lefe nan tasan A Rina wai An saci Zanen mahaukaciya! Ganin Kukan Yayi Yawa Tana Neman tara Mata Mutane Yasa Gwaggo Halima Ta Tsawace Ta, "Wai ke Kanki ɗaya Kuwa? Wallahi Kimin Shirun da Bakinan naki tun kafin Na Taso na tattakaki?" Itakam Safiyya Ta rafka Uban Tagumi Tana Aikin Kallon Yayar tata Cikin Zullumi da Taraddadi Tanaji A Ranta Lalle Ya Jabir Bai Kyauta wa Auntyn Tata ba, dan haka Cikin Kasalar Jiki Ta taso Izuwa ga Maman Ashraf ɗin Tana mai Share mata Hawaye Kafin Tasoma Cewa, "Aunty Kiyi Hakuri Dan ALLAH Komai Yayi Zafi Maganin sa ALLAH!"

Izuwa Yanzun Tarage Sautin Kuka Sai Gumji Takeyi. Dan Haka Safiyyah Taja Hannunta Zuwa ɗakin Gwaggo Halima tana mai ci gaba da bata Baki Suka samu guri Suka Zauna.


Itama Gwaggo Halima wanke hannun ta tayi daga cikin Naman kafin Taduba Girkinta Taganshi Yana Ci Gaba da Turiri! Dan haka Itama Sai ta nufi Ɗakin Kafin Ta zauna Gefen Gado Tana Mai Kallon su Safiyyah Na Aikin Rarrashin Maman Asharaf. Taɗan Numfasa Kafin Tace, "Banyi Tsammanin Wannan Rashin Hakuri daga gareki Ba Asiya, Kin Manta shi Namiji Mijin Macce Huɗune Halan? Sannan Kin mance da Irin Tarbiyyah da Muka baki? Meye Abin Mai Zafi Aciki?" Cikin Sheshshekar Kuka tace, "Amma Umma fa Kina Ganin Mutumen Nan Bai gayamin Batun Auren nan Sai Acikin Dangi Da'aka kai Lefe Naji Sannan Kinga yanda Yake Rawar Kai Akan ta Tun Kafin ta Shigo? Sannan Dan Allah menene Banayiwa Baban Asharaf da zai Sakamin da Wannan?" duk Su gwaggo Halima Suka Nutsu Suna Saurarenta.
Bayan ta tsagaita Gwaggo Halima Ta musƙuta daga Inda take Kafin ta Soma Cewa, "Naji duk Abinda Akai Maki Amma Kin Manta Shi Aure Sunna ne, ai ba dole Sai Ka ɓata ma Namiji ko Ka kyautata masa Zaisa ya Ƙaro Aure ba, a'a Shi Aure Kawai Sunnah ce Yanda Nagayama ki In kin Manta In Tambeyeki Ma'aiki (S A W) Matansa Nawa? Sannan Wacce daga Cikin su Kikaji Tayi Kishin Hauka? Wannan ma Ai Abun da kike Shi zai bawa Amaryar Damar Mayarda ke Bora Acikin gidanki Hakanan Shima Maigidan yaji kin Fita Ransa.

Kishi Halak ne! Kuma Yana da Azaba Nasani, Tau Amma In Ka Iya Masa Sai Kaci Riba in Kuwa Baka Iya sa ba Sai ka Kwashi Asara. Dan Haka ki Nutsu da Kyau Kijini."

Gwaggo Halima tayi Shiru tana ƙara muskutawa daga Zaunen da Take yayinda Maman Asharaf da Safiyyah Suka Ƙara Nutsuwa Suna Sauraronta Duk-da Kuwa Kanajin Ajiyar Zuciyar da Maman Asharaf keyi Akai-Akai.


"Yanzu ne Yakamata Ki ƙara ɗamarar Kusantar Mijinki da kyautatawa Harma wacce Bakya yimasa Ada Sa'annan Kizama Macce Mai Fin Ƙarfin Fushin ki Akan Abinda Yadangaceshi Ko Kishi Yarki. Wayyanan Abubuwan da Na faɗamaki (gaya maki) Bazasu yuwu ba Saikin Jajirce Kin kuma Jure Wani Malami Mai hikima yana Cewa, Namiji Yakan Kara Aure Inji Yaji daɗin Auren Saboda Yaƙara Samun Jin daɗin Auren Hakanan In bai Samu jin daɗin Auren ba zai ƙara Aure dan Yasamu Jin daɗin dan haka KISHIYA Tilas ce Ga Ƴa mace. Dan haka ina mai nusar dake tun wuri Kije kigyara Gidanki tun Kafin Wata tashigo Tafiki Tasiri Acikinsa dan dai kinga Bakida Wani Yaƙinin Auren Wanda Bazai Maki Kishiya ba, in kuwa Hakane Gujewa Kishiyar Bashine Mafi Muhimmanci ba A'a tsayawa Kiyi Tunanin Abinda Zai ƙara maki Martaba gurin maigidanki da Kuma Kishiyar taki Amma Ba wannan Haukan da Babu Abinda Zai Hana illai yaja maki Rushewar daraja."


Haka dai Gwaggo Halima tasa Maman Asharaf da Misalai da Nasihohi Irin Nasu Na Dattijan Mata dakuma Suka Cuɗanya da Rayuwa Suka San Menene Rayuwar.


Wanda Babu Shakkah Misalan da Nasihohin Sunyi Tasiri Matuƙa Akan Maman Asharaf harma da Safiyyah ƴar taya Yayarta KISHI kai Harma da Dr Jabir da tun ɗazun Ya'iso Gidan Kalaman da Yaji Gwaggo Halima Nayiwa yarta ne Yasashi Jan burki Yatsaya tsakar gidan Har' A ransa Yana ƙara Jadadda Albarkar dake kwai Cikin Auren Ƴar Babbar Gida ƴar Dattijan Mutane da Suka San Abinda Sukeyi.


Ƙaurin Da Gidan Yacika dashine Yatabbatarwa da Su Gwaggo Cewa Miyar Tasu dai ta ƙone, dan haka Cikin Hanzari Gwaggo Halima tafito da nufin Zuwa Kitchin ɗin Wanda tsirit Yarage Tayi Tuntuɓe da Dr Jabir Dake nan Tsugunne Bakin Ƙofar Tayi Hanzarin Cewa, "A'a Subhanallah! Jabiru zuwan Yaushe?" Ta leka Cikin ɗakin gamida Cewa, "Ke Safiyyah zo ki kawowa Yayan naku Abun Zama." Kafin Takaɗa kai Zuwa kitchin Tareda Cewa, "ina Zuwa Jabiru Miyata ce Ta ƙone."


Shikam Dr. Jabir Duk Yawani Ƙara Mutuwar Zaune Saboda Girma da Darajar da Yaƙara Ganin Gwaggo Halima da Ita. Yana ƙara ji A ransa Cewa Samun irinsu Gwaggo Halima yanzun sai An tona, dai-dai lokacin ne kuma Safiyyah ke ƙoƙarin Shimfiɗa masa Tabarma Nan gefen Ƙofar ɗakin. Kafin Tagaidashi Ta Nufi Ɗaki Inda Tabaro Yar Uwarta Sai dai Kafin tashige daga kitchin Gwaggo Halima ta kwalo Mata kira Kan Cewa ta Kawo Mata Allayahun da Ta Yanka Azuba Cikin Miyar.

Dan Haka taɗauki Robar Nama da Allayahun Ta Nufi Gurin Gwaggo Halima Hakan Yaba Dr Jabir Damar Miƙewa Yanufi Cikin ɗakin Yasami Maman Asharaf ta Rafka tagumi Haryanzu takasa Tsaida Hawayen da ke Zubo Mata Duk-da A Yanzun Tana jin Tasamu sassauci da kuma kwarin gwaiwar cewa Zata iya Zama da Mijinta Cikin Juriya dakuma Jajircewa Kan....... Rusunawa Yayi Agabanta yaɗora tafukansa Akan Cinyoyinta Kafin Yakira ta Cikin Sanyi Muryar da inba Dagaske kayi Bazakaji ba.

Maman Asharaf taɗago kai tana kallonsa Batareda ta'iya Amsawa ba, Tasani Tana son Mijinta Shiyyasa ma take Matuƙar Kishin Abinta Amma Gwaggo tace mata Hakan da Takeyi Shine Zubar da ƙimarta. Tau meye mafita Kenan Gareta? HAƘURI! Wani Sashe Na Zuciyarta Ka gayamata Hakan. Kwata-kwata tayi nisa daga duniyar Mutane Tunani takeyi Kawai Yayinda Shikuma Dr Jabir Yayi mata Zuru da Ido Yana Kallo.


Shikanshi Tunanin yakeyi Yana kuma Gaya masa Kansa Cewa Zaiyiwa Maman Asharaf Kishiya ne Kawai dan shiɗin Yana Son Khaleesat bawai dan Yagaji da Maman Asharaf ɗin ba ko nufin Wulakanci gareta ba. Tau. Kowanensu dai da Abinda Yake Saƙawa Acikin Ransa Amma da zaka Shigo Ka Risƙesu A yanayin da Suke zaka Zaci wani batu sukeyi Ko suke tattaunawa A tsakanin su.

Kuma an rasa mai ƙwarin gwaiwar da Zaiyiwa ɗan uwansa Magana

Wannan Kenan........


*********


Tunda Na sanarma Da Abdul-wahab Halin da Ake Ciki duk Yabi Ya Sukurkuce Yayi Zuru Yarasa Maganar Cewa, Yayinda Nima Nayi Shiru Cikin Tsura Masa Ido da Tunanin Ko in Sanar Masa da Matakin da Nake Shirin ɗauka? Tau Amma In Bai Bani goyon baya Bafa? "Kai! Shima bai cancanci Jin Wannan Plan ɗin ba dan Ba Shakkah Shima Ina Son In Auna Irin Zurfin Son da Yakeyimin dan Haka Shima Bari Na kawo Na Mujiya Na Zuba Masa, dan Inga Iya Gudun Ruwan sa Shima." Kawai Sai Nazaɓi Inyi Shiru Nima Yayinda Yaɗago Idanuwan sa Jajir dasu Yana mai kallona Kamar Wanda Ya Warke Daga Makanta A yau ɗinan Kuma Yasamu Sa'ar Ganawa da Abun da Yadaɗe Yana son Gani.

Kafin wani irin Tauhidi Yazowa Abdul-wahab Cikin Alhini Yaɗan Motsa laɓɓansa Yasoma Cewar, "Tamu Ƙaddarar Kenan Khaleesat, Muyi Hakuri In Har muɗin Rabon Juna ne duk Runtsi da Wahla Zamu Kasance Amatsayin Mata da Miji idan Kuma Har muɗin Ba rabon Juna Bane Tau duk Wani Ƙokarin da Zamuyi Baza mu taɓa Zama Mata da Miji ba Saboda haka Abinda Kawai Yakama cemu Hakuri da Adu'a."


"Amma sai inga Kamar Baka sona kamar Yadda ni Nake Mutuwar Sonka Abdull Bansan Meyasa ba? Ko dan kaga Nacika Sonka da Yawa ne? In ma Haka ne tau Ka......"

Abdul-wahab Yakatse ni Ta hanyar ɗagamin Hannun Kafin Yasoma cewa, "In ma Ina Sonki Khaleesat Sai Kuma Nagoyi Bayan Ki Saɓawa Iyayen ki? Da bakin ki Fa Kika cemin Dadynki Har Yasa Rana Lokaci kawai Ake Jira ko ba haka kika ce Ba?"


Nagirgiza Kaina Gamida Goge Kwallar da Tacika Idanuna Batarda Na samu Zarrar Yin Magana ba.


Yace, "Tau Kinga ni In Har Ni MASOYI Ne Na Haƙiƙa bazan So Naga Dadyn ki Yazama Karamin Mutum. Meye Ƙaramin Mutum? Shine Yayi Magana Kuma A samu Yasaɓa Alkawali ko Yacanza Maganar Wanda Nasan hakan Abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba. Sannan Ko Bancin Hakan ma Sunce Bancanci Zama Mijinki ba Saboda Ni Ban tara Abin Duniya ba Nima dai Kawai Naci ne Irin Na SO! Inba Shi ba Irin Wannan wu....."

Jin Abdull Yasoma Sakin Layi Saboda Ɓacin Rai da Yashiga Yasa Nayi Saurin Toshe Kunnuwa Najuya da Gudu Zuwa Cikin Gida Yana Kiran "Khaleesat! Khaleesat!! Khaleesat!!! " Amma Ina Ban saurare Shi Ba.


Cikin Matuƙar ƙunar Zuciya Yazube Ƙasa Yana maida Numfashi Tamkar Mai Ciwon Asma wanda Ganin Hakan Yasa Yusuf Cikin Hanzari Yanufo Shi Yana Cewa "Abdul-wahab!" Yakamo Kafaɗarsa Tareda Cewa, "Abdull Meyafaru Naga Itama Khaleesat Ta tafu Tana Kuka?"


"Yusuf Khaleesat Wani Za'a Aura mata Wanda Bani Ba Nan da Sati Biyu, Yusu Menayi Wa Iyayen Khaleesat da basa sona ne? Ko ina da wata muguwar ɗabi'a ce?" Duk inda Jikin Yusuf Rawa yake Shi Kanshi yashiga Tashin Hankali kan Wannan Maganar

Cikin Muryar Kuka Abdul-wahab Yake Cewa, "Dama Talauci Na Iya Zama Aibu? TALAUCI Nan Nima fa Bani Liƙawa Kaina ba ARZIKIN DA TALAUCI Nan Duk Na ALLAH ne kuma Shi Yake Badawa Ga Wanda Yaso Bawai dan Yin Zalunci Ba Sai don Jarabba Kowane daga Cikin Bayin sa... "Yafashe Da Wani Kuka Mai ban tausayi Kafin Yasoma Cewa, "Yusuf Manayiwa Iyayen Khaleesat Meye Nayi Wa Iyayen Khaleesat Mena ci Musu me....." Yusuf Yayi Hanzarin Toshe Masa baki Yana Basa Hakuri Kafin Yajasa Suka bar Cikin Gidan Yana mai ƙaƙarin Nema musu Abun Hawa da zai kaisu Gida. A wannan Karon Shi Kanshi Yana jin Ya tsani Iyayen Khaleesat Harma da Ita Khaleesat ɗin Saboda Sunci Amanar Abokin sa. Gidansu Yacema Mai kk napep ɗin da Yatara Yakaisu Yayin da Abdul-wahab Yace, "Ni Ka Kaini Gida Ba'inda Zanije."

Yusuf Bai Kula sa Ba yace Mai Kk Napep Yaja Suje. Tunda Suka shiga Kk napep ɗin Abdul-wahab Yahaɗe Kai da Gwaiwa Shi Ba Kuka yake ba Amma Yanda Zuciyarsa Ke Suya Gara Yayi Kukan Ƙila Yasamu Sassauci.


Taufa My Readers Muje Zuwa Danjin Yazata Kaya

Nikam Nayi Gabaaaaaaa
[9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 19 · 0% Book details