← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 40

Chapter.....30

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Shikuwa Abubakar Tun Wucewar Su Innarmu Bai Tashi ba Nan Yaci Gaba da Zama Cikin Kasalar Jiki da kuma Wani Irin RUƊANI Da Yayi Masa dabaibayi A Zuciya Sai Saƙe-Saƙe Kala-kala dake Zuwar Masa Cikin Zuciya, Wanda Taƙaimame Yakasa Na dafawa Akan MUTUWAR Khaleesat da DAWOWAR Ta Shidai Baiga Jana'izarta Balle dama can Yace Ya Tabbatar da MUTUWAR Tata, Labari Yaji Kuma Yayi Imanin Cewa, Bazai duk Mutane Su Taru Suyi Ƙarya Ba, Wani Sashe Na Zuciyarsa Yace, "Tau Suyi Ƙaryar Mutuwarta A Wanne Dalili? Saboda Basa Son Bawa Yayan ka Ƴarsu. Yaji Wata Zuciyar Tace Masa Hakan Sai Kuma Watar Tace Masa Su da Ƴarsu Inbasa Badawa Dole Sai Sun Mata Taɓon MUTUWA Harsu Sa Ta Makara? In ma Hakane Meyasa basuyi Wannan Hukunci ba A Wancan Karon da Suka Tashi Aurar da Ita ga Alhaji Saminu ba? "Kai!" Abubakar Yafurta Hakan Afili Tareda Ƙara dafe Kansa Ganin Kansa Zai Kulle Tamau Koma Yaƙulle Tamau Baya da Wata Mafita da Ta Wuce Karantar Innalillahi Wa Inna Ilaaihi Raju'un!!!" dan Haka ita Yariƙe Yaci Gaba da Yi Har'izuwa Sanda Likitan Nan Yasake dawowa Tareda Bashi Umurnin Zai Iya Shiga Gurin Maman Walida Yanzun Dan Haka Yamiƙe Cikin Kasalar Jiki da Na Zuciya Yashiga ɗakin Yasami Maman Walida Idanunta Biyu Sai Aikin Kallon ɗakin Takeyi Tana Ganishi Tasoma Ƙoƙarin Mikewa Zaune. Fahimtar Hakan da Yayi Yasa Ya'isa gareta da Hanzari Yataimaka Mata Tareda Jinginata da Filo Ta dai-dai ta Sosai, Kafin Shikuma Yajawo Kujera Yazauna Gabanta A Sanda Ita Kuma Take Tamabayar sa Meye Gaskiyar Abunda Tagani da Gaske ne Ko Mafarki ne Tayi? Girgiza Mata Kai Yayi, "Ba Mafarki Bane Gaskene, Amma Dan ALLAH Ina Son Mmn Walida Ke Saka Nutsuwa A Ranki Mubi Komai A Sannu, Nima Ina Cikin Makamancin Halinda Kike Ciki dakuma Nazurfafa A Bincike Sai Naji Kamar Ƙwaƙwalwata Zata Tarwatse Sbda Nakasa Gane Komai gudun Faɗawa Irin Halin da kika Shiga Yasa Nayi Ƙokarin Raba Kaina da Irin Wannan Tunanin Abunda Kawai Nabarwa Raina Yanzun Kawai Khaleesat Ba MUTUWA tayi Ba Akwai Wani Ƙulallen Ƙulli da Bamu Sani ba, Wanda Mukabi Tq Lumana Zamu Sanshi Amma Mukai Garaje tau Zamu Nakasta Kammu ne kurum Dan Haka Kema Nake Shawarta Ki da Bin Wannan Hanyar dan Tsira da Lafiyarki." Babu Shakkah Wayyanan Kalamin Sunyi Tasiriri Sosai Acikin Zuciyar Mmn Walida Yaune Kuma Taƙara Tabbatarwa Maganar nan Da Ake Cewa, "Tunanin Macce Baya ɗaya da Namiji Komai Girmanta Komai Kuma Shima Ƙanƙarta Sai In Shi Mijin ne Yayi Watsi da Wannan Baiwar ta Hanyar Gurɓata Tunanin Nasa. Dan Haka Sai Taƙara Gyara Ƙishingiɗar da Tayi Cikin Rashin Ƙarfin Jikin Nata Kana Tace, "Auta Maƙoshina Yabushe Taimake ni da Ruwa Masu Sanyi Insha Dan ALLAH!" "Ok Bari Na Kawo Maki."

Yamiƙe Zuwa Waje Sai da Yagayama Likita Halinda Ake Ciki Cewa Patien Tana Buƙatar Ruwa Masu Sanyi Za'a Iya Bata?" Likitan Yace, "A'a Kar Abata Masu Sanyi Adai Bata Matsakaita In Ma So Samu Ne Asamo Mata Ayaba Abar Ruwan." dan Haka Abubakar Yajuya Zuwa Harabar Asibitin Yasiyo Ayaba Mai Laushi Yadawo Yana Bata Tareda Sanarda Ita Umurnin Likita Kenan. Tau itama bata Musan ba Tunda Tasan Aikin Sune Kuma Suna Yi ne Dan Lafiyarta Kuma dai Ma itakam Taga Zurfin Tunanin Ƙanin Nata da Yaje Ya Tambaya. Da Taci ayabar Kuwa Sai Taji Lalle Ta Ƙara Samun Nutsuwa.

Bayan Yakawo Mata Tacin Yafita Zuwa Masallaci Saboda Azahar Takawo Jiki daga Masallacin Kuwa Inda Su Innarmu Yanufa Yasamu Abdul-wahab Na Zaune Kishingeɗe da Fillow Kayan Fruit ne Gabansa Yayinda Khaleesat Ke Aikin Ɓare Masa Ɓawon Ayaba Ko Lemu Yanaci. sai Ka Rantse Kamar Ba Abinda Yafaru.

I zuwa Yanzun Kuma Innarmu ma Ta Nutsu Itama Tana Riƙe da Carbinta Sai Abinda Ta Manta Nadaga Tsabihin da Takeyi Itama Ko Tayi Irin Tunanin Nasa ne? Ko kuwa dai ta Saduda ne Sbda Taga ba Abunyi? ALLAH Masani Sai Kuma Innarmu da Ita Kaɗaice Tasan Halinda Take ciki. Gudawa Kam dai Bata Tsaya ba Gama Lokaci -Lokaci Ka Kanganta da Buta Zuwa Bayi(Toilet). Yana Ma ɗaya daga Cikin Abunda Tayiwa Abubakar Ƙorafinsa A Yanzun Bayan Sungaisa da Tambayar Juna Yanayin Al'amurrah da ke ta Cuɗawa dasu Ayanzun Tamkar A RAYUWAR MAFARKI Ko Shirin FILM.

Bayan Yagama ji daga Innarmu Yace, "ALLAH Ya Sawwaƙa Bari Naje Na samo Maki Magani, Amma Abinda Yafi Kamata Kawai Ki Koma Gurin Maman Walida dan Macce Sai Macce Haka NAMIJI ma Sai Namiji ɗan Uwanshi." Innarmu Tagirgiza Kai Cikin Gamsuwa da Zancen ɗan Nata Kana Taɗago Tadubeshi Cikin Tausayinsa Akan duk Yanda Yayi Wani Firgai-Firgai Ko Babu RUƊANI Jinya Ba Abuce Mai Sauƙi ba ga duk Wanda Yayi Yasani.

Balle Kuma Ga Nasu Da Yazo Musu da Wani Irin RUƊANIN da Harsun Rasa Abin Misaltawa Dashi. Tace, "Auta Ina Fatar Ka Ƙara Juriya da Haƙuri Akan Wannan Halin da Muke Ciki Kaji? ALLAH Yana Ganin Halinda Muke Ciki Hasalima Shine Yajarabcemu Bawai Dan Yazaluncemu ba Saidon Yana Nufin Mu da Rahma Wadda Kila Nan Duniya ko Kuma Lahira Wannan Shine Yabarwa Kansa Sani Amma dai Ni Nasani Dukkanin Tsanani Yana Tareda Sauki Hakanan Bahaushe Yace BAYAN WUYA.... SAI DAƊI dan Haka Abubakar Ina Ƙarama Wasiya da HAKURI Akan Wannan Halin da Muke Ciki. Ina da Yaƙini Yanzun Ko Anjima Kai Koma Yaushe ne Taimakon ALLAH Zaizo Garemu." Wayyanan Kalaman Na Innarmu Sai Suka Kasance Kamar Wata Allaura ta Ƙwarara Gwaiwa ga Abubakar Hakanan Suka Samarmasa Da Wani Irin Tawakkali Maigirma Acikin Zuciyarsa. Bama Shi Kaɗai ba Har Abdul-wahab da A yanzun Yayi Ras! Kalaman Innarmu Sun Ratsa sa Balle Kuma Khaleesat da A yanzun Takejin ITACE SILAR KOMAI. Saidai da Zata Iya Duban Innarmu Tayi Mata Magana Da tace Mata, "Nima Ba Yin Kaina bane Innarmu SONEE SILAR KOMAI." Saidai Bazata iya ba Innarmu nayi Mata Wani Irin Ƙwarjini Hakanan Tana da Ƙima ta Surukuta A Gareta. Dan Haka Sai ta Ture ledar Fruit ɗin da Ke Gabanta Tamiƙe Tsam! Tanufi Waje. Duk Suka Bita da Kallo Batareda ko Wanen su Ya'iya Ce da ita Uffan ba. Hakanan Anrasa Mai Jarumta Tunkarata domin Tambayar Ainihin Abinda Yafaru. Ita Kuwa Khaleesat Bayan tafita Hannunta ta Wanke Kafin Ta Sanyo Arwallah Tadawo Tareda ɗaukar Sallayar Innarmu ta Shimfiɗa Ta Soma Sallah. Ajiyar Zuciya Abubakar Yasauke tareda Cewa, "Innarmu Bari Inje In Samo Maki Maganin."

"Tau Yayi Abubakar Bari inZo Muje daga can Ka Rakani ɗakin da Yayar Taku Take." Harta Sa Kai Zata Fice Sai Kuma Tadawo Tana Kallon Abdul-wahab da A yanzun Yakoma Kan gado Yalafe Tareda dafe Kansa da Hannu Idanun sa A Lumshe Shi ba Bacci Ba Kuma Shi ba A Farke ba.

Kawai Sai Innarmu takaɗa Kanta Kafin Tajuyo Gurin Khaleesat da Nufin Tayi Mata Magana Sai taga Bata idar da Sallah Ba Dan Haka Tabi Bayan Abubakar da Shi Tuni Yayi Gaba.


*********


Washe Gari Tunda Sassafe Dr Jabir Yahau Shirin Fita Gurin Aikin Nasa da Yakasance Yaune Rana ta Farko da Zasuje Suji Ta'inda Program (Shirin) Nasu zai Soma.


Dan Haka Maman Asharaf Tashiga Kai Kawo Dan Haɗa Masa Abinda Zaici Kafin Yafitan.

Ƙwai Ta Soya masa da Irish Sannan ta dafa Masa Shayi(tea) Nan inda yake Zaune Yana ɗaura Tie ɗin Coat ɗinsa da Yabi yalafe ɗas Ajikinsa Kamar dan shi Akayi Su. Takawo ɗan Madai-daicin Farantin ta'ajiye Kafin Kuma ta zauna Gefensa Tana Cewa "tau Food is Ready!" dubanta yayi Cikin Soyayyar ta dake Ƙara haɓɓaka Acikin Zuciyarsa Bakuma dan Komai ba, Sai dan Yanda Take Matuƙar Hidimta Masa kowane Lokaci Batareda Nuna ƙosawarta ba, Hakanan Kuma A Ko da Yaushe Tanayi ne Cikin Nuna Masa Zallar Ƙauna.


Ɗan Busa Masa Iskan Bakin ta Tayi Tareda Haɗa yan yatsunta Biyu Suna bada Sautin Ɗas! Ɗas!! Kana Tace, "Maigida Irin Wanna Nisan Zango Fa?" Firgigit!! Yayi Yana mai ƙara Kallon ta da Mayu Idanunsa Masu Matuƙar ƙwarjini Kafin Yasauke Wata Ƙatuwar Ajiyar Zuciya Gamida Cewa, "Eh Tau Ai keɗin ce Maman Asharaf Kullum Sai naga Kamar ƙara Maki Kyau A keyi, Ko Meye Sirrin?" Wal!! tayi da idanunta Cikin Jin daɗin Kalamin Nasa Saidai A Furincinta Bata Nuna Hakan ba dan Cewa Tayi, "HUBBINA Akwai ka da Zolaya Wani Sa'in wallahi." Yaɗan Sunkuya yaɗauki Kofin Shayin dake Ta Suracin Zafi Tareda ɗan Juya Shayin da ɗan Karamin Cokalin da ke Cikinsa Kafin Yakai Shayin Bakinsa Yana Kurɓawa A Hankali Kamar Bazai bada Amsar Maganar ba. Sai Yace, "Hummm! Haka Kike Tunani? Tau ɗauko Madubi Ki Gani Indai Zolaya Ce tau Nayarda A Hukunta ni ta Hanyar Ha....."


Ganin Zai Ɓaro Wata Magana Data Girmi Kunnen ta tai Hanzarin Taran Numfashin sa Da Cewa, "HUBBINA Lokaci Na Tafiya, Kuma Bacin Haka fa Bakyau Magana A Sanda Ake Cin Abinci."


Sarai Yafahimceta Maganar Ce Kurum Bata So, Dan Haka Sai Yamiƙe Yana Murmushi Tareda Yago Tisue ɗinda Cikin Kwalinsa Akan Center Table Yasoma Goge Bakinsa Kafin Yace, "Maman Asharaf Ni Naga Sanda Zaki Daina KUNYAR Nan Tawa Mutum Harda Albarkar Ɗa Amma Kuma Kamar Jiya Kika Zo Gidan?"

Maman Asharaf Batabi Ta Kan Zancen Nasa ba Madadin Hakan ma Flet ɗin Irish taɗauko Tareda Kosanto Shi tana Cewa, "Kai HUBBINA Yanzun Dan ALLAH Bazaka Ci Abincinan Ba Haka Zakaje Yunwa Ta Nakastamin Kai?" harararta Yayi Cikin Sigar Ƙauna Yace, "Anƙi Aci ɗin, Ni Nagane ɗuren Naki Harda Mugunta Acikinsa Wallahi."
Yanda Yaƙare Maganar Sai da Yabata Dariya dan Haka Cikin dariyar Tace, "Taufa Wace Mugunta Kuma daga Abun Arziki?"

"Ba Wani Abun Arziki Nagane So kike Nayi Ɓulele ta yanda duk Wadda taggani Tace Bata So...." Habawa Me Maman Asharaf Zatayi Inba Dariya ba dan Yanda Yake Maganar Kamar Wani Kwarkwasinu Yace, "Tau Nagane Wayo Naki daga yau Ai." Maman Asharaf Tace, "Kai Ai Yanzun Yammata Ma Sunfi Son Ɓulele In Baka Sani Ba In Baka Labari."

"Inji Wa?"

Tace "In Ji Su Yan Matan!"

"Tau Ban Yarda ba Sai Na Binceke Su Inji." Yafada Yana Ƙokarin Kwaikwaiyon Muryar ta. Dai-dai Lokacin Asharaf Yafito Falon Sanye da Kayan Barci Sai Mutsutsuke Ido Yake Alamun dai daga Bacci Yatashi Yana Zuwa Kuwa Ya Rarumi Kofin tea ɗayan Hannun Kuwa Yaɗebo Irish Zai kai Baki Ai da Zafin Nama Maman sa Ta Fisge Tana Faɗin, "Tau Acici Mala'ikun Tukunya Daga Tashi Barci Ko Brush Bakayi ba?"

Asharaf Ya Yamutse Fuska Zai Fashe da Kuka Yadubi Baban Sa Cikin Gwaracinsa Yace, "Dady Ce Momy Wunya Aji Tabani Tea." Dr Yadurƙusa Gaban Asharaf Yana dafa Kafaɗarsa Yace, "Sorry My Boy Zata Baka but Kabari Kayi Brush Kaji?" Asharaf Yagirgiza Kansa Cikin Tunzure Baki. Dr Jabir Yamiƙe Yana Faɗin "Yawwa My Boy Bakyau Cin Abinci Ba'ayi Brush ba Kaji." Yaƙarasa Maganar Cikin Sigar Lallashi Still dai Asharaf Sake Girgiza Masa Kan Yay, Dan Yaron Akwai Misƙilanci Kamar Baban Nasa. Dr Jabir Yazura Hannunsa Zai ƙarɓi Jakkar Labpton ɗinsa dake Hannun Maman Asharaf Ita kuwa ta Noƙe Tareda Cewa, "Muje Ai Sai Na Rakaka!"
Murmushi Yayi Sannan Yajuya Yanufi Ƙofa Yana Cewa, "Lalle Kam Gara kiyi da Kuka Inba Hakaba Turawa Nan Suyi Awon Gaba Dani."

Hannun Asharaf tariƙo Suka Mara Masa Baya Tana Cewa, "Taɓ! Su Sun Soma ma?"

"Tau Yi Wasa ki ga Yadda Zatayi Wuff dani Wallahi." Yakarasa Yana mai Taka Burki Bai Bata kuma damar Cewa Wani Abun Ba Yace, "Tau tsaya daga Nan dan Karwani Baturen Yaganki Yace Zai Maki Magana Nikuwa In Faskare Masa Kai."

Masu Karatu Zan ɗan Tsahirta Anan Muje Daku A Shafi Nagaba Tareda Alkalamin

FA'IK.
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 28 · 0% Book details