← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 12 OF 40

Chapter.....14

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


"Eh Ina Nufin keɗin Ai Yar Momy Ce Ko?" Dr Jabir Yafaɗi Hakan yana Mai Ƙokarin Sai saita Nutsuwarsa. Maman Ashraf Tadubeshi Cikin Salon So Tace, "Hakane Amma Ni Nafi Son Wancan Sunan da Kakemin Yafimin daɗi." Takara sa Cikin Shagwabar ta dake Kara mata kyau da Kuma Wani Irin Matsayin Acikin Zuciyar Dr Nata Yace, "Tau Angama NURUL KHALBI!" Tayi Murmushi Kafin Tace, "Da Meza ka Fara Abinci ko Wanka? " Yakanne Mata Ido ɗaya Sa'annan Yace, "Duka Bada su Zanfara Ba."


"Tau Dame Zaka Fara?" tafaɗi Hakan Cikin Yima sa Kallon Ƙasa-Ƙasa dan Bata Iya Jurar Kallonsa Cikin Ido Sai Taji Kamar Jiri Na Neman Kayarda Ita.


Shikuwa Dr Jabir Ashraf Yakalla da duk yabi Yaɗale Jikinsa Yana ta Wasa da Key ɗin Motar Dadyn Nasa da Sauran Gwalanci Irin Na Yara kafin yaɗago Yakallo Maman Ashraf ɗin Yana Yafito ta Tareda Cewa, "Zokiji!" Tamatso Yakama Kunneta Yana Raɗa Mata Magana Tayi saurin Rufe Fuska Tareda Saurin Miƙewa Tanufi Bedroom ɗinsa Tabarshi Yana yimata Dariya Shi kam.


*********


Cikin Kwanakinan Kwata-kwata Bana Tareda Sukuni tunda Muka dawo Asibiti Bana da Wani Aiki Daga Kwanciya sai Kwanciya Abinci Gashi Bana wani Cinsa Sai Innaga Yunwa Na Neman Yimin Lahni Sannan Insamu Abu Mai Ruwa Insha Nakama Wayoyina Duka Na Rufe Bana Mu'amala da Kowa da Komi Tun Abin Na ba Momy Haushi Tafita Harkata Harya dawo Bata Tausayi Tasoma Lallashina Saidai Duk-da Haka kwalliya bata biya kuɗin Sabulu ba Abin Kam Sai Yakoma bata Tsoro Takawo Ba mujiya Ta zuramin Bawai Kuma Dan Abin Baya damunta ba Sai dai don Tayi Duk Abinda Take Ganin Zatayi Amma Lamarin Ya faskara Gashi Dady Aiki Yarike shi Yana Son Zuwa Amma Ba Hali. Harma tagaji Da kai Masa Ƙorafi Shima Ya Nuradden Haka Dama Shi Bawani Cika Zuwa Yayi Ba. Sai Anɗau dogon Lokaci yake Zuwa Saidai Momy takudurce Matakin Ɗauka A Ranta Itakam Tagaji da Zaman Wanan Na nan Wannan na Can.


Da Sanyin Safiya ne, Misalin Karfe Bakwai Nasafe Momy Na shirin Fita Wurin kasuwancin ta Nikuma Ina Tsakar Gida Yau Nawayi Gari Da Sha'awar Cin Kwai Dan Haka Nafita Shago Nasiyo Na Sulala Ina Zaune Sunake Ci Kamar wacce ke Cin Magani Yayinda Momy keta kai Kawo Wajen Haɗa Kayan da Zata Fita Dasu. Almajirinda Ta ɗauka Aiki Yana Tai Maka mata Gurin Haɗa Abubuwan, Jefi-Jefi Muna ɗan Fira da ita duk dai Ƙorafi ne AKan Rashin Zuwan Dady. Wanda Acewarta bai taɓa daɗewa kamar ta irin Wannan Karon Ba.


Bayan Sun Gama Haɗa Kan Kayansu Taceda Sani (watau Almajirin dake Tayata) Yaje Ya Samo Musu Mai Kk Napep Tunda Haryanzun Wanda Yasaba Zuwa Ɗaukar Sun Bai zoba Kuma Takira Wayar sa Bata Zuwa. Sani Ya'amsa mata da Cewa "Tau."


Bai ɗau Wani dogon Lokaci ba Yadawo da mai Kk Napep ɗin. Yasoma Kwasar Kayyakin Yana fitar masu dashi Yayinda mai kk Napep ke Aikin Lodasu Cikin Kk Napep ɗin. Momy tadubeni Sanda Take Kokarin Fita Tana Cewa "Mu munje Sai Nadawo Yau Ki Girka Mana Shinkafa da Miya Zan bawa Sani Salat da Nama Yakawo."

Nayi Maza Nace, "Momy Adai sa Kifi Zaifi daɗi." Momy Tayi Saƙare Tana Kallona Dan Harta Manta da Rabon Ince Zanci Abinci Balle ince Ga Abinda Nake So Cikin Jin daɗin Sauyawar Tawa Tace, "Tau Yayi Zanbashi Yakawo Bayan Shi Akwai Wani Abu?" Nagirgiza Kai Gamida Cewa, "A'a Momy." Tajuya Tana Faɗin, "Tau Ni Natafi Sai Na Dawo."


"ALLAH bada Kasuwa Yakuma Tsare." Nabita da Wannan Kalamin.


Suka Fice tana Cewa, "Amin."

Bayan Fitar Tasu Na Kammallah Cin Kwai ɗinda Nakeyi. Nakwashe Kayakin kafin Naje Famfo Na Wanko Hannuna Nadawo Ina Gyashi Alamun dai Na ƙoshi Kenan. Nayi Hamdala Ga ALLAH Sa'anan Nasoma Haɗa Soket ɗin dake Falon Momy Ina Ƙokarin Kunna Tv Wanda Rabona Da Hakan Harna Manta.


Tashar Afrika tv3 Nakamo Naci gaba da Kallo Kafin Zuciyata Tayi Nisa Cikin Tunanin Farkon Haɗuwata da Abdul-wahab Cikin Azumi Gabda Shan Ruwa. Mukayi Sabo Mai Wuyar Mantawa Cikin Sauki. Na Soshi Sonda Bantaɓa Yiwa waninshi B, Muna Tsaka da Tunanin Cimma Burimu Su Momy Sukayi Mana SHAMAKI Tareda Taimakon Alhaji Saminu Wanda Babu Komai Tattare dashi Face Tsantsar YAUDARA Ni Atawa Wautar Momy Sun Hana mu Aure ne Saboda Bayada Kuɗɗi Nashiga Neman Kuɗɗi Wurin Manya Alhazai dan Nabawa Abdul-wahab Yasamu Yatsayu da Kafafunsa Kamar Yadda Momy harma da Tasa Innar Ke Cewa Shi Kaɗai ne Matsalar sa da zata sa Ba zaiyi Aure ba A Yanzun, Amma Bayan Nasamo Nazo In Kawo masa Cikin ɗaukina Shikuma yatareni da Mummunan Fahimtar da Yamin Harda Sharrin Cewa Ni MAYAUDARIYA CE Wanda Ko A Wancan Lokacin Nayima Sa Abunda Nayinne Saboda Samun Cikar BURIN RAINA Bawai dan Ina Nufin shi da Hakan ba Har Raina ba. Na Saɓawa Iyaye na Akan Hakan Na Saɓawa Mahallici Na Akan Hakan. Duk-da Bawai Nasaida Mutumci Nawa Na ƊIYA MACE Bane Amma Na YAUDARI Dayawa daga Cikinsu Ƙarshe dae duk BURINA Bai Cika ba Hasalima Wanda Nayin Dominsa Kallon MAYAUDARIYA Yakeyimin. Wasu Hawaye masu Zafi Suka Shiga Silalowa daga Cikin Kwayar Idanuna Zuciyata Namini Wani irin Zafi Dole Nadafe Zuciyar Tawa Ina Mai Kiran sunan ALLAH dan Neman Taimakon Sa. Babu Shakka Sai Yanzun Nagano Bangina Nawa BURIN kan Adalci ba Dan Haka Dole ne Nima naga Tawa SAKAYYAR Tunda daga Cikin Wayyanda Na YAUDARAR Harda Wayyanda Nayiwa Alkawalin Cewa Zan Aure Su Amma daga baya Na Tuɓure musu Shin Su Nasan Halinda Na bar Zuciyar su? Lalle Nayiwa BURINA Ginin TUBALIN TOKA Dan Haka Nine SILAR KOMAI Ba SONE ba dana ke Zargi.

Kaiconah! Kaiconah! Yanzun Wa Gari Waya? ga Kuɗin Nasamu Amma Wanda nanemesu Dominsa niɗin ma baya da Lokacina balle kuma Su Kuɗin dana Sama daga Abokan Hamayyarsa dayake Ganin dasune Nahaɗa baki Naci Amanarsa.


Babu Shakka Sai Yanzun Nagano Wautar dana Yi A Rayuwata Babu kuma Dalilin gyarata. Haka dai Nacigaba da Saƙar Zuci Tareda Ci gaba da Kuka Marar Sauti Har'izuwa Sanda Naji Sani Nakwaɗa Sallama A Tsakar Gida Nayi Maza nagoge Hawayen Fuskata Kafin Namike Nafito ina Mai Kokarin daidai ta Nutsuwa ta.

Yamiko min Leda "Ga Cefanen Inji Momy." Nakarɓa Ina Faɗar "Tau Yayi Sani." Zai Juya Kenan Saiga Sallamar Dady Aiban Sanda nayi wurgi da ledan Hannu Na ba Natare shi Cikin Murnar Muka Rankaya Cikin Falon Momy Sai Surutu Nake Masa Yayinda Yaran Unguwa Suka Soma Shigowa da Kayansa Sani Na tayasu.


Naciko Jug da Ruwa Masu Sanyi Nahaɗo da Ɗan Karamin Kofi Natsiyayawa Na'ajiye Gaban sa ina Mai kara Yimasa Sannu da zuwa. Shikuwa Yana Amsawa Tareda bina da Kallon Mamakin yanda duk Nafyaɗe Na Rame Kamar Ba Ikram ɗinsa ba, ƴar Duma-duma Yasanya Hannu Cikin Aljihunsa Yaciro Kuɗi Tareda Miƙawa Sani Yace Suje Yaraba masu Suda Sauran yaran da Suka Kwaso mashi Kaya Cikin Murna Suka Amsa Suna ta Zuba Godiya. Naje Na buɗe Tukunya Natarar Akwai Sauran Ɗumamen da Momy Tayi Nazubo Masa Cikin Kula Nakawo harda Cokali Na'ajiye Masa.


Dady yace Kawomin Roba In wanke Hannu na Ni kinsan Nafison In Sa Hannu Fa.

Nakawo Ina Cewa, "Aikam yafi Dady Dan Shine Sunnah!"

Dady Yabuɗe Kular Tareda Cewa, "Masha'allah Kamar Kinsan Ina Tafe Ina Tunanin Ɗumamen Momynku Nayi Missin Nasa Sosai." nakyalkyale Dariyar Dady Ina Cewa, "Tau Dady Sai Gashi Katarar Yanzun kam Sai Kayi Iya Yinka Ko?" yace, "Aikam dai. " Nace, "Dady Ina su Umman Adamawa dasu Jamila?" Watau Matar Dady Ta Can Da kuma Ɗiyan ta.


Dady Yakai Lomar Tuwo Mai laushi Da Sulɓi Tawuce Tacikin Makwogoronsa Yana Tantance Tsakanin Tuwon da Miyar Wanne Yafi daɗi? Kafin Yadubeni Yace, "Suna can, Suma Kuma Suna Kewarki." Ina Murmushi Nace, "ALLAH Sarki! Umman Adamawa Nayi Missin ɗinta Sosai itada Su Jamila."

Dady Yace, "Ba Wani Nan Ai da kinbini Munje, Ni Har Bana Tuna Ma Yaushe Rabon Kije Har Umman Taku Na Tambayata Kotayi Maki Laifi ne? Nace Mata May be dai Kin Soma taya Momyn taki Kishine Kamar Yayan Naki Nuradden." Na Ƙyalƙyale da Dariya Gamida Cewa, "Kai Dady Wane Kishi Kuma? Bandai Samu Naje Bane Shima Ya Nuradden Ba Kishi Yake Taya Momy ba Irin dae Tasa Rayuwar Kenan Ta Rashin son Zumunchi Tunda Ko Wasu daga Cikin Ƙannen Momy Sun Shaida shi Da Hakan." "Haka Naji Lauya." Dady Yafaɗi Hakan Yana mai Ƙokarin Tsiyaya Ruwan dake Cikin Jug zai Sha. Cikin Dariya Nace, "ALLAH Dady." Yace, "Tau Naji. Momy Taku Tana Wurin Kasuwancin Nata Ne?"

"Eh Dady." Na'amsa Masa Ina Kokarin Harhada Kayan da Yaci Abinci Da Nufin Kaisu Kitchin.


Yace, "Ok Kwanaki Kinyi jin jiki Har Asibiti Kukaje ko?"

"Eh Dady Baka Gani Ba Kaidai Kamar Zan Rasu." Yace, "Ba Wani Nan Raki dai Ne dake Harkika Tashi Hankalin Momy taki da Itama Tafiki Birkicewa." Yakarasa Maganar Cikin Sigar Wasa. Dan Haka Sai Nayi ta Dariya Naɗauki Kayan Nafito da Su Tsakar Gida.

Zuwan Dady yakwashe kaso Mafi Yawa daga Cikin Damuwar Danake Ciki Saboda Yajanye Hankalina Da Hira. kasancewar Dady Irin Iyayen Nan Ne Masu Sauƙin Kai Wa Ƴayansu. Inkaji Yana hira Damu Sai kace Ƙannensa ne ko Wasu Abokansa Hakan Yasa Akwai Shaƙuwa Ta Haƙiƙa Tsakani mu Dashi Wannan ma yasa da yawa suke Ganin Yasakar Mana Dama muke Abinda Muka So! Kuma Naɗaya Daga Dalilin Yan Uwansa Naƙin Aure Momy Acewarsu Musulma ce Saidai Bai wani Sha Mata kai ba. Nikaina Nasani Abinda Muke Mukswashe Lafiya ɗiyan sa Dake Adamawa Bazasu Soma Ba.


Karfe 1:30pm Na Rana Lokacin ma An Soma Sallar Azuhur A Wasu Massalatan Yayinda Wasu Massaltan Lokacin Suka Soma Kiran Sallah. Har Nagama Abincin Rana Ina Yanka Salak Ne, Shikuwa Dady Yayi Arwallah Yaje Massalaci. Momy Tashigo Sani Da Sauran Yaran da Suka Tayashi Kwaso Mata Kaya Suna biye da Ita.

Suka'ajiye Kayan Inda Suka Saba Ajiyewa Kafin Ta Sallami Sauran Yaran Yayinda Tace da Sani Yajira Azuba Masa Abincin Rana In Na Kammallah kam. Dai-Dai Lokacin Kuma Nafito Kitchin dayan Hanunna Riƙe da Yuƙar danake Yanke Salat Dayan Kuwa Ina Rike da Salat Dake Cikin Kwando Nai Mata Sannu Da Dawowa Tareda Shaida Mata Dady Fa Yana gari Yadawo. Tanemi Guri Cikin Matukar Gajiya Ta Zauna tana Cewa, "Eh Kam Ai naga Alama Tun daga Fara'ar taki Ƴar Dady Sani Kuma Yagayamin."

Nayi Murmushi Gamida Cewa, "Dady Wannan Karon Zuwan Bazata Yayi Mana." "Ai kam dae! Ga Ƙullon Dana Rago Nan, Yau Bazan Koma Ba dan Haka Maimaikon Abincin Dare Sai Ayi Alala dashi."

"Yauwa Momy Kamarma Kinsan Ko Ina Sha'awar Cin Alalan."

"Ai Fa Yau Komai Sha'awar Ci Kike, ga Alama Kuma Kina Fanshe Kwanakin Da Kikayine Kina Yajin Cin Abinci Na Ba Gaira ba Dalili."

"Kai Momy Wane Yaji Kuma?" Nafaɗi Hakan Cikin Shagwabar da Nadaɗe Banyi Mata Irinta ba Kafin Nadubi Sani Dake Can Gefen ta Zaune Ina Cewa, "Sani Zo Ka zuba Min Ruwa In Wanke Salat ɗinnan Inyi In Sallameka."

Sani Yasoma Zuba Min Ina ɗaureyewa daga Can Momy Tana Cewa, "Gaskiya kam Yasamu Yashiga Makaranta da Wuri tunda Yau Bamu Samu Mundawo Ma Da Wuri Ba." Ana Haka Dady Yashigo Gida Nan Suka Gaisa Da Momy Yawuce Falon Kafin Momy tayi Arwallah Azuhur Ta Nufi Dakin Ita ma.

=========


Duk Yanda Yaso Yin Watsi da Lamarin Yar Momy Abin Yacutura! Komai Yakeyi Ƴar Momy Ce ke ta Kai Kawo Acikin Ransa! Ko Yanzun da Yake Cikin Office ɗinsa Saman Kujerar daketa Juyi dashi Idanuwansa A Lumshe, Ba komai Yake Tunanin ba Ilai Ita. kyakyawar Fuskarta, Zara-Zaran Yan Yatsunta, Yanayin Shagwabar ta Da kuma Miskilanci ta Wanda Itace Macce Ta Farko Da Yataɓa Haɗuwa da ita Batareda ta nuna Kyaun shi Yaburgeta ba Kuma Tayi Masa Miskilanci.


A gurguje Yakamallah Aikinsa Kafin Yayiwa Motarsa Key Yadamƙi Hanya.

Lokacin Karfe 5:30pm Tagota Sanda Ya'isa Shiyyar (Unguwar) Tasu Khaleesat Kafin Yashiga Tambayar Tsirarun Mutanen da Yake Haɗuwa Dasu Inane Gidan Su Khaleesat.


Yaɗan Sha Wahla Kafin Yagane Gidan, Kafin Yafito daga Cikin Motar Tasa Yana Rabon Idanun Ina Yaron da Zai Aika Cikin Gidan Zai Ɓullo. Yajingina da Motarsa Tareda Fito da Wayar sa Yana Latsawa. Cikin Ikon ALLAH Sai ga Yara Suna tasowa daga Islamiyya dan Haka Yakira daya daga Cikinsu Ya'aikesa.


Lokacin Niɗaice Tsakar Gida Ina Wanke-Wanke Su Momy kuwa Suna Falo Itada Dady Sun Ɓarke da Firar Bayan Rabo Har Ina ɗan Tsokanarsu da Cewa "Tsoffi Anyi Missin ɗin Juna." Momy tajefo ni da Pillon Kujera Lokacin da Nake Maganar Tareda Cewa, "Kin Maida Mu Kakkanin Ki ko?" Ina Samun Sa'ar Kaucewa Filon da tajefo ni dashi Sai Nayo Waje Nabarsu Sunata Dariya.


"Salamu Alaikum." Sallamar Yarinyar Takatsaemin Tunanin Danake Naɗago Kaina Ina Amsa Sallamar Kafin Nace, "Sajida (Yar Makwabtanmu ce) Antaso daga Makarantar?" Tagyda Kai Gamida Cewa, "Eh Aunty Wai Wani Ne Awaje Yake Sallama."


"Wayace Maki Yana Nema?" Natambaye ta Ina maida Hankalina Gareta.


Takwaso Yamin Baki Irin Nasu Na Yara Da Cewar, "Im! Um!... Baice Kowa... ba."

"Tau Je kice Masa Ana Zuwa." Nafaɗa Ina Kokarin Mikewa Daga Wanke-Wanken Danakeyi Na ɗaureye Hannaye na Sa'annan Na Nufi Falon Momy Tareda Gayawa Dady Cewa, "Wai Wani Na Sallama A Waje."

"Wani?" Dady Yamai mai ta Maganar Cikin Mamaki dan Banda Makwabtanmu Na nan Kusa baiyi Waya da Abokansa Ko ɗaya kancewa Yana Gari Ba.


Nagirgiza Kai Gamida Cewa, "Yanzun Sajida Da'aka Aiko Tafita."


"Okey Bari Inga kowaye." Yafaɗi Hakan Yana Ƙokarin Sa Hullarsa Da Yajawo Saman Kujera. Daganan nima Na Juya Naci gaba da Wanke-Wanke Da nakeyi. Ba'a Jima ba Saiga Dady Yadawo Dai-dai Lokacin da Momy Taleƙo Daga Falon Tana Cewa, "Yakamata Ki Duba Alalar Nan Fah!" Na'amsa mata da Cewa "Eh Yanzun Nake Kokarin Zuwa In duba."


Dady Yace, "Ashe Dr Jabir ne Na Asibiti FA'IK Hospital Ikram kije Yana jiranki." yana gama Gayamin Yashigewarsa Falo Yabarni da Bin Bayansa da Kallo. Inajin Sanda Momy Ke Tambayar sa "Meye Halan?" Banji Amsar Da Yabata Ba Saboda Sun Isa Cikin Falon. Naɗan Jima Cikin Nazarin Kila wa Ƙala Kafin Nasamu Kwarin Gwaiwar Mikewa Najawo Hijabi Na Dake Kan Igiyar Shanya Nasaka Nafita Zuwa Wajen. Yana Cikin Mota Zaune Kafarsa ɗaya A Waje Waya Yakeyi da Wani. Sanda Na'isa Gurinsa Ina Masa Sallama Yaɗago Kansa Yana Murmushi Batareda Yacemin Komai Ba Kafin daga can Yace ma Wanda Suke Wayar, "Bro Zamuyi Waya Anjima." Batareda Yajira mai Zaice Ba Yakatse Wayar Sa'annan Yadubeni "Shigo Ciki Mana."

"Nan ma Yayi." Nafaɗi Hakan Ina Mai girgiza Kaina.


"Ƴar Momy Daru ko?" Yafaɗi Hakan Yana Mai Kallona. Nidai Ban Tofa Ba Madadin Hakan ma, Sai Nagyara Tsayuwa ta Tareda Harɗe Hannaye na A Kirji.

"Yazanyi Tunda Ni Nakawo Kaina?" Yafaɗi Hakan Gamida Fitowa daga Cikin Motar tasa Yajingina Gareta Yana mai Cigaba da Kallo na Kafin Yace, "Ƴar Momy Bata Iya gaisuwa Bane?"


"Ina Wuni." Nafaɗi Hakan Cikin Zumburar Baki.


"Bana so Tunda Sai da Na Roƙa."

"Kayi Hakuri!" Nasake Faɗa Cikin Salon Shagwabar da Bansa Ina na Koyo ta ba.


"kayi Hakuri!" Shima Yamai mai ta Abinda Nafaɗi. Kuma duk Mukayi Dariya Ni Dashi...........


Tau fa Meke Shirin Faruwa Ne Masu Karatu? Hummm Akwai BADAKALA Taƙin Karewa kamar Yadda Nasanar da ku Cakwakiyar Na Can Gaba Da Nake da Ƴakinin cewa da Mai Karatu Yasan KALART? Tau da Zai Cika da Ɗaukin Jinta Sai dai Yanzun FA'IK Ne Kawai Ke Cikeda Ɗaukin Sanarda Ita ga mai karatu dan Haka Muje Zuwa dai...............
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 12 · 0% Book details