← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 11 OF 40

Chapter.....13

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Abdul-wahab Kuwa Tunda Yasamu Bacci Yaɗaukeshi Bai Farka ba Sai da Yamma Lis! Innarmu Ta kyaleshi ne Yayi Bacci Saboda yasamu Hutun Kwakwalwa da Gangar Jikinsa. Koda Yatashi Tana Tsakar Gida Tana Sanwar Girkin Dare Tadubeshi Sanda Yake Fitowa daga ɗakin Nata Yana Hamma Tace, "Katashi?".

"Eh Innarmu Shine Ba'a Tasheni Nayi Sallah Ba?" Abdul-wahab Yafaɗi Hakan yana Yamutsa Fuska Alamun dae Baiji daɗi ba Anki Tashin sa yayi Sallah.

Innarmu Cikin Kulawa Tareda Tarin Ƙauna da Akasan Kowace Uwa Dashi Ga Ɗanta Ko Yarta Tace, "Abdul Ai Lalura ce Tasa Ko? Ya Jikin Naka Yanzun?"

"Da Sauki Innarmu." Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Yana 'Yar Miƙa Irin dai Ta wanda Ya Tashi Da Bacci.

"Jeka Kayi Sallar Ga Kunun Tsamiya Na Dama Ma."

Yanufi Ɗakinsu Yana Cewa "Tau Yayi Innarmu Yau Mekuka dafane Da Rana?"


"Shinkafa da Wake Ne." Innarmu Ta'amsa masa. Yace "Kai Amma Naji Daɗi Gaskiya ALLAH yabar Mana ke Innarmu Mu Kaɗai. " Innarmu dai Murmushi Kawae Tayi.

Wanka Yayi Sannan Yayi Brush Kafin Yayo Arwallah Yarama Sallolin da Suka Kufcemasa Bayan Yagama Yafito Yasami Innarmu Tashirya masa Komai Har Kwai da Kwai (Awara) Ta'aika Ansiyo Masa Dan Tasan Indae Zaici Shinkafa Da Wake Tau Ƙa'idar Sa ne Sai Yasa Awara Aciki.

Yazauna Yasoma Cin Abincinsa Cikin Kwanciyar Hankali da Nutsuwar Zuci Wayanda Yaɗan Rasa Acikin Yan Kwanakinan Yanaci Suna Fira Da Innarmu Wacce Mafi Yawanta Akan Aunty Su Ce.


Suna Taren Har'aka Kira Sallar Magarib Lokacin Innarmu Harta Kammallah Girkin ta Suka yi Arwallah Tare Innarmu ta tayarda Tata Cikin Gida Shikuma Abdul-wahab Yawuce Massalaci Bayan Fitowar Sallar ne Suka Haɗu da Su Abubakar. Suka Shigo Gida Taren Amma Ko Inda Yake Abubakar Bai Kallah ba. Abin Yamasa Ciwo Sosai Yalura Daga Sanda Suka Samu Saɓanin Kwata-kwata Abubakar yaɗauke Masa Wuta Dan Haka Yanzun Suna Shigo Wa Yasoma Yima Innarmu Maganar, "Innarmu Dan Autanki Gaba Yake Dani."
Innarmu Tatsaya Daga Abinda Takeyi Tace, "Gaba Kuma? "

Abdul-wahab Yasamu Kusa da Ita Yazauna Yana Cewa, "Gaba ko Innarmu Saidai Ni ne Mai Laifin Dan Haka Natuba A Shirya mu."

Innarmu Tadago Tana Kallon Abubakar dake Can Kusada Yar Karamar Tv Innarmu Tashar Rtv (Gidan Talabijin Na Jahar Sokoto) Yake Ƙokarin Kamowa "Kaji Abinda Yayanka Yace Dan Haka Batareda Nabi Ba'asi Ba Nace Abar Komai Yawuce Kayi Hakuri."
Abubakar dae baice Ƙala ba, Madadin Hakama Sai Yanemi plet Yazubo Tuwo Yazauna Yasoma Ci Abinsa gefe ɗaya yana mai Kallon Labaran da Rtv Ke Gabatarwa Karfe 7:30pm.

Yaɗago Yana Cewa, "Innarmu Kinga ni Ba Dama Nagayamaki Matsalar Wutar Nan da'ake Fhama da'ita kawai Gwamnati Bata Sa Baki Bane Amma Yanzu data sa Kinga Komai Yagyaru." Kafin yasakeɗibar Wata Loma Yakai Bakinsa. Zakin Miyar datasha Maggi da Daudawa nakai masa Har Kunne A Ransa Sai yabon daɗin Girkin Innarmu Yake. Cikin Al'ajabi Innarmu Take Kallonsa Kafin taɗora Da Faɗin, "Amma Ai Auta Kana jin Maganar danake Ma Ko?"

"Naji Mana Innarmu." Abubakar Ya'amsa Yana Mai Cigaba da Bawa cikinsa Hakkensa.

"Tau kuma Shine Kawani Shareni?" Innarmu ce ke Wannan Maganar. Abubakar yace "Tau Innarmu Yi Hakuri Andaina Insha'allah." Innarmu tayi Kwafa Kawai Kafin Tamike Tana Saka Carbinta Kan Ƙofar ɗakin. Tareda dubin Abdul-wahab da Yarafka Tagumi Yatsurawa Tv Ido Azahiri Kamar Kallon Yake Amma Ainhin Gaskiyar Hankali da Tunanin sa duka Basa Nan. Tace, "Kai Bazak Ci Tuwon Bane?"

"Zanci Innarmu Amma Sai Anjima Nida Nagama Cin Abincin Yanzu? Adai Kwai Kunun Aya?"

"Babu shi Dan Yau Duka Aka Saye." Innarmu Take Mayarwa da Abdul-wahab Amsa

"Tau Kuma Dan ALLAH Innarmu Saiki Saida Duka? "

"Kajimin Ɗa! Tau Kuma Sai Inƙi Kuɗi Ina ganinsu Meya hana Kabada Kuɗin Su Kace A ajiyema?"

"Tau Aini Banɗauka zai Ƙare Bane Dan Naga Ko Jiya Da'akayi andawo Dashi Kuma Nan Cikin Frij Yana Cike."

"Oh So Kake Kullum Nayi Tsimbo(Ba'a siyarba) Ko?" Abdul-wahab yayi Maza Yace, "A'a. bahaka nake Nufi Ba Innarmu." Innarmu Tace, "Tauwo Koda Naji, Nan da kake Gani Fa Tariya Nakeyi Daga Yanzu Zuwa Sanda Bukinku Zaitashi Saidai Kawai Aga Ina zaro Abina Ina lalurorina Batareda Na Nema Na Rasa ba. Banida Burinda Yawuce In Haɗa Aurenku Kaida Ɗan Auta Inga Kunkama Gidajen Kanku Kunfi Karfin Bukatar Ku Daganan Nikuma Zan Komawa ta Cikin Yan Uwana In Zauna. Shi kenan ALLAH Yacika Mani Burina!"

Anan Kuma duk Sai Jikinsu Yayi Sanyi Ba Abdul-wahab ɗai Da'ake Hirar dashi Ba Harda Abubakar dake Can Gefe Yana Sauraro Dan Haka daga Can Yace, "Innarmu Ki Koma kuma cikin Yan Uwan ki Kuma Tau Mu Meye Amfa..." "A'a Nafison Komawa Mahaifata Kusa da Yan Uwa na Koda Kuka ga Nabarosu Nadawo Nan Saboda Ku Ne Ina Son Rayuwarku Ta Inganta Bana Son Wani Yatakura Maku Inga kuma Kun Samu Karatu Na Isilama da Boko Wanna Kuma ma Shine Burin Mahaifinku Har Yakoma ga mahallincinsa Ko Safiyar da Zai Rasu Mun Tattauna Wannan Maganar dashi Kuma Alhamdullah Ko Yanzu Yadawo Zaiyi Alfahri Burin mu Yacika Wanda Ni Nasani Ba Jajircewa ta bace Face Taimakon ALLAH danake Nema Ba dare ba Rana kuma Alhamdullah Ina Ƙara Godiya Ga ALLAH."


Duk Jikinsu Yayi Wani Mugun Sanyi Da Wannan dogon Jawabin da Innarmu Ke Kwararo Musu Dan Haka Cikin Kasalar Jiki Abubakar Yataso yajingina Ga Jikin Innarmu Yana mai Cewa, "Nikam Innarmu Bazan Taɓa Zama Inda Bakinan Ba Duk Inda Naje Muna Tare." Cikin Zolaya Innarmu Tace, "Inkuma Matarka Bataso Fah Kasan Yayan Zamani Yanzu Ba Jituwa Sukeyi Da Surukai Ba Fa?" Abubakar Yace, "Innarmu Ba'ahaifi ɗiyar da Zan Aura tace Bata fi Son ki Sama Daniba Wallahi Bazan Zauna da Ita ba."

"Kaidai Auta Banda Cika baki Fah?" Innarmu Tafada da Nufin kawar Musu Da Alhinin da Tasa su Takuma Yi Nasara dan Dukansu Saida Suka Dara Barin ma Abdul-wahab dake Can Gefe Cikin Tunanin Waɗɗanan Kalaman Na Innarmu Kamar Tsumagiya ne A gareshi. Shi dayake Kokarin sarayar da Wannan Kokarin Na Innarmu Harma Ashe da Mahaifinsu Mai Rasuwa Akan Wata Banzan Soyayyar Tashi marar Makama da Tushe! (Anashi Tunanin Fa?) dan Haka Sai Yakara jin Cewa Tabbas Abubakar yafishi Gaskiya Shine dai Yattabata Sakarai!

Dan Haka da Karsashinsa Yataso Yarumgume Dan Uwansa Yana Mai Cewa "Autan Innarmu Nayarda da Abinda Kake Kokarin Nunami Dan Haka Kayafemin Da Mar...." Abubakar yayi Hanzarin Rufe Masa Baki Dan Baya Son Innarmu Taji Meyafaru Yace, "Yi Shiru Ya Abdul, Komai Yawuce Insha'allah! Nima Kuma Kayafemin Maganar da Nagayama dakake Ganin Kamar Raini Ce A Gareka." Cikin Kaunar dan Uwan Sa Abdul-wahab Yake Cewa, "Daina tunawa Komai Yawuce Kaji?"

Innarmu Tasa Hannunta Tana Mai ɗauke kwallar da Ta taru A Idanunta Tareda Cewa, "Ya'isa Ai, Sai Kutashi Kuje Sallah Kar Jam'i Yakufce Maku Dan Kunji Har Anfara Iƙama." Tare Suka Mike Suna Haɗa Baki Gurin Cewa, "Yanzu Kuwa Innarmu." Kafin Suka Fice Suna Masu Share Hawayen da Suka Zobo Masu. Itama Innarmu Suka barta Cikin Mutuwar Jiki Kafin Tayi Karfin Halin Mikewa Izuwa ga Sallayarta Ta Kabbarta Sallar Ta Isha'i.
(Ni Kaina FA'IK dake Laɓe Ina Ɗauko Maku Rahoton Sai da Nashare Hawayen Sbd Burgewar Wannan Familyn Ina mai cike da kwaɗayin Kowane Family yazama Irin Nasu.)


********

La'asar Ce Sakaliya Rana ta tafi Zata Faɗi, Gari Yaɗanyi Sanyi Sai Manyan Bishiyoyi daketa Reto Suna Kaɗa Wani Iska Kaɗan-Kaɗan duk-da kuwa yau Ankwallah Rana mai Zafi wanda Dayawa Suka Yi Hasashen Za'a Samu Ruwan Samane Kasancewar Dama Ana cikin Yanayine Na Damana.
Acikin Katafariyar Asibitin FA'IK Hospital Dr Jabir ne ke fitowa daga Office ɗinsa wuyansa Saƙale Da Microscop Yayinda Gefe Ɗaya Yake Rike Labcoat (Fara Rigarsu ta Likitoci) ɗinsa A hannu Yana Tafiya Amutakar Gajiye Ya'iso parking space ɗinsu Rumfar da Suka jere motocinsu Yadanna danna remot ɗin motarsa Tayi ƙara Kafin Yasa Hannu Zai Buɗe Amma Sai Yadakata Yajuyo yana Kallon Nas ɗin da Ta'iso Gurin Nasa tana haƙi Tareda Cewa, "Dr Ka'oje Dan ALLAH kazo Kayi Attanden ɗin Wata paceint Wallahi tana Bukatar Taimakon Gaggawa."

Yayi Tsam da Ransa Yana Kallonta kamar Bazaiyi Magana ba Kafin Yace, "Nas Zainab Wannan wane Irin Rashin Imanine Kuke Nunamin Tun Shabiyu Jiya Nabaro Gida ina cikin Asibitin Nan Ina Aiki da nawa da wanda ba Nawa ba Duk dan Taimako Still Yanzu Zankoma Gida Kuce kuma Yanzu Nazo nayi Wani Attanden Nimafa Ina Bukatar Taimakon Nan kuma Akwai Iyalina Gida Dasuke Suma Bukatar Taimakon Nawa ta Hanyar Basu Kulawa." yatsaigata Yana mai Sauraro daga Nas Zainab Yayinda tai Ƙasa da Kanta Tana Fhamar Ambata Masa "Sorry."

Yace, "Ba Maganar Sorry Bace Maganar Amin Adalci ce Nima. Ina Dr Jabo Yake Ne?"

"Yanzu Yafito daga Teater Yaje Massalaci Sallah?" Nas Zainab Tafaɗa tana Mai Rusunar da Kanta Ƙasa Tana Mai jin Bazata Iya Jurar Kallon Sihirtattun kyawawan Idanunsa ba.


Yaɗan Dafe Goshinsa Alamar Tunani Kafin Yace "Tau Dr Gwadabawa Fa?"

"Yana nan!" ta'amsa mashi A Taƙaice.

"Meyake Yi Shi?" Yasake Jefo Mata Tambaya.


Nas Zainab Tagaji da Amsa Wayyanan Tambayoyi Jikinta karkarwa Yake Mutumen nan Yanada Matukar Kwarjini da Haiba da kamala Da Kyawun da Kowace Ya macce Zata yi Sha'awar Yazamo Abokin Rayuwarta Batada Burin da Yawuce Itama tazamo Cikin Sahun Matansa Ita Ko Amatsayin Ta nawa zai Kata Tana So Wallahi Shiyyasa ma Yanzun Da'aka ce Akirasa Tayi Azarɓaɓin Cewa Itace Zata Kirashi Tau Gashi Kuma Tana Gabda Yin Nadama Akan Wayyanan Tambayoyin Da Yatasa ta A Gaba Yana yi Mata Kamar Wani Ɗan Jarida.
Shidai Haka Yake da Baiwa Kowane Aiki Inzaiyi Sai Kaji Kamar Shi Yakaranta Kuma Yafi Dacewa Das....."
Tunanin ta Yakatse ne Sanda Dr Jabir Yashiga Karkaɗa Mata Makullayen Motarsa A Fuskarta Tareda Cewa, "Heyyyyyyy Nas Zainab Are U Okey?"
Tayi Wani Irin Firgigit Tare da Cewa, "Afuwant Dr."

Yace, "Ina Tambayar ki Meyake Yi Shi?"


"Eh... A'a Shi.... Shi Yanacin Abinci ne Sai Yace Inje Gaka can In Kiraka tun Kafin Kawuce."


"Tau Kice Masa Koda Kikazo Nawuce Baki Sameni ba." Dr Jabir Yafaɗi Hakan Yana mai Faɗawa Cikin Motar sa Yarufe Tare da Bata Wuta Yawuce Yabar Nas Zainab Tsaye Tana Mai Bin Sawun Motar Tasa Da Kallo
"Tau Kice Masa Koda Kikazo Nawuce Baki Sameni ba." Tasamu Kanta Tana Mai Mai-maita Abinda Yace Tareda Kwaikwayon Muryar sa. Kafin Taɗaga Hannu sama Tana Adu'ar "Ya ALLAH Kamallakmin Wannan Gay Amatsayin Mijina." Tadafe Saitin Zuciyarta Tana Lumshe Manyan Idanunta Tace, "Wow! Gaskiya Dana Caɓa." Tana Juyowa Sukayi Ido Huɗu da Nas Asma'u Tana Cewa, "Nas Zainab Lafiya Naganki Anan?" Suka Rankaya Ward ɗinsu Nas Zainab Nasanar Mata Wanda Tazo Kira Nas Asma'u Tace "Wannan Uban Miskilanci." Nas Zainab Ta'amsa Mata dacewar "Shifa!"

Nas Asma'u Tace, "Sai dai Nan dakike Ganinsa Akwai Kirki dakuma Tausayi Fa."

Antaɓo Ma Na Zainab Inda Ke Mata Kaikayi Dan Haka Da Ɗokinta Tace, "Ah Wannan Kam Ai Duk Asibitin FA'IK Hospital Ba Kamar sa."


"Shiyyasa Ko da Yaushe Nake Ta Adu'ar ALLAH Yasa Da Rabon Yazama Mijina dan Irinsu Miskilai Dakike Ganin Nan Akwai Iya Tattalin Iyalinsu Zasu Sha Soyayya. " Jin Wannan Furucin daga Bakin Nas Asma'u Sai Nas Zainab Tahaɗe Girar Sama da Takasa Aranta Tana Cewa, "Kaji Munafuka Tau Kada ALLAH Ya'amshi Adu'ar taki." Da Wannan dai Hirar Tasu Ta Ƙare Har Suka zo Inda Zasu Rabu Nas! Zainab Ta Tafi Isarda Sakon Aikenta Itama Nas Asma'u Tashiga Hall ɗin Ɗakin da Majinya Ta Kwance Birjik Tanufi Teburen da Suke Zama Tana Gaisawa da Mutanen Ɗakin...


Dr Jabir Kuwa Tuki Yake Cikin Wata irin Kasala dake Taso masa Tun Daga Kasan Zuciya Har'izuwa Ruhi da Gangar Jikinsa Komai Yakeyi Fuskar Ɗiyar Momy Keta Masa Gizo Bai Taɓa Haɗuwa da Macce Mai Kyaun Tsari Da zubi Ba Irin Nata Duk-da Kuwa Kansacewar Sa Likitan Mai Cuɗanya da Al'umma daban-daban.

Yakai Hannunsa Yashafo Kansa Yana mai Lumshe Idanuwansa Kafin Yaɗan Furta A Fili "Ya ALLAH Ka Kawo Mani ɗauki." Yajawo Wayarsa dake ta Ɓurarin Neman Ceto Sai Yaga Sunan Dr Gwadabawa Ne Keta Yawon Kan Fuskar Wayar Tashi Yayi Tsaki Yana maida Wayar Kafin Yace "Saidai Kunemi Wani. "

Ƙara Wayar Tasake Yi A Zatonsa Dr Gwadabawanne Dan Haka Bai Kula ba Sai da Tasake Ring Sannan Yamiƙa Hannun Cikin Ƙufular Indae Dr Gwadabawane Zai Caɓa Masa Magana Amma Sai Yanemi Fushin Yarasa Saboda Sunan da Ke Yawo kan Wayar 'NURUL KHALBI! ' Abinda Aka Rubuta Kenan da Manyan Harrufa Da Murmushinsa Yaɗauki Wayar Tareda Cewar, "Tuba Nake Hayatina Gani Kan Hanya So A Haɗa min Ruwan Wanka Kafin In Karaso."

Yadanyi Jim Fuskarsa Cike da Walwala Kafin Yace, "Sereosly Nake Gayamaki Fa Hayatee dan Haka Kishirya Ko Kinyi Kwalliya ne Sai Mun Sake Wanka Tare." Dif! ta Kashe Wayar Tabarshi Rike da ita Wayar Yana wani Irin Murmushi mai cikeda Ma'anoni daban-daban Yasan Dama Za'ayi Haka Dan Kunyar Tsiya ce da Ita Sosai.
Sanda Yashigo gidan Lokacin Take Fitowa daga Kichin Tallabe da Faranti Da Manyan-Manyan Wermars Dake Jere Akai. An Ko Sha Kwalliyar Nan Da yake Cewar Kamar Wacce Zataje Gasar Kyau. Murmushi Kawai Tayi Tana mai Nufar Danin Area da Kayan da Ke Hannunta Yayinda Ashraf dake Ƙame Kan Doguwar Kujerar da Sukayiwa Ƙayatacen Falon Ƙawanya Yayi Cilli da Remot ɗin Hannunsa Yana Kallon Cartoon ɗinda Tv Ke Watsowa Yanufo shi Yana "Oyoyo Dady!"

Dr Jabir Yakamashi Yacaɓe Suna ta Murnar Ganin Juna Ashraf Yakkali Idanun Dadyn Nasa dake ta Lumshewa Saboda Tsabar Gajiya da Bacci Dake Cikin su Yace, "Dady karame... ko Mami?" Yaƙarasa Maganar Yana Kallon Mami tasa data Harɗe Tana Kallon su Fuskarta Cike da Walwala Yayinda Dady Ke Basa Amsa da Cewar "Badole ba my Son Nayi Missin Naku ne." Ashraf Ya Kyalkyale Dariyar Yarinta Yace, "Muma Haka Dady Harda Mami... Ko Mami?" Nan ma Mami Bamagana Sai Murmushi Kawai datake Aiko Masu Dashi Dan Haka Dr Jabir Ya'isa Gareta Tareda Ɗora Hannunsa kan Kafaɗarta Yana mai Cewa, "Ko Yar Momy Bata Jin Ashraf ne."

"Ƴar Momy Kuma?" Ta Maimaita Tana Mai Kallonsa.

Gabaɗai Sai Yadaburce Yasoma
Inda-inda, "A.a.... Eh Wai Ina Na.. Nufin.........


Readers Anan Zan ɗan Nisa Sai Muje Daku A Fage Nagaba Domin jin Yanda Zata Kaya Gadai Reshen Na Neman Juyewa Haryanzun dae Zamu Sake Tambaya Waye Dr Jabir Kuma Wace Barazana ce Ga Kyakykyawar SOYAYYAR Su Khaleesat? Makaranta Littafin SONE SILAR KOMAI Akwai fah BADAKALA Harma Curkuɗewar Al'amurrah Ga Wayyanan Mutanen Ataƙaice Zan Iya Cewa LABARIN Yanzun Ma Yasoma Kuma Akwai KWAMACALA Mai Cike da Ban Sha'awa Harma da Darussan Ɗauka Dan Haka Nayi Gaba Muje Zuwa Tareda Alkalamin 👇


FA'IK. ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 11 · 0% Book details