← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 40

Chapter.....26

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Kai Shidai da Bakinsa Wallahi Bazai iya Cema Khaleesat ɗinsa Haka ba. itakanta Maman Asharaf ɗin Tafahimci Sa Sarai! Dan haka Ta juya Tareda Cewa, "Ok Ina Zuwa minti Biyu."

Ba'ajima ba Kuwa ta dawo ɗauke da Farantin Da tajera Soyayyen Ƙwai da Shayi Mai Matuƙar Ƙauri da Kuma Bread Gefe. Ta'ajiye Gaban Dr. Jabir Tareda Rusunawa Gabanshi Cikin Tsantsar Tausasa Murya Tace, "Dan Girman ALLAH Kayi break Badanni ba! Baban Asharaf Tunda Lalurarnan ta taso Kake yiwa kanka Horo Da Yunwa Mussaman daga jiya Zuwa Yau.

Kaine Likita Kaine Yakamata Ace Kana faɗakar damu Kan Haka Bawai Mu Ba." Lumshe Idanuwan sa Yayi Yanaji A Ransa Abunda tafaɗa gaskiya ne. Kawai dai Abun ne Yafi Ƙarfinsa babu yanda zaiyi da Rayuwar sa wacce A Yanzun Tafita daga Ƙarfin Ikon Sa domin dai Acanda Shike Sarrafata yanzun kuwa Yadawo Itace ke Sarrafashi.


Sannu A Ahankali Yasake buɗe idanun nasa Fes A kanta tana durƙushe Gabansa Tareda Juya Shayin dake Cikin Glass Cup taɗebo Shuga Zata sa Yadakatar da ita Kan Cewa, "Sunyi Yawa Maman Asharaf Sa ƙwara Biyu Kawai." Haka tasa taɗan juya shayin da spoon Sa'annan taɗauko ta miƙa Masa Yakarɓa Yakai bakinsa Yana sha kamar Mai shan magani Saboda ɗacin da Shayin Keyimasa. Matsa masa tayi sai da yashanye tas! Kafin ta turo masa Soyayyen ƙwan Shima A gabansa.

Dago Fararen Idanunsa Masu Launin Madara Yayi yazuba su ga Matar tasa Batareda Yace Uffanba dama dai can Miskili ne balle kuma Yanzun da Komai Nasa ma Nauyi Yakeyi Masa.

Maman Asharaf Tasan Halin Yan Kayanta dan haka saita bi dashi ta Yanda tasan Tana Karya lagonsa. Haɗe Hannayen ta tayi Guri ɗaya Irin mai Roƙonan dai Kafin Tace, "Dan Girman ALLAH!BabanAsharaf." Ba Musu Yasake jan flet ɗin Soyayyen ƙwan Yasa Fork(Cibi mai Yatsu)Yasoma ci. Shima ɗin dai Kamar Wanda ke cin Magani Haka yadinga Cinsa.

Bread Tafitar A ledarsa Tana mai Ƙokarin Tura masa A Gaban Nasa wai A nufinta Yahaɗa, Amma Harar da Yawatsa mata Yakatse Hanzarin Nata ta sadda Kanta ƙasa Cikin Matuƙar Jin Ƙwarjinin da Idanun nasa keyi Mata dubanta yayi Yana Cewa, "Amma nace Kiyi Hanzari Ki Shirya Zamuje Gidan Mutuwar Nan tare ko?"

Miƙewa Tayi Tareda Cewa, "Kayi Hakuri Bari Na Shirya ɗin." daga nan Kuma tafita Zuwa ɗakin ta.

Can Ta Sami Su Sajida Na Shiri Kan zasu Wuce Tunda ga yanda Lamari Kuma Ya Rincaɓe.


Gefen Gado ta Zauna Gamida Cewa, "Wai da Gasken dai Wucewar Zakuyi?"

"Tau me kuma Zamu Tsaya yi Asiya?" Aunty Asabe Ta'amsa mata tana Ƙokarin Sakawa Yarinyar ta Kaya Ajikinta.

"ALLAH dai yajikanta Yayi mata Rahma Shine Kawai Abin Cewa dan Abin da Matuƙar ban Tausayi wallahi." Sajida ce Mai Wannan Maganar A Yanzun itama tana Ƙokarin Cusa Kayanta da na Ƴar Yarinyarta Yar Shekara 6 Acikin Jakkah!

Aunty Asabe Tace, "Tau Yaza'ayi da Lamarin Ubangiji? Wa'azi dai Ai Ana Ganinshi A duniyar Nan Saidai Zukatan Mu ne Suka Koma Kamar Na dutse Muna ƙin ɗaukar Darasi."


"ALLAH dai Yasa Mucika da Imani." Abinda Maman Asharaf Tafafa Kenan Kafin Tamiƙe Tana Faɗin, "Kedai Safiyyah Ba inda Zakije Dole Kijira Indawo." Safiyyah Ta Zumburi Baki Alamun dai bata so ta Zauna itaɗima tafi so Tawuce Shiyyasa Tayi ta Kallon Su Aunty Asabe dan Susa Baki Amma sai Sukayi Biris da ita Alamun dai Suna Goyon Bayan Maman Asharaf Kenan Suma dai.

Dan Haka Kawai Tamiƙe tabar Masu Ɗakin Tanufi Falo Tana Ƙunƙuni.


Maman Asharaf dai Bata Sake mata Magana ba, madadin Hakamma Sai Ta Nufi Bathroom dan Yin Wanka Harta kama Ƙyauren Ƙofa Sai kuma tatsaya gamida Juyowa tana fadin, "Yawwa Aunty Asabe Nace Yaza'ayi da Wannan Kayan Tau Yanzun?"


"Nima Abunda Nake ta Nazari Kenan Wallahi! " Sajida ce Mai Wannan Maganar.

Aunty Asabe Tace, "Ki Rabasu Kashi Ukku Kashi ɗaya Ki Ajiye Muku Zai Maku Amfani ɗayan Kuma Tunda Safiyyah Na Nan Ko kuma Kafin Mutafi Zamu Shirya Su A Leda-Leda Ki Rabawa Makwabtanki Musamman Masu Ƙaramin ƙarfi daga Cikin Su Sauran Kuwa Akai Can Gidan Rasuwar dan Zai Musu Amfani dan Ba Wani Girki Zasuyi ba Nasani."


"Good Idea! Aunty Asabe ALLAH yabar Mana ke dai wallahi." Maman Asharaf da Sajida Suke Faɗin Hakan.


Murmushi Kawai Auntyn Tayi because Basa Yanayi Mai daɗi da Shaƙiyancin Sai Ya wuce Haka.


A gaggauce Maman Asharaf Ta Shirya Tayiwa Su Sajida Sallama Kan Sai Sunzo dan Sune Zasu Kawo Kayan Gidan Gaisuwar Idan Suka Gama Shirya Sun Kamar Yadda Suka Tsara.


************


A Hankali Yake Ƙiƙorin buɗe Idanuwan sa Yana Mai Ƙokarin Tantance A Ina Yake? Ya Yunƙura da Nufin Tashi Yaji Duk Jikinsa A Tankwashe babu Wannan Damar, dan Haka yabi Hannun Nasa da ke Maƙale da plaster Harzuwa ga Inda Aka Saƙala Gorar Ruwa da Ake Masa Ƙarin Su. Sa'annan Yadawo ga Kallon Nasa ga Wanda ke Riƙe da Hannun Nasa Ƙaninsa ne Abubakar Sai Yasami Kansa da lumshe idununsa Cikin Ƙokarin Tambayar Kansa Dalilin Zuwan Sa Asibiti.

Daga gefensa Yaji Innarmu Na Tambayar Abubakar Cewa, "Ya Farka ne?"


Abubakar Yagirgiza mata Kansa Nufin dai Yafarkan Kenan.

Innarmu Ta dinga Yin Hamdala ga ALLAH Tareda Ƙara tsarkake sa Kafin Tace, "Tau Ai Saika Kira Likita Ko? Tunda Yace Musanar dashi In Yafarka." Wayyanan Kalaman Suka Sanyawa Ƙwaƙwalwar Abdul-wahab Caji Hakanan Komai Yasoma Dawo Masa Tiryan-Tiryan.

Idan Zai Tuna Fa Gidan Su Khaleesat Yaje Domin Halartar Ɗaurin Auren ta Aka Cemasa ta RASU!!!

Da Sauri Yamiƙe Zaune Yana dube-dube Kafin Yakalli Su Innarmu Gamida Cewa, "Innarmu da Gaske ne Abunda Naji? Eh Dagaske ne Khaleesat Tarasu? Ko kuwa Mafarki Nayi?"


Duk Suka Rufu A Kansa Suna Masu Ƙokarin Dannarsa Akan Zabure-Zaburen da Yakeyi.


Abubakar Nacewa, "Yaya Inaga Mafarki ne Kayi Amma Khaleesat Bata Mutu ba Tana Ray...". "KARYA NE!!! KHALEESAT TARASU NAGAN GAWARTA DA IDONA!!!!" Kai da Ganin Yanda Yake Maganar Kasan Baya Cikin Hankalinsa Ƙokarin Ma Yake Ya Turesu Yafice daga ɗakin.

Dole Innarmu Tafice da gudu Zuwa Kiran Likita Kan Yakawo Masu Agaji.

Tare Suka Dawo da Likitan Inda Tuni Abdul-wahab Yayiwa ɗakin Kaca-kaca Sai Ihu! Yakeyi Yana Sambatu. Dole Sai da Suka Samun Ƙarin Wasu Likitocin Kafin Aka Danne sa Aka Turtsa Masa Allurar Bacci.

Duk Ƙokarin da Yakeyi Na Yatashi Yayi Hargagin, Allurar Tahana Masa Wannan Damar. dan Haka sai Ya Koma Yana mai Lumshe Idanunsa Jikinsa duk Ya Mace. Ahakan idanun Nasa Suka Lumshe gabaɗai Yayinda wasu Hawaye Suka biyo ta Gefen Idon Nasa. Daganan Kuma Yayi tsit! Alamun dai Baccin Yatafi dashi Karfi Da yaji.

Gefe Likitocin Suka Koma Suna Sauke Ajiyar Zuciya Kafin Suka Sharce Gumi Tareda Ficewa daga ɗakin.

Innarmu Kam Kuka take Tayi Haka Zalika Shima Abubakar Sai Hawaye ke kwararo Masa. Yarasa ƙwarin gwaiwar Lallashin Innarmu.


Suna Cikin Wannan Halin ne Ango Yusuf da Tawagar Abokan su Suka Iso Dubiyar Jikin Abdul-wahab ɗin.

Wanda Hakan yatirsasawa Innarmu toshe Kukan Nata Tajawo tasbaharta Taci gaba da salati. Shima dai Abubakar ɗin Share Hawayensa Yayi Yajawo Gilashinsa Baƙi Yaɓama A Fuskarsa.


Duk Suncika ɗakin Sai Surutun Su Ketashi Abubakar Yajawo musu Kujerun Roban dake Gurin Wasu Suka Zazzauna Yayinda Wasun Sukai Tsaye dan Bazai Isheshu Ba. Duk dauriyar da Yusuf Yakeyi Sai da Yakasa Yafashe da Wani Irin Kuka Kafin Yakifa Kansa Kan gadon da Abdul-wahab ɗin ke Kwance Yana ta Aikin kukan Kamar Macce. Gabaki ɗaya ɗakin Yayi tsif Innarmu kam da Dama A Wuya take sai Tayi Hanzarin Fita daga ɗakin Zuwa Harabar Asibitin Tasamu Ƙarƙashin Dalbejiya ta Zauna Tana Mai Ci Gaba da Jan Carbinta Kuka Nata Ƙokarin taso mata Yayin da Tawakkalin ta Ke Kokawa dashi domin Hana Sa Zuwan.


Acan Kuwa ɗakin Duk Abokan Nasu sai Sukai Caaa! Akan Yusuf ɗin Suna Aikin Basa Magana. Yayinda Abubakar Yarasa Wannan Jarumtar Illai Hannayen sa da Yaharɗe A Kijinsa Yakoma Gefe Yana Kukan Zuci Wanda Akace Yafi Na Zahiri Ciwo. Hankincip Yusuf Yasa yana Share Hawayen sa Kafin Yaɗago Yadubi Abubakar Yace, "Tunda Muka Kawoshin Ya farka Kuwa?"


"Ya farka, Saidai Allurar Bacci Sukayi Masa da Ya farkan Dan Sunce Amfi Son Yayi Baccin." Abubakar yabashi Amsar Batareda Yadamu Yasan A Yaya yayi Maganar ba.


"Amma Ayi Haka Mutum Yayi ta Bacci Ba Ci Ba sha..." Wani daga Cikin Abokan Kansu da Ake Kira Shamsu Shine Yayi Wannan Maganar


Yayinda Wanin Shima daga Cikin Su Mai Suna Abba Yace dashi, "Ai tunda Kaga Sun Masa Hakan tau Shine Dai-dai tunda Aikin Sune Su."

"Hakane Kuma. Tau ALLAH yatashi Kafaɗunsa Yabashi Lafiya!" Shamsu ne Mai Wannan Maganar.


Yayinda Duk Sukayi Tarrayah Gurin Cewa, "AMEEN YA ALLAH!"


Sunɗan ɗauki dogon Lokaci A gurin Kafin Sukayi Musu Sallama Kan Zasu Wuce Abubakar ne Yayo Musu Rakkiya Suka Biyo ta Inda Innarmu Ke Zaune dan Yima ta Sallama Sai Suka Sameta Tana Sallah! dan haka Sai Suka bar Sallahun Abubakar Yasanar Mata Cewa su Sun Wuce.


Kusa da Zasu Hau Baburan su wasu kuwa Kk Napep Ango Yusuf Yaja Abubakar gefe Suna Tattaunawa kan Ciwon Na Abdul-wahab ɗin.


Abubakar Yace, "Ya Yusuf Wallahi Yaya yana Cikin Wani hali Kasan shi dama da Halin Nasa ba Komai yake Iyama Juriya Akai ba. Sanda Yafarkan Kamar Wani Taɓaɓɓe Shine ma dalilin da Yasa Likitocin Suka Danna Masa Allurar Bacci. Ni Tsoro na Kar Yayamu Yagamu da Ciwon Hauka ta Sanadi yar Wannan Masifaffen Son da Ban Taɓa Ganin Irin sa A Wannan Zamanin Namu Ba... " Abubakar Yaƙarshe Faɗar Hakan Cikin Rawar Murya Kamar zai fashe da Kuka.


Masu Karatu Zan ɗan Nisa Anan

Muje Zuwa A page na Gaba

Tareda Alkalamin


FA'IK.
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 24 · 0% Book details