Chapter.....20
So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Mallakar 👇
Fa'IK ✍
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.
FADAKARWA.
Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.
Bissmillahi Rahmanin Raheem
Wayyanan tarin tambayoyin Naci gaba da yiwa kaina Kuma Narasa Samun Amsar ko guda ɗaya Acikin su tau mezanyi? Kuka? Fita Neman wanda zai bani Amsar su? Inna Fita ina zan Sameshi? Dan haka sai nazaɓi Nayi Kukan Ko Sanyi Naji Azuciya ta.
Sai dai dole ne Innemawa kaina Mafita domin duk yanda takai Takawo Nice zan kwana cikin Matsalar duk yanda wani zai koka min Baikai nawa kukan ba! Inaji Araina wannan Karon Ma zansake Wani Yunkuri! Zan sake wata Sadaukarwa! Zan Sake Wani plan Karo Na ƙarshe Matuƙar Bai Kuɓutar dani Ba, tau Na Hakura Zanbi wannan Rayuwar duk Yanda ta zomin Kawai.
Zuwan Wannan Tunanin Acikin Zuciya ta, Sai Yasamarmin Salama Sosai Naji yakwashe Kaso mafi yawa na ƙuncin da zuciyata take ciki, Nasamu Wani kwarin Gwaiwa A yanzun dan haka Nafito Toilet ɗin da Wani Irin Karsashi duk-da Kuwa wata Zuciyar na Tsoratar dani Kan Wannan Plan Nawa Amma wacce take Son Abdul-wahab So Na hakika Tana kore Wannan Tsoron Kuma tana ƙarfafa Tareda nuna min Cewa Rayuwar Aure babu Abinda Yafi Dacewa Acikinsa Face Samun Wanda Kake SO!
Sanda Nafito Aka Yayyameni Da Cewa, "Ina Kika shiga dangin Ango Yan Kawo Lefe Suna ta Neman suga Amarya Amma Babuki ba Samatarki? " Nadubi zubee wacce Ke Maganar Tareda ce mata, "Mesuke Yiwa Gaggawa? In Sukayi HAKURI Nanda Sati Biyu Ai kuma Ina cikin su Tsamo-tsamo sai sungaji da ganina." Faɗar hakan da Nayi duk sukayo Caaa Akaina "Eyeeeee! Yar Is...(Haka muke ɓacin/zagin Juna in Muna jin shaiɗaincin mu)Watau dai Nafahimci Yarinyar nan Kin Taki wani Abu ko?" Nakoma Kan Kujera Na zauna Ina kuma dafe Kaina Tareda Cewa, "Kinga Hauwa Dan ALLAH ni ku ƙyaleni da Wannan Iskanci naku Wallahi kaina ke Ciwo."
Laila Ta Caɓe, "Aikuwa Ciwon Nan ƙaryarshi tasha ƙarya dan Kuwa Dr Yafi ƙarfin Shi?"
"Tau ke kika Sani Ciwo kan Aiken Dr ɗin ne?" Hauwa Ke faɗar hakan Cikin Salon Tsokana.
Itama Zubee Tace, "Ah tau, duk Sanda Suka Haɗu muka kai masa Ita Ai sai ke Neme shi Ki Rasa."
"Kuma fa Hakane." Laila ke Faɗar Hakan Tareda kama Haɓarta Alamun Gulma.
"Wani Aikin Sai Likitanmu." Hauwa ce mai Wannan Maganar Kafin duk Suka ɗauke da Shewa da kuma Dariya Suka Taɓe Har Suna Faɗomin A jiki Namiƙe Ina Cewa, "Ni kunga Karku jimin Ajiki gara ku Ƙashin ku Yana da Ƙwari yan Islamiyya Kawae." Nan ma Suka yo Caaaa A kaina.
Haka dai Muka Yini Da Ƙawayena Muna ta Caɓta! Wanda Mafi Yawanshi Faɗa yafi Yawa.
Nidai Sai ce Musu Nake Sun ɗau Bashi ALLAH kaimu Auren wata daga Cikinsu Sai Na Fanshe Iya Shegen da Suka min
Nam dai dariya Mukayi.
Sai gabda Magariba Kowacen Su Tayimin Sallama Suka wuce Da Alkawalin dawowa jibi dan jin Tsare - tsaren da Zamuyi Na Buki.
Hakanan Ma Gurin Momy duk Bakin Sun Watse, Sai Ƴan Tsiraru Makwabtanmu Da Basu Samu Shigowa ba Saboda Ayyukan Gida Da Dai sauran uzurori. Sune Ke Shigowa Yanzun Suna Ganin Lefe Wanda Sai da Nafito Arwallar Magrib Na Hangi Akwatan Anjerasu Sai Ƙyalli Sukeyi.
"Ba Shakka yayi Kokari, Amma Gaskiya Dr jabir bazan Iya Auren ka ba. Shiga Tsakanin Miji da Matarsa harda Albarka ɗa Ai Matsala ce. Gara ke Ashigo A sameki da Mijin da Ace kece kika shiga. ƙari ga haka ma Ni ina da Jarumi na, In Ba Abdul-wahab ba ina jin sai Rijiya, Ko Ya suka ƙare da Matar tasa? Kila ta Rotse Masa Kai, hhhhh" Zance zucin da Nake tayi kenan A Lokacin da Nake Arwallah.
Ina gamawa Na Nufi ɗakina dan Yin Sallah Nabar Makwabtanmu da suka Shigo A Lokacin sai ɗaga kayan Suke Suna "Kai!! Masha'allah! Wallahi Yayi Ƙokari ALLAH yabasu Zaman Lafiya.". Yayinda Momy take ta Murmushi.
*********
Suna Cikin Kafteria ɗin Makarantar su A Zaune Shida Abokan Karatun sa kowanen su kuma Nakaiwa Cikinsa Abinda Yasiya.
Wani Shinkahwa da Miya ne Wani kuma Kwai da kwai(Awara) ne da dankali dakuma Kabeji Wani Kuwa kok ce da Bons sai Donoth.
Abdul-wahab Na cikin Wayanda Ke Shan Kok da Bons da kuma Donoth. Dama Shi ba Ɗabi'arsa bace, Cin Abincin Waje wannan ma dai dan Sun fito ne da Yunwar da Aka san kowane ɗalibi Nafito wa da ita in Aka tashi daga Skull ko aka kammallah Lakca ga Masu karatu A manyan Makarantu Kenan.
Tj ne yadubesa yana Cewa, "Wai Saura Wata Nawa ne bukin Abokin ka (yana nufin Yusuf)da Kake gayamuna Za'ayi?" Abdul-wahab Yaɗan kora Kok ɗinsa kafin Yadubesa Yace, "Wata fa? Kace Sati dai."
Tj Yace, "A'a Kace Bukin ma Yaƙarato, Ai gara ma Haka dan Kar yazo Mana Gabda Exam ɗinmu Ko Ma Ana cikin Yinta."
"Wallahi Kaidai Ai ni zance Haka ma." Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Yana Mikewa gamida Sa Hannun Cikin Aljihunsa Yazaro ƴar dubu daya yana mai Mika ma Mamallakin Wurin Yace, "Kacire Har kuɗin Wannan." yafaɗa Yana nuna Tj. Bayan Ya karɓi Canji Yadubi Tj Tareda Cewa, "Ya? Zamu tsaya Mujira Lakcan Wancan Karfar Malamin Ko mu Fice?"
Tj Yamike Yana Goge Hannunsa da Tissue gamida Cewa, "Allaji Kawai Mutafi Abun mu Ma kaura dashi Wani Satin, Yau Ba wanda Nabaro A shago kaga kuwa ai Yakamata in koma in buɗa." Tboy Yasako Baki A Cikin zancen nasu da Cewar, "Kaji Daher ba Ai Karatun Naka ma Shagon Naka ne Rufin Asirinsa. Bro Ware Kawai Kaje Abinka Ka nemi Kuɗi Karatu A Ƙasarnan Ai Sai da kuɗi."
"A Lafiya dai Nawan! ALLAH shi kiyaye min Kai." Tj ke wannan Maganar Cikin Salon Gayunan Na Yan Skull in An Haɗu guri ɗaya Ana Cabta. Kafin duk Wurin suka ɗauke da sowa irin Wacce aka san Samari da Ita. Dahaka Dai Sukayi Sallama Da Sauran Abokan Nasu Suka Fito Get ɗin Makarantar Tareda Samun Kk Napep dan Tayi dropin Nasu A gida. Acikin kk Napep ɗinne Abdul-wahab Yazaro Wayar sa dan Yakira Shalelen Tasa(Khaleesat)dan Yagayama ta cewa yau Zasu Zo Hira..
**********
"Maman Ashraf Kina Hauka ne? Meke Damunki ne?" Dr Jabir ke Faɗin hakan Yana mai Ƙokarin Maida Wayarsa Aljihunsa sai dai ina? Tuni Ta shamace Shi ta Fisge Wayar Ta watsa ta A bangon ɗakin Ji Kake Tatsatsatsa!!! Wayar tayi ɗai-ɗai Ko wane Yanufi Wani Muhalli. B3 yayi gefe haka marfin Wayar Shima yayi nasa Gefen.
Tas! Tas! Kakeji Saukar Maruka A Fuskarta Yana mai ci gaba da Nuna ta Cikin ƙunar Zuciya Cikin ɗaga Muryar sa yana Cewa, "Maza kifece daga ɗakin Nan kafin In buɗa ido dan Wallahi Zan iya kakkarya ki."
Maman Ashraf ta Durkushe Sai kuka Take Mai cike da Sauti tana Tunanin Matakin ɗauka.
Yayinda Shikuwa Yanufi Wayar sa yana Ƙokarin haɗa Kanta. Wayakam Taci Screen.
Sai ganin Yayi Tamike Harta kai ƙofa Kuma Tadawo kafin ta soma Cewa, "Zanfita ɗin ba'ama A iya ɗakin ba, har Gidan Gaba ɗaya Kai Harma Rayuwarka duka Dr, Amma Sai Kabani Takarda ta dan Inba Munafunci Ba Tayaya Za'a Auren ka banji daga Gareka ba sai A dangi? Hummm!" tayi Shiru tana mai goge jini dake ɓulɓulowa Abakinta dan ba Kaɗan Yayi Mata marin Ba. duk Jar Fatar ta Shatin Yan yatsun sa Ne. Abinka da Fara Fata da basa Rena Abu. Tasake dubansa karo na Biyu Abinda Bata iyayi Ada Amma yau Saboda halin KISHI taji Bata Shakkar Hakan. Kafin Tasoma Cewa, "Dama ai sai da Ƴan Uwa na Suka Gayamin Matar Cushe bata Daraja Amma Naki kula Maganar su, gashi kuma Naga SAKAYYAR Zancen Nasu Domin dai Banga Abinda Narage ka dashi ba. Duk dai domin In gamsar da kai Amma da yake dai 'NAMIJI ƘANIN AJALI ne. Sai da ka tabbarmin da Hakan kuma Wai Ka kasa gaya....."
"Tau wai ke Waya Gayama ki Zan ƙara Aure ne dan Bana Sonki Ko kuma Dan Kin gaza Kyautata Tamin ne? Shi Aure Sunnar Manzo Rahma ne kuma kamar yadda Yayi mana Koyi Muyi Na Farkon Hakama Ya Sunnan Tama na Yin Na biyu ko Uku kai Har Huɗu ma Sa'anan ya horemu da amma in mun san Zamuyi Adal....."
Maman Ashraf Ta dakatar dashi ta Hanyar ɗaga Masa Hannunta, "Kaga Mal ni Bana wani son Wa'azinka Kabani Takarda ta inɗare Inbar Maka gidan ka Harma da Rayuwar ka, Wa'azinka Kuwa In Amaryarka Matar So Ta'iso Sai Ka soma yi mata Tun daga Daren da Aka Kawo ta har Yauma Tanadi wannan Matsalar kune ba tawaba."
Dr Jabir Yayi Saƙare Yana Kallon wai Yau Maman Ashraf ce ke Gabansa da irin Wannan Siffar Tana Gayamasa Wayyanan Baƙaƙen Maganganu Kawai Saboda tsabagen KISHI Abinda In kafin Hakan ce Tafaru Aka Gayamasa Bazai Yarda ba Saboda kallon da yakeyi Mata Na Ko Farce (yatsa)Aka Sama ta Abaki Bazata Ciza ba.
Sannu A Hankali Yatako Zuwa Inda Take Tsaye, Yayinda ita ma taja da baya Saboda yanda takejin tsanarsa A Yanzun ko Ganin sa bata Son yi Balle kuma Ya raɓe ta.
"Ki Tsaya ki Saurare ni Maman Ashraf Shifa Wannna Ab....."
"Wallahi ni Yanzun babu wani yare da zan Fahimta daga gareka Illah Yaren Ka Sawwake min Auren ka Inje ni gidamu Shine Kawai." Ta faɗi hakan tana mai ci gaba da Zubar da Hawaye.
Yamika Hannu da Nufin Riƙota Tareda Cewa, "Naji Zan miki Abinda Kike So Amma...."
"Amma me? Kanka Tsaye kawai Kamin Abinda Nake so Shine Kawai HALLACIN Da Zakayimin A Yanzun." Kafin taƙara ja da baya Tana Nuna sa da Yatsa "Kada kataɓani Banaso!" Shi Sai Abin Yadaina Ɓata masa Rai Yakoma Bashi Dariya.
Ta Lura Sarai Dashi Dan Haka Sai Kawai Tajuya tabar ɗakin. Yana kiran ta Amma Ina Makullin Motarsa dake Falon Tafiga Tafice daga gidan. Sai jin Tashin Motarsa Yayi koda Yafito har maigadi Ya wangale Mata Ƙofa Tafice A Matukar Gudu wanda ke bayyanar da Irin Ɓacin ran da Take Ciki, Yakuma Sani Sarai! Irin Wannan Tuƙin datake yi SAI ALLAH! Dan dama can Ba wani kware wa tayi da jan motar ba dan bai daɗe da koya mata ba dan haka da hanzarin sa Yaƙaraso Yana yiwa Maigadin Nasu Faɗa Kan Mezai sa Yabuɗe mata Get ɗin? Maigadi Yarusuna yana Cewa, "Ayi Hakuri Yallaɓai Naɗauka Fitar Arziki ce Shiyyasa Na buɗ...."
"Fitar Arzik? Haka Ake Fitar Arziki A garinku?" Dr Jabir yatare sa da Faɗin Hakan Cikin Ɓacin Rai! Kafin Yayi Tsaki Yajuya Izuwa cikin Gida Yana Neman Makullin Mashin ɗinsa Wanda In yayi Sha'awa Yake Hawa ya zaga Gari.
Kaitsaye Yabawa Mashin ɗin Wuta Yabi Sahun Maman Ashraf.
Tau fa!🤔🤔 Ƙaƙa ƙara ƙaƙa tau Yaza'a Ƙerke ne Wai? Muje A Chapter ta gaba my Readers..... Nayi Gaba Tareda Alkalamina
FA'IK ✍🏼
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪🏻J.A.W 💪🏻
❤❤SONEEE ....💕💕
(Silar Komai.)