← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 40

Chapter.....18

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻

GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem

Abdul-wahab Yayi shiru cikin Nazari da Tunanin Wannan Rayuwar da Mamakin Irin abinda Abokin sa Ke gayamasa Yanzun, babu Shakka shi kanshi yana matuƙar Son Khaleesat Sonda bai taɓa tunanin zai Risƙi kanshi acikin sa ba, tau sai dai Yana kawaici ne domin gujewa abinda zai tashi hankalinsa har hakan yashafi Dangantakar su Innarmu. hakanan baya son komawa ƴar gidan jiya acikin abinda Yadanganci karatun sa.

Yusuf yadafa Kafaɗarsa Sa'annan yakallesa kallo na tsanaki Yace, "Abdul-wahab ka Saurare ni da Kyau. karka zurfafa Acikin Wani Nazari haryazama Silar jefa kanka cikin wata Matsala, mafita ɗaya ce Zuwa Biyu, Nafarko dole Ka iya fin karfin Damuwar ka dan karya zamo Silar wargajewar Al'amurranka Sa'annan Kaje ka gana da Khaleesat Ko da Bazaku dawo da Soyayyar ku ba, tau ku SULHUNTA kai da ita.

Haka kuma Kuyafi Juna, ko ba komai Za'a samu Kafar yin Zumunchi kai da ita ko ba haka ba ma, Soyayyar ku bata cancanci kuyi irin wannan Rabuwar ba, yana da kyau Ace Kunyi RABUWAR ARZIKI ita kanta Abuce Mai daɗi. Wannan shine kawai Mafita."

"Tau Amma tayaya kake ganin hakan zai Faru?" Abdul-wahab yake faɗin hakan yana mai kallon Abokin nasa.


"Abune mai Sauki dai-dai ta danganta karku da Khaleesat, mai Wahlar shine yanda kai Zaka iya Kasancewa Mutum Mai kwarin Zuciyar da zai iya Shanye Damuwar sa ka kuma Kasance Wanda Zai Iya Mai da komai ba komai ba."

"Yusuf Bansan Yaza'ayi Na kasance Hakan ba! Nima kuma Inajin Ciwon Zama na Mutum Marar juriya akan Matsalar sa, tau Amma abu ɗaya Nabarwa Raina Shine, Haka ALLAH yayi tawa Rayuwar kuma bani da yanda zanyi wanda yawuce Karɓar ƙaddarata."

Yusuf Yasauke Ajiyar Zuciya mai Ƙarfi kafin yace, "Hakane Abdul, Amma dai ko yaya ne ka Ƙoƙarta ganin an ɗan samu Sauyi, Sa'annan mu Shirya zuwa gurin Khaleesat dan Ku SULHUNTA."

"Bazan iya zuwa gurin Khaleesat because Nagayama Nayimata Maganganu cikin Rashin Fahimta Wanda A yanzun ina kunyar haɗa idanu da ita."
Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Cikin Tsananin Takaicin Maganganu da yagaya matan sanda Tasameshi A Makaranta.


"Karka Damu Abokina Zanji da komai ni kawai kazo Muje. Kamar yadda Nafaɗa Abinda kawai Nake Buƙata a gurinka kazama mai juriya da fuskantar ƙalubale."


Abdul-wahab Yace, "Shikenan Ai, ALLAH yamana Jagora."

Yusuf Ya'amsa da "Ameen."

Daganan shiru yaɗan Ratsa mazaunin Nasu Na yan sakkani kafin Abdul Yadubesa Yace, "Yaaa? Muje Ciki ku gana da Innarmu ba?"

"Kaima kasani Ai." Yusuf yafaɗa yana harararsa.

Suka Nufi Cikin gidan Suna ci gaba da tattauna Yanda Abubuwan Zasu Kasance Musamman bukin Na Yusuf dake ƙarato wa.


Sun sami Innarmu Gaban Ƙatuwar Frizer ta, tana Aikin Jera Kunun Zaƙi dana Aya datake Sai dawa.

Sukayi Sallama Innarmu ta'amsa Tareda Cewa, "Lale Marhabin da Mutanen Ondo State." suka Zauna Yusuf na Cewa, "Innarmu Mutanen Sakkawato dai, Ni mi A haɗina da Ondo kuma?"

"Kasuwanci Mana!" Innarmu tabashi Amsa.

"Tau kuma hakane Innarmu, mun same ku Lafiya?"


"Ah Lafiya Lau, tun ɗazun nake Dakon Shigowar ku dan Auta Yagayamin kuna A Waje."


Yusuf yace, "Wallahi kuwa, sarkin Surutun nanne yahana mu shigowa muna can bakin Garka (ƙofa) muna ta zuba Surutu."

Innarmu Tace, "Aikam dai naga Alama."

Shikuwa Abdul-wahab Sai Aikin Zabga wa Yusuf harara yakeyi, dan yace masa Sarkin Surutu.

"Ga Kunun Nan Fa?" Innarmu tafaɗa Tana mai cigaba da gyara jera Kunun Acikin Frezar.

"Innarmu Sanda Ina can Ba ƙaramin Missin ɗin Kunan naki nayi ba Wallahi." Yusuf ke wannan Maganar dai-dai Lokacin da yake buɗe gorar Kunun Ayar yana korawa A makwagoron sa.


*********

Karfe 8pm Nadare Suna bakin Gidan mu Ni Sanda ma Nafito Naci karo dasu Ba ƙaramin Mamaki nayi ba.

Nayi ta Kallon Abdul-wahab da irin yanda yarame ga wani Uban Fari da yaƙara yi sai dogon Hancinsa yaƙara fitowa tamgarau.

Yusuf ne Yakatse Shirun Namu da Cewa, "Gamu munzo ban Hakuri Akan duk Abinda Yafaru muna Fatar Gimbiyar tamu zata dubeni mu da idan Rahma tareda mantawa da Laifin da Mukayi?"

Murmushi Nayi Sa'annan nace, "ka ganka Yusuf? Kai ko? Kai ko? Wallahi Kowaye yahaɗu da kai Zai shafa ma kanshi Lafiya."


Duk Sai Muka Shiga Dariya wannan Karon har Abdul-wahab yana tayamu dariyar. Na Juya Tareda Cewa,
"Ina Zuwa."

Fararen kujerun Roba guda Uku Nacewa Sani Yaɗaukarmin, Sa'annan Nikuma na tallabi plet ɗinda Najera Gorar Faro guda biyu Da Kuma glass Cup suma Biyu. Bayan sun Zauna Na'ajiye Gaban su Gamida Cewa, "Bismillah Kusha Ruwa." daganan nima Naja Kujerar Na Zauna.

Yusuf ne Yatsiyaya Musu Ruwan Acikin Cup Kafin Kowanensu Yaɗauka Yana Sha, Daganan Yusuf yasake Cewar, "Tau Aka ce dai Labarin Zuciya A Tambayi Fuska daga ma Irin Wannan tarbar da'aka mana Yanuna mana cewa komai Yawuce dan haka Ina dai ƙara bada hakuri Amadadin Abokina." Nace, "Kaine mai bakin, Shi Abokin Naka bayada Baki ko?" dai-dai Lokacin Abdul-wahab Yaɗago dara-daran Idanunsa Na Asalin ɗan Fulani Yakalleni dasu yasake kauda kai Nima Nakawar da Kaina gefe.


Yasake ɗago kansa Nima naɗago Muka Haɗa Ido yayi Hanzarin kawar da Kan Nasa nima kuma hakan Nayi.

Yaɗan Furzar da Iskan bakinsa, Yaɗago da Nufin Cewa Wani Abu Amma kuma muna haɗa ido sai Yakasa cewa komai.

Hakan da yayi Sai Yabani dariya Ashe Shima Abin Yabashi dariya Sai Muka Shiga yin dariyar tare.


Yusuf Cikin Al'ajabinmu Yakama Bakin sa Kamar Wata Macce Yace, "ikon ALLAH Abun Kuma kurman ci Yakoma? Tau Bari Kagani." Yamiƙe glass Cup Riƙe A hannunsa "Ni kunga Tafiya ta Kunga sai ku sake Sosai Kusha Soyayyar Taku, daɗin Abun dai Ina da tawa Masoyiyar, Bari Ma na Kira Abata A waya."


Cikin Sanyin Murya Nace, "kai kam Kashiga Ukku Yusuf..."


Yace, "Tara ma Kai!"


Cikin Abinda Bai Fice Sakkani ba Khaleesat da Abdul-wahab Suka Tsunduma Cikin Wata Irin Sarƙaƙƙiyar Soyayyar da a gurin su Za'a iya Cewa, ta zarce Zuma daɗi, tuni Muka manta laifukan Juna. Muka Cika kunnawa mu harma da Zukatan mu da Kalaman Irin kewar da mukayi ta Juna.


Hira Muke sha kamar ba gobe, Sai da Mukaji Yusuf Yana ta mana Magana Cewar, "Malamai Dare fa Yayi Ni Kun Barni Sai Sauro Ke cizo na ....."


"Maganin ka Kenan ni da Zan Samu Ganawa da Sauron Da Na Biyashi Yaƙara Cizon Naka!" Abdul-wahab ke wannan Maganar cikin tabbatarwa da Yusuf cewa So ya kai so.


Yusuf yace, "lalala! Sakkayar tawa kenan?"


"Au Namanta Sorry Abokina tuba Nake." gaba ɗai Mukayi Dariya.

Daganan dae Mukayi Sallama Suka Barni Cikeda Tarin Farincikin Akan
dai-dai tawar damukayi Da Abdul-wahab Wanda Zaƙin Soyayyar yasa Shaf! Na Manta da Maganar Dr Jabir.


Yayinda Sukuma Can suke tafe Hira ta ɓalle Tsakaninsu.
Yusuf Yace Masa "Shikenan fa Anyi mai Wuyar da kana Cewa bazaka zo ba."

Abdul-wahab yaɗan Lumshe idonsa Cikin Mayenso Kafin Yace, "Banzaci Abun Zai Zo Mana da Sauƙi Har Hakaba, Ban kuma zaci Zata Sauko Haka da Wuri Ba."

Yusuf Yadaki Kafaɗarsa Sa'annan Yace, "Ai Nagayama Kai kam Kadace Da Masoyiya Mai Sonka Da Gaskiya, gata kuma da Saukin Kai."


"Tau Kuma Shine Zaka Nemi Ciremin Kafaɗa." Abdul-wahab Yafaɗi hakan yana mai Harar Yusuf ɗin.

Hakadai Salon Hirar tasu Ta Kasance Har izuwa Sanda Suka Samu Kk Napep Zuwa gid. Acikin kk Napep ɗinma dai Hirar ce ta Yan Matansu Wanda Har Shima Mai Kk Napep yatsoma Masu Baki A Firar Sukayi tayi. Dama Ance "Hirar Samarin Bata Wuce ta 'Ƴan Mata! Hakanan Suma Yan Matan Hirarsu Bata Wuce Ta Samarin Su😅


*************

Da Sanyin Safiya Kuma sai ga Manyan Motoci Guda Kusan Biyar Suna Jerawa A Bakin Ƙofar Gidanmu.

Mutanen Ciki Suka dinga Fitowa Wayanda Mafi Yawancin su Dattijai ne Sanye da Malun-malun (watau Babbar riga) Sai Tsirarun Samari Da Suka Dinga Fitowa da Kwalayen Biskit da Alewa da kuma na chacoolate Gefe ɗaya Ga Kuma Katin-katin ɗin Lemu da Na Ruwan Faro Sai Kwandon Goro Wanda Nakasa Tantance iya Adadinsu. Yayinda Anan cikin Gida Kuma Dady Sai Kai Kawo Yake Tayi. Inda Tuni Ankai Tabarmi An shimfiɗa Masu Sun Zauna Sai Waya Yakeyi da Amininsa Cewar "Ya'akayi Haryanzun Alhaji baka Karaso Ba Har Bakin Sun Iso." ban san Me Aka Cemasa daga can bangaren da Suke Wayar ba, kawai dai Ya sauke Wayar Yana ɗan Tsaki.


Zuwa can Kuma saiga Dattijan Unguwar mu Suma Suna Shigowa Aka Soma Gaisawa Cikin Fara'a da Mutanen da Suka Zo. Cikin haka Shima Aminin Dadyn Namu Ya'iso Aka Shiga Musabaha Yana mai Bada Hakurin Rashin karasowar sa Da Wuri kan Cewar Mai Ne Yatsaya Yasha tau Kuma Yatarar da Layi A Gidan Mai.


A Hankali Na saki Labulen windor nawa Wanda tun ɗazu Nake tsaye ina Kallon Abinda Ke Wakana Atsakar Gidan Namu, Na Zube Kan Kujerar ɗakin Nawa Ina ƙara tabbatarwa Kaina Cewa Iyayen Dr Jabir ne Suka zo dan Acikin Samarin da Suka Rakko Dattijan Naga Wani Mai bala'in Kama dashi Wanda ko Shakka Bana yi Ƙanin sa Ne.


Tau Meke Shirin Faruwa ne?


Readers ɗina Muje Zuwa........ Tareda Alkalamin


FA'IK ✍🏻
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 16 · 0% Book details