← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 40

Chapter.....8

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.

Bissmillahi Rahmanin Raheem


Wannan Al'amari Ya Matukar Ɓatawa Innarmu Rai! Watau Akan Ta Nunawa Abdul-wahab Hanya Shine Zai Ɗau Fushi Da Ita? Lalle Wannan Zamani Yakai Inda Ya Kai Abdul Mai Tsananin Ladabi Da Biyayya Gareta Mai Tsananin Sadaukarwa Akan Komai Nata Yau Shine Kan So! Yake Neman Ɓauɗe Mata? Tunanunka Barkatai Sukai Ta Ziyartar Zuciyar Innarmu Suka Ƙara Haddasa Mata Kasalar Tashi Tayi Abinda Zai Amfane Ta Karshe Dae Tace "Ba'a Komai! Komi Yafaru Da Sanin ALLAH. " A dae-dae Wannan Lokacin ne Maman Walida Tashigo Gidan 'Yan Yaranta Sukai Ta Tureneniya Gurin Yimata Oyoyo! Taɗaga Kowanensu Cikin Farinciki Saida Aka zo Kan Ammar Tace, "Kai kam Dattijo na (Dan In Tana Nishaɗi Tana Kiransa haka.) Ka Girma Dan Haka Ka Girmi A ɗaga Ka." Duk Sukayi Dariya Shikuwa Ammar Yashiga Buga Ƙafa A Kasa Yana Kukan Shagwaba Tareda Cewa, "Momy Ni Bazan Yarda Ba, Ai Dady Ɗagani Yake Shikam. "

"Dady Kace Nikam Ina Nakai Karfin Dady Ne. Innarmu Sannu Da Gida. " Tamai Da Maganar ta Gurin Innarmu Ganin Inta biye ta Yaran Bazasu Gaisa Da Innarmu ba.

"Yawwa Ƴan Buki kundawo? " Innarmu ke Amsa Mata Da Hakan

"Eh! Duk Nagaji Wallahi. " Maman Walida ke Maganar Tana Nemawa kanta Inda Zata Zauna.


"Ai Ba Zama Yakamata Kiyi Ba Ki Nemi Abinda Zakici Ko?"


"A'a Innarmu Bana jin Yunwa Wallahi."

Innarmu Tace, "Tau Ai Shikenan Ina Amaren Suna Can An kai ko? "

"Amarya Na Can, Amma Innarmu Lafiya Kuwa? " "Da Akayi Me Fa?" Innarmu Ta Faɗa Tana Ƙokarin Nuna Bakomai. Maman Walida Tace, "Innarmu Naga Duk Idanki Yay Ja! Gashi Duk Dai Kamar Bakya Cikin Yanayi Mai Daɗi. Kodai Jikin ne Innarmu? " Innarmu Tace, "A'a Kawai Dai Ina Tunanin Sha'anin Yaran Zamani ne wai Kamar Abdul-wahab Dan Na Nuna Masa Abinda Zai Taimakesa A Rayuwa Shine Zai Ɗau Fushi Dani Baki Ga Yanda Yabar Gidan Ba."

Cikin Rashin Fahimta Maman Walida Tace, "Kamarya Innarmu? Nifa Ban Fahimta Ba Gaba Ɗai."

Innarmu Tace, "Wata Yarinya ya Jajibo Sukuma Iyayenta Suka Ce Bazasu Bashi Aurenta ba Dan....... " Nan Dae Innarmu Takwashe Iya Abunda Tasani Gameda Lamarin Ta Gayamata Maman Walida Tarafka Tagumi Cikin Mamaki Tace, " Amma A Fuska Kamar Abdul Bazai Aikata Hakan ba Shikuwa Meye Ya Matsesa A Lamarin Aure Da Yake Gaggawa Haka? Ko Bayan Haka Me Muka Aje Yanzun? Meya Tanadarwa Auren Da Zai Tunkari Wannan Maganar Hala?" Innarmu Ta Muskuta Cikin Takaicin Lamarin tareda Cewa, "Kema Dai Kin Gani 'Yar Nan."


"Innarmu Daina Ɗaga Hankalin ki Kici Abincinki Ki ƙoshi Kiyi Baccinki Barni Dashi Yadawo Zamu Gauraya ne."


Wannan Kenan!!!!!

A Gidansu Khaleesat Fa?


Tunda Kk Napep Ta Saukeni Na Shiga Gidanmu Ɗakina Na Nufa Nadaɗe Jingine Da Bango Cikin Tunani Da Makomar Rayuwata Wasu Hawaye Zafafa Ke Ta Gow Slow Kan Fuskata. Ban Taɓa Sanin Darajar Kuɗi Ba Sai Yanzun Ina Son Abdul Haka Shima Yana Sona Sai Dai Matsalar KUƊI Zata Kawo Mana Cikas! Koma Nace Takawo Mana Cikas! Ɗin.

Tunani Barkatai Ke Zuwa Mani A Kwakwalwa ta. Najima Ina Tufka Da Warwara Kafin Natsaida Shawarar Dana Ke Ganin Bani Da Mafitar Da Tawuce Ta. Dan Haka Da Karsashina Na Mike Nafito Tsakar Gida Ruwa Naɗiba Nashiga Wanka Banyan Nafito Nayi Yan Shafe-shafe mu Na Mata Nasamu Doguwar Riga Nasaka Kafin Nafito Na nemi Ruwan Zafi Na Shiga Falon Momy Inda Canne Kayan Shayi Suke Naɗibo Na Haɗa Tea Mai Kauri Nasha Duk Abinda Nake Momy Na Kule Dani Na Kuma Lura taji Daɗin Sauyin Nawa Saboda Tun Kunnowar Rigimar Na Birkice Masu Ba Wanka Ba Cin Abinci Ba Fira Ba... Ba... Ba.... Zayyawa Ko Da Yaushe Ina Cikin Ɗaki Makure.


Abincin Dare Yauma Tare Mukayi Kamar Yadda Muka Saba Momy Har Tana Cewa, "Ko kefa? Ja'ira Bazaki Gane Amfanin Zaɓin Da Mukayi Maki Ba Sai Nan Gaba Ko Bayan Rammu Zaki Shaidi Hakan."


"Aikuma Yanzun Komai Yawuce Momy ALLAH Sa Hakan Shi Yafi Zama Alkairi. "

Momy Tace, "Ameen Ƴar Albarka."

Da Haka Girkin Namu Ya Kammallah
Can Da Dare Yayi Kuma, Sai Ga Alhaji Saminu Yazo. Natsala Wanka Natafi Gurinshi Muka Sha Hira Sai Mamakin Sauyawa ta Yake Cikin Lokaci Ƙanƙani Haka. Nayi Murmushi Kawai.


**********

"Haba Abdul-Wahab Ina Hankalinka Yaje Da Harzaka Manta ko Kai Waye Da Kuma Irin Gwagwarmayar Da Innarmu Tasha Dan Ganin Rayuwar mu Ta Inganta Amma Lokaci Ƙaƙanni Zaka Manta Wayyanan Muhimaman Abubuwa ko Ka Juya Masu Baya? Saboda Kawae Son Wata Yarinya Wadda Iyayenta Tamkar Tuni Suke Maka Akan Muhimmin Abu Da Kake Kokarin Mantawa? Tunda Suma Sunce Bazasu Baka Ƴarsu Ba Saboda Suna Ga Bakayi Kaurin Wuyar Da Zaka Riƙe Yar Tasu ba Ashe Duk Wannan Bai Kamata Yazama Iznah Gareka Ba Abdul?" Maman Walida Ta Numfasa Da Wannan Dogon Bayanin Datake Ta Korowa Abdul-Wahab Dake Zaune Gabanta Durkushe Da Kansa Zuciyarsa Na Wani Irin Suya! Yana ji A Ransa Tabbas Duk Abinda Take Gayamasa Gaskiyane. Tau Amma Yazaiyi Da Son Khaleesat Dake Azalzala Zuciyar sa? Anya Ma Zai Iya Rayuwar Da Babu Khaleesat Acikinta?


Maman Walida Takatse Tunanin Nasa Ta Hanyar Cewa, "Duk Wayyanan Abubuwan Danake Gayama Abdul Ka Riga Kasan Da Su Sai Ma Ka Gayama Wani Su. Sai Dai Ina Tunar da Kai ne Saboda Inmma Ka Manta Ka Tuna In Kuma So Ke Ƙoƙarin Makantar Da Kai A Kansu Kai Ƙoƙarin Wartsakewa Kadawo Hayyacinka Sannan Ma Duk A Ture Wannan Abdul, Mu Kalli Irin Tashi Faɗin da Innarmu Tayi Danganin Rayuwar mu Ta Kyautata Yanzun Saboda ALLAH Yakamata Ace Yatashi A Banza Akan Wani Ɗan Ƙaramin Dalili Misali Shi Wannan Naka? Dan Haka Abdul-Wahab Kajini Da Kyau Daga Yau Baka Ba Wannan Yarinyar Ka ƙyalemusu 'Ƴarsu Suje Su Aurawa Wanda Suke Ganin Yadace Da Ita. Ina Fatar Abdul-Wahab Yajini?" Maman Walida Tafaɗa Tana Kama Kunnenta Irin Anji Da Kunnen Basira.


Abdul-Wahab Yagirgiza Kansa Yana Cewa, "Insha'allah." Kafin Kuma Yamiƙe Ya'isa Gurin Innarmu In Da Take Damun Furar Da Takan Siyo Wani Lokacin intayi Sha'awar Sha. Yadurƙusa Yana Faɗin, "Innarmu Dan ALLAH Kiyafemin Natuba."

Innarmu Ta Share Kwallar Da Ta Taru A Idanunta Tace, "Nayafe Maka ALLAH Maku Albarka Ku Duka."


Wannan Yafaru Yawuce!!!


Sai Ga Abdul-Wahab Ya Shiriricewa Makaranta Baya Zuwa Ko Yaje Baya Karatu Lokacin Exam Kuwa Da Anbashi Answer Sheet Sai Dai Yarubuta Sunan sa Yayi Submiting.

Yauma Suna Cikin Hall Ɗin Da Suke Zana Jarrabawa Ana Bashi Yarubuta Sunan Sa Yaje Yayi Submiting Har Zai Fita embigilator Dinsu Yakira Sa Ba Musu Yadawo Yadaɗe Yana Kallon Abdul-Wahab Kafin Yace, "Kai Kana Ga Hanyar Da kabi Zata Fissheka Kuwa? Ina Fa Hankalce Da Duk Wani Motion Ɗinka Nazuba Ma Ido Ne Kawai Inga Iya Gudun Ruwanka. Amma Naga Baka Da Alamar Sauyawa, A Fuska Gaka Dae Kamar Mutum Amma In Mutum Yabincika Sai Ya Sameka Shasha.... "
Abdul-Wahab Yafara Ƙoƙarin Kare Kansa Amma Sai Malamin Bai Bashi Damar Hakan Ba Yace, "Gate Out My Freind. Jeka Abinka, Dafuwar Mutum Mai ƙosar Dashi."


Jiki Babu Kuzari Haka Abdul-Wahab Yafito Hall Ɗin Yanufi Ƙarƙashin wata Bushiya Yazauna Cikin Nazarin Ƙila Wa Ƙala Da Yakasa Ƙaremasa.

Shi Kansa Ya San Abunda Yake Baya Kyautawa kansa Yasani Kuma Bai Dace Ba Amma Yazaiyi? Wallahi Duk Yanda Yayi ƙoƙarin Cire Son Khaleesat A Ransa Yakasa Sannan Yakasa Aiwatar Da Komai Ko A Gurin Aikinsu Duk Yabi Ya Sukurkuce Ko Ogan Sa Na Masa Ƙorafin Haka Har Ya Tambayesa Ko Lafiya Ce Bayada? Amma Shiru Babu Amsa. Shidai Kawai Yafi So Ne Yasamu Guri Shi Kaɗai Yazauna Ko Ya Kwanta Yayi Ta Tunani.

Dan Haka Yanzu Da Yake Zaune Cikeda Tunanin Meye Mafita Ya Yanke Shawarar Yaje Gidan Su Khaleesat Yaroki Iyayenta Su Taimaki Rayuwar Sa Su Bashi Aurenta Insun Bashi Duk Yanda Za'ayi Dole Su Innarmu Su Yarda Ayi Auren, Dan Wallahi Baya jin Rayuwarsa Zata Yuwu Babu Khaleesat.

Da Wannan Tunanin Yamiƙe Yanufi Gida. Yau Ko Bus Ɗin School Bai Iya Jira Ba, Yaɗauki Shatar Kk Napep Izuwa Gida, Sanda Yadawo Gidan Ba Kowa Innarmu Na Gurin Aiki Abubakar Kuwa Shima Na Shagon Ɗinki Dan Haka Yatsala Wanka Yafesa Turare Yafito Yana Ƙara Gyara Karin Fullarsa Dai-dai Lokacin Da Agogo Ke Nuna Karfe 5 Na Yamma Lokacin Rana Tayi Sanyi Sai Iskan Da Ke Kaɗa Manyan Bishiyoyi Dan Da Yuwar Za'ayi Ruwan Sama Dan Duk Gari Ya Rine Sai Kamshin Ruwan Sama Kakeji.

Yanayin Yakara Saka Zuciyar Abdul-Wahab Cikin Wani Irin Nishaɗi Da Yadaɗe Baijishi Acikinsa Ba. Kai Tsaye Bakin Titi Ya'Iso, Yasake Tarar Ɗan Kk Napep Dan Yakaishi Har Shiyyar (Unguwar) Su Khaleesat.

Yasauka Cikin Kk Napep Ɗin Yana Ƙoƙarin Lalubo Number Khaleesat Yakirata Gefe Daya Yana Murmushin Zai Mata Bazata Amma ga Mamakinsa Har Wayar Tagama Ɓurari Ba'a Ɗaga ba Amma Sai Yabawa Ransa Tana Wani Uzurine Dan Haka Sai Ya Sallami Mai Kk Napep Ɗin Da Yakawo Shi, Shikuma Yakarasa Gangarowa Bakin Kofar Gidan Nasu Khaleesat, Sai Dai Abinda Yayi Tozali Dashi Yafirgita Masa Lissafi Da Duk Wani Tunani Da Yakeyi Zuciyarsa Tai Wata Irin Bugawa Wanda Hakan Yasa Yadafe Saitin Zuciyar Tasa Da Tunanin Karta Faɗo Ƙasa! Saboda Irin Bugawar Da Yaji Tanayi Kafin Ya Soma Karanto
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju'u!!!!"
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 6 · 0% Book details