← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 38 OF 40

Chapter.....40

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Khaleesat Tayi Karab Cikin Maganar Tareda Cewa, "Ni Wallahi A Yanzun Nadaina Sonsa Nafasa Su Dady Su Bani Wanda Suke SO Ko Meye Shi Zan Zau......"


Baba Bukar Ya Watsa Mata Yatsun Sa Biyar Yana Cewa, "Ungo Nan, Wayasa Bakin Ki Manya Na Magana Ko Kinfi duk Wayanda Ke Nanne." Hakan Yasa Khaleesat Tayi Mui! Da Bakin ta Tunda Dama Can Ita Mai LAIFI ce Karta Ƙara Yin Wani. Yayinda Shikuwa Dady Ya Musƙuta Sa'annan Yace, "Wallahi da Zuciya ɗaya Nake Sanar da Kai Nabaku Yuƙa Da Nama Duk Abinda Kuka Zartar Shikenan Ina So Ingyara Kuskuren da Nayi A Baya Ina Kuma Neman Gafarar Ku Akan Wancan Ma Da Nayin. Dan Haka Ga ku Ga Ikram Duk Abinda Kuka Zartar Akanta Dai-dai ne In Kuma Kumma badata Ga Wannan Yaron (Abdul-wahab) Zanji daɗi Sosai In Ma Kun Hana Bazance Komai Ba."

Baba Tanimu Yace, "Tau Maddallah! Yanzun dai Babu Buƙatar Tone-tone Ina Son Amanta Komai Abarshi Yawuce Baiwar ALLAH Mun ba Abdul-wahab Khaleesat Kuma Yanzunan Ba Anjima ko Gobe ba Za'a ɗaura Auren Su Meye Ra'ayin ki?" Yaƙare Maganar Yana Mai Kallon Innarmu. Yayin da Innarmu Kuwa Ta Musƙuta Cikin daɗi da Farinciki Kafin Tace, "Wallahi Nayi Farinciki Sosai Nima Kuma da Ƙudurin Da Nazo Dashi Kenan Sai dai Wani Hanzari Ba Gudu ba Muna Neman Alfarmar Aɗaga Mana Ƙafa Mu Sanar Da Iyayen Yaron Na Wajen Ubansa Dan Karsu Zarge mu da Yin Abu Gaban Kammu, Sa'annan Kuma Bamu Riƙe da Sadaki Yanzun Bugu da Ƙari Dole Sai Munje Munɗan Tanadi Muhallin da Zai Zauna da Matarsa."

Baba Bukar Yayi Karaf Yace,"Batun Sadaki Naɗauki Nauyi Zanbiya Masa Batun dangin Mahaifinsa Kuwa ɗauki Waya Ki Sanar dasu Halinda Ake Ciki Yanzun."

"In Ma Katyne Babu Ga Tawa Wayar Ki Kira Ko ga Kuɗi Asa Maki A taki Wayar." Baba Tanko Ne Me Wannan Maganar Shima.

Dr. Faisal Yace, "Batun Gida Kuwa Kubar Komai A Hannuna Insha'allah Ba'abinda Zai Gagara."

"Ballatana Ma Ko Babu A ɗaura In Sun Kimtsa daga Baya Ai Ta Tare Ko?" Abinda Shima Baba Tanimu Yace Kenan.
Dr Faisal Yace, "Insha'allah Ma Ba Abunda Zai Gagara."

Nandai Innarmu Takarɓi Waya Takira Baba Lado Kasancewar sa Babban Wa Ga Dangin Baban Su Abdul-wahab Wanda Tayi Musu Bayani Dalla-dallah Kafin Kuma Ta Haɗasu da Baba Tanimu Ya Ƙara Kora Masu Bayani. Basuyi Wani Ja'Inja ba, Suka Amince Tareda Fatar A Hari Na Gaba Watau Na Abubakar.

Dan Haka Nan Take Dady Yatashi Ya Nuradeen Akaje Aka Siyo Dabino da Alewowi Goro ɗaine Ba'a Samo ba Wai Suntashi.


Bayan Gama Sallar Magarib A Massallacin Unguwar Su Khaleesat ɗin Liman Yayi Sanarwar Kowa Ya tsaya Akwai Ɗaurin Auren da Za'ayi Na Khaleesat.

Take Kan Mutane ya Ƙulle Wace Khaleesat kuma Bayan Wacce Ta MUTU? Liman Yace, "A saurara Khaleesat Ashe Bata Mutu ba duguwar Suma ne Tayi Ga Kuma Bayin ALLAH da Suka Ci Karo da Ƙabarinta Nan Bayan Sun Kai Nasu Mamacin Sukaji Numfashin ta Shine Fa Sukayi Jarumtar Cirota Da Harzasu Gudu Tau Amma Jajircewa da Kuma Shawarwarin Wasu Yasa Suka Tsaya tau tadai Jima Hannun su Tana Jinya Kafin Suka Samu Bakinta Tayi Musu Kwatancen Gida Shine fa Suka Maidota Gida tau Bayan Maidota Aka Buƙaci Kawai Aɗaura Auren Nata da Ake da Niyyar Kafin Ta Rasu." tau da Haka dai Aka Rufe Bakin Jama'a Aka Barsu Cikin Tarin Al'ajabi.

Nan dai Kuma Aka Ɗaura Auren Khaleesat da Abdul-wahab. Auren da Akasha Gwagwarmaya Kafin Tabbatuwarsa Auren da Aka Sha Artabu Kafin Tabbatuwarsa Auren da Aka Kai Ruwa Rana Kafin Ganin Yauɗin. Bayan Ɗaura Auren Kuma Aka Shiga Rabon Dabino da Alewowi Harma da Cimgam Ga Masu Ci Kenan. Kunun Ayan da Momy Tayi Na Saisuwa Shi Tafitar Aka Shiga Rabawa Jama'a Harma da Almajirai.

Inda Nantake Momy Tahura Wuta Taɗora Tunkuyar Tuwo da Miyan Kuɓewa Kafin Ƙarfe 9 Harsun Gama Cikin Taimakawar Su Aunty Shahuda da Kuma Mmn Walida da Tazama Ƴargida Sunƙulle da Aunty Shahuda Dama Gasu Kai ɗaya. Sai Aikin ƙuƙƙula Tuwon Akeyi Cikin Leda. Ya Nuradeen Kuwa Suka Haɗa Kuɗi Shida Dady Nan Take Kuma Ya Nuradeen ɗin Yaɗauki Sani Cikin Motar sa Suka Kwaso Kayan Drinks Su Pop Cola ne Wow! Ce dakuma Cok Kai Harma da Lemun kwalbar Da Baka Taɓa Gani ba. Aka Shiga Kwasa Ana Kaiwa Cikin Gida. Makwabta Kuwa Tuni Suka Shiga Ɓarkowa Cikin Gidan Saboda Samun Labarin Yanda Al'amari Yakasance Watau Kan Yanda Liman Yasanar da Mutane Unguwa. Sai Jaje da Barka Sukeyiwa Su Dady da Momy. Kowa Kuma Yashigo Zaici Yaƙoshi Yakuma Yi Guzuri dashi.

Habawa Tuni Gida Yacika Maƙil da Jama'a. Dama Kuma Irin Wannan Yanayin da Ake Ciki Na Halin Rayuwa Wani Rabon Sa da Abincin Tun Safe Wani Ko Na Safen Ma Bai Samu ba. Saboda Halin Matsin Tattalin Arziki da Ake Fuskanta ga Babu Tsaro Ga Yunwa Ga Fatara da Tayiwa Al'umma Ƙatutu😥 (Kai ALLAH Yataro Mana Ƙasarmu Ka Kawo Mana Mafita Harma da Sauran Ƙasashen dake Cikin Irin Wannan Yanayin Musamman Na Musulmamu.) kai Ranar Fa Anga Dandazon Jama'a Cikin ɗan Ƙanƙanin Lokaci. Kai Hatta Almajirai Saida Suka San Ana Sha'ani. Momy da Dady Kuwa Cewa suke, "Buƙin Karshe ne Sukeyi daga Khaleesat ɗin kuma Saidai Suyi Sha'anin Jika. Ai Kuwa Gara Su Zage Damtse. Gara Ma Shi Dady Akwai Wasu Gurin Matarsa Ta Gida Tau Kuma Suma duk Ya Aurar Sai Tsirarun Ƴaƴan da Take Riƙo ne.

Haka Fa Buki Yatashi Haiƙan Gida Yayi Albarkar Jama'a. Nikuwa Sai Nan nan Su Momy Keyi Dani Mezakaci Mekike So Ina Zaki? Wani Abu? Haka dai Suke Cemin Akan Duk Wani Motsi da Nayi Inda Nikuwa Naƙara Shiga NADAMA da Ganin Wautar da Natafka A Rayuwata Na Mance Irin Wannan Tsafatattaciyar Ƙauna da Iyayena Kimin. Wannan Tunanin Kan Ƙara Jefani Cikin Raunin Zuciya da Har Hakan Kan Haddasa min Sake Ɓarkewa da Kuka.

Sai Su Momy Sun Tsawatarmin Kan Indaina Ai Komai Yawuce.


Kai Ku Tambaya Ni Labarin
Abdul-wahab
(Angon Ƙamshi😅)


Wohoho Faɗar Farincikin da Ke Cikin Zuciyar Abdul-wahab ma Ɓata Lokaci ne. Tun A Massallaci Yana Jin Anshafa Fatiha Yakamo Abubakar Yarumgume Cikin Wani Irin Maɗaukakin Farinciki. Abubakar Yalafe Ajikinsa Yanajin Yanda Zuciyar Yayan Nasa Keta Bugawa Kafin Yaji Saukar Hawaye Akan Kansa. Yayi Hanzarin ɗago Kansa Yana Kallon Abdul-wahab Yace, "Ya Abdull Ai Kuka Kuma Yaƙare."

Murmushi Abdul-wahab Yayi Yace, "Ai Wannan Na Farin Cikine." Shima Kuma Yusuf Ya Matso Suka Rumgume Juna. Daganan Fa Su Baba Tanimu Ke Gabatar Dashi Wurin Jama'a Cewa Shine Angon Nanfa Aka Shiga Musbaha dashi Ana 'ALLAH Sanya Alkairi' Kamar Za'a Tsinke Masa Hannu. Bayan Anɗan Sarara Kuwa.

Can Bakin Titi Gurin Mai POS Suka Nufa Yabawa mai Pos ɗin Atm ɗinshi da Cewar Afitar Masa da Duk Wasu Kuɗinsa Dake Ciki Inda Hali Kuma Abashi Sabbi Fil. Yusuf Yazaburo Yana Faɗin, "Kai Kana Hauka ne, Mezaka yi Dasu?" In kun tanka Shi Tau Abdul-wahab ma Yantanka. Daga Sanda Mai Pos Yabashi Sabbin Ɗari-ɗari Kuwa Nan Yashiga Fallo Su Cikin Aljihu Yana Rabawa Sadaka Ga Almajirai Kai Harda Wayyanda ba Almajiran ba, Sai Karɓa Sukeyi Suna Sokewa (Haba Yanda Garin Nan Yayi Zafi😅) Nan fa Yusuf Yashiga Tareshi Yana Ƙokarin Hanawa.

Abubakar Yariƙe Yusuf Gamida Cewa, "Ƙyaleshi Yayi, Irin Wannan Ranar Ko Ba'a Sha Gwagwarmaya ba daɗi ne Da Ita Balle tasu da Ka Sani Ba Sai Angayama ba Saidai Kaba Wani Labarin ta, Kumama Wlh Ga Wayanda Yake Ba Nan Suna Ma Kallon Ɗan Baƙinciki Zaka Hana Musu Samu." Abubakar Yaƙarasa Maganar Cikin Raha. Yusuf Yayi Dariya Yace, "Tau Kuma Fa Hakane, Tau Ai Bari Kagani." Nan Yazaro Ƙatuwar Wayar sa Yarumgomo Abubakar Sukayi Salfe Kafin Kuma Yaruga izuwa Ga Angon. Yashiga Ɗaukar Hotuna da Vedio Me Abubakar Zaiyi Inba Dariya Ba? Yayinda Wasu Hawayen Farinciki da Tausayin Ɗan Uwan Nasa Ke Zobo Masa.

Dr Faisal Ma Na Gefe Sai Vedio Call Yakeyi da Dr Jabir Yana Nuna Masa Yanda Sha'anin Ke Guduna. Suna Dariyar Farinciki. Kai Abun Fa Sai Wanda Yagani.

Buki dai Ya ƙayatar Gaskiya, Sai Fatar ALLAH Yaba Ango da Amarya Zaman Lafiya. Buki dai Bai Tashi Ba Sai Karfe Goma Shaɗaya Inda Nan Innarmu Suka Haɗu da Faisal Sukayi Godiya Iya Godiya daganan Baba Tanimu Yahaɗa su Yayi Jan Hankali da Kuma Nasiha Mai Tsawo Kafin Kuma Aka Aje Ranar Tariyar Khaleesat Nan da Sati Biyu Shima Da ƙyar Baba Tanimu Ya Yarda Dan Shi Cewa Yayi Kawai Abdul-wahab Yaɗauki Matarsa Suje. Alabashi Tazauna Can Inda Suke Harzuwa Sanda Zasu Kimtsa. Sukuwa Momy duk Abinda Suke da Niyyar Yimata Sa Aika daga Baya. Tau Amma Sai Mutane duk Suka Taru Akan dai Abarshi Kan Wata Ɗaya Baba Tanimu Yace Ko Alama Ahakan dai Aka Samu Aka Kai Matsaya Kan Sati Biyun.

Dr Faisal Shine Yakwashi Su Innarmu da A Motar Sa Zuwa Gida Bayan Yayi Sallama da Su Baba Tanimu Kan Cewar Goben Kafin Su Tafi Zai zo Suyi Sallama.


Washe Gari Kafin Yatafi Gurin Su Baba Tanimu Nan Yafara Sauka Gurin Su Innarmu Bayan Tarba Mai Kyau da Yasamu Daga Garesu dagana Ya Buƙaci daga Abdul-wahab Me'ake Ciki Dangane da Inda Zasu Tare. Innarmu Ta Musƙuta Ta Soma Rattabo Masa Bayanin Kan Matsayar da Suka Kai Kan Cewa, 'Tunda Yanda Abubuwan Suka zo Gidan Na Innarmu Akwai Fili Gwargwado Ga Wani ɗaki Can Spare Nan Zai Ja Gina Yayi Masa Falo Gefe Kuma Afitar Masa Toilet Store da Kuma Kitchin Misalin dai Gini Irin Na Talaka.

Dr Faisal Ya Girgiza Kai Cikin Yabawa da Hazaƙarsu Kafin Yakarkace Yazaro Farar Ambulance Ɗin Takarda Yace, 'Tau Ga Tasu Guddumowa Shida Dr Jabir. Shi Dubu ɗari 5 Dr Jabir Ma Dubu ɗari 5 Kuɗɗi Sun Tashi Miliyan ɗaya Kenan. yakara da Cewar Suyi Haƙuri Ana Cikin Yanayi ne Na Ba Kuɗi Ga Abubuwa ne dai Barka tai. Su Innarmu Ma Sai Suka Rasa Bakin Magana Saboda Tsananin Mamaki. Abubakar Ne Ma Yayita Jarumtar Bufe Baki Yashiga Kwarara Masu Godiya Shi da Dr Jabir. Nanne Suma Su Innan Suka Samu Bakin Magana Harma da Uban Gayyar Watau Ango Abdul-wahab Sukayi Cikin Mutumci da Girmamawa Bayan Sun Karɓi Number Dr Jabir Kan Cewa Zasu Kirashi Shima Sumai Godiya.

Bayan Sun Dawo daga Rakiyarsa Abdul-wahab Yatafi Raka Maman Walida Zuwa Tasha Ta Koma Gida Dan Yin Shirin Buki ta Dawo, dan Har tace Bama Zata Koman ba Sai Buki Innarmu Tace Lalle Tafiya Ba Fashi Saidai Taje Ana Gobe Buki Tadawo.

Daganan Fa Suka Tasarma Aikin Gyara Muhallin da Abdul-wahab ɗin Zai Zauna Cikin Rufin Asirin ALLAH. Hakanan Sai Guddoma wa Suketa Samun Daga Gurin Jama'a Daban-daban Ko Ƴan Garejin su Kuɗin da Suka Haɗa Masa Yakai Dubu ɗari Maigidan sa Kyauta Sosai Yayi Masa. Innarmu Tayi Godiya ALLAH Har sai da Ta Zubar da Hawaye Ta Kuma Ƙara Tabbatar wa duk Wanda Yariƙe ALLAH Dagaske Tau Lamarin sa Bai Ɓaci Takuma Ga Ranar Tashin Dare Datake Tayi Tun Suna A Kauyen Su Na Sanyyinah Kan ALLAH Yashiga Lamarin ta Yataimaka Mata Wajen Kula da Marayun Ƴaƴanta Kar Yabarta da Wayon ta Ko dubarar ta Gashi Kuma Ubangiji Mai Tausayi Yakarɓa Dan Rasuwar Mal Rabi'u Uban ƴaƴanta Bata Taɓa Cewa Yau ya Zasuyi? Kullum Suna Cikin Rufin Asirin ALLAH. Yauda Mal Zai Dawo ta Tabbata Zaiyi Farinciki da Ita.

Wannan Kenan!!!


Akwai Wata Magana Fah Masu Karatu Akwai Wani Sirrin da bukinnan Zai Ɓangaɗo Ku muje Zuwa

Tareda Alkalamin

FA'IK ✍🏼
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 38 · 0% Book details