← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 40

Chapter.....19

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


Tau Meke Shirin Faruwa Ne? Tambayar da Nasake yiwa Kaina kenan Ko Shakka bana yi Auren Na Ne da Dr Jabir ke Shirin Tabbata. Tau Amma Ya Makomar Shirin mu da Abdul-wahab? Tau Yanzun ke Kin isa Ki tunkari Su Dady ma Da Wannan Maganar, in ma kinje Kice Musu Meye? Haka nayita Karatun Wasiƙar Jaki wanda Ko ƙaɗan Nakasa Gane Bakin Zaren Ƙarshe dai Zuciyata Ta na Sanar min Babu Abinda Yakamace ni Face TAWAKKALI da Kuma barwa ALLAH Lamari na.


Tau Amma Zan Iya Jure Rashin Masoyina Abdul-wahab? Tau ko Zakije Ki Gayawa Su Dady bakya Son Dr Jabir Abdul-wahab Kike So?

"Never! Kai Bazan Iya Ba Wallahi!" Nafurta Hakan Afili Kamar Wata Wacce Ki Shirin Kamuwa da Hauka, Haukarma Sabuwar Kamu. Nayi Lamo Acikin Kujerar Zuciyata Naci gaba da Zantuka Masu Kama da TUFKA da WARWARA! Ƙarshe A Fili Nake Tambayar Kaina Tau Wai Ita Kuma Wannan Rayuwar haka take Cike da Kalubale?


Ina Cikin Wannan Halinne Momy Tashigo ɗakin Nawa Fuskarta Cike da Fara'a Tasha Gayu Sai ƙamshi Take Bazawa Alamun dai Itakam Suna Cikin Farinciki Tadubeni Tareda Cewa, "Kije Falo Dadynku Nason Ganin ki Kuma Yayanki Yace Yana kiran Wayarki Baya Samu Lafiya dai Ko?"


"Lafiya lau Momy Na Kashe Wayar ne Kawai." Nabawa Momy Amsa Ina Mai Ƙoƙarin Samo Wata Jarumta Inya Yafa Kaina ita dan Ɓoye Halin da Nake Ciki Anawa Ganin Iyaye na Basu Cancanci Wannan Rainin Hankali daga gareni ba kuma koma mey........


"Aiko Yakamata ki buɗa Wayar Sa'annan Ki Tashi kiɗan Watsa Ruwa Ki ɗan Kimtsa!" Momy ce ke Wannan Maganar tana Kokarin Juyawa Harta Kai Bakin Ƙofar Fita Tadawo gamida Cewa, "Yawwa Haryanzun banga su Hauwa'u da Laila Sunzo ba (ƙawaye na) kin kuwa Sanar Musu?"


"Ban Sanar Musu Ba, Abinda Ni Ban Ma sani Ba Momy Sai dai Kawai Naga Mutane?" Nakarashe Maganar cikin Shagwaɓa


"Ai kuwa dai Yakamata yanzun Ki Kirasu Ki Gayamusu." Momy tafaɗi Hakan Tareda ficewa daga cikin ɗakin Nawa. Batareda ta Bawa Wancan Maganar danakeyi Mata Muhimmanci ba. Sarai! Na Lura Momy Tafahimceni Amma Sai tai Kamar Ba ta ta Kaina Alamun Wannan Karon dai Bazata Saɓu ba. Ganin Tunanin nawa ba mai Karewa bane Najanyo Hijabina Nasa, Kafin Na Nufin Cikin Falon Su Momy Inda Na Samu dady Shima Yaci Ado da Babbar Riga Shida Amininsa Suna Zaune Momy tacika Gabansu da Abincuccuka Kala-kala Ga Kayan sha nan Kala-kala Sai Tauna Naman kaza Sukeyi Gefe ɗaya Dady Nata Wayoyinsa Ga Alama Kuma Yan Uwa da Abokan Arziki Yake Sanarwa.

Nasamu Gefe na Rakuɓe Na Zauna Cikin Yan kewar Buri Da Ƙara Tabbatar wa kaina Auren Dr Jabir ya wajaba Gareni kamar Yadda Rasa Abdul-wahab Ya wajaba Gareni. Cikin Sanyin Murya Nagaida Aminin Dady Ya'amsa Min Cike da Fara'a Kafin Ya sanyamin Albarka Tareda ƙara Gayamin Lalle Na tabbata Ƴar Halak! Tunda Fidda Surutun Mutane Kuma Kowa Yaga dangin Dr Jabir Yasan Nazaɓo Irin Albarka Zan Kuma Shiga Dangin da Yadace. Kwata-kwata Bana wani Jin daɗin Wayyanan Kalaman na Aminin Dady Hasalima Wani Bakinciki ne Ke turnuke Zuciyata saidai Ina Ƙokarin danne wa ne.


"Yawwa Kina Ji Ba?" Naɗago Na Kalli Dady Sanda Yake Faɗar Hakan Bayan ya kamalla Wayar da Yakeyi Yakuma Ajiyeta Gefe. Yaci gaba da Cewa, "Kamar dae yadda kika gani Iyayen Dr Jabir Sunzo Harma Munkai Karshen Magana Nan da Sati Biyu Insha'allah Za'a ɗaura Auren ku."

"Sati Biyu????" Cikin Wata irin Kiɗima Na Furta Hakan.

"Eh Sati Biyu Saboda Shi Jabir ɗin Wata ɗaya Yarage Masa Zashi Ƙasar Indiya Ƙaro karatu Akan Wani Kwas! Kamar Yadda Suka Faɗa Tau Suna so Ayi Komai A Kammallah Kafin Lokacin Kuma Nima Haka Yayimin."


"Amma Dady Sai Kace Kun Gaji dani Sati Biyu Fa." Hawaye Suka Ɓallemin Dama Mai Neman Kuka ne Anjefe Shi da Kashin Shanu


Dady Yamurtuƙe Fuska Kafin Yace, "Dubi Wani Sakarci Kuma? Wane Irin Gajiya kuma Kin taɓa Ganin Nagge ta Gaza da Ƙahon ta? Akwai kuma wata Ƙauna da zamu nuna maki Wacce Ta wuce Mu sadaki Izuwa gidan Aurenki Ikram?"

Hawaye Nacigaba da Gowslow A Fuskata Nace, "Amma Dady..."


"Amma me? Kinga Ikram Hakan da Akayi Shine Dai-dai, Insha'allah Babu Abinda Zai Gagara duk Abinda Kike so Kije Ki rubuto Zanyi Maki Kai Har kayan ɗaki Anjima Kishirya Muje Ki zaɓa Ina fatar Kinji?"

Nagirgiza Masa Kaina Wanda Haryanzun Nakasa Daina Hawayen Wanda ni Natabbatar Bawai dan Ance Sati Biyu Bane.

Yace, "Yawwa Karɓi Ga sadakin Ki Naira dubu 50 Anjima Kuma Mata Na Nan Zasu Kawo lefe."

Nakara Girgiza Kaina "Dady Kawai Kavar Kuɗin A Hannunka Ni Ba'a bunda Zanyi dasu." Dady yace, "Jeki Ki Kaiwa Momynki Can Ku Shawarta Abinyi dasu, Ni Ta Wajena Ba'a bunda Zai gagara Insha'allah dan Nadaɗe da Shirya wa Wannan Ranar tunda Dama Nasan Tana Zuwa."


Nasa Hannu Nakarɓi Kuɗɗin Kafin Namike Ina Cewa, "Tau Yayi." haka Hawaye na Basu Tsaya ba.


Dady Yace,"Yawwa ALLAH yamiki Albarka."

Koda Nafito Tsakar Gida Ba Kowa bansan Ina Momy taje ba Dan Haka Nanufi Dakina Ina Zuwa nayi Watsi da Kuɗin A Tsakiyar Gadona. Nazube ƙasa kafin Na Fashe da Kukan da Ni Kaina Bansan dalilin sa ba, Amma Wani Sashe Na Zuciyata Yana Rayamun Cewa Halin Ko Inkula Ne Dasu Dady Ke Nunamin Akan Damuwa ta Ko wanen Su Bai damu da Ya lallasheni ba. Shine Yake Sani Kuka.

Kafin Kace Kwabo Gidamu Yacika da Makwabtanmu Da Sauran ƙawayen Momy. Sai Saukewa Da ɗorawa Suke dan Ganin Abinci Yawadaci Kowa.

Momy kam sai kai kawo take Cikin Farinciki Ba'abinda Ya shalleta Dani. Zuwa can Sukuma Sai ga Su Hauwa da Su Laila harda su Zubee Kawayen Amana. Inaga dae Momy ta kirasu Wannan ma dai Yaƙara tabbatarmin da Cewa Momy A wannan Karon Sunɗauki Mataki A kaina Ne Kuma Suna Sane da Halin da Nake Ciki Musamman ma Momy dai.


Zuwan su keda Wuya Ɗakina Yakamace Da Shewar Ƴan Mata Kafin Suka Tasani Gaba da Surutu dolena Nayi Wanka Nayi Shirya Cikin Wani Matirial Kalar Purpul Sai Wani Kyalli Nake Kamar Yaune Amarcin.


Duk Suka ɗauka "Haba Koke Fa? Amma Kin Zauna Mana kamar Wata Wadda Aka Kwanto Daga Bakin Kura?"

Daganan Laila Taɗauko Turare Tana Fesa min. Nature ta Ina Cewa, "wai meye Hakane?" duk Suka Kama Baki Kafin Hauwa Tataso daga inda Take Zaune Tace, "Bani Nan! kin taɓa Jin Wanka Yacika Ba Turare."


Hakadai Sukaita Min Iskanci Iri-iri Kamar Yadda Kukasan Kowayenne Kawaye Nayiwa Ƙawarsu. Su A Zaton su Kawaici ne Nake. Gidan Yaƙara Kacamewa ne Sanda Yan Kawo Lefe Suka Iso Wata Daga Cikinsu Taƙarkare Iya Ƙarfinta ta Rangaɗa Guɗa Aaaaayirrrrrr! Nan Fa Aka Shiga Ina Aka saka da Su Ana Ta Jere Musu Abinci Iri -Iri. Da Abubuwan Sha Kala-kala dai-dai Lokacin Wayata taɗauki Kara Najawota Ina Mai Ƙokarin Tantance Waye Yake Kirana. Sunan DR. JABIR! Nagani Yana ta Yawo Kan Scereen ɗin Wayar Nayi Kamar Bazan ɗaga ba Sai Kuma Naɗaga.


Duk Yanda Naso Yimasa Shariya Sai Abun Yagagareni Saboda Shiɗin Wani Irin Mutum ne da ba Kowane irinsa ba. Muka gaisa Cikin Mutumci haryake Sanar dani Naji Sati Biyu da Aka Ajiye? Ai kuwa kamar Jira Nakeyi Na Hau Bakina Ina Cewa Yazasu Sa sati Biyu Sai Kace Wacce Aka Gaji da Ita? Shi Sai Abun Ma Yabashi dariya Shine Yake Tambaya ta "Tau Acikin Nida Su Dadyn Waya gaji dake?" Ni Kaina Sai Lokacin nagano Wautar Maganar tawa Sai Kuma Nayi Shiru.

Yace, "kinga? Wannan Ba Wani Abun Damuwa Bane. Ai Angayama ki Uzurin da Yasa Akayi Hakan ko?" Nagirgiza Kaina Kamar Ina gabansa.


Daga can Yace, "Banji Kince Komai Ba."

Nace "Eh Dady Yagayamin."


"Tau Kingani So Nake Ayi komai Cikin Tsanaki, Yanzu Hakan Abubuwan Sun Haɗe mi Ina Ƙokarin ganin Yanda Zan tsara Su Bayaga Wannan Akwai Wani Muhimmin Abu Da Yadace Ingayamaki Duk-da bansan Yazaki Karɓeshi ba Saboda Na Sanar Maki A kurarren Lokaci amma Ni A Nawan Tunanin Ko Yanzun Ba wata Babbar Matsala bane." Yaɗan Numfasa Kamar Wanda ke Shakkar Abinda Zai Faɗa Kafin Yace, "Khaleesat Ina da Mata Harda ɗa Ina Fatar Idan Kikazo Zakuyi
Zama na Fahimta da Juna."


Wani Irin Faɗuwar Gaba Yariskeni Wanda Sai da Na Zauna kan Kujera Ba tareda Na Shirya Hakan ba, Kafin na lalubo Yawu Acikin Bakina Na Lashe Laɓɓana Da Suka yi Bushewar Nan take Nace, "Kana da Mata?"


Yace, "Bafa Wata Matsala Maman Ashraf Tana da Hankali kuma Zaki Sameta Mai Saukin Kai Nima Kuma Zanyi Adalci A Tsakanin ku Abunda ɗai Nake So Ga........"


"Haka kake Zato ba? Haka kuma Mahaukacin Tunanin ka yake Saƙa ma Macuci Kawai!" Tafaɗi Hakan Tana Kokarin Fisge Wayar dake Hannunsa Yakalle ta Amamakance Yana Cewa, "Ke Kina Hauka ne ko...... "Dif! Naji wayar taɗauke

Namike Tsaye Ina Karanto Innalillah! duk yan ɗakin Sukayo Caaa A kaina Lafiya Wanda ni Kwata-kwata Ma Na Manta da Cewar ba Ni kaɗaice Aɗakin Ba. Wanda A dazun Kowa harkar Gaban sa Yake Innalillahi da Sukaji Ina Karanto wa ne Yadawo Da Hankalin su Kaina.


Dole Nayi Murmushi Nace, "Kai Ba'a Komai fa Ni dashi ne Kawai."
Gabaki ɗaya Suka Sa Shewa Gamida Taɓewa Kafin Hauwa Tace, "Lalle Dr Nan Ƙarshe ne." Nan Fa suka Shiga Dariya ta.

Yayinda Nikuma na Sulale Nashige Toilet Ina Rufe Kofa Wani Kuka Yazomin Nikam Wace Irin Rayuwa ce Hakane? Meke Shirin Faruwa Danine? Meyasa Dr Jabir Zai yaudareni Yaƙi Gayamani Cewa Yana da Mata sai Yanzun? Shin Su Dady ma Sunyi Bincike Ko Waye Shi? Ko Kwai Sun gaji dani ɗinne dagaske Mararraba Suke Biɗa Dani???


Muje Zuwa Readers ɗina......
[9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 17 · 0% Book details