← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 40

Chapter.....31

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Maman Asharaf Takama Baki "Kai HUBBINA Ina Wani Zai Yimin Magana ma Kuma Munatare?"

"Tau Ina Ruwan su tunda Ba Addinine dasuba Sufa Agurin su Komai Ƴanci ne."

Maman Asharaf Tace, "Baban Asharaf Baka da Dama, Nidai ga Jakkar Ka." Taciro ta Tana saƙala Masa ita A Kafaɗarsa Taɗora da Cewa, "Asauka Lafiya ALLAH Yatsare Mana Kai." Sai Ji Sukayi Shima Asharaf Yace, "Ashauka Lafiya Ayya Yashale Mana Kai." Mezasu inba Dariya ba? Dr Jabir Yaɗan Sunkuyo Yana ɗan Tsakulan sa A kumatu Gamida Cewa, "Ameen ɗan Dady." daganan Yajuya Suna Gaisawa da Wani Bature da Yafito daga Nasa Part ɗin, Cikin Shirin Fita Shima.

Da Ido Kawai Yayi Ma Maman Asharaf Alama Cewar Su Koma Ciki. Sbd Ganin Baturen Yanufo Inda Suke. dan Haka Sai Taja Hannun Asharaf Suka Koma Cikin Tana Kullo Kofar Part ɗin Nasu.

Shi kuwa Dr Jabir Gaisawa Sukayi da Baturen Daganan Suke Gabatar da Junansu Yayinda Baturen Yace Sunan Sa Jacob Shima Dr Jabir Yasanar Masa Da Sunan Sa Daganan Kuma Suke Sauka Akan Step ɗin gidan Saman Suna Ci Gaba da Ba Juna Sanayyah.

Ƙarshe dai da Motar Jacob ɗin Suka Fice. Baturen Mutum Akwai Son Mutane ga Iya Tsari da Kuma Tsayuwa Akan Aƙida.

Maman Asharaf Kuwa Asharaf tayi Ma Brush dan dai ma Wanka Taso Yimasa Amma Sai Ya'azazaleta Shi Tea Zaisha. Dole Tamasa Brush Tabashi Tea ɗin Da Nufin Inyaƙare Tamasa Wankan. Daganan Kuma Tashiga Aikin Kwashe Kayan da Ta Kawo Ma Shalelen Nata, Zuciyarta Fal Tunanin Irin Dacen MIJI Da Tayi da Yakanyi Komai Don Samun Farincikinta. Abunda Yan Lokkutan da Suka Wuce Yaso Shuɗewa Saboda Auren Sa da Khaleesat da Yataso Ashe Kuma Auren Bama Mai Yuwa Bane. Tayi ta Tuna Artabun da Suka Sha A Lokacin. Wani Tayi Dariya wani Taji Kunya A Yanzun.

Duk-da Kuwa Harga ALLAH Bata Yi Murna da Mutuwar Khaleesat ɗinba, Hakanan duk Abinda Tayi A Wancan Karon, Tayishi ne Akan Kishin Mjinta Wanda Ba'a Raba Kowace Macce Dashi.

*********


Mmn Walida Ta Warke Sumul! Sai Ƙarfin Imani da Tawakkali da ke ɗawainiya da Zuciyoyin Su.

Hakanan Yanzun Sun daina Tsoron Khaleesat ɗin, Sun Saduda Kan Tunanin da Abubakar Yaɗora su Akai. Bugu da Ƙari Likitan nan da ke ta ɗawainiya dasu Tundaga Sanda Abin Yafaru Yazo Yasame Su Tareda Sanar dasu Cewa, "Abdul-wahab Yasamu Sauƙi Kuma Kowane Lokaci Zasu Bashi Sallama Bayaga Haka Yana da Magana Dasu Mai Muhimmaci Akan Abinda Yadangaci Tsakanin Khaleesat da Abdul-wahab Hakanan Su Kwantar da Hankalinsu Khaleesat Ba MUTUWA tayi ba Gaskiya, Akwai dai Wani ƘULLALLEN ƘULLI da Yake Buƙatar Warware Masu Shi Tau Amma Fa Sai Lokaci Yayi.

Maganar Sa Tasake Jefa Su Innarmu Acikin Wani ƘULLIN Bayan Wancan ƘULLALLEN ƘULLI da Yace Zai Warware Masu, Tau Amma Basa Son Hayaniya Kuma dai Sunyi Amanna Cewa, "Komai Nisan Jifa Ai Ƙasa Zai dawo." dan haka Bari Su Jirayi Lokacin Sugani. Daganan Kuma Sai Alakarsu ta Dawo Lafiya tsakanin su da Khaleesat ɗin Suke Komai Tareda Ita Lafiya -Lafiya. Hakanan daga Cikin Masu Zuwa Dubin Nasu Ba Kowane Yasanta Ba, Balle Yasan Matsalar da Ake Ciki. Yusuf ne Tau Kuma Shima Kwana Biyu Mura Ta Kwantar dashi Zazzaɓi Yakeyi Sosai Harma Saida Akayi Masa Ƙarin Ruwa. A Sanda ma Innarmu Taji Sai Cewa Tayi Ai dole ne ma Yayi Mura Ai ko Kai-kawo ɗinda Yakeyi Cikin Sanyinan daga Sokoto Zuwa Kware Ai Yasashi Mura.

Saidai Abinda Innarmu bata Saniba Shine, Yusuf Yanayin Mura ne Irin Wacce Kowane Ango Sabon Aure Kanyi, A Farkon Kwanukan Angancinsa(Wannan Sirrin Kuma Maza ne Kurum Suka Sanshi😜) Tau Kwana Biyu da Yin Wannan Maganar Da Sanyin Safiyar Yauɗin da Ta Kasance Ranar Litinin Aka Bawa Abdul-wahab Sallama Bayan Likitocin Ƙwaƙwalwa Sun ɗora shi Akan Shawarwari da kuma Magungunan da zai Ci Gaba da Sha Har Izuwa Sanda Zai Ƙara Warware wa. Sun Kuma yimasa Huɗubar Ya Rage Sa Abu Acikin Ransa Sannan Yarage Yawan Tunanin da Dai Sauran Tsare-tsare Irin Nasu Na Likitoci daga Bisani Kuma Akayi Cike-Ciken Takardu Aka Basu Sallama.

Duk Wannan ne Dai Yana Faruwa ne Ƙarƙashin Jagorancin Likitanan dai Mai ƁOYAYYEN Suna Wanda Tun Sanda Suka zo Asibitin Shi ke Basu Kulawa Akan Komai Nasu.

Yanzun Haka Office ɗinsa Suke Zaune yayinda Yake Hakimce Kan Kujerar Sa Yana Yan Rubuce-Rubuce Akan Fayel ɗin Marassa Lafiya dake Gabansa. Bayan Yakamalla Kuma Yaɗago Yana Mai Ƙokarin Cire Medical glass ɗinsa dake Kan Fuskarsa Yaɗan Busa Shi Kamar Wanda Yayi ƙura Sa'anan Ya'ajiye Gefe Yana Mai Ƙare Ma Su Abdul-wahab ɗinda Ke Zaune A Gabansa Kallo Inka Cire Mmn Walida dake Can Tana Ƙoƙarin haɗa musu Kayansu dakuma Abubakar da kecan Gurin Nemo Musu Motar da Zata Kwashe su Zuwa Gida.

Murmushi Yayi Sannan Yace, "Innarmu Ina Tayaki Murna da Ganin Wannan Ranar da Fatar Kuma ALLAH Yatsare gaba. Yaƙara Bawa Abdul-wahab Lafiya."

Innarmu tace, "Allahumma Ameen Kuma Muma Muna Godiya Ƙwarai da Gaske Bisa ga ɗawainiyar da Akayi tayi Damu Tun Sanda Mukazo Asibitin Nan ALLAH Yataimake ka Akan Aikinka Yakuma Yimaka Albarka Yajiƙan Magabata."

"Ameen Summa Ameen Innarmu Nagode." Likitan Yafaɗi Hakan Cikin Matuƙar Farinciki da Adu'ar Innarmu Kafin yaɗora da Cewa, "Kamar Yadda Nasanar da Ku Ƴan Kwanaki Biyun da Suka Shuɗe Cewa, Khaleesat Ba MUTUWA tayi ba Akwai dai Wani ƘULLALLEN ƘULLI da In Lokaci Yayi Zan Warware Maku Tau Lokacin Yayi, Sai dai Yanzun Kafin Azo Gaɓar Warware Muku ƘULLIN Ina Neman Alfarmar Kuje da Khaleesat Gidanku Tazauna gurinku Zuwa Sanda Nake Son Komai Ya dai-dai ta Sai Inzo Ayita Ta Ƙare. In Ma Goben ALLAH Yasa Abunda Nake Tsarawan Yadai-daita A Goben Tau Karku Cire Tsammanin Zaku Ganni A Goben Insha'allah."

Innarmu Takawo Gwauron Numfashi Ta Sauke Cikin Jin Irin Wannan Murɗaɗɗen Al'amari Tace, "Badamuwa Likita Zaka Samemu Da Yimaka Yanda Kace Ɗin, Muma Kuma Muna Fatar Komai Yatsarun Gobe dan Fita daga Cikin Wannan Ruɗu da Ruɗanin da Muke Ciki."

Ɗan Murmushi Likitan Yayi Gamida Ɗan Juyawa Akan Kujerasa Sa'annan Yace, "Tau Shikenan Innarmu Ina Godiya da Wannan KARAMCI Kuma Karku damu da Yawa Harku Zurfafa Cikin Wani Tunani da Zai Iya Sababba Maku Wani Tention! Insha'allah Komai Yakusa Zuwa Ƙarshe."

"Muna Fatan Hakan!" Innarmu ta Faɗa. Dai-dai Lokacin Kuma Abubakar Ya'iso Office ɗin Bayan Wata Nas tayi Masa Iso Gurin Likitan. Ya Sanar dasu Cewa, Ga Mai Motar Ya'iso.

Dan Haka Likitan Yamiƙe daga kan Kujerar da Yake Zaune Tareda Cewa, "Tau Innarmu Zaku Iya Tafiya Ga Wannan."Yamiƙo Mata Farar Ambulance Kafin Yaɗora da Cewa, "Kuɗine Ba Yawa Ku ɗan Ƙara Kuyi Na Mota ALLAH Yakai ku Lafiya."

Innarmu Tace, "Ɗannan Irin Wanna Hidima Haka Batayi Yawa ba?"

"Batayi Ba Innarmu Badan Aikin Yayimin Yawa ba Ma Ni Zan Kaiku Hargida."

"Tau ALLAH Yayi Albarka Yasa Agama da Duniya Lafiya, Yakuma Sanya Muku Albarka Acikin Aikin Ku."

"Ameen!!!! Innarmu Abunda Muke Buƙata kenan A Gurin ku." Likitan Ya'amsa da Hakan Kafin Yaɗan Tako Masu Zuwa Wajen Office ɗinsa Yadafa Kafaɗar Abdul-wahab Tareda Cewa, "Abdul-wahab yau Sai Gida Ko?"

Abdul-wahab Ba Baki Sai Fara'ar Da Yake tayi Kamar Wanda Akayiwa Bushara Da Kujerar Hajji. (Kunsan fa daɗi ne Ga ita ga Wanda Baije ba Kuma Ba Kuɗin Zuwa😅) Murmushi Kawai Likitan Yayi Tareda ɗan Bubbuga Kafadar Abdul-wahab Kafin Yace, "ALLAH Yakaiku Lafiya." Yaɗan Juyo Yana Miƙawa Abubakar Hannu Sukayi Musabaha Kana Yaɗora da Faɗin, "Wish U All d best Abubakar." Yajuya Yatafi Abinsa Yabarsu Suna Ta zabga Masa Godiya da Tarin Fatar Alkairi. Sunaji Nan duniya Ba Mutum Mai Kirki Kamar sa.

Innarmu Suka Shiga Yin Sallama da Mutanen da Akayi Sabo dasu Na ɗan Zaman da Akayi Suna Masu Yimusu Adu'ar Suma ALLAH yakawo Masu Wa'adin Zaman. Haka Suka Raba Masu Sauran Kayakin su Irin Su Jikkar Pure water da Sukan Siyo da Kuma Kayan Fruit ɗinda Tun da Suka Zo Asibitin Basa Rabo dasu da Dai Yan Sauran Tarkace Hakanan.

Wayanda Aka Shaƙu dasu Sosai Kuwa Aka Shiga Musanye Number Tareda Bawa Juna Adrees. Daganan Kuma Sukayi Haramar Tafiya.

Abdul-wahab dai Sai Kallon Mahaukatan dake Gurin Yakeyi. Yana Ayyana Daɗa Shima Haka Yayi Tayi ko? Kai ALLAH Yabar Masa Mahaifiyarsa Harma da Yan Uwansa. Haka Suka ɗunguma Cikin Mota Cikin Wani Irin Farinciki Ma Bayyani.

Daganan Suka Kama Hanya yayinda Hira Ta Ɓarke Tsakaninsu Inka Cire Khaleesat da Tayi Nisa A Duniyar Tunani Kala-kala. Duk-da Kuwa Sukan Haɗo da Ita Acikin Firar Tasu Saidai Nata Raddin Baya Wuce Uhumm Ko A'a Ko Kuma Murmushi.


Karfi Goma Shabiyu (12:00pm) Motar tasu Tayi Parkinq Acikin Unguwar Tasu Bada Wani Jinkiri Ba Suka Shiga Fitowa Yayinda Mmn Walida da Abubakar Suka Shiga Firfito da Kayan Su. Yaran da Suka Baibaiyesu Suna Oyoyo Ga 'Innarmu (dama Innarmu Mutuniyyarsu ce Sosai Kullum Baka Rabata dasu Cikin Gidan ta dan Haka Sanda Batanan Sai Sukayi Maraicinta.) Sune Sukai ta Shigar Musu da Kayan Cikin Gida. Inda Hayaniya da Murnar Yara Tasanarda Iyayen Su (watau Makwabtansu Innarmu) Cewa An Sallamo Su Innarmu daga Asibiti.


Take Nan Fa Suka Shiga Shigowa Yiwa Innarmu Barka Musamman daga Cikin su Wayanda Basu Samu Zuwa duboshi (Abdul-wahab)Ba.


Tsakar gida Suka yi Shimfiɗa Iskar Hunturu Nata Kaɗasu dan Muna Yanayin Sanyi ne Kuma Yau Antashi Garin Yayi Dum!(Babu Rana). Mmn Walida da Khaleesat Suke Aikin Kakkaɓe ɗakunan Nasu Innarmu Wani Abun Ma Yayi Hunhuna Sbda Rashin su A gidan.

Haka Suka Shiga Wanke-wanke Duk-da Ma Innarmu da Mmn Walida Nata Ƙokarin Hana Khaleesat ɗin Aiki Amma Ina Taki Tare Sukayi Komai. Abinci Kuwa Basu da Matsalar sa dan Tuni Makwabta Suka Dinga Yo Masu Aiken sa Gashinan Iri-iri.

Humm Ku Tambayeni Zuciyar Abdul-wahab?


....................
FA'IK. ✍🏼✍🏼✍🏼
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 29 · 0% Book details