Chapter.....23
So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mallakar 👇
Fa'IK ✍
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.
FADAKARWA.
Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.
Bissmillahi Rahmanin Raheem
Sai da Aka Kira Magrib Yusuf Yazo Yana Tashin sa, Dan Baccine Yatafi Dashi Sosai Wanda Baima Zata ba, Arwallah Sukayi Suka Rankaya Zuwa Massalaci Bayan Sun idarda Sallah Suka Nufo Gida Bakin Ƙofa Suka Samu Abubakar Yayi parkinq da Mashin Yana Jiransu.
Saida Suka Gaisa Kafin Abdul-wahab yahau Mashin ɗin da Nufin su Wuce kawae Yusuf Yacakumeshi Tareda Cewa, "Ai Wallahi Baka Isa ba, Yazaka Wuce Bamu ci Abinci Kuma Bakaje Kayiwa Umma Sallama ba?" Abdul-wahab Yahararesa Sa'annan Yasauka daga Mashin ɗin Yanufi Cikin Gidan Batareda Yace Uffan Ba.
Shidai Abubakar Sai Aikin Kallon su Yakeyi Yana Murmushi dan Duniyar ALLAH Yusuf da Abdul-wahab Suna Burgeshi Hardai Inyaga Suna Drima Kamar Bazasu Shirya Ba. Tau Suna nan dai Har Saida Suka Yo Sallar Isha'i Sa'annan Suka Wuce Duk-da Kuwa Cewar Abdul-wahab Baiso Hakanba Amma Yusuf ya Rinjaye Shi.
Bayan Sun Iso Gidan Abubakar Yaje Maida Mashin ɗin Abokin sa Da Ya'aro Yayinda Shikuwa Abdul-wahab Yashigo Cikin Gida Yasami Innarmu Zaune A tsakar gida Tana Aikin ɗaura Lalle Wata Yar Makwabtansu Na Tayata. Kallo tabishi dashi Kafin Ta'amsa Gaisuwar da Yakeyi Mata Kai tsaye ɗakin su Yanufa Innarmu Takaɗa Baki takirasa
"Abdull!"
Cak! Ya tsaya Kafin Yayi Ƙoƙarin Saita Nutsuwarsa Sannnan Yajuyo Gareta Gamida Cewa, "Na'am Innarmu?"
"Yanaga Kashigo gida Hajaran Majaran ne Haka Lafiya?"
"Ba'akomi Innarmu Kawai Nagaji ne Wallahi." ya'amsa yana mai Ƙokarin Nuna Ba Komai ɗinan.
Innarmu tagirgiza Kai Kafin Tace, "Tau Amma ai Ka Nemi Abinci Kaci ko? Kila bacin Gajiyar harda Yunwa Naciki."
Ɗan Murmushi Abdul-wahab Yayi Kafin Yace, "Eh Zanci Wai Ina So inɗan Watsa Ruwa Ne."
Innarmu Tasake Girgiza Kan ta Gamida Cewa, "Shikenan Ai ina Shi Auta? (Tana Nufin Abubakar)"
Abdul-wahab yanufi ɗakin Nasu Yake Cemata Yaje Yamaida Mashin ɗinda Ya'amso.
***********
Mai Karatu Yakamata Musan Waye Dr Jabir da Ahalinsa.
Dr Jabir dai Ɗane ga Malam Badaru Haifafen Garin Birnin Kebbi.
Dr Jabir Shine ɗa na Farko A gurin Iyayen sa Sai Ƙannensa mata Ukku da Suke Binsa.
Mahaifinsu Mal. Badaru Mahaifiyarsu ce Kaɗai Matarsa Suma Kuma Su Huɗu ne Rak! Mata Biyu Maza Biyu Dr Jabir Shine Ɗa Na Farko Sai Kuma Ƙanwarsa Sajida Mai Bimata Mu'az Sai kuma Ƴar Auta Fa'izah.
Asiya (Maman Asharaf) ɗiyar Kawun sa Ce, Mahaifinta Shine Yayan Mahaifiyar Su Dr. Jabir Asiya itace Babba Sai Kuma Ƙanwarta Safiyyah Sukaɗai ALLAH Yaba Mahaifinsu duk Sauran Rasuwa Sukeyi.
Dan haka Auren Dr. Jabir da Asiya (Maman Asharaf) Auren Zumunchi ne Wanda Yasamu Asali Tun Sonda Shi Mahaifin Asiyar Keyiwa Dr. Jabir Kuma Yakasance Ma A Hannunsa Dr. Jabir Yatashi Har zuwa Sanda Akayi Auren Nasu Kuwa. Faɗar Kuwa Irin Kamalar da Kuma Tsagwaron Ilimi na Islam da Boko da Suke dashi ma ɓata Lokaci ne Hakanan Arziki dai Suna dashi gwargwado Cikin Family Nasu Ba Hayaniya Sosai Duk-da Baza'a Rasa Ƴar tawayar dake Tare da su ba tunda dai Munsan Rayuwar Ba Hundret Pacent Bace. ALLAH ɗai Ya'ishi Kanshi.
Wannan Kenan!!
Tunda Aka tsaida Ranar Aure na Yazama Gidan Namu Ba'abunda Suke Sai Shiri Ko Tsintsiya Kaga Anshigo da Ita Gidan Katamabaya Za'a cema Ta Buki Ce.
Yau Saura Kwana Uku Buki Tuni Komai Ya Kam-Kama Na Abinda Yadangaci Buki Tuni Dangi na Nesa yan Adamawa da Kogi Suka Soma Isowa Gida Yasoma Albarkar Jama'a! Sai Jike-jike da Hade-Haɗe Ake Bani Wasu Insha Cikin daɗin Rai Wasun kuwa Sai Momy da Ƙanneta Sun tasani Gaba da Masifa Sannan Fa Zansha! Ta ɓangaren gyaran Jiki Shima ba Kama Hannun Yaro. Ƙawaye Na Jiki kuwa Kullum Nan Suke Wuni Ana Tsare-tsare Yanda Abubuwan Yakamata Su tafi. Nidai Nawan dasu Ido ne Kurum! Saidai Inaji Ajikina Bazata Saɓu ba Raba Kaina da Soyayyar Abdul-wahab! Wannan Wani Abune Tsararre Acikin KUNDIN ƘADDARATA tun daga 'Lauhul Mahfuz' sbd Haka Nashiga Tufka da Warwara Kan Yanda Zan Samarwa Kaina Mafita. Waya Kuwa Kullum Sai Mun Raba Dare Munayi da Abdul-wahab Yana Mai Ƙara Sanarda ni Irin Tsantsar Ƙaunar da Yakemin Tareda Cewa Babu yanda Zamuyi da Ƙaddarar mu Saidai Mu Karɓa da Hannu Biyu.
Dr.Jabir Kuwa In Yakira Sai Naga Dama Nake ɗagawa Sanda Yazo Hira Kuwa Haka zai ƙarashe Surutunsa Yawuce Batareda Yagane kaina Ba!
********
Suma dai Su Abdul-wahab Shiri Sosai Sukeyi dan Bukin Yusuf Yana ƙaratowa dan haka Basu ba Zama Kullum Cikin tsare - tsare Ake.
Dan Haka sai Kan Abdul-wahab Yaɗau Caji Sosai! Komai Kuma Yaƙara Rincaɓe Masa Har Wata Yar Rama Yayi Ga Wani Uban Fari Kal! Da Yaƙara Yi Sai Siririn Hancinsa Yaƙara Fitowa Yana Ƙokari iya Ƙokari dan Ganin Yamanta da Khaleesat A ransa Hakanan Baiyi Ƙasa A Gwaiwa ba Wajen Yin Adu'ar ALLAH yacire masa Sonta indai har itaɗin ba rabonsa bace Kuma ba Alkairi Bace Agareshi! Saidai Kullum Kamar Wanda Ake ƙara yiwa Allurar Son Khaleesat ɗin dan haka sai yayi Tawakkali Ya fawallawa ALLAH Komai Ta ɓangaren Yusuf ne Kawai Yake Samu Matallafi Mai Bashi Shawara Yana kuma ƙara tunatar dashi Alfanun Fin Ƙarfin Damuwar Tasa!
Tuni dai da Aka Soma Bukin kamar yadda Aka san Al'adar Basakkwace Akan Sanya Amaryar Lalle ne Ranar Laraba sauran Ranakun da Kan Biyo Baya Amarya da Yan gidan su Kan Shirya yan Bukukuwansu Irinsu Ƙauyawas day, Fulanis Day, Party, Kamu, Deener, da Dai Sauran su harzuwa Ran Assabar inda nanne Ake Tuƙewa da Ɗaura Aure da Dare Kuwa 'JIRGIN SUNNAH' Yatashi da Amaryar zuwa gidan Mijinta!
Tau A wurin su Ma Haka ce Takasance Kuma Komai yana tafiya lokaci guda (ina Nufin Gidan su Khaleesat da Kuma Nan Suma Yusuf) Saidai A ɓangaren Su Khaleesat Ansamu Cikas! Domin dai Ana tsaka da Buki Wanda Yazo dai-dai Ranar Jumu'a Ranar Kuma Akayi Ƙayatacen 'Kamu' Ana jiran Gobe Assabar Aɗaura Auren Amaryar ta Tare.
Tau Amma me? dare liss Angama 'Kamun' Kowa yagaji Sai Ma huta Yake Nema Amma Mezai Faru? Amaryar daga Dawowa Kamun tashiga ɗakin dan cire Kayan tana Mitar Sun Isheta da Zafi Kawai Akaga tazube ƙasa babu Alamun Numfashi Tareda Ita Lamarin da Yajanyo Hankali Ƙawayenta suka Yo tururuwa Akanta Suna Kuwar kiranta Kamar Maƙwagoronsu Zai Tsage! Amma ina Amarya Khaleesat bataji sai Wani Kumfa ke Antayowa daga bakinta yana kwarara A Ƙasa!
Momy kamar Zata Tashi Sama ta ratso ɗakin da Mutane suka sanya Khaleesat ɗin Atsakiya Suna Kuka! Momy ta durƙushe Gabanta Tana Aikin Shafa Mata Ruwa A Fuska bakinta bai Futa da Faɗin "Innalillahi Wa 'innalaihi Raju'un!" Amma ina Ihunka banza dan Babu Alamun Rai Tare da Ita. Momy Cikin Kuka tamike Tanufi ɗakinda Dady Yake Tana Kuwar kiransa,"Dadynsu Khaleesat Ta Mutu! Nashiga Ukku Zo Kagani Dadynsu! Khaleesat ɗita Babu Ciwo ba Komai Amma ta Mutu!"
Kalaman Sunzowa dady Kamar Saukar Aradu da Ya Nuradeen dake can Shima ɗakin da suka saba Sauka dan Haka A Sakwane Suka Fito Har suna Karo da Juna Wajen Shiga ɗakin. Wanda Tuni yarikice da Koke-Koken yan Uwa da Abokan Arziki! Ya Nuradeen yaɗaga Hannun ta Amma sai Yakoma Yaraf! Yafaɗi tabbacin Babu fa Numfashin Tareda Ita.
Wasu Hawaye Masu Zafi Suka Fito daga Cikin idanunsa da gudu suka Soma Anbaliya A Fuskarsa yaɗago yana Cewa, "Shikinan Momy Kun kashe Khaleesat da Kanku Zuciyarta ta buga! dama Nace Muku Ku Bar Lamarinan Tunda Bata so Abata wanda takeso Amma Kunƙi tau Gashinan Kun Kasheta!" yaƙarasa Maganar Cikin Rawar murya! Duk Ilahirin Jikin Momy Rawa Yakeyi yayinda Shi kuwa Dady Duk Wuta taɗauke Masa Hankalinsa In Yayi Dubu duk Yatashi! Yace, "Wace irin Maganar Banza ce Kakeyi Nuradeen?"
Yayinda Momy Kuwa Sai karkarwa Jikinta Ketayi Tana Mai Cigabada Share Hawayenta.
Ƙanwar Momy ce Watau Mami Iyabo Cikin Hausarta da bata Fita Sosai Tace, "Ba Wananne Yakamata Ayi Ba Muɗaukesi Zuwa Asibiti domin Ceto Rayuwar si..."
Kamar Jira Suke tayi Maganar Dady Yajuya Yana Mai Cewa "Bari Naje Na samo Mana Abin Hawa Kutallafo ta Mugani!" Sai Ƙokarin Sharce Zufa Yakeyi.
Mami Iyabo ce Ta Sunkuci Khaleesat ɗin dake Miƙe Samɓal Babu Alamun Numfashi Tareda ita Zuwa Waje. Lamarin da Yaƙara Tunzura Zuciyoyin Mutanen da ke Gurin Kenan ganin Cewa Yanzun Fa Ake Tareda Ita Ƙalau! Kai Mutum Ba bakin Komai yake ba A gurin ALLAH!
Momy kam biye ɗai take dasu Batareda tasan ma inda take jefa ƙafarta ba Balle tagano Cewa bata da Mayafi ko Takalmi ba. Ɗaya daga cikin Ƙawayen Amaryar ne ta lura da halin da Momy ke ciki dan Haka tayi hanzarin Lalubo Hijabi tabawa Momy da kuma Silifat ɗinda tagani Batareda tasan Wa yake dasu ba!
Tau waye yake tasu ma Yanzun? Illai dai komai Kasamu Ka yaɓa! Gudan Amarya da Aka taru domin ta ba Lafiya? Koda Suka fito Dady Yayiwa wani Makwabcinsu Magana Harya fito da Motar sa dan haka Su Momy da Mami Iyabo Shigewa Sukayi Baya Tareda Amarya Khaleesat Dama Shi Dady Tuni Yana gidan Gaba. Duk Yadda Wasu Suka So Zuwa ba Wuri, dan Amaryar Mike take Samɓal! Ba Wurinda ke Motsawa Dole haka Suka Haƙura Suna mai Fatar ALLAH yakawo mata Sauki! Ya Nuradeen Kuwa Titi Yanufa Yasamu Mai Kabu-kabu (Ɗan Acaɓa) Yatara Yabi Bayansu.
Gidan Uwargida Fa Sarautar Mata?
(Maman Asharaf)
Uwargida Tayi Kyau Abinta Cikin Wani Tsadadden Les! Kalar Mlik Sai Ƙyalli Takeyi Tana ta Kai Kawo Cikin yan Uwa da Abokan Arziki da Suka zo tayata Shirya Abinda Zatayi Taron Bukin Ta Na Gobe.
Kayan Snack ne Annan Suna ta Aikin Tuyawa, Harda Su Sajida Ƙannen Dr Jabir ɗin Suna Nan Ita Suke ta Taya KISHI.
Dan Haka Ko Wannan ɗai yana ƙara kwantar mata da Hankali Taji Cewa lalle Itace Sarautar Mata Donoth ɗinda Ake Toyawa ne taɗebo Cikin Flet Kafin Tabuɗe ɗan Ƙaramin Frij dake Girke A Kitchin ta Jawo Gwangon Maltina Mai Sanyi Har Yana Raɓa tadora Akan Farantin Tanufi ɗakin Oga, Yan Uwa sai Tsiya Sukeyi Mata Ana ta Dariya!
Masu Karatu Anan Zan Numfasa Muje daku A Gaba
Tareda
Alkalamin
FA'IK.
[9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪🏻J.A.W 💪🏻
❤❤SONEEE ....💕💕
(Silar Komai.)