← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 40

Chapter.....7

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.

Bissmillahi Rahmanin Raheem

Daram Dam Dam!! Shine Abun Da Zuciyata Tayi Naɗago Ina Kallon Dady Mu Cikeda Tashin Hankalin Da Nakasa Ɓoyewa Nace, "Dady Alhaji Saminu? "

"Eh Alhaji Saminu Kuma Nabashi Damar Turo Magabatansa Saboda Haka Saiki Kula Banbancin Ki Da Matar Aure A Yanzu Kaɗanne. Ke Yanzu Ƙarama Ce Amma Nan Gaba Zaki Gano Alfanun da Mu Iyayenki Mukayi Maki.

Alhaji Saminu Yagirmemiki Nesa Ba Kadan Ba, Sannan Shi Yake Da Kuɗin Da Zai Tallafi Bukatunki Amma Abdul-wahab Shi Ƙuruciya Ke Ƙuruciya Tau Waye Zai Kwaɓi Wani? Sannan Shi Kansa Meyaci Balle Yabaki? Babu Wani Abu Da Zaki Tsira Dashi Face Soyayyar sa Wadda Ita Ɗin Bata Iya Cika Guraben Ingantan Rayuwarki Ba. Banbanci Dae Zayyawa Tsakanin Alhaji Saminu da Abdul-wahab Kuma Duk Wani Mai hange Na Alfanu Zaya Yaba Da Zaɓin mu A gareki Banda Ke Da A Yanzu Da Soyayya Ta Makantar Ta Kuma Rufewa Ido."

"Dady Kutaimaki Rayuwata Wallahi Bana Son Alhaji Saminu Ni Abdul-wahab Nake So. Wallahi Bazan Iya Rayuwa Babu Abdul-wahab Dan ALLAH dady Ku....." "Ke! Ke! Ke! Kin Ishi Mutane Da Hayaniya Oya Fice Daga Falon Nan Shasha Kawai Ana Nunamaki Gata Kina Wani Haukan Banza. " Dady Ke Fadar Hakan Cikin Fusata Sai Ga Momy Tashigo Falon Tana Faɗin, "Bari Nayima Maganin Yar Banza. "


Tana Faɗin Wannan Ne Tana Dube-Duben Inda Zata Samu Wayar Wuta Ganin Hakan Yasa Nai Azamar Ficewa Daga Falon Ina Ta Kuka Tareda Ihun Wallahi Bana Son Alhaji Saminu

"Ja'ira Daki Tsaya Ki Ga Yanda Zanyi Maganinki." Momy Ce Ke Wannan Maganar Ranta A ɓace

Kan Katifa Nazube Inata Gurshuƙeƙen Kuka Kamar Raina Zai Fita Inajin Wannan Shirin Kamar A Mafarki Tayaya Zan Iya Rayuwar Da Ba Abdul-wahab? Sannan Shima Kamar Yanda Nafahimci Maganar Da Suke Can Gidansu Akwai Matsala Duk Meye Masababbin Wannan Damuwar Meye Laifin Sa? Dan Baya Da Kuɗi? Tau Ai Ba kuɗine Farinciki Ba.


"Wayyo ALLAH Abdul-wahab Inba Kai Mutuwa Zanyi. " itace Kalmar Da Nake Ta Nanatawa Cikin Kuka


*******

Sanda Su Abdul-wahab Suke Komawa Gida Ana Gabda Sallar Magarib Dan Har Wasu Massalatai Ansoma Kiran Sallah Adaidai Wannan Lokacin Ne Kuma Kk Napep ke Aje Maman Walida Da Yan Yaranta Guda Uku Ammar (mai Sunan Babansu) Da Walida Sai Kuma Hanifah.

Cikin Farinciki Su Abubakar Suka Tareta Suke Kuma Tayata Sauke Kayan Suna Cewa, "Maman Walida Kinyo Tafiyar Dare." Cikin Gajiya Da zaman Mota Tace, "Kudai Ku Bari Kawai Motar Tamuce Ta Lalace Mana Dai-Dai Nan Garin Talatar Mafara Kafin Ta Saɓa Hanifa A Kafaɗa Tanufi Cikin Gida.

Sukuwa Su Abdul-wahab Da Abubakar Suka Shiga Hidimar Shigarmata Da Kaya Cikin Gida. Innarmu Kuwa Sai Kai Kawo Takeyi Da Yan Jikokinta Cikin Farinciki Da Murnar Ganinsu Bayan Tsawon Lokacin Da AKa ɗauka Basu zo Sakkkwato Ba. Kowanensu Buta Yaɗauka Yayi Arwallah. Su Abdul-wahab Suka Nufi Massalaci Yayinda Sukuwa Su Innarmu Sukayi Haramar Tasu Sallar Nan Gida.

Bayan Sungama Sallah Innarmu Tagabatar Musu Da Abinci Da Kuma Fura Mai Sanyi Itadai Maman Walida Furar Kawai Ta iya Sha Saboda Gajiya Kafin Innarmu Tadubeta Tana Mai Cewa, "Akwai Ruwa Ki ɗiba Ki watsa Ko kya Wartsake. " Dan Haka Sai Tamike Taɗibi Ruwan Ta watsa Tafito Ne Sanda Su Abubakar Suka Dawo Daga Massalaci Nan Kuma Aka Shiga Firar Yaushe Gamo? Inda Nanne Abdul-wahab Yazaro Wayar Sa Yaturawa Gimbiyar sa Sakon Sun Dawo Sai Dai Ga Mamakinsa Haryanzun Ba Reply Ɗinta. Abinda Kuma Bai Taɓa Faruwa Ba.


Dan Haka Duk Sai Walwalarsa Tarage Yakeji Tamkar Yayi Tsunsuwa Yaje Gareta Yaji Meyake Faruwa. Sai Firar Tasa tazama Rabi da Rabi Hardae Maman Walida Ta Sanya Baki Da Cewa "Nikam Ƙanina Abdul Ko Da Wata Matsalane? Duk Nakasa Gamsuwa Da Yanda Nasameka menene?"


"Badole Aunty Ki Kasa Gamsuwa Da Yanda Kika Samesa Ba Yaɗaukowa Kansa Abunda Zai Hargitsa Masa Lissafi." Abubakar Ne Ke Wannan Maganar Acikin Ransa Amma A Fili Sai Yake Cewa,"Maman Walida Ai Dole Ki Samesa A Haka Exam Zasu Soma Bayan Sallah Nan Fa?"

"Eh Tau ALLAH Yataimaka Sai Adage Da Karatu Da Kuma Nafilfilin Dare Ko Mu Haka Mukeyi Sanda Muna Jarking" Ta Kammala Maganar Tana Dariya Wanda Sai Da Kowa Ya Dara Dalilin Haka Ma Sai Firar Tajuye Ta Koma Ta Skull Maman Walida Tashiga Basu Labarin Yanda Tayi Karatunta Can A Da Su Kuma Suna Gayamata Irin Sauyin Da Aka Samu Yanzu A Karatun Nan Kuma Tashiga Basu Labarin Irin Burin Da Taciwa Karatun Ta Taso Ta Kammallah Ta zama Ma'aikaciyar Jinya Dan Ta Tallefesu Saboda Taga Irin Banbancin Da Ake Nuna Musu A Dangi Sai Dai ALLAH Bai NuFa Ba.


Sai Dai Kuma Tana Farinciki Da Cewar Gashi Yan Ƙannenta Zasu Cika Mata Burin Hakan Dama Burin Innarmu Na Son Ganin Sunyi Karatu Sun Zama Wani Abu. Sanda Take Maganar Abubakar Yaɗago Kansa Yana Mai Kallon Dan Uwansa Tareda Yimasa Alamar Ka Gani Ko Yaya? Shikuma Abdul-wahab Sai Yay Biris Tareda Yimasa Kallon 'Ku Ta Shafa Nidae Aure Nake So. '


Da Sanyin Safiya Innarmu Nata Kai Kawo Tsakanin Madafi Da Ɗaki Karin Kummalo Take Hadawa Kwatsam! Taga Santaleliyar Budurwa Tafado Gidan Da Sallamar Ta Innarmu Ta tarye Ta Cikin Mutumci Tana Mai bata Guri Tace Ta Zauna.

Bayan Na Zauna Ne Muka Kara Gaisawa Cikin Kunya Nace Mata Gurin Abdul-wahab Nazo Cikin Mamaki Tai ta Nanata Sunan Kafin Tace, "Yana Ciki Bari Nai Masa Magana. " Kafin Innarmu Tanufi Ɗakin Su Abdul-wahab Ɗin tana Buga ƙofarsu Akai Sa'a Abdul-wahab Ɗin Yabude Ƙofar Kafin Innarmu Tace, "Kayi Bakuwa." Batareda Ta jira Cewarsa Ba Tai Juyawarta.

Tana Zuwa Cikin Fara'arta Tace, "Yana Zuwa Kinji 'Ƴata? " Nace Mata "Tau. " Kafin Tajuya Taci Gaba Da Kai Kawonta Tsakani Kitchin Da Ɗaki Tana Kula Da Girkinta Duk Inda Ranta Yake Yaɓace Saidai Bazaka Taɓa Ganewa ba Saboda Tsananin Dangana Da Kuma Hakuri Irin Na Innarmu.

Shikuwa Abdul-wahab Tsaye Yayi Cikeda Zullumi Da Tarardaddi Wacece Tazo Neman Shi Hargidan Su? Shida Ba Wasu Yan Mata Yake Dasu Ba Khaleesat Ce Kuma ko Sau ɗaya Bai Taɓa Gigin Kawota Gidan Nasu Ba Tau Wacece? Tambayar Da Yakasa Amsawa kansa Kenan Dan Haka Sai Yazaɓi Yazo Kawai Yaga Ko Wacece. Wani Irin Luguden Tara Zciyarsa Tayi Sanda Yayi Tozali Da Kyakykyawar Fuskarta Fara Fat Wacce Babu Wani Kwalli A kanta Sai Annuri Kyau Take Fitarwa Wanda Ake Kira Natural Ɗinan.


"Khaleesat! " Yafurta Hakan Batareda Yasani Cewa A Fili Yayi Maganar Ba. Jin Amon Muryarsa Yasa Na Ɗago Ina Kallonsa Yakaraso Cikin Kasalar Jiki Kafin Yace, "Khaleesat Waye Yanuna Maki Gidanmu? "

"In Banda Abunka Ai Matanbayi Baya Ɓata Habibi. "

"Hakane, Sai dai Abin Da Mamaki Please Ki Gayamin Waye Yanuna maki Gid..... "

Cikin Ƙosawa Nataresa Da Cewa, "Wannan Ba Shine Abinji Ba Kuma Dae Nice Nazo Gurinka Da Tawa Matsalar Dan Haka Kabari Nafaɗi Tawa Matsalar Kaima In Wannanne Yadameka Sai Ka sameni A gida Zangayama Wanda Yakawo ni. "


Abdul-wahab Ba Baki Sai Kunne Yarasa Abin Cewa Face Kai Kawai Da Yake Ta Girgizawa Kafin Yadan Motsa Laɓɓansa Da Nufin Cewa Wani Abu.. Nataresa Da Cewa, "Abdul-wahab Matsala Gagaruma Ke Tunkarar Soyayyar mu Iyaye Na Suna Neman Hana Mana Cikar Burinmu Dan Sun Bada Aurena Ga Waninka Yanzu Haka Ansa Rana Nan Da Wata Ɗaya Shine Nazo Naji daga Gareka Meye Abinyi?"

Abdul Duk Hankalinsa Yatashi Ya kuma Ruɗe Yace, "Tau Meyayi Zafi Haka Khaleesat? Meyasa Su Momy Bazasu Dubi Irin Soyayyar da muke Wa juna ba? Meyesa Su Momy Bazasu Kalli Makomar Rayuwar mu Ba idan Har Suka Rabamu Da Juna ba?"


"Abdul-wahab Duk Ba Wannane Gabansu Ba, A Yanzu Kuɗi Suke Kallo A yanzu Zamani Yazo Da Kuɗi Sune Komai In Kana da Su Tau Ba'a Bukatar Wani Bincike. "

"Hummm! " Abinda Abdul-wahab Yayi Kenan Domin Duk Inda Wani Tunani Nasa Yake Yatsaya Cak!


"Habibi Nazo ne Muje A Ɗaura Muna Aure A Kowane Wurine Kaga Yadace Muje Sannnan Duk Inda Ka'ajiyeni zan Zauna. Wallahi Abdul Bazan Iya Jurar Rashinka ba Zan Iya Komai Dan Ɗorewar Soyayyar mu. "


Abdul-wahab Yajuya Yakalli kowane Sashe Na Gidansu Babu Kowa Atsakar Gidan Nasu Sai Su Kaɗai Kafin Yadawo Da Kallonsa Gareni Yace, "Khaleesat Wannan Ba abune Mai yuwuwa ba Zo muje Gurin Innarmu. Gara Dai Aje Can Gidan Naku A gyara Matsalar. " "Matsalar Bata Gyaruwa Indae Gidanmu ne Da Tana Gyaruwa Bazan zo Gidanku A mamakance ba. Kaidai Wannan Kawai Shine Mafita."

Abdul-wahab Bai Damu Da yabani Amsa ba Sai kawai Yajuya Ya Nufi Ɗakin Innarmu Yana Yafito ni Da Hannunsa Cewa, "Zomuje."

Innarmu Takare Komai Nata Zaune Kawai Take Tana Juya Kunun Dake Gabanta Cike Da Boket Domin Tabbatarwa Yaji Sugan Da Tasa Masa Yayinda Su Walida Ke Gabanta Rike Da Cup Dinsu Jiran Tazuba Masu kallo Kawai Ta bimu Dashi Wanda kai Da Ganinsa Kasan Yana Cikeda Tarin Ma'anoni.

Muka Durkushe Mu Duka Biyun Gabanta Kafin Naɗago Kai Dan Kara karantar Fuskarta Sai Dai Nafahimta Ita Wannan Matar Dae Komai Nacinka Baka isa ka gano Komai A Fuskarta ba Saboda Kwarjininta Da Haibarta Duk Sukan Ɓoye Komai.

Abdul-wahab Yace, "Innarmu Wannan Itace..... " "Karka Ɓatawa kanka Lokaci. Naji Duk Abinda kuke Cewa na Kuma Fahimci Komai. Ai Kaga Abinda Nake Nuna Maka Ko? Cewar Ka Tsaya Kafara Gina kanka Takwan Ko? Rayuwar Ta sauya Yanzu Mutane Hannu Mai Miya Aka lasa. Sannan Inba Da Rigima Irin Taka Abdul-wahab Meka taka Yanzun Da zaka iya Aure? Sadaki Muhalli Ko Meye?. " Innarmu Ta numfasa Cikin Takaicin Halin 'Yayan Zamani. Da Rashin Kunyar Da Suke Da Ita Wai Abdul-wahab Ne Zai zo ko Budurwar ce Zata Baro Gidansu Taxo Gurin Saurayinta Duk A kan So! "Baiwar ALLAH. " Tafaɗi Hakan Tana Mai Kallo Na "Kiyi Hakuri Kije Kibi Umarnin Iyayenki Kinji? Mu Talakawa ne Bamu Da Abin Aurar Da Abdul-wahab, Domin Abdul-wahab Bashi Da Abin Aurenki, Sannan Bashi da Kuma Abinda Zai Riƙe ki. Iyayenki Sunfi ki Sanin Abinda Yafi Dacewa Dake Dan Haka Amatsayi Na Uwa Ina Baki Shawara Komawa kiyiwa Iyayenki Biyayya Kinji? "


Innarmu Nagama Fadar Hakan Takarbi Kofin Walida Daketa Rigima A Zuba mata Kunu Ta Sanya mata Kunun Sannan Tamika Mata, Kafin Takama Hannun Hanifa Tanufi Da ita Waje, Dan Ita Yanzu tafarka Daga Barci.


Abdul-wahab Yadurkushe Nan Ƙasa Wasu Hawaye Zafafa Suna Saraftu A Fuskarsa, Cikin Sanyin Jiki Namike Ina Mai Share Hawayen Da Ke Gow Slow A Fuskata Nakama Hanyar Fita Waje. Ina Gabda Fita Gidan Abdul-wahab Yaccimin Yana wani Tangaɗi Kamar Wanda Yasha Barasa. Najuyo Na kallesa Kafin Nasake Maida Idona Kan Titi Ina Neman Abin Hawan Da Zai Mai dani Gida.


"Kiyi Hakuri Khaleesat, Komai Yayi Tsanani Maganin Sa ALLAH, Zanzo Gidan Idan Anjima Muji Yaza'a Mu ɓolluwa Lamarin "

Shi ne Kalaman Da Abdul-wahab Yake Faɗamin Bayan Nahau Kk Napep Nadago Fuskata Cike Da Hawaye Nace, "Abdul Karka Wani Wahlarda Kanka Ni Nariga Na Samarwa kaina Mafita Kowa dae Kalmar Ɗaya ce Kuɗi! Kuɗi!! Kuɗi!!! Dan Haka Ni Zanyi Abinda Nake Ganin Yadace. Dan Haka Karka Ɓatawa kanka Lokaci Zuwa Gidamu Dan ko Kazo Bazan Saurare Ka ba."

"Meyasa Zaki ce Haka? Haba Khale...." Naɗaga Masa Hannu "Karka Karyamin Gwaiwa Abdul Kaje Ka Kawai" Kafin Nayiwa Mai Kk Napep Umurnin Kawai Muwuce. Nan Muka Bar Abdul-wahab Tsaye. Kamar Iccen Da Aka Dasa Yarasa Gaba Zai Ko Baya Zuciyarsa Na Tafarfasa Hawaye Naci Gaba Da Gudu A Damdamalin Fuskarsa Yajuyo Yanufo Cikin Gida Wani Irin Duhu Gidan Ke Masa.


Kai Tsaye Ɗakin Su Ya Nufa Ya Sami Abubakar Lokacin Yafarka Daga Barci Yanazuba Makilin A Brosh Dinsa Da Niyyar Zai Fito Ya Wanke Bakinsa. Turus! Abubakar Yayi Yana Kallon Abdul-wahab Ɗin Da Yashigo Duk A Firgice Kafin Yace "Yaya Lafiya?"

Shiru Ba'amsa Daga Abdul-wahab Ɗin. Dan Haka Abubakar Yajuyo Yazo Ya Zauna Kusa Dashi Yana ƙara Tambayarsa, Ga Mamakin Abubakar Sai Ga Abdul-wahab Na Wani Irin Kuka Wanda Tunda Yake Bai Taɓa Ganin Yayi Irinsa ba. Lamarin Da Yatayarwa Abubakar Hankali Kenan Yafita Ɗakin Nasu Da Gudu Yana Kiran Innarmu Tazo Tagani.


"Innarmu Zo Ki Gani Mene Yasamu Ya Abdul?" Yana Faɗar Hakanne Tare Da Ƙokarin Jawo Hannun Innarmu Yayinda Ita Kuwa Tafisge Daga Riƙon Da Yayi Mata Cikin Fushi Tace "Ba inda Zanje Ai Duk Wanda Baiji Bari Ba yaji Hoho Gashinan Dae Kuma Tun Ba'a je Ko'ina Ba Yaga Illar Abinda Nake Nuna Maku. " Cikin Rawar Murya Abubakar Yake Cewa, "Wai Me Yafaru Ne Innarmu? Kun Sani A Kwana Dan ALLAH kumin Bayani."


"Babu Abinda Yafaru Yarinya Yaje Nema Sukuwa Iyayenta Suka ce Bazasu Bashi 'Ƴarsu Ba Dan Baida Kuɗi." Innarmu Nagama Faɗar Hakan kuma Taɗauki Buta Tashiga Arwallah Dan Yin Sallar Walha Kamar Yadda Tasaba.


Shikuwa Abubakar Yayi Tsaye Cikin Zullumi Da Taraddadi Kafin Yasake Nufar Ɗakin Nasu Ya'iske Abdul-wahab Yahaɗe Kai Da Gwaiwa Yana Ta Aikin Sauke Numfashi Yadurkushe Gabansa Yana Mai Cewa, "Yaya Kaga Abinda Nake Nuna Maka Ko? Kaga Illar Abinda Nake Gayama ko? Tun ba'aje Ko'ina ba ko?. Shi..... "


Wata Irin Tsawa Abdul-wahab Yayi Masa Yana Cewa, "Ka'isheni Auta Kafice Kaban Wuri Bana Son Jin Mugun Surutun Ka."

Dole Abubakar Yamike Cikin Sanyin Jiki Yararumi Merkealin da Brush Dinsa Yafice Cikin Ƙunar Zuciya. Akan Wannan Halin Da Suka wayi Gari Dashi. Gashi Maman Walida Tunjiya Dataje Bukin ƙawar Tasu Bata Dawo ba Su Walida kawai Da Ammar Tabari. Kila Da Tana Nan Data Shawo Kan Matsalar Tunda Innarmu Najin Maganar ta Da Shi Kansa uban Gayyar Watau Abdul-wahab.


Shikam Abubakar Baya Da Zaɓi Illai Yashirya Tsaf Kafin Ya Lalubo Yan HandOut Ɗinsa Yazo Yaɗibi Abin Ƙari Ya Karya Kumallo Kafin Yace, "Innarmu Naje Skull Sai Nadawo."

Fuska Ba Yabo Ba Fallasa Tace, "ALLAH Yatsare. " Minti Biyar Da Fitarsa Shima Abdul-wahab Yafito Goye Da Jikkarsa Ko Wanka Baiyi ba Balle Aje Maganar Yayi Break Fast Ya'isa Gurin Innarmu Yace, "Innarmu Zanje Makaranta."

Ko Inda Yake Bata Kalla ba Tace, "Adawo Lafiya." Ko'ajikinsa Yakama Hanya Yafice.


Tirkashi! Lokacin Ƙanƙani Fa Komai Na Neman Wargajewa A Familyn Nan Kuma Duk SONEEE SILAR KOMAI

Muje Zuwa muji Yazata Ƙarƙe!
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 5 · 0% Book details