← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 20 OF 40

Chapter.....22

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Bissmillahi Rahmanin Raheem


NOT EDITIN....


A hankali Na sauke Labulen Windor Nawa da tun ɗazu Nake tsaye ta gurinsa Ina Hangen Irin Tashin Hankali da Abdul-wahab ke Ciki Ina Mai kuma Ƙara Amincewa Zuciyata Irin Son da Abdul-wahab Yake yimin.


Cikin Sanyin Jiki Nasanya A hannuna Nagoge kwallar tausayin Kammu davTa taru A idona Kafin Na Koma Kan Kujera Na zauna Batareda Nasan Taƙamammen Abinda Nakeyi Ba, Kawai dai Nasan Ina Cikin Wani Irin Ƙunci da Tambayar Kaina Shin Meye Illar Aure na da Abdul-wahab ne da Har Iyayenmu Suke Yimana SHAMAKI ne? Meye ne dan Mun SO Juna ta Hanyar da Tadace ne? Yanzun Basa Tsoro ko Tunanin Mudinga Zaman Banza? (Wa'iya zubillah) eh Mana Tau Ai Wannan Sunshiga Haƙƙemu. Ire-iren Wayyanan tunannuka Su Suka Abokanci Zuciyata Har'izuwa Wani dogon lokacin da Halin Damuwar da Nake Ciki yasa nakasa Tantace Yaushe ne ma kuma bana ma Buƙatar In sani dan ni A Yanzun tunda Narasa Abdul-wahab Komai ma Na Duniyar Na Hakura dashi Kawai dan Haka sannu A hankali Na Sulale Ƙasan Carpet ɗinda Ke malale A tsakiyar ɗakin Nawa Naciga ba Zubbda Hawayena Wayanda Nakejin Ba Ranar daina Su Harsai Sanda Aka cemin Anbarni Ko Lalle Yau Bana da Miji Sai Abdul-wahab Lamarin da Nakeji Kamar da Wuya Inji Masu Iya Magana Sukace "Gurguwa da Auren Nesa."


*******


Tunda dai Suke Cikin dakin Ba'abunda Sukeyi Illah Tufka da Warwara! Kuma An rasa daga cikinsu Mai Yiwa ɗan Uwansa Wata Magana Musamman ma dai Dr Jabir Da shine YAFI CANCANTA yace Wane Abun tunda Shine Yaɓallo Ruwan Dan Haka Shi Yafi Kamata Yatare su.

Ana Cikin Hakan Har kiran Sallah Magarib Yariƙsu A Haka Wanda Yayi dai-dai da Dawowar Alhaji daga Kasuwa Kuma Suka Ji Muryarsa A tsakar Gida Yana Magana da Su Gwaggo Halima dan Haka Cikin Sanyin Jiki Duk Suka Miƙe Suka Fito Kafin Suka Rusuna Gefe Suna Gaidashi Yayinda Shikuma Yabisu da Kallon Mamaki Kafin Yaɗago Kansa Yana mai Kallon Gwaggo Halima Cikin Alamun Tambaya Amma Sai Gwaggo Halima takawar da Kanta madadin Hakamma Sai taɗauki Buta Tanufi Dromm ɗin Ruwansu dake Girke Tsakar Gidan Nasu Taciko Masa da Ruwa Takawo Gabansa Nufin Dai Zaiyi Arwallah Zuwa Masjid dai-dai lokacin da Shikuma yake Amsa Gaisuwar Tasu Daga bisani Yake Tambayarsu Lafiya Kuwa?


Dr Jabir ne Mai kwarin gwaiwar Cewa, "Lafiya lau Alhaji Mundai Zo Gaishe ku Ne Kawai."


Alhaji Badan Ya yarda da Maganar tasa Ba yagirgiza Kansa Kafin Yace Masa, "Tau Madallah Aikun Kyauta zo ɗauki ga Buta Kayi Arwallah muje Sallah Naji Har Sun Tayar Ke Asiya Zoki Cikomin Wata." Maman Asharaf da Dr Jabir ɗin duk Tare Suka Miƙe Shi Yaɗauki Butar Yasoma Naɗe Lonk slive ɗinsa Bayan Yacire Tsadadden Agogon dake Kan Kyakykyawan Hannunsa iTa Kuma Taɗauki Butar Zuwa cikowa Alhaji Dan Shima Yayi Arwallah.

Ganin Hakan Yasa Su Gwaggo Halima Da Safiyyah Suka Nufi Kitchin dan Ƙarasa Aikin Nasu.


Tare Sukaje Masallaci Bayan Angama Kuma Suka Jero Suka dawo gida Alhaji Na Tambayarsa Yanayin Aikinsu Shima Yana Amsawa masa Cikin Girmamawa, Lokacin Gwaggo Halima Na Kan Yar Tsuggonunta Tana Raba Abinci Yayin da Safiyyah Ke Aikin Tayata Ita Kuwa Maman Asharaf tana ɗaki Kan Darduma Dan bata jima da gama Sallar ba Ita. Alhaji Yazauna Kan Shimfiɗarsa Yayinda Dr Jabir Yadawo Gefen sa Ya zauna Cikin Nutsuwa Yana Sauraron Jawabin Na Alhajin


Can Yajefo Masa Tambayarsa Kwana nawa ne Suka Rage ne Auren sa? Dr Jabir Yace, "Bazai Wuce goma ba yanzun." Dai-dai Lokacin ta'ajiye Masa Farantin Abincin dake Jere Cikin Kwanonin Silba da Kuma Kofin Sulba Da'a ka Cike da Ruwan sha Shima, dan Haka Alhajin Ya'Umurci Dr Jabir Da Ya Wanke Hannun sa Suci Abinci Dr Jabir Ba Yanda Zaiyi Dolen sa Ya Wanke Hannun Nasa. dan Yariga yasan Waye Alhaji da Kuma irin Nasa Aƙidun Suka tsoma Hannayensu Acikin Kwanon Tuwon Suna Ci Sannu A Hankali Kuma Alhajin Naci gaba da Bugun Cikin sa Dan jin Matsalar da Takawo su Gidan. Hakanan ko Cikin Hikima da dubara irin Tasu ta Manya Haryajiyo Abinda Yake Son Ji daga Bakin Dr Jabir ɗin A wannan lokacin Kuma shi Alhajin Yatsame Hannun sa daga kwanon Abincin Yajawo buta ya wanke Hannun sa kafin Yakuskure Bakin sa sa'anan Yafuskanci Dr Jabir.


"Dama ni Nasan Abinda Yakawo Jabiru Kawai Zuru Nayi Maku dan Dama Can Na Nasa Tun Kafin Kuzo ɗin Sai kunzo Dan Nasan Halin Mata Na Kuma Kaidin Su Akan Kishi Shiyyasa ma Tun Kafin Irin Haka Naja Ma Mahaifiyar tasu Kunnen da Sauran dukkan Yan Uwan ta, dan Haka kaima Abinda Zan Sanar da Kai Yanzun Shine Sai ka Ƙara Hankuri Buhu-Buhu Sai kuma Kazamo Namijin duniya Acikin Gidanka In ba Hakaba? Tau Wallahi Kana Kallo Gidan ka Zai Tarwatse Saboda Kayi Adalci a tsakanin Iyalan ka Itace Mallaha Ta Farko Gareka Sannan Kazauna Katsara Yanda Zaman takawar Iyalin ka Yakamata ta Kasance, Kada Kazamo Maiyin Abu Gaba-gaɗi Ai Kana Fahimta ta ko?"

Dr Jabir da Tuni Shima Yawanke Hannnun Nasa Daga Cin Abincin Da suke Yana Nan Rusune Gaban Alhaji Ya sunkiyar da Kai Kamar Mai Neman Gafara Yagirgiza Kansa Batareda Yace Uffan ba.

Dan Haka Alhaji Yaɗora da Cewa, "yawwa Idan Kafahimci Hakan Shine Maganin Matsalar Karka Musgunawa Ko Wacce daga Cikinsu Domin Dukkansu Matan ka ne Kuma Amana Aka Baka Kuma ɗiyan Wasu ne Kaima Kuma Zaka Haifa Kuma Zaka Bada Auren So duk irin Riƙon da Kayi Masu Shi Za'ayi Wa Nakan Saidai Kuma Bance Akan Tsallake Jarrabawa ba Asamu Akasin Naka Halin Ba Wannan kuma Jarrabaw ce daga Min indillah Idan Akayi Hakuri Aka Karɓi Jarrabawar Ta Fuskar data Dace Sai Ka An Samu Sakamako Mai Kyau." tau Haka dai Alhaji Yasaka Dr Jabir Gaba da Nasihohi da Shawarwari Harma kuma da Faɗakarwa Akan Halin Duniya da Kuma Irin Zaman da Yacancanta Yayi da Iyalin Nasa. Wayanda Dr Jabir Yaƙaru dasu Sosai Hakanan Iyayen Na Maman Asharaf Sun Ƙara Wata Irin Ƙima da Darajar duk Yanda Yaso Yakwatanta Abun Yafaskare sa. Cikin hakan Alhaji yasa Aka kira Masa 'Yar tasa Itama ya zauna da ita ba faɗa ba kyara Dan yayi Mata Uzuri Kan shi ya Yarda KISHI Halak ne kan Abinda kake So, Abun buƙata dai baifi Kasamu Ma'abota Hankali da Zasu Fahimceka Su kuma ɗora ka kan Hanya managarciya.


Tau Itama dai haka Yayi mata nasiha da Lurarwa Irin Tasu ta dattijan Sannan Yagargaɗeta Cewa Babu Yaji dan Yana Zubar da Ƙimar Ya mace. Daganan Ya cikata da tarin Kyaututtuka Na turare da Yan Ƙayatattun kayakin da Campunan da suke Mu'amala ta saye da saisuwa ke Basu Irin Botikai da robobi Da dai sauran su Sannan yace tayi List ɗin duk Abinda Take Buƙata Zai Siya mata kada ta matsawa mijin Hidimun Sunyi Masa Yawa.

Haka dai Suka Shigo Motarsu Suka Nufi Gidansu Cikin tarin Alkairi Albarka daga SURUKAN KIRKI Wani gefe kuma Dattijan Kirki Shi Kanshi Dr Jabir A yanzun Yanajin Cewa Ko A iya wannan Idan Yacuci ɗiyarsu Haƙƙensu Bazai Barshi ba. Saida Suka biya Gurin Ƙanwarshi Suka ɗauko Asharaf Kasancewar School ɗaya Yakeyi da Yaranta Dan Haka In Ba'aje ɗaukar Daga Cikinsu ba Sai Wanda Yazo ɗaukar ɗayan Yahaɗa duka Yaɗauke su Inyaso Shi Dr ɗin ko Ita Maman Asharaf Sai taje gidan ta ɗaukoshi hakanan Itama Ƙanwar ta Dr Jabir Mijinta ko direban ta Ke Zuwa ɗauko Yaranta In Sunbi Asharaf Can gidan Su.


Nan ma saida Suka ɓata Lokaci Kafin Sukayi Musu Sallama Suka Nufi Gida Suka Bar Sajida(Ƙanwar Dr Jabir ɗin) Cikin Mamaki da Tunanin Shikuwa Yayan ta Mezaisa Shi Wani ƙarin Aure Suna Zaman su Lafiya da Matarsa Yaje Kawai Yajajibo wa Kansa Wata Rigimar? Karshe dai Tawatsar da Hannayen ta Alamun Shi Yaga zaya Iya. Kafin Afili ta Furta, "Mudai Asiya ce Tamu bamu San Wata Amarya ba dan Ko Banza Itace Ƴar Uwar mu Ta jini." kafin Tajuyo ta koma Ciki dan Tana Wannan Tunanin ne A sanda Motar tasu taɗaga Tabar ta tsaye Nan Harabar parkin space ɗin gidan su.


************

Su Abdul-wahab Kuwa Kai tsaye Mai Kk Napep ɗin gidan Su Yusuf Ya'ajiye Su Yusuf Ne Yasallameshi Kafin Yabi Abdul-wahab Da ɗan gudun sa Danshi Abdul-wahab Suna Sauka Wucewarsa Yayi Cikin Gidan.

Dakin Yusuf Suka Zube Abdul-wahab Yatallafe Keyarsa da duka Hannayen Sa Biyu Tareda Tsurawa Fankar dake Saman Rufin Ɗakin Tana ta Aikin Bada Iska Hawaye ne Ke Silalowa A Fuskarsa Kunci Nakara Samun Muhalli Acikin Zuciyarsa, Gefe ɗaya Yana ALLAH Wadai Da Irin Wannan Zuciyar Tasa da Takasa Cire Son Abinda Bazata Taɓa Samu Ba. Can Kuma Sai Yake Tambayar Kansa Wace Irin Ƙiyayya ce Iyayen Khaleesat Keyi Masa? Meyasa Suka Kasa Gano Irin Tsantsar Soyayyar Da Yakeyi Wa Ƴarsu? Tabbas Yasan Baya da Kuɗi Amma Yanada Sana'ar da zai Fita Yanema Yazo Yaci dasu Yana kuma Da Yaƙinin Zata Iya Riƙesu da Duk Wani Lalurorinsu Amma Su Sunce ƘUƊI! Tau Mey.....


Yusuf Yashigo da Kular Abinci Ya'ajiye Da Ruwan Pure water guda Tareda Gorar Soɓo guda Biyu Sai Raɓa Sukeyi Alamun dai Sunyi Sanyi. Kafaɗar Abdul-wahab Yabuga Tareda Cewa, "Kaman ta Komai dan ALLAH Taso Muci Abinci Sa'annan Muyi Magana."


Batareda Yaɗago Ba Daga kwancen Yace, "Yusuf A Yanzun Bana Sha'awar Komai Bana Jin Kuma Zan Iya Cin Komai."

Yusuf Yayi tsaki Kafin Yace, "Matsala ta da Kai fa Kenan Rashin Tawakkali Dan ALLAH Ka...."


"Kaga Malam Karka Wani Isheni da Surutu Abinci Nace Bazan Ci Ba Dan Haka Karka Wani dameni Kawai Ka ƙyaleni Inji da Abunda Ke Damuwa ta Ni Da Zaka Ma Fice Daga ɗakinan Kaci Abincin Zanji daɗi Wallahi dan ko Warinsa Bana son Ji!"

"Abincin Ne Ke Wari Abdul-wahab?" Yusuf Yafaɗa Cikin Sakin Baki Akan Mamaki.


Banza Abdul-wahab ɗin Yayi Masa Yana Mai Ci Gaba da Tunanin sa da Nufin Bazai Taɓa Kammalla shi Ba Harsai Yasamawa Kansa Mafita.


"In Bazakaci Abinci Ba Saika Sha Ga Soɓon Ko dan Ka sanyaya Zuciyarka Dan Yana da Sanyi." yaƙare Maganar Gamida Miƙawa Abdul-wahab Gorar Soɓon. Daga Inda Abdull Yake Kwance Yamiƙo Hannunsa Yakarɓi Gorar Kafin Yamiƙe Yaɓalle Murfinta Kafin Yakai Bakinsa Yasoma Sha Bai Dire Gorar ba Sai da Ya shanye Tas Ya'ajiye Gorar Yakoma Yayi Kwanciyarsa Irin Ta ɗazu. Kaida Gani Yasha ne Kawai Dan Kada Yusuf ɗin Yacika Shi da Surutu. Gefe Yusuf Yakoma Yasoma Cin Abinci Rayuwar Tasa Shima duka Babu daɗi Akan Irin Halin da Abdull ɗin Ke Ciki Saidai Babu Abunda Zasuyi Wanda Yawuce Haƙuri Hakanan Kawai Su Rufe Babin Khaleesat A Rayuwar su.

Hakadai Yatsakuri Abinci Shima Yatarka ta Kayan Yanufi Cikin gidan Nasu Ummarsa Ke Tambayar sa Yabasu Ci Abinci Ba Shine Fa Yake Gayamata Halin da Ake Ciki Tashawo Lulluɓi Suka Zo Tare A ɗakin na Yusuf Suka Tarar Abdul-wahab Na Nan Yanda Yake Yayi Nisa Cikin duniyar Tunani ga Hawayen na Cigaba da Kwarara daga Cikin idanuwan sa Wayanda Yake ji tamkar Ruwan zafi ne tafasassu ne Ake Kwarara Masa Akan Fuskarsa.

Sallamar Ummarsu Yusuf Yasa Yayi Firgigit Yasoma Share Hawaye Kafin Yashiga Gaisheta.

Cikin tausayin sa Take Amsawa Kamin Tasoma Yimasa Nasiha Kan yayi Hakuri, Komai Na Duniya Muƙaddari ne daga ALLAH duk Abinda Yaso Shi Yake Faruwa dan Haka indai Da Rabon Zasu Auri Juna shida Khaleesat duk Ƙin Iyayen ta Akan Abun Insha'allah Sai Sun Auri Juna idan Kuma Bai Ƙaddara ba Duk Son Su Da Abun Bazai taɓa Faruwa ba." taƙare da Cewa, "Saboda Haka Kasawa Ranka dangana Ka Kuma Ci Gaba da Adu'a Komai Yayi Maganin sa ALLAH Kaji Ɗana? (Dama haka take cemasa) Abdul-wahab Yakasa Magana Sai girgiza Kawai Yakeyi. Daganan Ummarsu Yusuf ɗin Takoma Cikin gida yarage daga shi Sai Yusuf ɗin, Yusuf ɗin Ma Yana ganin Shirun Nasu Yayi Yawa kawai Sai Yamiƙe Ya kunna Masa Karatun Ƙur'ani Cikin Mp ɗin da Ke ɗakin Sa'anan Shima Yafice Zuwa waje.

*Muje zuwa dai Readers........
*
[9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 20 · 0% Book details