← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 33 OF 40

Chapter.....35

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Mallakar 👇

Fa'IK ✍


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.


Na Sadaukar Da Wannan Chapter Ga Yar Uwa A Harkar Rubutu HADIZA SALISU SHARIF. Wacce Tarigamu Gidan Gaskiya Ya ALLAH Ka Karɓi Bakwancinta Ka Kyautata Tamu In Tazo. 🙏


Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!


Ya Sauke Ajiyar Zuciya Kana Yace, "Ok! Bari Nayi Maki Gwari-gwari Inji Matar Bagware. Daga Sanda Momy Ta Kawoki Asibiti Ranar Farko kenan da Muka Fara Haɗuwa Na Ganki Nasan Akwai Tarin Abubuwa A tattare da Rayuwar ki daganan Nikuma Nafara Bibiyar Rayuwar ki Harna Gano Irin Soyayyar dake Tsakanin ki da Abdul-wahab Da Yanda Iyayenku Suka Ki Amincewa (Musamman Iyayen ki)Har zuwa Sanda Alh Saminu Yazo da Niyyar Aurenki Kika Masa Korar Kare Wanda A Zaton Iyayen ki Shine Yaƙi. daganan Kikaji Cewa Ai Ga Dalilin da Yasa Iyayen ku Basa Son Auren Naku Watau Suna Ganin ME NA SAMA YACI.... Balle Na Ƙasa Yasamu. Watau Bayada Aiki Mai ƙwari Da Zai Riƙe kiyi Rayuwa Irin Wacce Suke Buƙata.


Sai ke Kuma Kika Shiga Bin Maza Musamman Alhazai Kina Tatsar su KUƊI Kawai dan ki tara Ki bawa Abdul-wahab Saboda Shima Yayi Kuɗin da Iyayenki Suke Buƙata Abarki Ki Aure shi Tau Nan Ma Plan ɗinki Bai Ci Ba dan A Sanda Kikaje Gurin Abdul-wahab ɗin Shi Kuma Amatsayin Mayaudariyah Yake Kallon Ki. Mutanen Unguwar Ku Suka Miki Mummunan Shaida Harzuwa Sanda Dady Yazo Yaji Ya Fatattakeki Kika Maida Mota Amma Kuɗin Haryanzu Suna Nan A Wancan Acc ɗin Baki Maida Ba Kuma Baki Taɓa Su Ba Hakane?" Cikin Wani Irin Sanyi jiki da Matuƙar Mamakin yanda duk Akai Yasan Wannan Na Girgaza Masa Kai Tareda Cewa "Eh."

Shikuwa Yaɗora, "Indai Taƙaice Maki Zance Harkawo Yanzu Da Na Shigo Rayuwar ki Da Tawa Manufar Nima Baki Saduda Ba. Kina Nan da Ƙudurin Na Bazaki Auri Kowa Ba Sai Abdul-wahab Hakanan Nasan Kina Nan Kina Shirya Wani Plan Yanzun da Akace An Sanya Ranar Auren Mu Shine Kuma Bansani Ba Menene Kike Shiryawa?" Shiru Nayi Cikin Nazari da Tunanin Harzuwa Sanda Naji Yana Cewa, "Karki Manta da Alkawarin da Kikayimin." Jin Hakan Yasa Naɗago Ina Cewa, "Hakane Ina Shiryawa Saidai Wallahi Nayi Mamaki yanda duk Kasan Wayyanan Abubuwan, Saidai Ba Wannan ba Kafin Nabaka Amsar Tambayarka. Bari In Fara Sanar Dakai Dalilin da Yasa Na Aikata duk Wayyanan Abubuwan Nafarko ALLAH Yajarabceni da Wani Irin Son Abdull Wanda Nima Ban San Iya Adadin sa Ba tun A Ranar Farko da ALLAH Yaɗora ƙwayar Idanuna Akanshi Kuma duk Yanda Nayi Ƙokarin Cire Hakan A Raina dan Bin Umurnin Iyayen Nawa Sai Inji Nagagara Yin Hakan. Hakanan Shima Yana Min Irin Wannan Son Shiyyasa Ma Mukayi AMMANA Cewa Bazamu Iya Rayuwa Matuƙar Bama Tare da Juna Saboda Shima Yasamu Matsalolin Sosai da Gidan Nasu Akaina.

Gameda Plan ɗinda Ka Tambayeni Kuwa Maganar Gaskiya Abunda Na'aje A Raina Kawai indai Har Kuka Matsa Sai Anyi Auren Nan Tau Kawai Ana Gobe Ɗaurin Auren In gudu Zuwa Wata Duniyar Bazan dawo Ba Har sai Sanda Su Dady da Momy Suka Gane MANUFA TA Ko Kuma Inshi Abdul-wahab Ya yarda Kawai Mugudu Zuwa Inda Za'a Fahimce mu Muyi Auren mu Wannan Shine Plan ɗinda Na Tsara."

Nayi Shiru Ina Kallon Sa Yayinda Shikuwa Yayi Shiru Cikin Nazari Kafin Yayi ɗan Murmushi Yaɗago Ya na Kallo na "Kin gamsu da Wannan Hanyar da Kika Bi?"

"Nagamsu Sosai Nasan Kana Jiyemin Faɗawa Wani Hali Inna Bar Gidan Ko?" Nacigaba Batareda Najira Amsarshi Ba Dan Bana Buƙata "Idan Na Zauna Ma Cituwa Zanyi Bana Tunanin Zan Iya Rayuwa da Wani Ɗa Namiji Inba Abdul-wahab Ba, Bana Tunanin Zan Iya Biyayya Ga Mijin da Zan Aura, Bana Tunanin Zai Samu Kulawa ta Bana Tunanin Kasancewa Cikin Walwala Komai Daren daɗewa ko Kai Babu! Babu!! Da Yawa Dr Ka Kuwa San Babu Mijin da Zai Juri Hakan dai Ko? Bugu da Ƙari Ga Babban Zunubi Ina Gidan Wani Amatsayin Matar Sa Amma Ina Alaƙa ko Tunanin Wani. Shiyyasa Kawai Na Zaɓi Bin Wannan Hanyar Tunda Nayi Iya Nawa Ƙokarin Dan Fahimtar da Momy Sun Kasa Fahimta ta.


Dr Zuciya Bata da Ƙashi Haka Kuma Shaiɗan Fa Ba Rago Bane In Har Aka Hana Mana Rayuwa Ta Hallatacciya Hanyar Muna Iya Kuma Risƙar Kammu Ta Hamratacciya Hanya Idan Muka Yi Hakan Kana ga Zai Mana Kyau? " A Wannan Lokacin Muryata Ta Soma Rawa Tuni Hawaye Ke Kwarara A Idanuna Kamar An buɗe Famfo Cikin Kukan da Ke Tasomin Ina Ƙokarin danne shi Na ɗora Zancen Nawa Da Cewa, "Ai Kaga Ko gudun Faruwar Hakan Yana Sa Ingudu Ko? Bansan Meyasa Su Momy Suka Kasa Fahimta ba Meye Illar Abdul-wahab Yana da Aikinsa Gwargwado da Zai Fita Yasamu Muci Shikuma Arziki Na ALLAH ne Ba Wanda Yasan Inda Rana Zata Faɗi, Tana Yuwa Mai Kuɗin da Suke So In Aura ɗin Zuwa Gaba Yasamu Karayar Arziki Abdull ɗinda Baya da Yayi ARZIKIN. Haka Kuma Tana Yuwa Ko Bai Samu Karayar Arzikin ba Shima Abdul-wahab Yayi Nasa ARZIKIN Bayan Haka Tana Yuwa Ina Auren Wani Can Amma Saboda Soyayyar da Mukeyi wa Juna Yazamana Muna Tare Kaga Kuma Haka Ai Baidace Ba Ko?" Kai Haka Nayita Kawowa Dr Jabir Misalai daban-daban Gwargwadon Iya Nawa Tunanin da Kuma Yanda Zai Fahimci Illar Abinda Su Momy Ke Sonyi Mana Wanda Kuma Tuni Zuciyata Ta Karye Na Soma Kuka Wiwiwi dan Haka Nakifa Kaina Kan Center table ɗin dake Gabamu Nacigaba da Yin Abuna Saboda Wani Irin Ƙunci da Nakeji Yana Tasomin Mussaman In Na Tuno Irin Rabuwar da Mukayi da Abdul-wahab A Wancan Ranar da Kuma Yanda Suka Bar Gidanmu.

Idanun Dr Jabir Suka Kaɗa Sukayi Jazir Kamar Barkwano Aka Watsa Masa Cikinsu Saboda Yafi Kowa Sanin Abinda Takeji Tunda Shima Tashi Masoyiyar Aka Raba Shi da Ita Akayi Masa Auren Zumunchi da Maman Asharaf Har Kuma Gobe Yanaji Cewa In Masoyiyar Tasa Zata Fito daga Gidan Auren ta Koda Takai Tsufan Kwando ne Zai Iya Auren ta.

Cikin Sanyin Murya Yace, "Is Ok, Kukan Ya'isa Haka Karɓi Wannan Kishare Hawayenki."

Ba Musu Na Karɓa Ina Goge Hawaye na Saidai Ina Gogewa Wasu Na Zuwa. Dan Haka Ƙyallen Yajiƙe Sharƙaf da Hawaye na.

Yace, "Baifa Kamata Kina Wannan Kukan Haka Ba Dan Bazan Samu Nutsuwar Yimiki Bayanin MAFITAR Da Nasamo Miki da Kuma Irin Taimakon da Nake da Ƙudurin Yi Maku Ba." Jin Wannan Kalamin Yasa Hawaye Suka Kafe Kaf Babu Abinda Nake Buƙata da Muradin Ji Irin Mafita da Taimakon da Yace Zaiyi Mana.

Ganin Hakan Yasa Yaɗan Nisa Gamida Cewa, "Yawwa Ko Kefa." Kafin Yaɗora Da Faɗin, "Na Gamsu da Kalaman Ki Sarai Kuma Ko Bacin Hakan Kullum Ana Nuna Mana Illar Auren dole Duk-da Bance Bayada Fa'ida ba, Amma dai Yana da Kyau Ake Sa Kula Cikin Abubuwan dan Gudun Kilu ta Ja Bau Nawa Ne Aka Yiwa Auren Suka Sawa Mazajen Guba? Nawa ne Akayi wa Auren Suka Shiga Duniya Yawon KARUWANCI Nawa Ne Aka Yiwa Auren Yakasa Daɗi Aka Rabu? Kai gadai Matsaloli Nan Barkatai."

Naɗago Kaina Ina Mai Sake Kallon Sa Ina Ji A Raina Nan Duniya Ba Mutum Mai Fahimta Kamar Dr Jabir Hakan Yasa Darajar sa Da Nake Gani Ta Ƙaru A Idona.

"Tau Kagani Kaima dai Ga Ma Wayyanan Matsalolin Wayanda Ni Nawa Tunanin Ma Bai Kai Kansu Ba." Acikin Zuciyata Nake Maganar Batareda Nasan Cewa Ashe Tafito Fili ba, Sai Ji Nayi Dr Jabir Yace, "Wayyanan Ma Wayanda Nasanine Nima Wani Ma In Zai Gayama Maki Nashin Sanin Sai Kiji Mu Bamu Faɗo Komai ba."

"Hakane." Nafaɗa Cikin Sanyin Muryar da Duk Wanda Yaji ta Zai San Taci Kuka Harta Shaƙe. Shikuma Dr Jabir Yaci Gaba da Koromin Nasa Jawabin.

"Tsakani da ALLAH Ni Bana Son Wani Na Aure Ki." Nayi Hanzarin ɗago Kaina Ina Kallon Sa.

Yagirgiza Kansa Irin Na Tabbatarwa ɗinan. Yaci Gaba, "Kamar Yadda Kikaji Bana Nemiki Bane Dan Na Aure ki Bane Na Nemi ki Ne Dam Na Taimaka Maku Domin dai Daga Sanda Kuka Zo A Rana Ta Farko daga Asibiti Nafahimci Irin Halin da Kike Ciki Wannan Yasa Na Shiga Bibiyar Rayuwar ki Har Na Gano Komai Sai Nazaɓi Bin Wannan Hanyar dan Na Taimaki Soyayyar ku Keda Abdul-wahab Kuma Bawai dan Bana Sonki Ba A'a Nadai Lura Indai Son Gaskiya Nakeyi Maki Tau Na Taimaka Maku Ne Kawai Ta Wannan Hanyar Saboda Haka Duk Abinda Kika Ga Ina yi Na Abinda Ya Danganci Aurenki Wallahi Plan ne Sai dai, Babu Wanda Yasan Wannan Maganar Dagani Sai Mahallicina Sai Kuma Ke Yanzun da Nasanarwa Saboda Anzo Gaɓar da Yakamata Ki Sani bugu da Ƙari Kuma, Ki ɗora Daga Inda Natsaya Domin Yanzun Aikin Ke Zaki Cigabada." Yaɗan Yi Shiru Tareda Jawo Gwangwanin Maltina dake Gabansa Yatsitsiya A Cup Yana Sha. Yayinda Nikuma Nake Kallonsa Cikin Ƙullewar Kai A Kan Maganganunsa Da Kuma Jin Mamakin Cewa Wai Duk Neman Aure na Da Yakeyi Ba Gaske Bane Plan Ne.

"Kallon Ya'isa Haka fa." Yafaɗi Hakan Cikin Sigar Wasa.

Yayinda Nikuwa KUNYA Tayi Min dirar Mikiya dan Haka Sai Na Sunkuyar da Kaina Ƙasa Tareda Ci Gaba da Wasa da Awarwaron Hannuna. Ina Mai Cike da Zumuɗin Son Yaci Gaba da Gayamin Inda Maganar Sa Ta Dosa. Ina ga Hakan da Yafahimta Ne Yasa Yayi Shiru Yana ɗan Jamin Aji Ko Miskilancin Nasa ne Kawai Ya Motsa? Oho! Ina Cikin Wannan Nazarin Ne Naji Muryar sa Tacigaba da Ratsa Kunne Na. Yana Mai Cewa, "Tunda Su Momy Sun Kasa Fahimtar Wancan YAREN Dole Zamu Fahimtar dasu Ta Wannan YAREN da Indai Basu Fahimce sa ba Tau Babu Wani Yare Kuma da Zasu Gane. Gameda Cewar da Nayi Anzo Gaɓar da Kece Zaki Ci Gaba da Buga Wasar Kuwa Shine... Akwai Wata Allura da Mu Likitoci Mukeyi. Tana ɗauke Ma Mutum Numfashi Na Tsawon Zuwa Lokacin da Aka Buƙata dan Haka Wannan Allurar Ita Zaki zo Wurinane Inmaki Ita Adai-dai Lokacin da Yarage Saura Kwana ɗaya Buki. Za'a Tafi Akan Kin MUTU Aɗaukeki Zuwa Maƙabarta Bayan An binne ki Mutanen Sun Watse Sai A Tono ki Muje dake Wani ƁOYAYYEN Wuri da Sai Komai Yadai-daita Mun Kuma Tabbatar da Su Momy Sunyi Laushi Sun Kuma Yi Nadama Akan Abinda Suka Aikaita Sai Ke Kuma Ki Dawo Ina Fatar Kin Gane Karatun?" Yaƙare Maganar Yana Mai Kallo Na. Yayinda Ni Kuwa Zuciyata ke Dukan Ukku -Ukku Tun Daga Sanda Yazo Gaɓar Da Za'a Binneni Ina Mai Tambayar Kaina Anya Kuwa Zan Iya Wannan Babbar Kasadar Kuwa? Kamar Ya Fahimci Tunanin da Nakeyi dan Haka Yaɗan Musƙuta Cikin Son Ƙarfafa min Gwaiwa Yace, "Tabbas Akwai Babban Ƙalubale Sosai Acikin Aikinan Amma In Kika Jajirce Zaki Iya, Sannan Yin Hakan Fa'ida Biyu Gareshi. Nafarko Zaki Samu Cikar Burin ki Sa'annan Zaki Ƙara Tabbatar da Irin Sonda Abdul-wahab Keyi maki Hakanan Suma Iyayen Naku Zasu Tabbatar da Irin Girman Soyayyar Dake Tsakanin Ku Su Barku Kuyi Auren Ku Cikin Farinciki.

Saidai Bazan Matsa Maki ba, Nabaki Nan da Kwana Biyu Kije Kiyi Shawara Saidai Da Sharaɗin Bazakiyi Wannan Maganar da Kowa Ba Hakanan Bazaki Shawarar Ta Da Kowa ba, Because Wannan Ko Acikin SIRRI SIRRINE Maigirma dan Haka Da Zuciyar Ki Kawai Na'amince Maki Kiyi Shawara Sannan Karki Manta ni Kawai Inayi Ne Dan Na Taimaki SOYAYYARKU Bayaga Wanna Bana da Wani Abu da Zan Ƙaru Dashi." Kafin Yaɗan Tsahirta Da Yin Maganar Yana Mai Duban Agogon sa dake Ɗaure A Tsintsiyar Hannunsa Yaɗago Yana Kallona Gamida Cewa, "Tashi In Maida Ki Gida Lokacin Sallar Magarib Na Matsowa Ga Kuma Yanayin da Muke Ciki Yanzun Kowane Lokaci Ruwan Sama Na Iya Tsugewa."


Kuzo Muje Musamu Mafaka Kar Ruwan Yatsuge damu Sai Muci Gaba da Labarin


Tareda Alkalamin👇


FA'IK. ✍🏼
[9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

💪🏻J.A.W 💪🏻


❤❤SONEEE ....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 33 · 0% Book details