Chapter.....41
So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mallakar 👇
Fa'IK ✍
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
💪🏻J.A.W 💪🏻
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.
FADAKARWA.
Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.
Bissmillahi Rahmanin Raheem!!!
Wannan Kenan!!!
***********
Tau Ɓangaren Na Nima Sai Hamdalah Domin Iyayena Jarumai Ne Masu Zafin Nema Dama Kuma Komai Akwai, Wasun Kawai Aka Sabunta Lefe Kuwa Tuni Abubakar Yazo Yaƙarbe su Kan Zaiyomin ɗinkuna Kala-kala Dan Dr Jabir Yace Komai Da Yayi Ba Kansa Yayiwa ba Dama Can Abdul-wahab ɗin Yayiwa.
Walwalar Gidanmu Tadawo ALAƘATA Tagyaru da Iyayena Muna Cikin Zammamu Mai Daɗi Bugu da Ƙari Yanzun Shima Dady Sanadin Wannan Abun da Yafaru Alaƙarsa ta gyru da Yan Uwansa Zumunchi Suke Yanzun Sosai Komai kuma Kowanen su Zaiyi Sai da Shawarar Yan Uwansa Hakanan Dady Yakwashe Mu Zuwa Adamawa Kwana Biyu Asabar da Lahdi Mukayi Muka Dawo Daganan Ya Nuradeen Yadamƙi Hanyar Legos Da Burin In Yaje Zaiyi Ciku-Cikun Adawo Dashi AREWA Saboda Yagaji da Zirga-Zirga.
Yanzun Haka Momy Suna Zumunchi da Matar Dady Ta Adamawa Saɓanin da Da Basa Wani Yi Harma Tayi Alkawalin Zuwa Buki Inya Tashi.
Ana Gobe Buki Yan Uwa da Abokan Arziki Aka Shiga Ɓarkowa Gida Yaɗauki Harami Komai Yakacame Sai Shagali Akeyi Tunkuya Aɗora Wannan A Sauke Wancan Saboda Buhu guda Dady Yagir Mana Agida Da Kayan Miya Birjik.
Yayinda Mami Iyabo Tazo da Fulawarta Domin Yimin Kayan Gara dasuka Danganci Dibilah Cin-cin Alkaki da Donoth da Dai Sauran Su. Dataji Abunda Nayin Kuwa (dan Ita Momy Ta Faɗa Mata Kasancewar ta Ƙanwarta Da Suke Rabon Fhara Guda) Nasha TiƘa Gurinta Akan Wahalar Da Na Basu Shine Tace Sai Rama Kukan da Nasa ta Mukayi ta Dariya.
Yanzun Ma Zaune Take Kan Ƴar Tsuggonunta Tana Suya Cin-cin Yayinda Sauran Sukenan Ana Gwarzar Fulawa Tacemin, "Miƙomin Wani Mazubin Wannan Yacika In tsame Kar Cin-cin Yaƙone." Namiƙo Mata Ina Cewa, "Mami In ɗanyi Maki Tastin Inji Yayi daɗi?" Taharareni, "Shiɗai Kika Iya Gawa Taƙi Rame Kawai(Sabon Sunan da Take Kirana dashi Kenan Tunda Kowa Ce Masa Akayi Dogowar Suma ce Nayi Kamar dai Yadda Liman Yasanar da Mutane.) Tana Faɗar Hakan Kowa Yakwashe da Dariya Nikuma Na Zumɓuri Baki, "Ni Wallahi Mami Bana Son Wannan Sunan Nafasa Maki Tastin ɗin." Tace, "Meye Ruwana Daga Kawai Ma ALLAH Yahutar dani?" Nayi Hanzarin Dawowa Tareda Tsumbula Hannun na Cikin Robar Cin-cin ɗin Ina Cewa, "Eh Lalle Nagano." Mutane dai Sai Dariya Suke Mana Saboda Mami Iyabo Akwai Barkwanci Shiyyasa Wani Lokacin Kamar Jika da Kaka Muke.
**********
Ɓangaren gidan Ango Ma Haka Sha'ani Keta Gudana Su Mmn Walida Sai Kai Kawo Ake Kamar Yadda Su Yusuf da Abubakar Aka Kasa Zama Yaudai Gidan Angon Komai Yayi Fes ɗankaramin Gida Mai Kyau An Malale Ko Ina Na Gidan Da Tayels (Irin Haɗin Gambizar Nan) Ciki da Falo ne Sai Kuma Kitchin da Store dakuma Toilet da ke Jere daga Gefe Sai Ƙamshin Fenti Da Akeyi Yauɗin Ke Tashi. Saboda Zuwa Anjima Ƴan Jere Zasu Zo.
Innarmu Kam Sai Kai Kawo Takeyi Cikin Yan Uwa da Abokan Arziki Ana Ƙokarin Ganin Komai Yatafi Dai-dai.
KASHE GARI.......
Data Kasance Ran Assabar Aka Tashi Da Buki Haiƙan Aduk Gidajen Biyu Kowa Sai Kai Kawo Yakeyi Cikin Matuƙar Farinciki da Nishaɗi.
Gidan mu Yacika Tamƙam da Al'umma Sai Hidamar Buki Ake Tayi Nikuwa Sawa da Hissuwa Nakeyi Insaka Atamfa Insa Les Insa Shadda. Harzuwa Sanda Aka Zauna 'Walima' Malama Zuwairiyyah (dan Ita Momy Ta Gayato)Tayi Wa'azi Akan Haƙƙoƙin AURE A Musulunci Da Irin Yanda Mace Yakamata Ta Kasance A Gurin Mijinta Lakaca Guda Tasauke Akan "Wace Macce Mafi Soyuwa A gurin Mijinta?" Kai Mutane Sunƙaru Sosai Sai ALLAH Shiyi Mata Albarka Ake Harma da Momy da Tazama Sanadiyar Kawota. Yayinda Su Aunty Shahuda da Mmn Walida (da Yake da Lokacin Walima Yayi Yan Gidan Ango Sunzo.) Suka Shiga Rabon Kayan Buki Irin Su, Take Awaye da Ƴan Ƙananan Botikai Wasu Abin Kwasar Shara Suka Samu Kuma Kowane na Manne da Stikacs ɗin Sunayen mu.
Aka Tashi Walima Cikin Farinciki da Annushuwa. Misalin Ƙarfe Takwas Motocin Ɗaukar A Marya Suka Hallara Gidamu.
Ɓangaren Ango Kuwa Suna Can A Wani Masallacin Jumu'a Inda Malamai Kusan Biyar Sukeyin Lakca Akan Abinda Yadangaci AURE. (Kasancewar Abdul-wahab ɗalibi Mai Kuma Zama Majalisin Malaman Ahlis Sunnah. Shine Fa Aka Sa Wannan Walimar Wadda Tasoma Gudana Bayan Gama Sallar Magarib) Malamai Sunyi Lakcoci Masu Zafi Akan Aure daga Cikin Su Akwai Mai Taken, "Wanene MIJI Mafi Daraja Agurin Matarshi." Wani Malamin Kuwa Yayi Lakca Akan "Falalar Aure" Wane Kuwa Yayi Akan "AURE BAUTAR ALLAH." Taƙarshen Itace "Yanda Yakamata Ma'aurata Su Kasance A Rayuwarsu Ta Aure." Suma dai Anci Ansha Anyi Hani'an. Kuma Kowa Kagani Yaci Ado Sosai (Kunsan Maluman Ahlus Sunnah Akwai Gayu Dama😅) Tau Itama dai Haka Tashi Cikin Farinciki da Nishaɗi Ango Nacikin Abokai Baki Yaƙi Rufuwa Sai Ƙyalli Yakeyi Cikin Wata Tsaleliyar Shadda Fara Tas! Shi da Abubakar Baka Gane Waye Angon.
Karfe Tara Dai-dai Aka Ɓanbaro ni Jikin Dady da Akai Kaini Gurinsa da Nufin Yayimin Nasiha Aka Shigar Dani Mota Sai Kuka Nakeyi.
Ƙawayena Suna Tayani Musammama Na Unguwar mu Kasancewar Su Kullum AnaTare.
Ina Zaune Tsakiyar Tattausan Gadona Nasha Lulluɓi Haryanzu Hawaye Nakeyi Yayinda Sukam Ƙawaye Na Suka Gyagije Suna ta Sha'anin su na Shaƙiyanci. Saiga Ango Da Tawagar Abokan Su Sunshigo Nanfa Guri Yaƙara Kacamewa Aka Shiga Siyen Baki Nidai Duk Abinda Suke Inaji Harsuka Gama Aka Kwashe Ƙawayena da Nufin Kaisu Gida Angon Yaɗaga da Nufin Musu Rakiya Suka Maidashi Suna Masa Shaƙiyancin Su da Akasan Kowayen Abokan Ango Nayi.
Bayan Fitarsu Yakasance daga Ni Saishi, Sai ɗakin Namu Yaɗauki Shiru Inbanda Ƙarar Fanka dake Aikin Bada Iska Aɗakin Baka Jin Komai. Sannu A Hankali Abdul-wahab ɗin Yamiƙe Tareda Cire Hullarsa da Babba Rigar dake Jikinsa Ya'ajiye Gefen Gado Yafita Zuwa Falo.
Sai Gashi Yadawo Da Ledoji Ya'ajiye Sa'annan Yahayo Gadon Tareda Yayi Mani Rufin Mayafin da Ke Kaina Nikuwa Nayi Saurin Runtse Idona Tareda Saukowar Wasu Hawaye Akan Fuskata Suka Wuce da Gudu.
Murmushi Yayi Tareda sa Yatsansa Ya Lakuci Hawayen Yakai ga Fuskarsa Yana Duban Yatsansa Nasa Yace, "Ina Fatar dai Wayyanan Hawaye Na Farinciki ne Ko?" Nidai Ban Tanka Sa Ba. Yace, "Barka mu da Ganin Wannan Ranar da Kafin Risƙar ta Sai da Muka Tsallake Siraɗi daban-daban."
Nanma dai Nayi Shiru. Yasake Cewa, "Ina Cewa Bakin Nan Tunɗazu Muka Sayeshi Ko Bai Sayu Bane Insake Saye?" dagama Faɗin Hakan Yakaimin Wata Sumba(Kiss) Wanda Bansan Sanda Na zabura Ba Nace, "Meye Haka dan ALLAH?" Mezai Inba Dariya ba "Ai Yanzun Kin Magantu." Yace, "Tashi Ki Nemo Mana Flet Mana." Miƙewa Nayi Muka Fito Tare Na Nufi Inda Nake Kyautata Zaton Nanne Kitchin ɗin Yayinda Shikuwa Yafice.
Ina Tsakar Gida Flet da Cup Nake ɗaureyewa Axuciyata Ina Yaba Irin Ƙoƙarin da Su Momy Sukayi Min Acikin Kitchin ɗina. Babu Abunda Babu Kuloli Kala-kala Ga ɗan Ƙaramin Gas da Suka Siyamin Dasu Blanda, jug-jug Da Kuma ɗam Madaidaicin Oven. Maganar Gaskiya Sun Shaƙemin Kitchin ɗina Makil da Kayan Aiki Wanda A Wannan Zamanin da Muke Ciki Kitchin ne Abin Kallo ga Mutane.
Ina Cikin Adu'ar ALLAH Yasaka Masu da Alkairi, Abdul-wahab Yashigo Gidan Ɗauke da Faranti da Wasu Sabbin Kuloli Jere A Sama. Ya Kalleni Yayi Murmushi Yace, "Afuwant Nasa Amarya Aiki." Ya'ajiye Farantin Gefe Yana Naɗe Hannun Rigarsa Kafin Yace, "Ɗauki Faranti Shiga dashi Ciki Bani Wannan Inƙarasa." Nace, "A'a Nikam Ibada Ce Kuma Nariga Nasoma ta Daga Yanzun Sai Sanda Kaɗaga Min Ƙafarka Na kuɗe Aljannah." Yakama Baki Kamar Wata Macce Gamida Faɗin, "Tau, Bakin Kuma Yabuɗu Yanzun Kenan?"
Falo Muke Zaune Ina Aikin Zuba Masa Lallausan Tuwon Semo da ɗanyar miyan Kuɓewa da Ta Wadatu da Nama ga Kuma Ƙamshin Manshanu dake Ta Tashi Cikin ta. Natura Flet ɗin Gabansa, "Bismillah!" Nafaɗi Hakan Can Cikin Maƙoshi Dan Bana Tsammanin Yamaji.
Yakalleni Ya Kalli Felt ɗin Abincin Kafin Yayi Murmushi Yace, "Amarya Kinsha Kamshi. tau Ai Matsowa Zakiyi Muci Ko?" Nace, "Ai Ni Naƙoshi." yayi Maza Yahaɗe Fuskarsa, "Amma ɗazun Kince Min 'Ibada Ce Kuma kin Riga Kin Soma daga Yanzun Sai Sanda Naɗaga Kafata Kika Kuɗe Aljannah'." Yayi Shiru Yana Mai Sauraro Daga Gareni Nace, "Lalle Haka Nace."
Cikin Nutsuwa Yace, "Tau Kuma Yiwa Miji Musu Yana Cikin Ibadar ne?" Nayi Maza Na Girgiza Kaina Nufin dai A'A Yace, "Tau Matso Muci Abinci Innarmu ce Tagirkashi da Kanta, Kuma Tasan Wayeni Ƙwalama Bata Ƙosar dani Hakanan Bana Cin Wani Girki In Ba Nata Ba, Shiyyasa Duk Ruɗun Buki Bai Hana Ta Tashiga Kitchin Tayimana Wannan Girkin ba. A Sanda Tabanin Kuwa Cewa Take Intabbatar Kinci Kin Ƙoshi Saboda Tasan Irin Wannan Ranar Ba Komai Amarya Kanci Ba."
Muna Cin Tuwon Mai Laushi da Matuƙar Daɗi Nace, "Hakane Kam." Yakai Loma Yana Faɗin, "Tau Wai Meyasa? " Nai Maza Nace, "Oho Karka Tambayeni Nikam." Ƴar Dariya Kawai Yayi.
Saida Mukaci Muƙoshi Dan Abdul-wahab Bai Barni Nayiwa Cikina Ƙyata ba.
Muje daku Muji Ya Amarci Zai Kaya?
Tareda Alkalamin
FA'IK ✍🏼
[9/7, 11:53 AM] FA'IK: Typing....... 💻
❤❤SONEEE ....💕💕
(Silar Komai.)