← Book details So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 40

Gabatarwa

So Ne Silar Komai Part 1 Complete Hausa Novel · about 41 min read

[9/5, 9:12 PM] FA'IK: SONEEE....
(Silar Komai)
Fage...1 (Book one)
Mallakar 👇
Fa'IK ✍️
07039676994
Typing....
GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.

Bissmillahi Rahmanin Raheem

Yanayine Na Hunturu Karfe Goma ne Amma Sai Kazaci Karfe 7 ne Saboda Tsananin Sanyi Daya Haddasawa Kowa Qiwar Fitowa Duk Kuma Wani Da Yayi Kundun Balar Fitowa Tau Dole ne ka hangeshi Lullube Da jibgegiyar Rigar Sanyi, Wani Santalelen Matashi Nahanga gefen Titi, Yayi Zaune Saman Wani Dan Kwalbati Dake Gefen Titin. Abin Mamaki Shikam Daga Shi Sai Farin Yadin Dake Jikinsa. Babu Rigar Sanyi A Jikinsa Kuma Ko Alama Bai Nuna Yama San Sanyin Akeyi. Abun Da keda Ban Mamaki Kenan. Kawai Naga Yayi Tsaki Yamike Yashiga Cikin Gidansu Yana Kokarin Share Hawayen Da ke Ta Kokarin Safka A kyakyawar Fuskarsa. A Tsakar Gidan Yatarar Da ita Tana Kokarin Kimtsa Jikinta Tana Hada Yan Kayanta A Bakko Wanda Hakan zai Nuna ma Alamun Fita Zatayi Tunda Matashin Nan Yashigo Tadaga Kai Ta kalleshi Bata Sake Kallonshi Ba Ta Ci Gaba da Sabgoginta.
Abunda Yakara Daga Hankalin Wannan Matashin Kenan Yakuma Haddasawa Hawayensa Cigaba Da Gudu A Fuskarsa Ya durkusa Yana Mai dubinta Da Fuskar Nadama Yace, "Innarmu Dan Girman ALLAH ki ya......" Cike Da Fusata wacce Yakira Innarmu Din Takatsesa Ta Hanyar Daga Masa Hannu, Tace, "Bana Bukatar Jin Komai Daga Gareka. Ni Wallahi Da Zaka Kyaleni ma Sai In Fi Shakar Numfashi Cikin Sa'ada, Kuskure ne Nagane Nayi Kuma Baxan Kara Sake Yin Makamancinsa Ba. Shine Kawai." Cike Da Sheshhekar Kuka Da Tarin Nadama Yabuda Baki Zaiyi Magana Takara Katsesa Itama Din A Yanzun Muryar Ta Na Rawa, "Amma dae Nace Bana Bukatar Jin Komai ko? Ka kyaleni Yafi min Sa'ada In Kuma Haryanzun Bukatar kake KaCigaba Da Nuna min Iyakata Tau Bismillah!." Tadire Wannan Maganar A fusace Kafin Ta juya Zuwa Dakinta Wanda Da Ka kallesa Kasan Yana Cikeda Maraicin Abubuwan Da Zasu Qawata Shi.
Shidinma Matsahin Jiki Ba kwari Yanufi Nasu Dakin Kafin Yazube A Yar Tsamurarrar Katifarsa Yana Mai Kyacewa da Wani Irin Kuka Dake Tasowa Tun Daga kasan Zuciyarsa. Wanda Kaitsaye Zaka yanke Masa Hukunci Cewa na Nadamar Abinda Ya Aikata ne. Can Kawai Yamike yasoma Gaura Kansa Da bango Yana Kuka Tareda Cewa "Nayi Nadama! Natsani Kaena! Nayi Nadama Innarmu Wallahi In Baki Gafartamin Zan Hala....." Kanensa Dake Cikin Toilet ne Yay Saurin Fitowa Ya tushe Masa Bakinsa Gamida Rikesa Shima Din Hawaye yake Yana Cewa, "Haba Yaya Kadaina Fadar Haka Ka Kuma Daina Abinda kake Kakuwa ga Yanda Kajiwa Kanka Rauni? Comon Big Bro in Rai ya bace Bai Kamata Ace Hankali Yadaina Aiki ba." Wanda Yakira Yayan Yadubesa Cikin Sharaftu Hawaye "Abubakar kabarni Na Girbi Abunda Na Shuka ban kyautawa Innarmu ba Ban kyauta ba Ban...." Yakasa Karasawa Sbda Kuka Yaci Karfin sa Abubakar yace Masa "Tun Farko ai Yaya Sai da na Nuna maka Gashinan Yanzu wa Gari Ya waya?" "Neni Abubakar Kuma Natabbata Sakarai Wanda Bai San....." "Yaya Duk Wannan Bata Taso ba, kabar Jifar kanka Da wayyanan muna Nan kalaman..." "Dole najefi Kaina Da wayyanan kalaman Inma Akwai Wasunsu kasanar Dani Danna Fadawa Kaina Ikram Ta Cuceni Taci Amanata Ta Kuma Wargaza Rayu...." Abubakar yasake Rufe Masa Baki Yace "is enough Yaya. Kana da Sauran Dama Haryanzun. Kazo Mu sake Gina Rayuwarmu Kamanta da Batun Wata Ikram...."
Abdul Yadubesa Yace, " Tayaya Zan Manta Irin Wannan Tabon Tayaya Zan iya Gogeshi Eh ? Ka gayamun Abubakar Ina Sauraren ka?" Izuwa Yanzu Abubakar Yafara Tunanin da Kuma Fargabar Anya Abdul Dinsu Kuwa Nada Hankali? Inkuwa Yana Dashi Tau Yana Cikin Hayyacinsa? Da Wannan Tunanin yakamo Hannun Dan uwan Nasa ya zaunar Dashi Kan katifar Dakin Nasu, Kafin Yaje Yayi burkuce A Dakin Nasu Yasamo kyalle Yazo Yana Dorawa A Goshin Yayan Nasa. ALLAH yatakai ta Raunin Ba Sosai Bane.
Kaitsaye Abubakar Yafita Daga Dakin Nasu Yanufi Inda Innarmu Ke Dafenta-Dafenta Yagama Bude-Budensa Babu Komai Cikin Tukanen, yadanyi Tsaki Kawai. Sa'anan Yakoma Dakinsu Yadauki Flaks Kai tsaye Gurin Mai Shayin Unguwarsu Yanufa Da zuwansa suka Gaisa Da Habu Mai Shayi Kafin Ya'amashi Flask Dinda Abubakar din ke Miko Masa Yana Cewa "Harna Cire Ran Yau zaka Zo ma Ai." Abubakar Yayi murmushi Yana Neman Gurin Zama Kan Bencin Da ke laye A Gurin Inda Cosmtomomin Habu Mai Shayi Ke Zaune Wani Na Shan Shayi da Bread Wani Kuma kwai ne Da Endomi Ke Gabansa Kuma Dukkaninsu Sunyi Shiru Sai Aikin Bama Ciki Hakkensa Suke. Habu Mai Shayi Yana Kokarin Zuba Masa Ruwan Liptom Din A Flask Yasake Cewa, "Takwara Lafiya kuwa Nidae bansanka Miskili ba Da Yayanka Ne Abdul Ma banayi Mamaki ba." Karo Na Farko Da Abubakar Yayi Dariya Yace, "Kaidai Habu Surutu bayama Wahla Shi Yaya Abdul Shaidar da Aka Masa Kenan ko? Abun da yasa kaga banyi Saurin Zuwaba Bana Da Zuwa Class Da safe Shiyyasa, Kuma Kaga Gari Da Sanyi Fitowa yau Sai Mutum Yayi Dagaske." "Indon wanna Da Wannan Kam, Gari Yau Antashi Da Sanyi." Habu Yafadi Hakan Yana mai bude Robar Da Yake Sa Shuga Da Nufin Yadiba Yasa Acikin Flask din Da yariga Yazubo Masa Ruwan Zafin Abubakar Yayi Maza Yace Masa "A'a Karka Sa Shugan Bana Bukata Samin Lipton Guda Biyu." Bayan Yasa Ya Miko Masa Yana cewa, "Wanna Ruwan Lipton Na Yayan Kane Abdul." Abubakar yakarbi Flask din Yana Cewa "Koma dae waye Ina Ruwanka? Kajimin Mutum Da Sa'ido?" Yasa Hannun Acikin Aljuhunsa Yaciro Kudi Yamika wa Habu Mai Shayin, Kafin Yajuya Yanufi Wani Mai Shagon Yabar Habu Na Dariya Gamida Cewa, "Baxaka Tsaya Ka karbi Canjin ba?" Shidai Abubakar ko juyowa Bai ba. Dan Yasan Inya Biyewa Habu Mai Shayi Sai Su Kai Yamma Suna Abu Dai. Shima Dae Habu Soke Kudin Yayi A Aljuhunsa Dan Yasan Suna Haka In har Yabar Masa Canji Tau Hakan Na nufin Da Yamma ko Da daddare Zai Dawo Ya karbi Ruwan Lipton.
A Wurin Masu Shagon Bready Ya Siya Da Kayan Tea Sa'anan Yakama Hanyar Gida Cike Da Tunanin Yanda Cikin Gidan Nasu ke Cikin Matsala A Yan kwanakinnan. Dan Tsaki Yayi A ransa, Wanda Yayi Dai Dai Da karasowarsa Dakin Nasu. Abdul yadago Daga Tagumin da Yayi Yana Mai Cewa, "Kaima kanajin Haushi Nane ko? kayi Hakuri kanena Wallahi Duk Abinda Yafaru, Yafaru ne Cikin Kuskure Amma Bawai Dan Niyyah ba." Abubakar ya janyo Wani Cup Yashiga Hidimar Hada Shayin. Sai da Komai Yahadu Yakawo Gaban Abdul Din Yace, " Yaya Ga Shayi ka karya Sannan Muyi Magana. Ni Banyi Tsaki Dan Ina Jin Haushin ka ba Sai Dan Yanda Walwala Da Farinciki Suka Kaura Daga Gidannan Namu Tun Bayan Kunnowar wannan Matsalar Kuma Tun Farko Yaya Da ka karbi Shwara ta Tau Da Hakan Duk Bata Faru ba." Abdul Cikin Jin Takaicin kansa Yace, " Kuyi Hakuri kaida Innarmu Nasan nayi Ba dai dai ba Amma Wallahi SONEEE Silar Komai Bawai Dan Ina da Niyyah hakanba Amma Na....." "Yaya Mubar Wanna Maganar Zamuyi ta Daga Baya Abunda Nakeso Dakai Yanzu Ga Break Fast Nan Na hadaMa ka karya Kayi wanka Ka Kuma Canja Kaya Sai Mu Zauna mu San Ta Inda Zamu Gyara matsalar pls." Abdul Yadubi Qanin Nasa Ido Cikin Ido Yace "Da zaka Taimaka Qanina da Munyi Wannan Maganar tafiye min komai. A Yanzu banaji Ina Da Wani Bukata Sama Da Gyara wannan Kuskurenda Na'aika ta Ciki kuwa Harda Abinci da Komai Zan iya Hakura Dasu." Abubakar Yayi murmushi da Kai tsaye Kasan Ba na Dadi Bane Kafin Yadubi Yaya Nasa Yace, "Yaya Ko A wancan Kuskuren Da kake Neman Gyarawa A Yanzun Taurin Kanka ne Yajanyo Hakan Kakuma Yimin Afuwa Da wannan Furucin Banida Wani Harshe Da Zan Amfani Ne Bayada Wannnan. Dan Haka Yanzun ma Idan Kaki Karbar wannan Shawarar Watau tafara Gabatar da Cin Abincin ka Da Kuma kimtsa Jikinka Tau Bana Raba dayan Biyu Yar Gidan Jiya Za'a Sake komawa. Sabo da Haka Ina Mai Rokonka Da ka Karbi Kayan Karinnan Ka Karya."

Abdul Bai Musa ba Yajanyo Kayana Shayin Ya Soma Sha Wanda Kai da Ganin kasan Yana Shane Kawai Bawai Dan Yanajin Gardinsa ba. A Kasalance Yake Komai Nasa. Bayan Yafito Daga Wanka Jallabiya Fara Kar! Yadauka Yasa Kafin Yajingina Da bango Yana Mai Kallon Qanin Nasa Watau Abubakar Da Yattara Duk Hankalin sa Akan Wani Littafi Na Biology.
Cikin Murya Mai Nuna Alamun Ma Mallakinta Nacike Da Tarin Damuwa Abdul Ya Soma Magana, "Abbakar Na kammallah Sai Muyi Maganar Da kake Cewa Ko?" Abubakar yadan Rufe Littafin Biology Din Da Yake Nazari Kafin Yajoyo Ga Yayan Nasa Yana Mai Murmushi Kafin Ya Soma Da Fadin, "Duk Mai Faruwa ta Faru Yaya Dan Haka Duk Wata Damuwa Kayi Watsi Da ita Kafara Sabuwar Rayuwa Matakin Gyara Na Farko Da Zamu bi Shine Mufara Neman Gafarar Innarmu Sannan Mudora Na Gaba."
Cikeda Tarin Damuwa Abdul Yalumshe Idanuwansa Kafin Yasake Budesu Yana Kallon Fuskar Qaninsa Mafi Kuma soyowa Gareshi, Yana Rayawa A Ransa Ina Ma'a ce Baya Zata Dawo? Wallahi Da ya Dawo da ita, Ya Hana Duk Wani Abu Da Yafaru Sake Faruwa. A Hankali Abubakar yakama Hannunsa Yana Rintse Sa Cikin Nasa Yace "Kada Kayawaita Damuwa da Tunani Yaya Kamanta Duk Abinda Yafaru Ka daukeshi Amatsayin Kaddarace Kawai Wannan Shine Zai Karfafemu Wajen Gyara Abubuwan Da Suka Lalace."
Abdul Ya Sauke Wata kakkafar Ajiyar Zuciya Kafin Yadora da Cewa "Kana ga Yanda Innarmu Tadauki Zafi Dani Zatai Hakuri?" Cikeda karfafawa Abubakar Yake Girgiza Masa Kai game da Cewa "Da Izinin ALLAH Zamu Ciwo Kan Innarmu Zatayi Hakuri Kasan Itadin Mai Son muce Kuma Mai Sadaukarwa Akan Komai Namu Dan Haka Bana Zaton Zata ki Yafiya Gareka Yayana." Abdul ya Sunkuyarda Kansa Cikin Wani Bakinciki da Tsanar Kansa Yace "Qanina Daina Tunamin Hakan, Wallahi Kara Tsanar Kaina Nake Kana Kuma Tuna min Irin Butulcin Da Nayi wa Innarmu ne Akan Wata Macce Kaicona Ni Abdul Nayi Asa..." "Kash! Yaya Nagayama Kai Daina irin Wannan Tunanin Kabar Komai Yawuce Kama kanka Fata Nagari Kaji Yaya? Ba Wanda Baya Kuskure Kuma Ba Wanda Yake Tsallake Kaddararsa."
Tau Da irin Wayyanan Kalaman Abubakar Yayi Ta Tausar Yayan Nasa Dasu Wanda Babu Shakka Sunyi Tasirin Akansa Sosai Dan Har Yasamu Yadan Jincira Har Kuma Gashi Barci Na fisgarsa Dan Haka Sai Kawai Abubakar Yamike Ya kunna Masa Karatun Kur'ani Acikin Kira'ar Maheer Zain Acikin Yar karamar Mp Dinsu Da Suka Hada Kuddi Suka Saya. Wannan Abun bakaramin Kara Samarwa Abdul din Nutsuwar Zuciya Yayi Wanda Harshi Kansa Abubakar din ya Amfana. Kafin Kace kwabo Sai Ga Abdul Yana Barci lakadan. Ko Banza Yayi Kwana da kwanaki Bai Runtsa ba. Ganin Hakan Abubakar Yayi murmushi Tareda Mikewa Ya sunce Kayan sa Yadibi Ruwa A boket Yanufi Bayinsu Dan yin Wanka Dan Karfe 1 Tana Karatowa Kuma lokacin Yake Da lakca A Makaranta.
Yafito Sai karkrwar Sanyi Yake Sabo Shi Kansa Yasan ba Karamar Jarumta Yayi ba Na Wanka Da Ruwan Sanyi A Irin Wannan lokacin ba. Sai da Yagama Shiryawa Kafin Yahada Tea Da Bread Yasha Kafin Ya Rarumi Jikkarsa dake Cike Da Hand Out Yafita Yana karawa Jawa Abdul Kofar Dakin. Murmushi Yayi A sanda zai gota Kofar Dakin Innarmu A Ransa Yana Cewa, "Innarmu Badai Fushi ba, Gashi Ya Abdul yajamin Nadaina Samun Dumamen Mai Dan Dadi." Kai Kawai ya Girgiza Kafin Yafice A waje Yana Jiran Abokin Karatunsa Da Zai Biyo Masa Da Mashin.
Bai Dau Dogon Lokaci Ba Sai Gashi Ya'iso Yaku Haye Suka Damki Hanyar Zuwa School.


************
Da Yamma ne Sosai, Sai Dai Rana A lullbe Take Sabo Da Sanyi Ko Ina Yayi Lumshi Mutane Sai Hada-Hada Suke Kowa Na Kokarin Ganin Yayi Saurin Kammallah Abunda Yake Dan Isa Gida Da Wuri Saboda Yasamu Ya Adana Kansa Tun Gabatowar Magarib.

Innarmu Na Cikin Jirin Wayyanan Mutanen Dan Agaggauce Ta iso Gida Ta Soma Da ajiye Yar Bacconta Kafin Tashiga Share Gidan Tsaf Daga Bisani Ta Shiga Kiciniyar Girki Dan Kwana Biyu Batayi. Amma Ga Alama Yau ta Dan Sauko Daga Dokin Fushin Da Ta hau Tsakar Gida Ta Ajiye Yar Tsugguno Tazauna Tana Aikin Tsintar Shinkafa A ranta Sai Lissafin Sauran Kwana Nawa Yarage Azumi Yazo Da Kuma Irin Shirin Tarbarsa Da Yakamata Tayi. Tana Tsaka Da Wannan Tunanin ne Abubakar Yafado Gidan Da Sallamarsa Innarmu Ta'amsa Sallamarsa Batareda Tadago Ta kalle sa ba Murmushi Kawai Yayi. Yawuce Dakinsu Ya'ajiye Jakarsa Kafin yazube Kan Yar katifarsu Cike Da Gajiya da Kuma Tunanin ta Ina Zai Fara ne? Yana Cikin Wannan Nazarin Ne Aka Turo Kofar Dakin Nasu, Ga Tunanin sa Innarmu ce Haryana Murnar Ta Sauko Kenan Tunda Gashi Yau Ya ga har Girki Take Musu Sabanin Yan kwanakin da Suka Shude Sai Dai Taciko Cikinta Daga Gurin Da Take Aiki In kuwa Hakan Bai Samu ba Sai dai Tajika Gari Da Shuga Tasha Tayi kwanciyarta.
Wata Irin Kakkafar Ajiyar Zuciya Yasauke Yana Mai Kallon Abdul Din Da Yashigo Duk Sukayiwa Juna Murmushi Irin Na Yake. Abdul Dae baice Masa Komai Sai Dai Yanufi Ina Suke Ajiye Jikkar Pure water Dinsu Wadda Sukan Siya Idan Gari Yayi Musu Dadi Inkuwa Baiyi ba Suje Randar Innarmu Suciko Jug Su Sha pure water Yazaro Kafin Yamika Masa Yana Mai Cewa, "Amshi Kasha Bawai Dan Kana Jin Kishirunwa A Irin Wannan Hunturu ba Sai Dan Irin Bushewar Da Makoshi Kanyi Idan Ana Cikin Irin Wannan bacin Rai." Abubakar din Yamika Hannun sa Yakarba Yana Cewa, "Kaji Ka da Wani Zance Ya Abdu Ai Yanzun Alamun Sauki Na Zuwa Kai Baka Ga Alamar Innarmu ta Sauko Ba Gashi Yau Har Girki Za'a Rangada Mana." Abdul Yayi Dariyar Da yadade Baiyi Ba Tun Faruwar Wannan matsalar Kafin Yace, "Kaifa Ja'iri ne Wani Lokacin Innarmu dince Tace maka Dammu Takeyi? In Kuma Baki Zatayi?" Abdul Yamike Yana Fadin, "Koma Dai Dan Waye Ni yau Sai Naci Girkin Nan Nayi Missin Dinsa Nakuma Gaji Da Ruwan Shayin Da Nake ta Durawa Cikana Sai Indome Wadda Bata Rikon Ciki." "Dama Ai Kai Indae Akan Cikine Nan Kafi Auki?" Abubakar ya waro Ido, "Tau Kaga Laifinane Ya Abdul Ai Komai Za'ayi Sai An koshi Akeyinsa. Ni Kaga Zomuje Ma." Yafadi Hakan Yana Mai Jan Hannun Yayan Nasa Inda Kai Tsaye Suka Fito Tsakar Gidan Inda Innarmu Ke Zaune Kan Yar Tsuggunonta Tana ta Aikin Tsintar Shinkafa. Ta gefen Ido Take Kallonsu Taga Ina Suka Nufa Wurinta Sukazo Kai Tsaye Suka Zube Kan Gwaiwowinsu Aikuwa Da Azama Tamike Tanufi Dakinta Suma Suka Mike Suka Bita Tasake Banke Labulen Dakin Tafito Zuwa Tsakar Gida Nan ma Suka Sake Biyota. Bata Kasa A Gwaiwa Ba Tasake Komawa Daki Abinta A Yanzun Kam Abubakar daene Mai Kwarin Zuciyar Binta Cikin Dakin Shikam Abdul Sai Ya Durkushe Nan Bakin Kofar Dakin Yana Fitarda Wasu Irin Zafafan Hawaye.
Abubakar Din ma Na'isa Gabanta Yazube Yana Mai Dora Hannuwansa Kan Cinyoyin Innarmu Kafin Yace Komai Sai Ga Innarmu Tafashe Masa Da Kuka Dama Can Kwarin Zuciya Ce kurume Take. Kuka Riris Innarmu Tafashe Musu Dashi Wanda ko A Rasuwar Mahaifin Su Batai Irin Sa ba. Kai Suna Ma Iya Rantse wa Tun Wayon Su Basu Taba Jin Tayi Kuka ba. Saboda Itadin Innarmu Macce Mai juriya Da Kuma Hakuri Da Tsananin Ibada Dan Haka Ko Da Yaushe take Cikin Kamala.
Dole Suma Kukan Yakwace Musu Dukda kuwa Taurin Rai Da Aka San Da Namiji Dashi Mussamman ma Abdul Da Yakara Tsanar Kansa Wai Yau Akansa Innarmu Ke Irin Wannan Kuka? Innarmu Mai Tsananin Sadaukarwa Akan Sha'anin su Idan Har Bai Sa that Farinciki Ba Anya Ta canci Irin Haka? Shikuwa wace Irin Rudewar Duniya ce Ta sameshi Haka? Wayyanan Tamboyoyin da Tunanunka Da Sukai wa Zuciyarsa Rubdugu Suka Bashi Kwarin Gwaiwar Mike wa Yanufi Dakin Amma me Yana Kan Niyyar Shigar Innarmu Tadaka Masa Tsawa Acikin Muryarta Da ta wadatu Da Bacin Rai Cewa, "Karka Kuskura kashigo min Nan Wallahi kana Shigowa Zan Sallamaka."
kalamanda Suka Takawa Abdul Burki Kenan Yakuma Zube Bakin. Kofar Yana Wani Irin Rishin Kuka.
Yana Ta Nana Cewar, "Ikram Kin Cuceni Kinci Amanata Kin Hada Ni Da Mahaifiyar mu Mafi Soyuwa Garemu
Innarmu In Baki Yafemin Ba Ni Na San Nalalace Kawae. Wayyo ALLAH Na SONEEE (Silar Komai) Shine Ya Tarwatsa Rayuwata Da Ta Ahalina Ikram Kinci Yaudareni Menayi Miki Kika Zabi Cutar Dani Haka?" "ka Gyara Maganar ka Me Nayima Ka Zabi Kwarewa Kwarin Gwaiwa Ta Akanku? Abdul Na Hakura Da Kowa Nawa, Na Yafe Duk Wani Farinciki Saboda Dae Naga Rayuwarku Ta Inganta, Ashe Ni Bansani ba Kuskura Nayi? Na Dauke KU Komai Nawa Ashe Ni Bansani ba Ku A Gurinku Bahaka Bane? Zaku Sa Yan Uwana Sumin Dariya? Zaku Sa Yan Uwana Suce Dama Mun Gayamaki..."
Kafin Tayi Shiru, Tasanya Gefen Zanenta Tana Fyace Majina.
Abdul Nadama! Tsanar Kansa! Bakinciki! Duk Sai Suka Masa Dirar Mikiya A Zuciyarsa. Dan Haka Sai Yarasa Abunda Zaiyi kawae Sai Yazabi Yayi Kukan watakil Yasamu Sa'ada A Zuciyarsa Kuma A Yanzun Yana ga Shine Abu mafi Arha Da Sauki A Gareshi. Abubakar Dake Durkushe Gaban Innarmu Shine Kadai Keda Kwarin gwaiwar Magana Shima Acikin Kukan yake Cewa, "Kiyafe Mana Innarmu Wallahi Mu Badamu Ba Ya Abdul Shima Kuma ba Laifin Sa Bane SONEE......Silar Komai." Cikin Muryar Bacin Rai Innarmu Tace Masa, "KU Daina Yaudara ta Abbakar Da Cewa SONEE ....Silar Komai Kawai Kune Silar Komai Son Zuciya Ne Silar Komai Amma Meye Amafni Wannan Son? Nace Meye Amafnin Wannan Son indae Bai Zama Silar Alkairi Ba Ai Bai Kamata Ya Tarwatsa mu ba......" Abdul Ya Rarrarafo Kamar Dan Karamin Yaro Ya Iso Gareta Yana Cewa, "Natuba Innarmu Nabi ALLAH Nabiki Dan ALLAH Kimin Alfarmar Saurarena Kiji Ta Inda Abun Yafaro....kinji Innarmu? Dan ALLAH badanni Ba." Shima Abubakar Sai Yasako Bakinsa Yana Taya sa Roko Tareda Cewa, "Innarmu kidaina wannan Kuka Bazamu Taba Yafe Ma Kammu ba Indae Bamu Share Maki Hawaye ba Bai Kamata mu Sakaki Hawaye Dan ALLAH Innarmu Ki Saurare Ya Abdull Kiji Uzurinsa." Magiyarsu Da irin Kuka Da Rukumkumeta Da Sukayi Duk Da Irin GirmanSu Hakan Yakara narke Zuciyar Innarmu Tayi Laushi Dama Dauriya Kawai Take Kunsan Kuma Tsakanin 'Da Da Mahaifiyarsa Sai ALLAH Wurin Yadan Dau Shiru na wayyansu Yan Lukkutan Kafin........


ASALI DA TUSHEN LABARIN........👇
........... Muje Zuwa Readers Nawa Muji Wai Tayaya So Yazama Silar Komai? In ma Yazamo Silar Meyesa Yazama? Kuma Ma Dame-Dame Yazamo Silar?
Akwai Badakala Acikin SONEE....Silar Komai... Takin Karewa Ta Inda So Zai Sa 'Da Yacanzawa Mahaifiyar sa Duk_da Irin Tarin Alkairinta Garesa. Haka Budurwa ta Canzawa Saurayinta Duk kuwa Kasancewarsa Mai Sadaukarwa A gareta Yanda Kuma Ita Kanta Buduwar Son Zai Sata Canzawa Izuwa Wata ta Daban Ba Yanda Take ba.
Kudai kubiyoni Page 2 Inda Zamu Ci Gaba Da TUFKA DA WARWARA Akan SONEE........
Dafatar Kuma zakuyi Hakuri Da Yanayin Rubutun Kasancewar Bansamu Nayi Edit ba.
[9/5, 9:12 PM] FA'IK: SONEEE....


(Silar Komai.)


Fage...2.


Mallakar 👇

Fa'IK ✍️
07039676994

Typing.....


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏.

Bissmillahi Rahmanin Raheem


ASALIN DA TUSHEN LABARIN.


Mal Rabi'u Shine Cikakken Sunan Mahaifin Su Abdul Wahab Da Abubakar Da Kuma Auntynsu Mai Suna Aisha. Kuma Shine Miji Ga Fatima Wacce A Dangi Suke Kiranta Da Inno Diyanta Kuwa Suke Cema ta Innarmu. Kamar Yadda Tarihi Yanuna Su Din Yan Asalin Jahar Sakkwato Ne Acikin Kauyen Sayyinah. Mal Rabi'u da Matarsa Fatima Watau Innarmu. Auren Zumunci Sukayi, Wanda Bayan Aure Suka Tare Nan Cikin Gidansu Rabi'u Din. Gida Mai Cikeda Dangi Iyaye Da Surukai Duk Ake Curkude Guri Guda. Gefe Daya Ga matsalar Zama Gidan Taro, Tau A Haka dae Zaman Nasu Yamika Inda Innarmu Haifuwarta Ta Farko Tahaifi Yarta Macce Suke Kiranta Da Aisha Daganan Tasake Haifo Danta Santalele Suke Kiran sa Da Abdul Wahab Daganan Sai Mai bimasa Abubakar.
Dagashi Kuma Bata kara Samun. Wani Cikin ba. Kasancewar Mal Rabi'u Mai Zafin Nema Da Kuma Himma Da hazaka Sai Iyalan Suka Fita Zakka Acikin Gidan Nasu Suka Banbanta Da Sauran Matan Yannensa Da Kannensa Dama Sauran Mata Dake Gidan. Saboda Shi Rabi'u Yana Kokarin Ganin Ya Wadata Su (Iyalinsa) Da Komai Na Rayuwa Wanda Shine Abu Na Farko Da yafara Jawowa Innarmu Tsana Da Tsangwama A Gidan. Suka Shiga Hassadar Ta Akan Yanda Tafisu Komai. Saboda Haka Zaman Gidan Sai Hakuri A Gurin Innarmu. Dama Can Ita Bamai Zafi Bace Akan Lamarin Rayuwa, Gashi Kuma Ko Da Yaushe Mijinta In Sun Samu Kebewa A Dakinsu Yana Kara Nuna Mata Muhimmanci Hakuri Komai Zai Wucewa ne.

Acikin Haka Dae Suka Sanya Diyarsu Babba Watau Aisha Makaranta Cikin Ikon ALLAH Ta Kamallah Makarantar Secondary Wanda Tana Karewa Mutanen Gida Sukayo Caaa Akan Shi Mal Rabi'u Ya Aurar Da ita. Suna Cewa, Ga Sa'aninta Nan Duk Sunyi Aure Sai Ita Kadai. Babu Yanda Zasuyi Duk-da Kuwa ita Aishar Taso Ci Gaba da Karatun Amma Zatabi Umurninsu Babanta Ko Dan Nuna Masu, Su mutanen Gida Cewa Yanda Suke Cewar Ai Innarmu Bata Barshi A Haka ba. Bahaka Bane Babansu Ya'isa Da Iyalinsa. Akasha Buki Da Wani Saurayinta Dan Asalin Jahar Zamfara Suka Tare A Gidan sa Dakenan Sakkwato Da Tafiya Tai Nisa Sai Suka Koma Mahaifar Mijin Nata Watau Zamfara Tunda Dama Nan AIKI ne Kawai Yakawo Shi.

Bayan Wata Biyu Mal Rabi'u Ya kwanta Jinya Jinyar Da Bai Tashi Ba Kenan Sai Darul Salam. Rasuwar Mal Rabi'u itace Abu Mafi Girma Da ta Samarda Wani Katon Gibi Ga Matarsa Innarmu Da Kuma Yayan ta Watau Abdul Wahab da Kuma Dan Kaninsa Abubakar Dan Ba'a Ce Da Aisha ba Tunda ALLAH Yanufa Tayi Aure, Dan Haka Ko da Gibin Ya sameta Kadanne Bisa Ga Yan Uwanta.
Innarmu iya Chanjin Rayuwa Da Kuma Kin Zumunci Irin Na Mutanen Zamanin Nan Namu Taganeshi Tun Yan uwa Da Kannen Mal Rabi'u Na Taimakonsu Harta Kai Ga Sun Daina Dan Haka Karatun Da Suke Yalalace Abinda Suka Ci Shima Neman Gagararsu Yake. Rayuwa Dae Tai ma Su Innarmu Daurin Minti Dama Yan Uwan Su Dayane Da Mijinta. Balle Tace Bari Ta Nufi Nata Dangin, Yan Uwanta ma Wani Lkcin Sunfi Tausaya Mata Da taimakon ta. Dan Dama Ba'a Taruwa A Zama Daya. Itama Can Aunty Aisha Tana Taimakon su Ta Hannun Mijinta.

Dama Can Ita Innarmu Itakadai ce Agurin Mahaifiyarta, Sai Gurin Babanta Ne Suke Da Yawa, Kuma Kowa Yasan Yadda Yan Uba Suke. Ba kasafai Ne Ake Samun Fahimtar Juna Haka ba. Tau Yau dae FARI Gobe BAKI Haka Rayuwar Taita Zuwar ma Innarmu, Dan Su Abdul Wahab da Kaninsa Abubakar ba Wani Wayo Suke Dashi ba. Akwai Sanda Innarmu Ke Hakura Da Abincin intaga ba Yawa tabarmusu Su Suci. Suma din Bawai Dan Yana isar Su ba Dan Wani Lkcin Har Kuka Suke Mata Mussamman ma Dae Abubakar din Da Shine Karamin Sosai. Haka Innarmu Zatayi ta Hawaye Tana Lallashin Sa Harta Samu Suyi Bacci Inda Daddare ne Kenan, Inkuma Da Rana ne Harsu Hakura. Gefe Daya Ga Dariyar Da Faccalolinta Suke Mata da Kuma Gori Harma Da Izgili Cewar, "Yaudae Matar So! Anzama Abun Tausayi. Yau Kuma Ina Galihun? Ai Karya Fure Take Bata 'Yaya, Wai Ita Ana Kula da Ita Tafimu Komai Tau Yau Ina Gatar? Ai Sai Abunda Kuma muka Dafa Muka Samma Ki." Sai A Bushe Da Dariya A tafa Can tsakaninsu Suke Wayyanan Maganganu. Dae dae Rana Daya Innarmu Bata taba cemusu Ta tafasa ba. Sai Dai Ma Tashiga yin Wasu Yan Sabgoginta kodai Ta Gyra Dakinta Ko ta Tattaro Wankin Yaranta Tayi, Ko ta Dauki Buta Tai Arwallah Tashige Tayi Nafila ta Soma Karatun Kur'ani. Ko Kuma Tadauki Yar wayarta Ta Itel Da Mijin Aisha Yasiya Mata Saboda Su Rika Gaisawa Da Aishar, Sai Takamo Fm Din Dake Cikin Wayar Tana Sauraren Wasu Shirye-Shirye Masu muhimmanci mussamman ma Dae Na Addini da Ake Hira Da manyan Malummamu. Wanna Kam Baya Wuce Innarmu Koda Yaushe Tana makale Da jin Su Saboda Tana Karuwa.

Wannnan Kenan!


Dare Yatsala Sosai Kowane Bawa Yana Makwanciyarsa Duk Gari Yayi Tsit! Sai Kukan Tsuntsaye DaKuma Haushin Karnuka Da Kake Ji Daga Can Gidajen Masu Su Jifa-Jifa. Wani Iska Akeyi Kadan-Kadan Gaskiyar Bahaushe Da Yace, 'Dare Mahutar Bawa.' Masu Barci Nayi, Masu Ibada Nayi, Masu Sabon ALLAH Nacan Nayi, Masu Wata Bukata Da Suke Ganin Tafi Dacewa Da Irin Wannan lkcin Suma Sun Dukufa Sunayi. Innarmu Ce Tai Kokarin Mikewa Sanda Taji Alarm Dinda Ta Sanya Abdul-wahab Ya Sanya Mata A Yar Itel Dinta. Wannnan Yake Tabbatar Mata Cewa Karfe Hudu ne Dae-dae. Dan Karfe 4 Tace Abdul-wahab Din Yasaka Mata. Bayan Tamike Kaitsaye Butarta Ta Dauka Tafito Tsakar Gida Inda Iska keta Kadawa Alamun Dae Akwai Yuyuwar Asamu Ruwan Sama A Wannan Dare, Dama Kam Wannan Zafin Da Ake Sha Sai Haka. Bayan Tafito Daga Toilet Arwallah Tayi, Kafin Tafito Da Robobinta Ta Tara A Inda Suke Tara Ruwan Sama Da Nufin In ALLAH Yasa Anyi Ruwan Saman Zata Samun Na yi Musu Wanki Kayansu Da Sauran Yan Bukatunsu.

Sallayarta Ta shimfida Kafin Ta Fuskanci Alkibla Bayan ta Kimtsa Kanta Da hijabinta Dake Ja Har Kasa, Daganan Ta Dukufa Nafil-fili Wayyanda Tun Ina iya kiddidige Adadinsu Harna Gagara. Bayan Tayi Wayanda Take Gani Sun wadaceta Tazauna Jan Carbi Kafin Tadaga Hannayenta Tana Ta Adu'a Wanda Tayi Tayi Tun Hawaye Suna Kwaronyo wa A Fuskarta Har Yaxace Da Sheshahekar Kuka Wanda Hakan Yatilasta Mata Durkushe wa Kan Cinyoyin ta Tana Rufe Fuskarta Da tafukan Hannayenta (Ina Kuke? Kunji Yanda Salihan Bayi keyi Ko?)

Daga Wannan Lokacin Bata Runtsa ba Sai Da taji Anfara Kiraye-kirayen Assalatu Sannan Ta Tayar Da Su Abdul-wahab Ta Tasa su Gaba Sukayi Arwallah Kafin Tasanya Hannun Abubakar Cikin Na Abdul-wahab Din Tace, "Kuje Massalaci, Kuma Banda Wasa Ana kammallah wa kudawo." Sukace 'Tau.' Tajuya ta Koma Daki Ta kabbara Tata Sallar.


Gari Nafara Haske Aka Tsuge Da Wasu Irin Ruwa Masu Karfi Wanda Yahaddasawa Kowa Zama Cikin Daki Innarmu dae, Dole Tafito Zuwa Nema Musu Kalanzir Dinda Zata Yi Amfani Dashi. Dan haka Tajike Shataf! Da Ruwan Saman Da Ake, ALLAH Ma Yataimaketa Cikin Gidan Nasu ne Daga Cikin Matan Wata ke Sai da Kalanzir din. Dole Ta Canja Kaya Kafin Tayi Kokarin Zuba Kalanzir Dinda Tasiyo Acikin Dan Karamin Stove Dinsu Watau Risho. Ta daureye Tukunya Kafin Ta Dora Ruwan Zafi. Ayan kwanakinan Suna Cikin Wadatar Abubuwa, Saboda Ba'a Dade Ba Da Aisha tareda Mijinta Sukayo Masu Aike.
Kunun koko Ta Dama Musu Kafin Tasake Dora Sanwar Dafa Dukan Macaroni, Irin Wacce Ake Aunowa Dinnan CE Tasa Aka Auno Mata Kwano Biyu. Kawo Yanzun Kuma Ruwan Da'ake Yadan Tsagaita Sai Dan Yam-Yam Da'ake.

Su Abdul-wahab Da Kaninsa Abubakar Tafara Gabatarwa Da Kunun Bayan ta saka Musu Suga Tace Su Motsa. Ita Kuma Tafita Gyara Ruwan Saman Da Ta Tara, Tai Sa'a kuwa Duka Robobin Suncika. Bayan ta tarshe Su Guri Daya Tadawo Dakin Nasu Wanda Yayi Dae-dae Da Shigowar Hamza Yaron Gidan Ya'ajiye Mata Kwanon Da Sunan Dan Hasafin Da Suka Saba Samu Daga Gidan. Tace, "Hamza Ana Godiya." Kafin Kuma ta Dora Da karba Gaisuwar Da Yakeyi Mata. Bayan Su Abdul Wahab Sun Gama Shan Kokon Da tazuba Masu Sannan Tabasu Dumamen Da Hamza Yakawo Sukaci Kafin Ta SallameSu Suka Kama Hayar Zuwa Makarantar Allo, Bayan Tabisu Da gargadin Su kula Da Hanya Mussamman ma Dae Abdul-wahab Da yakasance Shine Babban. Sa'anan Tadawo Dakin Ta Duba Yar Jallof din Macaronin Data Dora Taga Yana Nan Yana Zabarbaka Dan Haka Sai Ta Zuba Kunun Koko Itama Ta Zauna Tasha, Kafin Taduba Dan Sauran Canjinta Taga Suna Da dan Kauri Dan Haka Tanufi Tsakar Gidan Tasiyo Tokar (Sabulun Wanki) Dan Nanma Akwai Mai Saida Tokar (Sabulu) Daga Cikin Matan Gidan. Kaitsaye Ta Soma Wankin Kayansu Gefe Daya Ta'ajiye Yar Wayarta Tana Sauraren Shirin Da ake Gabatarwa A Lokacin Mai Suna Zauren Fikhu Wanda Abdullahi Ibrahim Sokoto ke Jagoran ta Tareda Wani Kwararren Malami, Da Yake Bayani Akan Sabbuban Tsarki. Daga Baya Kuma Masu Saurare Suka Soma Kira Suna Tamboyoyi Akan Abinda Yashigemusu Duhu Daga Sallah Ko Wani Abu makamancinsa. Wanda ke Bukatar Karin Bayanin Kan Karatun Mal Kuwa Sai Yace Ga Inda Bai Gane ba.

Hankalin Innarmu Yayi Nisa Acikin Saurare Kuma Tana Wankinta Taji Girkinta Yasoma Kauri Dole Tasaki Wankin Ta Nufi Dakin Dan Saukeshi. Bayan Ta Gama Wankin Ne, Tana Tsaka Da Shanya Wanda A Wannan Lokacin Agogon Dake Kan Wayarta Ke Nuna Karfe Dai!(1) Na Rana. Dama Kuma Yau Dole Lokaci Yayi Gudu Tunda An Wayi Gari Da Ruwan Sama Ga kuma Yanda Garin Duk Ya Rine Baka Ma Gane ma Rana Tayi. Wannnan lokacin ne Su Abdul-wahab Suka Dawo Da Makarantar Allo. Innarmu Ta Tarasu Gefe Daya Ta Zuba Musu Abinci Tana Cewa, "Abdul Kuci ku Gama Kazo Ka karbomin Katin Inkira Yayarku Naga Dazu Tana min Flashing Watakil Habibu (Mijin Aishar) Yayi nisan Kiwo Dole Kati Yay Mata Wahla." Duk Suka Hau Murnar Za'a Kira Auntynsu Suna Rikinci. "Innarmu Ni Za'a Fara Ba Inyi Magana Da ita" wannan Yace, "Ni Za'a Bawa." Innarmu Tace, "Bana Son Rigima Kuci Abincinku Yau Ba Wanda Zanba Yacinye min Kati."

************

Tau Irin Hakan Dae Shine Yanda Innarmu Ke Renon Yan Marayun Yaran ta, Da Basu Da Matallafi Sai Ita Sai Kuma Wani Daga Cikin Dangi Da In Yadubi ALLAH Yataimaketa Akan Sha'anin Su Da Auntynsu Aisha da Mijinta Dake Kan Nasu Kokarin Suma. Acikin Hakane Wani Daga Cikin Dangi Yafito Yana Mai Neman Aure Innarmu Cikin Abinda Bai Gaza Wata Biyu ba Suka Fahimci Juna Aka Daura Auren Su Saidai Baifi Wata Uku Ba Auren Nasu Matsaloli Suka Dabai bayesa Domin Dae Babu Jituwa Tsakaninsa Da Yayan ta, Kuma Data Shiga Hidimar Yaran Nata Yake Tashi Da Bala'i Kamar Anzubawa Fulawa Is. Hardai Takai Yace Indai Tana Son Zaman Nasu Yadore Tau Tabada Yaran Ga Dangin Ubansu Ai ba Ita keda Hakken Renonsu Ba. Abinda Innarmu Tasanar Masa Bazai Taba Yuwa ba.


Domin A Nan In Duniyar In Ancire Iyayenta Da Kuma Mijinta Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Tau Bata Da Tamkar Yaranta. Dan Haka Rabuwa Dasu Ba'abune Mai Yuwa ba. Shiko Yace "Tau Taje Yasaketa." Tace masa "ALLAH Yasa Hakan Shi Yafi Zama Alkairi." Wannan Yasa Tasake Dawowa Tsofon Dakinta Wanda Take A Da. Duk-da Su Yan Uwan Rabi'u Sun So Hana Mata Shi. A Cewar su Abu Zasuyi Dashi Sai Suka Samu Rashin Goyon Baya Daga Sauran Dattijan Da Suka Rage Adangi Suka Tsawatar Musu Cewa, "Wannan Kuma Basu Isa ba Sunciye Gadon Yara. Sunyi Ribda Ciki Da Dukiyar Marayu Saboda Kin ALLAH Kuma Suce Matsugunni Ma Bazasu Barmu Su ba? Tau Innarmu Tawaye Ce In ba Tasu ba Tunda Ai Cikinsu Ba BARE Dan Haka Akul Dinsu Da Wannan Maganar." Jin Haka Yasa Suka Shafawa Kansu Lafiya (Dama In Akwai Tsoffi Masu Albarka Acikin Gida Akanci Albarka cinsu Wani Zubin A Raga maka ma DominSu. Wani Sa'in Bama Gane Hakan Sai Bayan Ransu Sai muga Abinda Bai Faru ba sanda Suke Raye Yau Yafaru Saboda ba Idonsu Nan Kusa.). Zaman Innarmu Karo Na Biyu A Gidan Taro (Family House) Kalubale Da Ta Tarar Yama Fi Na Farko, Sai Dai Imaninta Yashanye Komai. Tayi Tawwakalli Itadin Ko da Yaushe Baka Ganin Fuskarta Da Wani Kunci Zaka Ga Fuskarta ta Cikin Hasken Musulunci Da Kuma Tawwakalli Wanda Ko Da Yaushe Baka Raba Hannun ta Da Casbaha Ko Alkur'ani Hakanan Bata Gaza Akan Kai Kukanta Gurin ALLAH Ba Ako Wane Dare. Kari Ga Haka, Sallar Walha Bata Wuceta Sannan Tana Tuna Wata Kalmar Mamarta Datake Cemata "Fatima Ita Wannan Duniyar Dakike Gani Mumuni Yafi Shan Wahla Acikinta ALLAH Yana Jarabtar Mumini Da Abubuwa Masu Tsauri Amma In Yayi Hakuri Zaya Samu Daukaka." Kuma Sanda Mal Rabi'u ke Raye Komai Yana Yawan Cemata "Duniya Kurkun muminice Inno Saboda Haka Komai Yake Faruwa Muyi Hakuri Insha'allah watarana Zaya Wuce, Nidai ALLAH yaga Zuciyata Bani Da Wani Buri Da Yawuce Inga Na kyautata Rayuwarki Da Ta Yaran Nan Namu Ta Hanyar Sama Maku Ilimi Nagartacce Sai Dai Wani Lokacin Ina ji Ajikina Kamar Burina Baxai Cika ba inaji Kamar Nidin Bazan Dade Tare Daku ba." Aduk Sanda Yace Mata Hakanan Sai Ta tareshi Da Tattausar Muryar ta Cewa, "Kadaina Fadar Haka Insha'allah Burinka zaicika Kuma Zaka Kasance Taredamu Wayyanan Abubuwan Suke Tare Da Innarmu Suke Kuma Kara Karfafa Mata Akan Fuskantar Kalubalen Rayuwa.


Bata Jima Sosai Ba Wani Manemin Yasake Fito Mata Sai Dai Shi Yasha Banban Da wancan, Danshi Cewa Yayi Tunda Tana Da Yara Dole 50-50 Zasuyi Ma'ana Raba Dae-dae Akan Daukar Nauyin Gida. Misali Zai Auno Gumi Ita Tayi Cefane Ko Kuma Dae Makamancinsa Kuma Nan Zata Zauna Dakinta Zai Dinga Zuwa Duk Sanda Girkinta Yazagayo Tunda Itace Matarsa Ta Ukku. Haka Innarmu Ta'amince Aka Sha Buki, Dafari Dae Yana Kwatantawa Da Tafiya Tai Nisa Kuma Sai Labari Ya Canza Salo. Ba Ruwansa Da Abinda Yadangace Ta Sannan Babu Zaman Lafiya Kullum Zagi Da Tsinuwa Dole Dae Shima Auren Ba Shiri Ya Tarwatse, Daga Karshe dae Innarmu Sai Hakuri Tayi Da Sha'anin Auren. Tunda Kowane Da Irin Tasa matsalar Kuma mafi Yawa Saboda 'Yayanta Ne. Kafin Nan Kuma Sai ga Tambarin Da Suka Mata Cewar Itadin Mai Farar Kafa Ce Waye -waye. Aka Zo Gabar Da Ta Kasa Hakuri Tayi Wa Yan Gidan Nasu Wankin Babban Bargo Wanda A Ranar Sun Sha Mamaki Ba kadanba. Dama Ance Mai Hakuri Bai Iya ba. Dole Kowacensu Tashiga Taitaiyinta Tana "ALLAH Baki Hakuri."
Da Wannan Bacin Rai Ta Ziyarci Kawarta Akan Shawarar Meye Abinyi? Kawarta Tace Ta Tashi Suje Gurin Malaminsu Na Isalamiyyah.

Bayan Gaisheshi Da Sauran Tambayar Ya Bayan Rabo Sai Kuma Tashiga Zayyana Wa Malam Abbas Halinda Take Ciki Takare Da Cema Sa Ita Gabaki Daya Garin Na Sayyinah Yafice Mata Daga Rai, Indai Ba Barinshi Tayi Ba, Tau Ko Da Yaushe Da Irin Abinda Zata Fuskanta. Kuma Dae Kai Itakam Ma Yanzun Kawai Bata Bukatar Ci Gaba Da Zama Garin Kawae." Malam Abbas Yashiga Nazarin Lamarin Tareda Girgiza Kai Kamar Kiski (Kadangare) Kafin Yace "Hakamma Dae-Dae ne, Tau Amma Ba Wannan Abun ji Ba, Inda Zata Nufa Kuma Tayaya Zata Rike Yan Marayunta?" Bayan dae Tunani Da nazarce-Nazarce Da Suka Zurfafa Itada Abokiyar ta Dakuma Malaminsu, Suka Tsaida Shawarar Ita Innarmu Ta Dawo Nan Cikin Garin Sakkwato A Shiyyar (Unguwar)Arkillah. Da Alkawalin Malam Abbas Zai Hada Ta Da Wani Amininsa Dazai Zame Mata Jagora Akan Komi Gefe Daya Kawarta Ma Tace kaunwar Innarta Na Nan Zata Hada Da ita. Nan Dae Suka Kitsa Suka Kimtse.
A Wannan Ranar Innarmu da Abokiyar Ta Mai Suna Saudatu, Suka Tattara Duk Kayan Dakinta Suka Sai dasu Gurin Dillaliyyah Sa'anan Taso Har Gonar Da Take Gado Tahada Ta Saida Amma Saudatu Ta Nuna Mata tabarta Zatayi Amfani Wani Lokacin Mussamman Ga Diyanta. Zama Ba Kaddara Ba Dadi.


Da Wannnan Shawarar Tabar Gonarta Hannun Wani Kawunta Wanda Tasu Tazo Daya. Yace, Za'a Dinga Mata Noman Rani Irin Su Kabaje, Da Salat, Da dai Sauransu. Adan Dinga Tura Mata Kudinta Itama Can Inta Samu Tana Iya Aiko Musu Sukara Cigaban Noman Ahaka Suka Rabu. A Wannan Ranar Innarmu Bata Runtsa ba Har Karfe 4 Nadare Tana Aikin Kimtsa Kayan Ta Bayan Kuma ta kammallah Shirinta Tashiga Nafil-fili. Karfe Bakwai Na safe Tashigo Motar Da Zata Kawota Cikin Birnin Sakkwato Itada 'Yan Yaranta. Bayan Tayi Sallama Da Duk Wanda Yakamata Tayi Sallama Dashi. Aminiyarta Saudatu Har Tashar Mota Ta Rakota Da Alkawalin In An Kwana Biyu Zata Zo Gurinta.

Wannan Shine Dalilin Barowar Innarmu Mahaifiyar ta, Watau Sayyinah Zuwa Cikin Garin Sakkwato Daga Nan Kuma Tasoma Zama Gurin Kanwar Innar Aminiyarta Saudatu Kuma Sunyi Zama Na Mutumci Tunda Innarmu Bata da Qiwa Komai Na Gida Yimata Take Kuma Ga Yaranta Ta Dora Su Kan Tarbiya Mai Kyau Dan Haka Sai Zaman Su Yayi Dadi Da Inna Indo. Gefe Daya Ga Aminin Malam Abbas Yana Taimakon ta Akan Wadansu Al'amurrah Kuma Tana Ganin Haske Cikin Lamaru Nata Kafin Kace Komai Sai Gata Tadawo Cikin Hayyacinta Ita Da 'Yan Yaranta Suma Har Sun Fara Karatunsu Na Boko Da Isalamiyyah. Aiki Innarmu Take Tukuru Domin Ganin Ta kyautata Rayuwar Yan Marayunta. Itace Akawo Mata Wanki Tayyi Itace Surfe Itace Reno ma mutanen Yaransu Wasu Su biyata Harma Da Kyautatawar Sutura Da Abinci. Wanin Lokacin Har Inna Indo Ta Samma Ta Itama Danshine Take Cewa Zaman Innarmu Agurinta Alkairi ne. Gashi Ta rabata Da Aikin Gida Sannan Kuma Ga Kyautar Da Take Mata In AnyimaTa Itama.
Suna tsaka Da Wannnan Kyakyawan Zaman Su Ne. Kwatsam Kuma Sai Ga..........
Taufa Readers Sai Ga Me?
Muje Zuwa Labarin Fa Yanzun Aka Somasa.💪
Acikin Labarinan Akwai Lamurrah Masu Ban Sha'awa da Mamaki Harma Da Tausayi Da Kuma Wata Irin Gagarumar Soyyaya Da Zata Zo Taxama Silar Komai. Gefe Daya Zakuji Yadda 'Ya Mace Take Zama Jaruma Akan Matsalolinta Tayi Uwa Tayi Makarbiya Ta Zama Uba Ta Kuma Zama Uwa Sa'anan Kuji Yadda Tsagwaron Soyyaya Zaisa Itadin dae Haryanzun 'Ya Mace Zata Zamo Mai Sadaukarwa. Tashin Sanse Da kowace Irin Kwamacala Akwai Acikin Book Dinan Na SONEEE.....(Silar Komai)
Ina Fatar Goyon Bayanku Wanda Shine Zai Karfafeni Wajen Cigaba da Kayatar Daku👌
[9/5, 9:12 PM] FA'IK: 💞 SONEEE....💕💕


(Silar Komai.)


Fage....➡️3


Mallakar 👇

Fa'IK ✍️


Typing.....💻


GARGADI.
Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye.

FADAKARWA.

Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. 07039676994

Bissmillahi Rahmanin Raheem


Kwatsam! Sai Gasu Sun Wayi Gari Da Wani Bakon Al'amari Da Yazo Musu A Bazata Da Kuma Wani Irin Rudani Sosai.
Inna Indo ce Sun Kwana Lafiya Amma Sai Wayuwar Gari Sukayi Da Inna Indo ta Karba Kiran Mahallici(Rasuwa).

Bakadan Rasuwar Inna Indo ta Sanya su Al'ajabi ba, Duk-da Kuwa Cewa Itadin Mutuwar Wajibice Ga Kowa, Kuma Bata Sanarwa Balle Sallamar Gani Tafe, Kawae da Lokaci Yayi shikenan Kuma kamar dai Yadda Akace ne 'In Ajali Yayi Kira Tau ko Babu Ciwo A je." Haka Suka Shiga Zaman Makoki Na tsawon Kwana Ukku, Inda Inna Indo Tasamu Shaiadar Arziki Agurin Jama'a. Kowa ya budi Baki Alkairinta yake Fadi. Bayan Kare Zaman Makoki ne Kuma Aka Shiga Bincike Dame-Dame Inna Indo Tabari? Dawa-Dawa Ke biyarta Bashi?Da Waye take Biya Bashi Itama? Tau Dama Ita Inna Indo Diyarta Daya ce, Kuma Tana Aure A Garin Bernin Kebbi,Dan Haka Itace Jagoran Komai Sai Diyan Yanne Wanda Saudatu Aminiyar Innarmu Tana Cikinsu. Bayan dae komai Ya kammallah, Karshe Dae Sai Kitsawa Sukayi Kan Innarmu Taci Gaba da Zama Acikin Gidan Akan Sharadin Zata Biya Kudin Hayar Gida A Gurin Diyar Inna Indo. Innarmu Kuma Babu Tantama Ta'amince Kuma Anan Take Ta lissafe Kudinsu Kasa Tabasu. Dan Haka Yanzu Sai Gida Yadawo Gurin Innarmu Kadai Da Yan Yaranta Biyu. Daga Nan Sukayi Sallama Da Innarmu Kan Zasu Koma Gidajen Aurensu, Saudatu kadaice Ta Kara Kwana Biyu Bayan Sunyi Kama-Kama Wajen Shawarar Yadda Innarmu Zata Cigaba Da Zamanta Batareda Tanema Ta Rasa Ba, Shiyyasa ma Inda Inna Indo Ke Aiki Suka Je Akan Za'a Maye Gurbinta Da Innarmu. Aikinde Shine Wanke-wanke Da Kuma Yin Girki Wani Lokacin Da Wanki Da Sauran Yan Abubuwan da Kan Tusgo. Dan Sunce wa Gidan Ita Innarmu Diyar Inna Indo ce Mai Rasuwa. Dalili Da Yasa Suka Karbi Innarmu Kenan da Kuma Tayin Taci Gaba da Aikin da Ita Inna Indo Take. Dan Acewar Masu Gidan, Inna Indo Mutum ce Harda Rabi Kuma Sunyi Zama Da Ita Na Amana Tsawon Shekaru 20 Dan Haka Zuri'arta Abinso ce A Garesu.

Wannan Kenan

Bayan Dae Innarmu taraka Aminiyarta Saudatu wacce Bata Da kamarta Tasha, Sukayi Sallama Da yiwa Juna Fatar Alkairi. Innarmu Aka Dawo Aka Soma Fuskartar Sabuwar Rayuwa. Dafarko tadan Sha Wahla Sabo da Rashin Sabo Da Zamanta Ita Kadai A Gidan Da Kuma Gurin Aiki, Amma Da Aka Kwana Biyu Kuma Sai Ta Saba Tacigaba Da Aiki Tukuru Gefe Daya Tasamawa 'Yan Yaranta Makarantar Boko Da Isalamiyyah Suke Zuwa.
Kuma ko Da Yaushe Cikin Hidimtawa Take Dan Dae Karsu Nema Su Rasa. Cikin Haka Aunty Aisha Tadawo Nan Mahaifi Tunda Wannan Shine Haifuwarta ta Tafarko. Zuwan Aunty Aisha A Gidan Yakara Dadi Suka Rage Kewa. Ga Kuma Mijinta Nayo Musu Aike, Dan Haka Suci Mai Kyau Su Sha Mai Kyau. Nanne Dai Kuma Suma Yan Yaran Innarmu Suka Dukufa Aikin Hannu. Abdul-wahab Yake Fita Aikin kaniKanci Shikuma Abubakar Ke Zuwa koyon Dinki. Izuwa Yanzu Rayuwa Ga Innarmu Sai Hamdala Dama Kowa Yasa ALLAH Gaba Lamarinsa Bai Lalacewa. Yanzun Kam Itada Sanyinnah Sai Dai Taje Ziyarar Yan Uwa ko In Buki Yatashi Wanda Take Zuwa, Kuma tamusu Sha Tara ta Arziki Wanda Hakanma Yakara Tabbatarmusun Itadin Dae 'ALKAMAR SAMAN DUTSE CE ALLAH KE BATA RUWA BADA SON MAKIYA BA🤗' Dan Haka Wasu Daga Cikinsu Suka Aje makaman Yakin Su Suka Dawo Ake Harkar Arziki, Wasun Kuwa Suka ki Sallamawa A Cewar su Yanzun ne ma Aka Fara. Dan Su Aganinsu Bai Kamata Ace Tafisu Komai ba Mussamman ma in Suka Tuna Cewa Sudin Ma Masu Iyaye Da Kuma Mazaje Basu Samu Irin Rufin Asirinta ba. balle Innarmu marainiya Ta Bangare Iyaye da Miji?

*********

Tsakar Rana ne Sosai Ana Kuma Matukar Zafi In kaga Mutum Na Zufa (Gumi) Sai kace Ruwa ne Yakwarara Ajikinsa. Saurayine Kyakyawa Dashi Dan FULANI Sak Dashi. Naga Yana Ta Aikin Kwakwale-kwakwale Acikin Wata Kk Napep (Nufin Dae Yana Gyaranta ne) Yana Cikin Aikin su Naji Wani Mutum Na kwala Masa Kira Wanda nake kyautata Zaton Ogansu ne. "Abdul-wahab Ka Gama Gyara ma Matar can Motar ta Wai? Tunfa Daxu Nake Ganinta Nan Zaune?" Abdul-wahab Yace, "Oga ban kammallah ba Na'aika Asiyo Wasu Kayane Daza'a Samata A Motar, Kuma Haryanzun Dan Aiken Bai Dawo ba." Oga Yace, "Waye Ka Aika Halan?" "Samuel." "Samuel?" Oga Yamaimaita Sunan Cikin Takaici Kafin Yadora Da Cewa, "Kaima Ai kasan Abinda Kayi, Samuel Ai Ni in Ina sauri Bana Aikinsa Dan Nasan Halin Shiriri tarsa. Kaga?" Abdul-wahab Yadago Yana kallonsa Dan Jin Mai Zaice Masan "Kawo In Karasa Gyara ma Wannan Napep Danshi, Je kabi Sawun Samuel Kazo Kayi Hanzari Ka Gyara Wannan Matar Motarta Lokaci Yana Tafiya Kuma kaga Kila Sai ta Koma Zata Tanadi Abin Budin Baki."
Hajiyar Tasako Bakinta Cikin Zancen Nasu Da Cewa, "ALLAH ma Albarka, Mutumin Nan Kamar kasani. Ina Zaune zullumin Danake Kenan. Mai min Aiki Kwana Biyu Tana Gida Jinyar Mahaifiyar ta Take." Oga Sunday Yace, "Tau in ba Damuwa Zaki iya Samun Abun Hawa kije Gida, saiki Bamu Address Dinki Shi Abdul-wahab Din in Ya Gama Gyara Zai Kai Miki Gida."

"Aikuwa, Hakan Yayi." Hajiyar Tafadi Hakan Tana Mai Kokarin lalubo key din Motar Acikin Jakarta.

Kafin Ta dago Kanta Tana Mai Mikawa Abdul-wahab key din Tareda Sanar Dashi Adreshinta. Daganan Kuma suka Tare Mata Mai kk Napep. Yayinda Shikuwa Abdul-wahab Yatafi lalubo Samueil. Gabda Shan Ruwa Yagama Gyara Motar Dan Haka Dole yabiya yakarbi Kayan fruit (lemu dasu ayaba) Da Yasaba Siya Masu Akullum Kafin Yanufi Gida. baishiga Gidan ba Yaro Yabawa Cewa Yakaima Innarmu Zaije Yadawo." Su Innarmu da Abubakar Suna Tsakar Gida Saman Tabarmar Da Innarmu ta Saba jere Musu Kayan budin Baki, Sanda Yaron Yakawo Sakon Yana Sanar Dasu Yanda Abdul-wahab Din Yace. Sae Suke Mamakin Hakan, Dan Sun Saba Duk Runtsi Gida Suke Shan Ruwa A Tareda Innarmu.
Dan Haka Ran Innarmu A Bace Tamikowa Abubakar Yar Wayarta Tana Cewa "Nemomin lambarshi inji Dalilin shi nakin Zuwa Gidan."


"Bari wayarki Innarmu Ina da Katy Cikin Tawa Wayar Bari inkirashi inji."
Abubakar ne ke Wannan Maganar Yana Kokarin Fitarda Wayarsa dake Cikin Aljuhunsa.


Kara day, Biyu, Ana Uku Aka Daga Wayar "Ya Abdul ......" "Dan ALLAH Karka Cika Ni da Surutu Oga Yasani maida Motar da na Gyara Gashi ma Na kawo wa Mai Motar Zan Dawo Yanzu."
Abubakar yakashe Wayarsa Yana Dan Karamin Tsaki Gamida Cewa, "Kajimin Ya Abdul Sai kace Nima Bana Jin Kishirunwa azuminan ko Ni Nasa Shi yin Azumi..." Innarmu Na tsura Masa ido Tace, "Meyace maka halan? Ai Shiyyasa Nace maka Ka kiramin Shi A Wayata."

"A'a Innarmu Bafa komai bane ba, Yace Motar da ya Gyara A Gurin Aikinsu ne Ogansu Yace ya mayarwa da Mai ita Kuma Yanzun Zai Dawo."

"ALLAH maidashi Lafiya." Innarmu Tafadi Hakan Kuma Ga Alama dae Bata ji Dadin Hakan ba. Kafin Tamike Tana Cewa, "Tashi Kayi Arwallah."

Tare Sukayo Arwallah Kafin Suka Zo Suka Fara Budin Baki. Ba Abdul-wahab Nan, Dan Haka Sai Sukaji Duk Abin Ba Dadi. Akwai Shakuwa Sosai A Cikin Iyalan Innarmu. Bayan Sunyo Sallar Magariba Suka Dawo Dan Cigaba da Budin Baki, Sai ga Abdul-wahab Din Yashigo Kaitsaye Kuma yararumi Kofin Da Abubakar Yacika Kunun tsamiya Dashi Dan yasha. Abubakar Yayi Saurin Fisge Kofin Yana Mai Matsawa Kusa da Innarmu Yace, "Kaji Ka dae Yaya Abdul Nima Fa Yunwar Nakeji." Abdul-wahab Yasake Yun kurowa Da Nufin Zai Amshi Kofin Innarmu Tashiga Zancen Nasu Da Cewa, "Wai KU meyasa bakwa Girma ne? Bazaka Dau Naka Cup din kadibi Wani Kunun ba Dole Sai Nashi?"

"Innarmu Nashi Yahuce. Wanga(Wannan) Kuma da Zan Diba Yana da Zafi ne Shiyyasa Fa." Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Wani zunbura Baki Kamar Dan Yaron Goye.

"Tau Amshi Bari Nazuba Wani." Innarmu Tamika Masa Nata Abubakar Yayi wuf Zai Amshe Yana Cewa, "Innarmu Wallahi Bazaki Bashi ba. Aikema Zubawa kikiyi kika Jira Yahuce Shima Yazuba." Abdul-wahab Yafisge Kofin Yana Kaiwa Bakinsa Yasha Yayi Masa Gwalo Yace, "Dan Ciki Baki (Bakinciki) Kawai." Itadai Innarmu Bata ce Komai ba Sai ma Tanemi Yuka Tana Yanka Kayan Fruit dinda Abdul-wahab Yasiyo Bayan ta wankesu. "Wayyo! Innarmu!" Tajuyo Afirgice, kafin Tai Magana Abubakar Yace, "Ya Abdul ne Ya Mitsile Mun Hannu Dan Zan Dau Dankalin Da ke Gabansa."

"ALLAH yashiryaku." Abinda Innarmu Tace Kenan. Tau Haka dai Suka Gama Budin Bakin Sai Hayaniya Suke Mata. Dama Haka Suka Saba, Shiyyasa Daxun Da Abdul-wahab Din Bai Nan Sai suka Ji Ba Dadi.
Haka Suka Kammallah Cikin Farinciki Kafin Suka Mike Abdul-wahab Yadauki Darduma Shida Innarmu Zasuje Masallaci Sallar Asham (Tarawihi) Shikuwa Abubakar Tela Dole Gurin Dunki Aka Nufa Dan Karkare Dunkunan Mutane Da Aka Amsa. Daza Su Rabu Har Abdul-wahab na Zolayarsa Cewar, "ALLAH Yasa Yaro yaki Gama Dunkunan Mutane Yasha Waju (Duka)Wurinsu." Abubakar ya Zunbura Baki, "Kina Jinshi Ko Innarmu ba?" Innarmu Tace, "Rabu Dashi Dan Autana, Lafiya Lau Zaka Gama Dinkuna In Yazo Hada Lefe Karka Masa Dinki."
Abubakar Yabar ke Da Shewa! Kafin Yamasa Gwalo Yawuce Da Gudunsa. Yayinda Abdul-wahab Yace, "Zaka Dawo ne Ka sameni Ai." Innarmu Tace, "Nidae Wuce Muje Kanaji Har Antayar Da Salla."


Koda Yaushe Haka Innarmu Take Tareda"Yan Marayunta Da Ayanzun Suka Girma, Suka Zama Santala-Santalan Samari Kowa Kuma Yake Da Sana'ar Hannunsa Gefe Daya Suna Ci Gaba Da Karatunsu Inda Abdul-wahab Yake Karantar Aikin Lawyer A Jami'ar Usman Dan Fodiyo Shikuwa Abubakar Yana Karatun sa A Umar Ali Shinkafi polytechnic Dakenan Sokoto Inda Yake Karantar Computer seince. A Tare suka Rubuta Jamb Tau Amma Shi Abubakar Makin Nasa Bai Kai Yanda Jami'ar ke Bukata ba Dan Haka Sai Yashiga poly din Amma Yinin Ranar Yaci Kuka Sai da Su Innarmu Sukai ta Lallashinsa Kan Karbar Kaddara.

Tau Yanzu Karfinsu Yakawo, Dan Haka Komai Sun Daukewa Innarmu Sai Aikin ne Kawai Bata Bari ba, Dan Acewar ta Sun Saba Sosai Da mutanen Kuma Suna Girmama ta.
Azumi Yayi Nisa Sosai Kowa Kuma A Yanzun Shirin Sallah Yake Mussamman Bangaren Dinke-Dinke. Anshigo Goma Ta Wuya Inji Malam Bahaushe.
Danhaka Azumi Bugun (Dukan) Mutane Sosai. Yau Takasance Jumu'a Ce Ankuma Kwalla Rana Sosai Kamar Yadda Akan San Kowace Jumu'a Da Rana. Mutane Sai Sayen Pure water Ake Ana Zubawa A Jiki Yayinda Sauran Samari Suka Nabba'a Zuwa Tafki Suna Wuni Acikinsa. Abdul-wahab Yana Kasan Rumfar Wurin Aikinsu. Yau Basu Da Aiki Kwarai, Dan Haka Yayi Tunanin Bari Yakira Abokinsa Yusuf Mai Tukin Kk Napep Yazo Yadaukeshi Sufita Tare.

Dan Wani Lokacin Hakan Suke In Yana Nishadi Yakan Kira Yusuf Din Yazo Yadaukeshi Sufita Aikin Napep Din Tare. Haka Shima Yusuf Din Duk Sanda Yabada Kk Napep Din 'Taba' Ga Wani Sai Yazo Garejinsu Yazauna. Yauma Suna Tare Suna Aiki. Ana ta Kiraye-kirayen Sallah Magrib Sukayi Parking Gaban Wata Mata Dake Gefen Titi Tana Tuyar Kwasai Da Dankali Dakuma Doya Harma Da Plantain Gefe Daya Ga Kunun Koko. Wurin Duk Yan Kk Napep Ne Da Masu Mashin-Mashin Dakuma Dai-Daikun Mutane Da Suke Ta Hada-Hadar Budin Baki Gurinta. Suna Parking Gurin Yusuf Yayo Musu Odar Komai d Komai Amma Abdul-wahab Din Yakasa Cin Komai Saboda Shi Inba Abinda Innarmu Tadafa Ba Bayaci Wannan Abinda Suka Sabane Shi Da kanensa. Yusuf Yakallesa Yana Danna Bready Da kwasai Abakinsa Yana Mai Cewa, "Meye Kayi Wani Zaune? Kaci Mana" Abdul-wahab Yace, "Ni Gaskiya Muyi Sauri Kawai Ka Kaini Gida inba Abincin Innarmu ba baxan ci ba." Yusuf Ya kallasa Yana Dariyar Nan Ta Shaidanun Abokai Yace, "Tau Yayi Dan Innarmu."

Bayan Yaci Dabino Sai Yadauki Ruwan pure water Yasha. Dayan Pure Water kuwa Yafashe Yasoma Arwallah. Kamar Wacce Aka Jefo Yaganta Agabansa. Farace Tas! Kuma Tana Da Wushirya Tsakiyar Haurunta Na Gaba Gata Yar Madaidaiciya A Tsawo Baza'a Ce Mata Mai Tsawo ba Kuma Baza'a Ce Mata Gajeruwa Ba. Sai Dan Dumulmulallen Jiki Da Take Dashi (Yar Duma-duma 😀) Sanye Take Doguwar Riga Mai Matukar Laushi Ga Dan Karamin Hijab Da Mata ke Cewa Hapsunnah Ta Yane Jikinta Dashi Wanda Iyakarsa Bisa Kafadunta. Duk Acikin Abinda Bai Gaza Minti Biyar ba Abdul-wahab Yafahimci Hakan.

Rike Take Da Flet Mai Dauke Da Soyyayar Doya Da Kuma plantain Gefe Daya Ga yaji, Sai Kuma Lemun kwali Mai Sanyi Da Take Rike Dashi Tace, "Bansan Meyasa Ba Tun Daxun Nakasa Sukuni Kan Naga Baka ci Komai ba. Shine Nace Bari Nayi maka Wannan Hidimar Ko Da ko Zaka Gwasalani ne."

"Mexai Sa In Gwasalaki Bayan Karamci Kika min? Wanna Ba Halin Mutane Kirki Bane Dan Haka Nagode Kwarai da Wannan karamci Sosai."

"Tau Ka Karba Kaci Abinda Nakawo Ma please?" Tafadi Hakan Da Wani Salon Rokonsa Kamar Inya ci Cikinta Zaiyiwa Aiki. Abdul-wahab yagirgiza Kai, "Kiyi Hakuri Ni Inba Innarmu ce Tayi Girki Banaci." Tabude Baki Da Nufin Yin Magana Mamarta Ta Kwalla Mata Kira Tana Ta Fada, Cikin Yarensu Da Abdul-wahab Bai San Wane Iri Bane Sai Dai komeye Take Cewa Baya Rasa Nasaba Da Tana Mata Fada Akan Tabarta Da Ayyuka Costumers Sun Mata Yawa Tazo Ta Sallami Wasun.

Abdul-wahab Yace, "Kingani Ba, Yakamata Ki Koma Kan Aikinki."

"Ba Zan Koma ba Kuma Bazanji Dadi ba Indae ba Karba Kayi ba." "Ai Nagaya Maki Tsarina, Inkuma Baki ji Da Kyau Bane Bari In Sake Gayamaki. 'Ni Bancin Girkin Da Ba Innarmu Bace Tayi Shi ba." Tadade Tana Kallonsa Kamar Baxatayi Magana Ba Kafin Ta Sauke Ajiyar Zuciya, "Tau Shikenan, Yanzu Bari Nasama A Leda Ka Kaima Innarmu Din injini." Yayi maza Ya Girgiza Kansa "A'a Gaskiya Tau A Wace Dankatar Zan Kai Mata Abu Ince Gashi?"

"Bisa Ga Dangatar Musulunci Ko Itadin Ma Zaka Kawar Da Ita ne?"

Yagaji Da Surutu Dan Yana ma Mamakin Yanda Suka Dade Suna Magana. Dan Haka Sai Yace Mata Takawo Zai Kai. Kafin Yamike Yanufi Masallaci dake Kusa da Gurin Dan Yin Sallah. Dama Shi Yusuf Tuni Suna Massalacin. Bayan Sunfito Sun Shiga Kk Napep Zasu Wuce Sai Gata Tana Miko Masa Ledar Tareda Wayarsa Tace "Niyyar Ka Katsere Ko? Tau Da Kayima Kanka Dan Dazu Kana Arwallah Ka Tafi Kamanta Da Ita." Batareda Yace, Komai ba Yamika Hannu Yakarbi Wayar Da Ledar

A Ransa Sai Mamakin Yake Lalle Da Yatafi Da Yayiwa Kansa. Shikuwa Yusuf Harda Turo Kansa A waje Yana Mata Godiya Ita Kuwa Cewa Take "Ina Gaida Innarmu." Yusuf Yace, "Zataji." Kafin Suka Soma Tafiya Sai Shakiyanci Yake Yiwa Abdul-wahab Yana Kwasar Dariya.

"Mutumin Kayi Kasuwa Fa? Lalle Wannan yarinyar Taciri Tuta Cikin lokaci Kankani Har Ka Gayamata Su Innarmu?" Shidai Abdul-wahab Shiru Yayi Masa, Burinsa Su Isa Gida Yaci Girkin Innarmu.

Da Asuba Suna Suhur Sai Ga Kira Da Bakuwar Number Bayan Sallama Take Tambayarshi "Ina Innarmu Ka Kaima Mata Sakon Da na Baka?" Sai da Yacire Wayar A Kunnesa Yaduba Da mugun Mamakin Ina Ta Samu Number Kafin Yasake Maida Wayar A Kunnesa Da Nufin Tambayar ta "Ina Kika Samu Number Na?" Sai tarigashi Cewa "Karka Tambayeni Ina Nasamu Number ka, Ni Da Kaina Zanbaka Wannan Amsar Yanzun Ka'amsa min Waccan Tamabayar Dana ma." Jikin Abdul-wahab Yayi Sanyi Da Yanda Yagu Su Innarmu da Abubakar SunTsura Masa Ido Sai Yakasha Shan Kunun Da Ke Hannun Sa Yabuge Girgiza Cupin Kawae.

"Ya Kayi Shiru? Katyna Fa Ke Tafiya." Dagacan Tace Masa Haka.

"Ina Wani Uxurine Yanzun, Zamuyi Waya Anjima." Da Fadin Haka Da kashe Wayarsa Duk Lokaci Daya Yayi su.

Yadauki Cupin Kunun Yasoma Sha A Hankali "Idan Bakayi Hanzariba Za'a Kira Assalatu Bakaci Komai ba." Yadago Yana Kallon Innarmu Dan Ya tantace Da Wane Kalar Yanayi Tayi Masa Magana.....Sai Kuma Jikinsa Yadauki Makarkata.


Nima Jikin Nawa Makarkata Yadauka Wayar Tagagareni Riko Saboda Nima nashiga makamancin Rudanin Da Abdul-wahab Yake Ciki. Dan Haka Zan Dan Nissa Anan.........
Muje Zuwa Raedars Nawa Shin Meye Yake A Rufe Wanda Bamu Sani ba? Kuma Meye Na Wannan Fargabar Da Abdul-wahab Keyi? Mutara Daku A page Na Gaba.
[9/5, 9:13 PM] FA'IK: 💞💞 SONEEE....💕💕


(Silar Komai.)
Chapter 1 · 0% Book details