← Book details Na Faɗo Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 43

Sashe 15

Na Faɗo Daga Bene Na Zarce Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ungo wadannan ledojin kayan miya da kayan lambu ne a ciki, wannan kuma kaji ne an fige an yanka ma.

Gobe sassafe sai ku tashi da aikin
an jere zasu tawo daga Zaria kuma fitowar safe zasu yi." Ledojin na kar
a a hannunta, sauran suna
asa.

Kayan ruwa da lemun kuma Amadudu ya shiga dashi
akinshi.
aki na kai kayan sai da nayi har sallar isha sannan na aika Shafi'i kitchen ya
auko mun bahun
arami.

Kajin na juye sai da suka cika madaidaicin bahun dam.

Haka na kinkima da
yar zuwa tsakar gida na shiga aikin gyaran kaji nan.

Mustapha yayi sallama ya tafi da su Sulaiman Hauwa kawai suka bar mun.

Ina wanke kajinnan marata na karta mun.

Gawayi na ha
a na
aura tafashen kajinnan a
atuwar tukunya dan kajin sun yi guda takwas masu abun ne to da abunsu kura da kallabin kitse.

A kan kujerar tsugunno Kaila ya shigo ya same ni, ni ni ka
ai a tsakar gidan gashi ba wuta, sai hasken waya na kunna.

Sannu da zuwan da nayi mishi ma da
yar ya amsa ni, yayi shigewarshi
akin
ar gwal.

Sai goman dare na sauke tafashe na tafi dashi
aki, ko lomar tuwo ban kai bakina ba.

Haka na kwana ina ciwon mara, washe gari kuma na shiga hidimar aikin
an jere, Hindatu da Hajiyayye babu wanda yayi yin
urin taya ni.

Tun sassafe na kira Anty Use da Anty Karime a waya na sanar musu da batun abincin jeren, sun ce zasu zo da safen su taya ni aikin.

Kuma na aika ma Sabira.

Zuwa
arfe taran safe duk suka hallara, har mun soma tuyan kaji, Sabira kuma tana zaune tana gyaran kayan lambu.

Ganin su Yaya Use ne yasa Hindatu zuwa ta kama mana aikin.

Kayan miya ta gyara yara suka tafi kai ni
a, ni kuma ina gefe ina
arar maggi ina cije le
e na ciwo.

"Tani ki je ki tambayo Rammai me za'a girka ma ba
in kinga na gama da suyar naman." To kawai nace, na yi sallama a
akin Hindatu Baba Rammai na can.

Bayan mun gaisa nake tambayarta mai za'a girka"
"Wannan ai ya rage naki Tani.

Komai na hannunki du abunda kuka san zai burge ba
in sai kuyi.

Dan Allah ayi abinci mai da
i dai ga kaji nan wadatattu mutanennan masu arziki ne sosai, a kamanta musu."
To shikenan Baba Rammai"
Fitowa nayi na same su.

To tace mu yi koma meye, ya kuke gani me za'a girka?" Yaya Use tace.

"To ni dai ban san kalolin abincin zamani ba, ban iya ba ko ba gaskiya ba, nafi
warewa a abincin gargajiya." Yaya Karime tace.

"Nima dai wallahi ko jallof
in taliya ban iya girkata ba, in nayi duk sai ta ra
e a cikin romon" Sabira tace.

"Babu damuwa ni na iya, sai ku taya ni muyi.

Party jallof rice za mu yi, da pepper chicken, sai ayi musu coslow tunda akwai kayan lambu da yawa" To da taimakon Sabira data kasance kan gama komai muka kammala girke_girken mu.

Ni dai bani da manyan kuloli na zamani, Hajiyayye nayi_nayi da'ita ta ba da nata a zuba abincin ta
i, daga
arshe da Baba Rammai tasa baki sai kawai ta fashe da kuka ta kuma rantse ba zata bayar ba.

Sai Sabira ce ta je gidanta ta
akko mana manyan kuloli na Alfarma, tsabar
yalli ras nake ganin fuskata a kular nan.

Bayan mun kammala komai Baba Rammai tace a kai
akin Hindatu a ajjiye abincin.

Yaya Use ce ta shigar da komai, a tsakar gidan suka zauna suna cin nasu abincin.

Ni kuma na shiga wanka, ina fitowa na shiga
aki na saka riga da zani na atampa wanda Habiba Bala ta bani.

Babu abinda na shafa a fuskata.

Dirin motoci da ihun yara na jiyo a dai_dai window na suna fa
"Kayan amarya ek_ek" Sai naji zuchiyata na son le
awa in ga wa
anne irine matan da suka tawo jeren.

Ai kuwa da sauri na matsa bakin windon na le
a.

Wasu manyan mata
osassun
an boko na gani a tsaye a bakin motar kaya, sai turanci suke yi a tsakaninsu da juna.

Kaila na hango cikin girmamawa ya isa garesu, sai
an guntun turanci suke yi mai, shi kuma yana zare idanu gudun kar su kai shi ma
ura, dan
an turanci nashi bai wuce cikin cokali ba, shima ya iyane a sanadiyyar zaman shagon wani inyamuri a bayan banki, shagon takalma da jakunkuna.

Kamar akan gidan suke yi mishi magana dai, dan naga suna kallon gidan suna yamutse fuska, ajjiyar zuchiya na sauke na bar windon.

Su Yaya Use ne da Sabira suka shigo, a tsaye suka ganni da wannan riga da zani na atampa, rigar tayi mun yawa har wuyan na zamewa.

"Ba
in ku sun iso Tani, ni naji sai turanci suke ta zazzagawa a waje." Kafin in kai da magana muka jiyo sallamarsu da wasu muryoyi masu da
i, daga
angarena Yaya Use ce ta amsa musu.

Suka
arasa zuwa cikin gidan Baba Rammai da Hindatu suka tarbesu.

Daga haka muka soma jiyo muryoyin maza da shige da ficensu.

Yaya Use ce ta fita, ni ko waje na samu na zauna ina fama da marurun zuchiyata.

Bata jima ba sai gata ta shigo.

"Tabb lallai Kaila ya
ebo matar da tafi
arfinshi gaba da baya.

Yarinyarnan da zai aura daga gani
ar masu dashi ne.

Kunga kaya irin na gani da fa
e kuwa.

Hmmm daga kamfanin da aka sai kayan ma aka tawo da ma'aikata maza su suke gyara
akin.

Ji nayi wata Baturiya tana fa
ama Rammai." Baki ni dai na ta
e abina.

Baba Rammai ce ta
aga labulen
akina tace.

"Ai ya kamata ace kin zo kin tarbi ba
i ko Tani?

Sannan ki basu abincinsu sun shawo hanya" Da To na bita tare da yun
urawa na tashi tsaye.

"Muje in taimaka miki ke da ba ishasshiyar lafiya ba" Harara Baba Rammai ta sakar ma Sabira, taja tsaki ta saki labulen tayi gaba abunta.

A
akin Hindatu aka sau
i ba
in, Hajiyayye tace dangin kishiya basu isa sun zauna a
akinta ba.

Tun muna aikin abinci tayi ficewarta daga gidan, amman ba zata wuce ma
ota ba gidan
awayenta.

Da sallama muka shiga cikin abun mamaki a cikin ba
in babu wacce ta amsa sallamarmu sai Yes kawai suka ce mana.

Dauriya na aro na yafa na zauna aka gaggaisa, Baba Rammai ta nuna ni da cewa.

"Hajiya kinga wannan itace uwar gidan Kaila.

Amman bazawarace ya aureta." Naji zafi sosai, ba
in a wula
ance suka shiga bina da kallo, ni ko murmushi nake yi, abinci muka gabatar musu da abun sha, kana muka fice a lokacin idanuna ya cika tab da ruwan hawaye.

Sai zuwa yamma lis suka gama abinda ya kawo su, su kai mana sallama.

Sai magriba su Yaya Use suka tafi bayan sun yi mun girki suma sunci, Sabira kuma ta
an jima da tafiya itama zata je ta kula da nata iyalan.

Da su Sulaiman ta sake tafiya.

Ina zaune muna cin abinci ni da Hauwa nake jiyo hayaniyar Kaila da Hajiyayye a tsakar gida, wannan karon hayaniyar tayi tsamari, dan ina jiyo yanda Kaila ke kutuntumama Hajiyayye ashariya, dama Kaila gwanine wajan rashin daraja, akwai shi da ruwan ashariya.

Da
yar dai fitinar ta lafa ni ko ina
aki a kwance abuna ban ko leko ba
ofata ma rufe take na saka sakata.

Haka ranaku su kai ta shu
ewa ana saura kwana uku biki, gida ya cika da
an Wudil dangin mahaifin Kaila, da
an Akwanga dangin Baba Rammai.
annen
anin Mahaifin Kaila ne kacal suka sauka a
akina, yara kuma suna gidan Sabira acan suke kwana.

Aikin girki kuwa nice gaba_gaba taimakamun kawai jama'ar bikin ke yi, amman in ban
aura sanwa ba babu wanda zai fito ya
aura.

Ana jibi
aurin aure aka tashi mutum hu
u biyu daga
arayin Baba Rammai , biyun kuma
an Wudil ne domun kai akwatin Amarya wanda dama ita yaba ku
in ta sai komai domin irin yanda take ba gaye hakkinshi.

Sassafe suka kama hanya domun a ranar suke son dawowa, basu suka shigo gida ba sai taran dare.

Washe gari aka shiga hidimar biki gadan_gadan wanda a ranar Kaila da mutanenshi suka nufi Zaria acan zasu kwana in an
aura aure su tawo da Amarya da danginta.

Ranar juma'a gida ya cika da ma
ota
an uwa da abokan arziki duk sun hallara, Yaya Use da Yaya Karime tun taran safe.

Mu mu kai ruwa mu kai tsaki a girkin
an biki.

Tuwon shinkafa miyar taushe mu ka yi, sai jallof
in shinkafa da kaji da akai ma masu kawo amarya da abokan ango.

Saye nake cikin wani lashi
inkin doguwar riga, yana daga cikin kayan da Habiba Bala ta bani, babu ko kwalli a idona balle in shafa mai.

Yara kuma nasa musu kayan sallansu, abunka da yara sai murna da
iriniya suke ana biki a gidansu.

Hajiyayye ma
akinta cike dam da
an uwanta da
awayenta na anguwa.

Taci ado kamar itace Amaryar,
awayenta sai ko
ata suke faman yi, an yi saloon, an yi
unshi, duk da na sallah da tayi bai gama fita ba amman akai akayi mata, har me kwalliya
awayenta suka
akko mata.

Misalin
arfe shida da rabi na yamma motocin kawo Amarya suka soma tsayuwa a dai dai bakin windo na.

Cikin
an mintuna yiriri_yiriri ya shiga tashi a kofar gidan.

A wannan lokacin ina kwance ina hutawa ne, su Yaya Use kuma suna cikin gida suna rabon tuwon dare.

Tuwon masara miyar bushasshiyar ku
ewa su ka yi.

Ina jiyo takun dangin Amarya, a kunnena najiyo wata
ar tsohuwa tana fa
in ki shiga
akin ki da
afar dama, ki yi adda'a kamar yadda muka shigo dake gidannan Allah yasa sai dai a fitar da gawarki.

Murmushi kawai nayi ina dafe da cikina dake mun juyin waina.

Bayan hayaniyar mata ta lafa ne na soma jiyo hayaniyar Kaila da abokanshi.

Ina jiyo sallamarshi Amman bakina yayi nauyi na kasa amsawa sam.
Chapter 15 · 0% Book details