Sashe 8
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka tashe ni bye." "Hmmm ka dai kore ni toh Allah ya baka mata a kauyan daka baro tun da baka son muyi iri d'aya." "Wallahi ba amin ba, duk basu da hankali musamman ma INdo kai! wannan yarinya ba hauka ne yake damunta ba harda jahilci kasan shi yafi hauka. Gasu k'azamai tunda naje garin banga wayayye ko wayyayi ya ba wallahi, ba amin ba dan kamar yadda kake son nutsattsiyar mata haka nima nake so kuma 'yar gayu mai ilimin zamani da na addini.." "Twinnie kad'auki zafi da yawa so sorry dan Allah, bari naje na dawo bye.." "Ok sai ka dawo." Da haka suka rabu sai da Abubakar ya shiga cikin gidan yayi sallama dasu Maman sa sannan ya fita, yayin da Sadeeq ya kwanta duk da cewar maganar da d'an uwan nasa ya fad'a tasa baccin ya gudu sabida takaici hakan yasa ya tuno da INdo yaja tsaki tare da mik'ewa ya koma cikin gida ko zaiji dad'in ranshi a gurin su Maman su. *IHSAN MEDICAL CENTER* Ahankali yake karasawa asibitin na ihsan medical center dake unguwar sultan road nassarawa gra agarin na kano,sanye yake cikin kananun kaya kirar suit blue tacikin kuma fara ce hannunsa rike da jakar laptop d insa fuskarsa sakale da farin glass se bulbula kamshi yake haka yashiga harabar asibitin,yana shiga ya hango nurse hidaya k arin juyawa yake ta cinmashi da sauri, Welkm Doctor,Ina kwana..?! Fine Alhamdulillah nurse hidaya.. Yana gama fada yai gaba ya barta wajen Office d insa ya nufa inda sunansa ke rubuce boldly ajikin k ofar office din Dr Abubakhr kamar kullum Mani Cleaner ne aciki yana tsaftace office din se mopping terrazzo din yake dake ta shekin kyalli,da sauri Mani ya tsugunna yana kwasar gaisuwa Sannu da xuwa yallabai Barka da safiya Barka dai Mani. Kan kujera dr abubkhr ya xauna yana dudduba files din kan tebur din one by one,har Mani yakarasa ya feshe office din da freshener, Yallabai na kammala Yawwa Mani godia nake xaka iya tafiya Har Mani yakai kofa yadawo yana sosa keya, Yallabai anbani sako wajenka amma wallahi na sha afa da sunan,nurse dinnan ce de da tai transfer daga Cotonou Sarai abubkhr ya gano wacece naccaciyar yarinyar data nace masa ce, To Mani ba damuwa tunda kamanta sunan kaje kawai Shiru Mani yai da alama ya zurfafa tunani be jima ba ya dago yana murmushi, Yallabai natuno nurse natasha ce da sassafe xuwana kenan tabani sako nabaka nikuma hartamin alkhairin Naira dubu yallabai Toh madallah cewar Abubkhr tareda shan kunu Kyakkyawar farar takarda datasha xanen heart Mani ya ajiye akan tebur se faman sosa keya yake don wannan bashine karo na farko ba da nurses suka sabayiwa ogan nasa haka,cikin dakakkiyar murya Abubkhr yace Jeka Mani sena neme ka.. To Yallabai Nagode ahuta lapia.. Mani nafita abubkhr yaja tsaki ko duban takardr beyiba ya mike don yin round na patients fitarsa kenan suka kusan yin gware da nurse Deexah uniform dinnan sun matse koina na jikinta ya bayyana se wani rausaya take tana karkada jiki, Dr..Pls tace hakan cikin wata irin siga Please what ?!inada patients daxan duba pls.. yakarasa hade da kaucewa ta gefanta xe wuce tai hanxarin shan gabansa bayan tahada tafukan hannayenta biyu sama alamar roko, Dan Allah dr ka saurareni minti d aya pls Allah data ambata yasanya shi tsayawa ba tare daya karasa tafiya ba amma bejiyo ba fuskarsa kan agogon dake daure a hannunsa yana jiran minti dayan ta cika, Ki magana kafin minti dayan ki tacika pls Dr Meyasa kake mun haka? Kaso me sonka,ka agaxawa xuciyata kaceto ta daga fadawa kogin halaka,duk asibitin nan babu wanda na xaba amatsayin wanda zuciata take muradi sekai Karasa maganar ta yayi dede da cikar minti dayan data ambata don haka yai gaba abinsa yashiga bin round na patients sedaya kammala tsaf sannan yashiga office din abokinsa wato dr luqman, Sundan taba hira sunayi suna tafawa sannan luqman yashigo da wata hirar, Nikwa Abokina nagaji da kawo korarrafin da ake kawomun akanka wlhy,yanxunnan nurse deexah tafita hawaye kwance shabe shabe kan fuskarta dukde akan ka,dama yanxun nake maganar koba ka shigo ba xanxo na sameka don nikam nagaji Murmushin takaici Abubkhr yayi cikin nutsuwa yace, Toh Aboki bani shawara shin mexanyi akai? Ni Ina ganin kaxabi d aya kawai ka aura kaga ai dole sauran su kyale ka ko?! Ajiyar zuciya Abubakhr yai kafin yace, Gaskia Aboki kabani mamaki wallahi domin bantaba saka a sahun mutanen daxasu bani shawarar naxabi d aya daga cikin nurses dinnan na aura ba,karka manta duk wani namiji yana sone ya auro yarinya yar mutunci me dattako da sanin yakamata wadda yayan daxata haifa ma xasuyi alfahari da kasancewarta uwa tagari, To axahirin gaskia de magana d aya ce xanyi wallahi duk cikin nurses dinnan babu wadda xan iya xaba a matsayin wacce xan dauka nakai ta gidana wai amatsayin matata ta aure,Kowa Allah ya hadashi da rabonsa kawai ko ya kagani?! Shiru dr luqman yai yana cin faratansa da alama yarasa tacewa,knocking akai a kofa har sau uku hakan yasanya abubkhr bada izinin shigowa bayan yace, Yess Shigowa tai sanye cikin abaya baka bakinta dauke da sallama hannuwanta rike da files cikin siririyar muryarta kamar anbusa sarewa tace, Gashi Doctor,duk nagama komai har room 13 dakace nayi mata inducing ruwan.. Okay nurse Mareeyah thank you..Xaki iya tafiya Dama abinda Mareeya ke jira kenan tai hanxarin ficewa abinta,baki galala abubkhr yabude yanabin k'ofar data rufe da kallo kafin yadawo da kallonsa kan Doctor luqman cikin sauri yace, Dr ai naxatan nurses d'innan sun gama aikinsu sun koma ya kuma Naga wannan?! Oh mareeyah riketa mukai wallahi yarinyar ta iya aikinta ga hankali da nutsuwa wallahi ba ruwanta da shiga harkar mutane kullum ita kad ai xakaga tana aikinta Mareeyah.. Dr abubkhr ya maimata sunan Kwarai sunanta mareeyah..A a kode kafada a da... ai luqman ne k arasa ba abubkhar yai hanxarin ficewa Cikin sa a ya hangota tsaye a corridor tana shimfida sallaya xatai sallah, Salam alykm.. cewar Abubkhr daga bayanta.. Wa alykm Salam tabashi amsa tana k arin gyara mayafin data yafa Ya salam,,abubkhr yafurta azuciyarsa Dakyar da lalubo salati yasamu ya saisaita kansa kamar bashi ba yace, Dama uhm..Idan baxaki damu ba magana nakeso nayi dake Babu damuwa amma xanyi sallah de tukun.. Tohm shikenan take ur time xanjira cewar abubkhr Ya jima azaune sedata idar tai addu ointa tukun sannan ta nannade praying mat dinta ta mayar cikin jaka, Ina jinka dr.. Okay.. Sunana Dr Abubkhr.. Allah sarki..Ni sunana mareeyatul qibdiyya. Nice name qibdiyyah, Nande abubkhr yashiga gaya mata meke tafe dashi da abunda ke cikin zuciyarsa,itade mareeyah kawai kallonsa take tana mamakin dama yana magana haka?!Abubkhr be bar maareryah ba har seda ya tabbatar ya dana mata tarkon son sa tukun sannan sukai exchanging numbers zuciyarsa fes yakoma gidah, Kullum de abinda ke faruwa kenan abubkhr har gidah yake xuwa xance wajen mareeyah ashema basuda nisa su su abubkhr suna unguwar Court Road ita kuma Mareeyah tana Hausawa,Sosai suke gwangwaje soyayya abun su shikuwa sadeeq har yanzu be samu wadda ta kwanta masa ba duk ya gwada amma babu sa a ga cuku cukun transfer dayake nema amma yakasa samu haka ya hak ura yafara shirin komawa makarantar tsefawa dake kauyen Sani a k aramar hukumar sumaila.. **** Ranar asabar da safe sadeeq yatasamma titin sumaila bayan yasha adduoi daga mahaifansa da kuma dan uwansa abubkhr wanda sam be so komawar d'an uwan nasa kauyan kayayau d'inba, Yana shiga cikin unguwar kuka sunan unguwar tasu kenan ya fara jiyo hayaniya sama sama be tabbatar da muryar ba seda yaxo daf da dandaxon jama ar da suka taru suna kallon fadan da ake ta muryarta yagane kowacece siririn tsaki yasaki jin muryar INdo ce dan turmutsawa taron yai ya hangota sanye cikin kodadd'un kayanta se jurwayen fitsari riga daban xani daban d"ankwali kuwa ba'a xancensa se tumurmusar fad'a suke da wasu yara maza kuma duk itace me karfin ciki,wani daga cikin taron ne yace Ke y ar nan kome sukai miki ki hak ura ki kyalesu tunda ke macace dan allah Cikin turo baki had'e da k'ank"ace idanuwa tana girgixa kugunta data d'aure da shamilallan hijabinta tace, Ta kwarankwasa baxan hakura ba,Babban bala'in can,se in xauna gani sokuwa sumin lefin sannan na hakura wallahi babu xancen hak uri a dishenari(dictionary)na ramuwa ta da ta taxama dole.. Tana gama fada tacigaba da kokawar da take yu cikin xafin nama sadeeq ya k'arasa cikin su ya wanke mata fuska da mari hade da hankadata gefe yatsan sa yasa yashiga nuna ta, Ke wai wacce irin kidahuma ce ne eh?! Kina mace kike fad'a? fad'anma da maxa dandaxon mutane akanki ko kunya bakya ji? Tukun nama me akai miki da kika kamasu kina duka kaman wata tinkiya.. Rike baki Indo tai tana kada Kai Kai ka Kai Kai Kai wacece tinkiyar?! Kece tinkiyar To wallahi ka bude kunnuwanka kaji niba tinkiya bace kuma kwarankwatsa ka kara cemin tinkiya seka gani. Haba nifa kana shiga rayuwata da yawa makaranta ce de nace ni INdo Malam hamxa nadena xuwa tsefawa inifam d'ina ma na yadashi amma saboda tsabar shisshigi da neman sani seka tsoma wannnan bakin naka a xancen da ba naka ba Tana gama fada ta shuri bokitan su ubale da idi na talla da suke fad'a tai gaba dasu tana sharara uban gudu,ganin haka yasanya su ubale binta a d'ari suna rokonta da tabasu bokintan tallansu da ta kwashe, Karkad'a kai kawai sadeeq yai wani b'angare na zuciyarsa na tabbatar masa da lallai yarinyar nan ba aljanu bane kad ai da ita Lallai babu shakku aciki kwakwalwarta ta tabu, da haka ya k'arasa gidansa yashiga bakinsa d'auke da sallama tamkar da mutane a ciki. *HAJJA CE* [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...