← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 53

Sashe 1

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Bismillahir Rahmanur Rahim..... "Hakk'in mallakar Hajja ne, kar wanda yayi min sauyi a cikin sa please." Page *1* A makaranta. "Uwani halilu?" "Present sir.." "Baraka lado?" "Present sir.." "Sahura Ayuba?" "Present sir.." "Indo malam Hamza?" "Labbaika, present, sir, mah, nazo..." Saurin kallon ta malamin yayi jin yauma a yadda ta amsa mai kafin ya zare glass d'in dake manne akan saman idan fuskar shi, ya d'ora dara-daran idanun shi akan nata da nufin ko zata ji tsoron sa sai yaga ta kafeshi da idanuwan ta tamkar zata cinye shi, yayi saurin wurga mata uwar harara ranshi a matuk'ar had'e yace mata cikin tsawa. "Ke..! Baki da hankali ne...?!" Indo ta mik'e tsaye tana gyaran hijjab d'in ta wanda yayi dikil-dikil da daud'a wuyan ya yage tun daga wuya har zuwa k'irjinta sannan tace, "Da sauk'i dai malam..!" "Naga alama ai koma gurinki ki zauna wawuya kawai.." Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba. Komawa tayi ta zauna sai faman soshe-soshe take yi akan ta wanda hakan da alama ba za'a rasa kwaron kwarkwata ba dan yadda take yi ya nuna hakan. sai da ya kammala kiran sunayen su tas! sannan ya mik'e ya fita yana jiran lokaci ya cika sai ya kuma dawowa yayi musu subject d'in turanci wanda aka sari basa fahimtar uban komai a ciki, idan kuwa yana son su fahimta toh sai ya had'a musu da yaren hausa sannan zaiji ruwan amsa da tambayoyi amma idan da turanci zai kwana yana yi sai dai su kafamai idanuwa tamkar zasu cinye shi. Yana fita wajan mintuna biyar sai gashi ya kuma dawowa hannun shi d'auke da wasu littattafai manya da kananu. yana shiga ya tarar duk sun kaure da surutu yayin da ya kai idanunshi can k'arshen ajin ya hango INdo da wani yaro taci uwar d'amara da hijjabin ta suna dambe. Dorinar hannun shi ya d'akko yayi gurin. sauran yara na ganin shi suka fara watsewa aka bar INdo da lurwanu a gurin. yana zuwa ya fara tsulawa INdo dorinar ganin ita ce me fifik'arewa kafin ya tsulawa lurwanu yana cewa. "Ke! Sakar mai riga wawuya kawai." Axabar bulalar ne yasa ta saki amma da ba tayi niyar sakin shi ba sai ta fasa mai baki kamar yadda ta furta tun farkon fad'an nasu. Malam Sadeeq na kallon su yace. "Me ya had'a Ku?!" Idanu kwal-kwal zasu kawo ruwan kuka lurwanu yace. "Malam itace..." Caraf be k'arasa fad'a ba INdo tace, "Malam wallahi k'arya yake shine ya fara..." Shima lurwanu dan kar tamai sharri ya kuma tare zan cen, "Wallahi malam k'arya take yi kawai na ajiye..." "Billahillaxi malam shine ya..." "Keep silent or something else's, sha-sha-shai kawai.." Babu abin da suka fahimta a cikin abin da yace dasu sai dai yana yin yadda yayi musu maganar da kuma kalaman shi na karshe ya tabbatar musu da cewar fad'a yake musu hakan yasa suka yi shiru suna bin kyakyawan bakin shi da kallo ba kamar INdo da take tunanin ko alawace ji take kamar ta lasa dan yadda ya burgeta. Komawa yayi wajan teburin shi ya zauna sannan yayi musu alamar suzo baki d'ayan, suka bishi INDO sai faman ture lurwanu take yi a haka suka k'arasa wajan da malam Sadeeq yake jiran su, "Kai me ya had'a ku da ita?!" "Malam itace kawai muna zaune sai tazo tana tab'ani da kafa nayi mata magana ta dena takani shine tak'i taci gaba har muka fara fad'a da ita." Tun kafin ya bata izinin magana INdo ta fara tana hararar lurwana bakin ta har kumfar yawu yake sabida masifa, "Kai..Kain uban can..! Na rantse da Allah malam shine ya d'alamin kaure a baya na shine na rama ya kuma yi min kawai muka fara fad'a dan shi masifaffe ne ya raina ni.." "Ya isah haka kowa yaje ya zauna bana son surutun ban za." Tashi suka yi suka tafi dama can karshen aji nan ne wajan zaman INdo dan haka ta tafi malam Sadeeq yayi saurin dawo da ita, tana zuwa yace da 'yan layin gaba suyi mata guri anan ta zauna cike da jin haushin malamin dan taga alamar baya son ta bare yabi bayan ta a duk cikin al'amarinta. A haka ya kammala musu yabar ajin duk sun gundure shi ga haushin basa ganewa da turanci har sai yayi da Hausa. Ana tashi ya hau mashin d'in sa kai tsaye ya wuce inda ya sauka. Wanka yayi sannan yayi sallar azahar ya koma gefe ya zauna bayan ya janyo wayar shi, laluban d'an uwan shi ya fara yi cikin sa'a ta fara k'ara yana d'agawa yace, "Hi twins ya gida ya gurin aikin naka?!" Daga can 6angaran ya amsa cikin sanyin murya kamar yana rad'a, "Lafiya lau all twins ya student's da fatan dai kana samun yadda kake so koh?!" Shafa k'eya yayi tamkar yana ganin shi sannan ya lashi lips d'in shi yace, "Nop! Twins ga baki d'aya makarantar bata yi ba wallahi, gashi nazo an wani bani formaster teaching kuwa sai dai nayi da hausa wata Kalmar ma ban san yadda zan fassara musu ba wallahi sai dai na barsu a haka." Dariya yayi mai sauti ya san dole a bawa d'an uwan shi haushi duba da yadda baya son wasa a harkar karatu gashi an kai shi inda zasu samai hawan jini, cikin basarwa yace. "Common Sadeeq ka sani ko anan ma girlfriend d'inka take, dan Allah kasaki ranka kasan 'yan kauye da son mutane za kaji dad'i kuma zasu soka kai dai kawai ka samo mana wifey d'in ka acan..!" Kit! Sadeeq ya kashe wayan sam beji dad'in wayar da suka yi da d'an uwan nashi ba yau, a maimakwan ya lallab'a shima a'a sai ma yi mai fatan tsiya da yake yi na samo mata dan wulakanci. shi kam Abubakar murmushi yayi jin ya katse ya san haushi yaji sabida yayi mai fatan tsiya. zai samu yaje garin har gurin shi ya bashi hakuri yaga kuma yadda suke yi. Bayan wasu awanni, Sauri yake yi ya k'arasa cikin masallacin dan gudun kar a tayar yana hanya, sai da yazo dai-dai wajan wata kwata zai tsallaka kawai yaji an kwararo ruwan kanzo gabaki d'aya aka b'ata mai wandon dake jikin shi. Bin katangar gidan yayi da kallo cikin wani mugun takaici kafin yayi wani yunk'urin tuni an fara zagaye shi abin takai cin ma harda d'aliban shi. sai sannu suke zabga mai tamkar wanda yaji ciwo. "Kai subhanallahi Malam Sadeeq ya a kai haka?" Kafin ya bashi amsa wanda yayi maganar ya kalli wani yaro tare da cewa, "Kai yi maza shiga nan gidan kace a temaka mana da ruwa a buta." Juyawa yaron yayi shi kuma headmaster ya kalli Sadeeq cikin jimami yace. "Garin Yaya hakan ta faru Malam Sadeeq?!" Da kyar ya samu ya tsaida takaicikin shi kafin ya kalli headmaster yana kallon inda aka b'ata mai yace, "Wucewa zan yi zuwa masallaci, su kuma ba tare da suna kulaba kawai suka watso k'azanta sai kace a cikin gidan su duk ba wannan ba sun b'atan lokaci na rasa jam'i." "Ashha-ashha malam yi hakuri kasan kauyan namu ne sai hakuri duk haka suke yi kayi hakuri dan Allah. Dai-dai lokacin yaron da aka aika suka fito shi da INDO hannunta rik'e da buta gefen butar ya fashe sai da ta d'an kar-kata ta taho tana cewa, "Waye yake neman ruwa a buta?!" Karaf suka had'a idanu da shi da sauri ta dashare baki tana matsawa wajan shi ruwan sai zuba yake ta kalleshi tare da cewa, "La'ilaha'illallahu Malam Sadeeq kaine a k'ofar gidan mu yau?!" Banza yayi mata yana kallon butar ganinta jage-jage gashi duk ta fashe ya sashi yin saurin juyawa tare da kallon headmaster yana cewa, "Rankashi dad'e bari kawai na koma gida naga nan duk b'ata lokaci ne na gode..." Ba musu headmaster yayi mai sallama da sauri ya wuce sauran mutane na bashi hakuri ita kuma INDO tana fad'in, "Malam ruwanfa? ko na biyo ka dahi koka ka fasa na maidahi gida?!" K'in kulata yayi ganin haka yasa INdo ta murgud'a mai baki tamkar yana ganinta sannan ta koma gida tana mitar kawai yasa sunyi asarar ruwan su a k'asa bayan suma babu kala ne suke yi. Yau kwana biyu kenan INdo bata zuwa makaranta, sai a kwana na uku taje tun daga bakin k'ofa zaka tabbatar da yau tazo sabida yadda ajin ya kaure da shegen surutu da hayani. yana shiga ya ganta zaune akan tabur d'in da malamai ke zama idanunta sanye cikin eye glass wanda idanun (glass) d'in suka ciccire ta rik'e pencil tare da d'ora kafa d'aya kan d'aya tana yin irin na Malam Sadeeq, "Mary alto." "Zuwaira jamilu." "Mansur bawa." Gabaki d'aya ajin aka d'auki ihu da shewa dan sam basu kula da zuwan shi ba. har INdo ta mik'e tsaye tana dariya tare da cewa, "Alkur'an haka malam Sadeeq yake yi.." Suka k'ara tuntsurewa da dariya ana cewa, "Ohhh ke INDO...!" Tsittt taji anyi hakan yasa ta waigawa bakin k'ofar dan ganin yadda kowa ke kallon wajan, karaf suka yi idanuwa hudu da malam Sadeeq wanda yayi kicin-kicin da fuska tamkar hadari tayi saurin komawa wajan zamanta wanda in dai shine a ajin toh anan take zama sai ya fita take komawa gurinta na ai na hi wato karshen aji. Yana shiga duk aka tashi ana gaida shi kowa ka gani cikin tsoro yake dan basu san matakin da zai d'auka akai ba, "Good morning sir..!" Sai da ya samu guri ya ajiye register da sauran littattafan hannun shi sannan ya kalle su yayi musu alamar su zauna da hannu, gyara glass d'in idanun shi yayi sannan ya kalli inda INdo take zaune ta kwalalo mai idanuwa yace mata, "You! come here.." Tashi tayi cikin d'ari-d'ari dan babu wanda be san kalmar come ba, tana zuwa ya matsa mata tare da nuna mata kujerar gurin yace, "Seat down..." (Zauna) Zama tayi dan taga ne abinda yace sabida yau da gobe idan sun gaida malamai ana ce musu seat down so kuwa ya san
Chapter 1 · 0% Book details