Sashe 13
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kod'add'iyar shadda doguwar riga wanda ta d'age mata sannan ta dawo tsakar gida ta zauna tana kallon kunshinta. Wani irin tsanar malam Sadeeq da Abubakar suka sake mamaye cikin zuciyarta ta cewa Inna. "Inna wanki zanyi gobe na tafi gidan yakumbo Tsahare, wallahi billahillazi bazan sake zuwa makaranta ba saye zan yi tafiya ta naga ta tsiyarsu mugaye." Cikin dafe k'irji Inna tace "ke 'yarnan saye kuma? Kiyiwa Allah da ma'aiki kiyi shiru da maganar tafiyar nan kinsan dai babanku baya son zuwanku garin nan tun abinda ya faru tsakaninsa da jummala." "Inna wallahi saina tafi, kina jinfa abinda mugun malamin nan yace, wai idan na dena zuwa makaranta saiya saka an d'akkoni toh wallahi barin garin zanyi hena dad'e sannan zan dawo a'he." Hankalin Inna ya tashi dan tasan idan baban su yaji toh lashakka sai anyi fitina duk da cewar tsaharan k'anwarsa ce amma tun a haihuwar shehu suka samu sa6ani akan naman suna shikenan sukayi baram baram kuwa yace bashi ba d'an wansa sannan yacewa Inna ya haramtawa 'ya'yansa zuwa garin idan sukaje kuma Allah ya isah. Tashi INdo tayi tabar gidan ta shiga gidan Rukayya, tana ganinta ta fara murna tare da cewa. "Kai INdo shine ko a kawo min kyautar ingani ko?!" Saida INdo tasamu guri ta zauna sannan tacewa Rukayyan "Yo ai basu bani ba, wai wani ban yanke farce ba ninasan dama malaman nan ba kaunata sukeyi ba kawai dan dai nafi karfin sune bayadda zasu yi dani shegun." "Kan uba! Yanzu kina nufin babu abinda malam Sadeeq yayi miki?!" "Sai duka nama dayayi kuma nace Allah ya isa." Nan suka cigaba da hira har INdo na bata labarin tafiyarta saye gobe Rukayya tace. "Kai INdo sai kuma yauhe zaki dawo?!" INdo na watsa shinkafa da wake tana cewa "babu lokaci idan na tafi henayi aure zan dawo yasin." "Kai INdo baxaki dawo ba kenan?!" Rukayya ta kuma tambaya cikin jimami, ita kuwa INdo ko'ajikinta tace "Eh bazan dawo ba he randa malam yadena zuwa garin nan." "Kai Allah ya wadaran wannan malamin da yaja zaki tafi, zamuyi rashinki INdo barema Inna." "Kyale Inna can na barota sai masifa take dan nace zani saye wai bazani ba toh alkur'an saina tafi." Haka suka dinga hira da Rukayya har bayan la'asar sannan ta koma gida inda ta tarar da Inna ta gayawa babansu yace toh babu inda zata ta kule d'aki bata sake fitowa ba. Tun asubar fari ta farka ta tsinci kayanta tasa a d'ankwali ta d'aure ta d'auk'e fitilar da aka haska d'akin da ita wato shekarau mekwayayen nan k'ananu a jikin katako tayi sad'ab-sad'ab gidan a kulle yake ta jefa kullin kayan ta katanga sannan itama ta kama ta dirga ta kwashe kayan nata ta an taya da gudu sai bakin titi ko tsoro bataji. Tayi tafiya sosai sannan gari ya fara haske daman babu buk'atar yin sallah dan bawani yi takeyi ba sai taga dama. Mota na zuwa ta tsayar dasu ta shiga dama da d'ari ukunta a hannu data ara wajan Rukayya. Can gida kuma tunda suka farka suke neman Inndo, duk gidan da akasan tana zuwa saida akaje bata nan. Kuka Inna tasanya domin tasan yau INdo tayi mata abinda zai iya 6allamata aure, lokacin da baban yaji cewa yayi k'arya Inna takeyi tasan ta tafi dan haka itama ta shirya tabi bayanta su dawo tare kasan cewar sunsan zata iya zuwa. Ko kud'in mota Inna batada su amma a haka malam Hamza ya takura mata kan cewa sai taje ta dawo da INdo haka ta fito tana hawaye. A bakin titi malam Sadeeq ya ganta harya wuce ya dawo duk da cewar ta rufe fuska da mayafin jikinta tana share hawaye yaje yace. "Baiwar Allah kiyi hakuri lafiya dai ko..?" Shiru batayi magana ba duk da besan kowace ba ya zaro d'ari biyar ya bata babu yadda zata yi ta k'ar6a tana ta zazzaga mai addu'a shidai ya wuce ita kuma mota na zuwa tashiga tana fatan Allah ya temaketa can din INdo ta tafi, ayau bazasu kwanaba zata dawo da ita. Wajan k'arfe biyu da rabi INdo ta shiga wata rugar fulani anan cikin sayen bakinta a washe hannunta d'auke da kullin kaya, suna zazzaune k'ark'ashin bishiya suka hangota nan da nan yakumbo tsahare ta had'e rai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana dakan fura haka INdo ta k'arasa gurin tana dashare musu hak'ora. "Wacece wannan kamar mai sunan Gwaggo..?!" Cewar talatu yayar malam Hamza dake kwance, INdo ta k'arasa tare dayin cilli da d'ankwalin kayan nata tace. "Nice nan yakumbo talatu ahe duk kuna nan, yau dai gani a garin ku ina kwananku...?!" Duk suka amsa suna tambayar ta su Sagiru da Nafeesa da Shehu tace lafiya lau amma banda yakumbo tsahare daketa faman dakan fura, ko ajikin INdo ta mik'e tare da zuwa wajanta tana cewa. "Sannu yakumbo tsahare, ina su lawisa take..?!" "Ke karki yimin rahin kunya aradun Allah kuwa, idanma Ubanki ne yau ya turoki toh dagake harshi d'in zan iyayi muku rahin mutunci jacan ki bani guri ni." "Allah baki hakuri daga tambaya.." INdo ta fad'a tare da komawa wajan su yakumbo talatu aka kawo mata d'umamen tuwo da fura da nono tana ci suna hira har su lawisa suka dawo daga tallar nono, murna da farin ciki ba'a magana duk da cewar Lawisan cikima gareta har tayi aure tsiranta da INdo shekara biyu ne. Cikin gidan suka wuce suna zazzaga shirmen su. Inna kuwa la'asar sakaliya ta iso saye sabida da kyar ta samu motar da ta kawota a d'ari da talatin. Saida tayi sallah sannan taci kwad'on rama da fura bayan sun shaida mata cewar INdo tazo amma sun tafi tatsar nono, hankalin Inna ya tashi tace ta kalli malam iro mijin yakumbo talatu tace. "So nake a yau mu koma gida gahi bata kusa kuma ina neman yadda zanyi mu samu kud'in komawa." Malam iro ya kalleta da mamaki sannan yace. "Haba dai Maryamu, yanzu fisabilillahi har yaushe zaku koma gida, hasalima ita INdon bata kusa kuma da kyar idan zata yadda tabiki dan tasamu yara, kuma na tambayeta randa zata koma tace sai an kori wani malami a garin naku." Inna ta fashe da kuka malam iro ya kalleta yana jin tausayinta dan yasan tsoran d'an uwar matar tasa takeyi. Hakuri ya dinga bata ita dai hawaye kawai takeyi gashi tana matukar kaunar malam Hamza duk da cewar shima yana matukar santa amma hakan baya hanashi yimata wulak'anci. Har magariba su INdo basu dawo ba sai wajan k'arfe takwas na dare, koda taga Inna batayi wani murna ba kotaji tsoro ita kuma nauyin mutane ya hanata yi mata magana. Cikin dare Inna tasamu INdo ta gama lalla6ata akan ta yarda gobe su koma amma fir tace wallahi bazata koma ba nan zata zauna sai lawisa ta haihu koda zata koma. Da gari ya waye haka Inna ta kama hanya dama tunda taje yakumbo tsahare bata ko kalli inda Inna takeba har ta kama hanyar komawa sumaila. Koda Inna ta koma gida malam Hamza baya nan, kafin ya dawo harta sarrafa musu gero tayi musu burabusko yana dawowa yaci yayi hani'in data sanar masa cewar INdon tak'i dawowa sai yace. "Kyaleta Maryamu ni kaina na huta da fitinarta taje can karta dawo d'in." Bayan sati biyu. Tunani da damuwa da begen son ganin INdo suka addabi zuciyar Abubakar, duk iya yinsa na ganin ya kawar da hakan daga cikin zuciyarsa hakan ya gagara. Ya rasa meyagani a tattare da ita har yakejin irin abinda yakeji cikin ransa da gangar jikinsa, yasan duk lokacin da asirin zuciyarsa ya fito fili zaisha wulak'anci gurin Sadeeq dama sauran abokansa. Tashi yayi ya tafi Sumaila kauyen na sani direct babu wanda ya sanarwa. Yana zuwa zuwa ya tarar su Sadeeq sun tashi daga makaranta yarama sai fitowa sukeyi, samun kanshi yayi dayin gaba zuwa unguwar su INdo ko Allah zaisa ya ganta, amma har Sadeeq ya dawo ya tarar dashi besamu yaga ko kyallin kallabinta ba hakan kuma ya hargitsa ilahirin tunaninsa na Ina zai ganta? "M twinnie..! Ta6 lallai kaida kace min kaida garinnan saidai in wucewa zakayi shine yau na ganka at this time..?!" K'ak'alo murmushi Abubakar yayi yana kallon hanya dan befidda ran zai hangota ba. Ganin yadda Sadeeq d'in ke kallansa ne yasa shi saurin cewa. "Malam Sadeeq nasu INdo, wai kuwa har yanzu kana basu kyautar?!" "Meza'a fasa twinnie? Itace dai tun ranar bata sake zuwa ba, dana tambayi babanta rannan danaje gidan yace wai ta gudu kauyen su sai randa aka koreni zata dawo kaga kuwa ba rana kenan.." Daram..! K'irjin Abubakar ya buga besan lokacin da ya furta "what...?!" *HAJJA CE* [7/1, 5:02 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _Shafin yau naki ne tawan *HALEEMATU G KHALEEL* (Aneesa didi), Allah yayi miki albarka ya k'ara nisan kwana Allah ya tayaki rik'on Namcy na khadijatu (shareefat) Allah ya azurtaki da miki Nagari ina sonki fisabilillah like H Page *11* Sadeeq ya bishi da kallon mamaki ganin yadda ya furta kalmar tamkar yace masa shine yabar garin ko Mama. Kallansa ya kumayi kafin ya juya yayi hanyar shiga gida yana cewa. "Kai twinnie bafa Qibd'iyya nace maka ba naga har kana ihu." Harya bud'e gidan ya shiga Abubakar betaso ba, hanyar gidan su INdo yabi da kallo ji yake tamkar zai ganta amma bako kurarta haka ya k'araci zamansa kafin ya tashi yabi Sadeeq cikin gidan. Lokacin daya shiga tararwa yayi Sadeeq harya shiga wanka hakan yasa shi zama tare da dafe goshinsa sabida tsananin saramai dayaji yana yi. Fitowa Sadeeq yayi zama yayi kusa dashi yana kallansa soyake ya gano wani abu a tattare da d'an uwannasa, Abubakar ya d'ago ya kalli Sadeeq ganin yana mai kallon tuhuma yasa shi wayan cewa ta hanyar cewa. "Twinnie wai yaushe zakuyi hutu ne?!" Sadeeq ya mik'e tare da janyo singlet zai sanya yace "kasan ba'a fiyeyin hutun maulud ba so kawai sai term ya k'are ni yanzu mafa na farajin dad'in makarantar sabida suna bani had'in kai yanzu shi yasa na dena neman transfer." "Oh idan na fahimta kana nufin kace dama Humaira ce ke