← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 53

Sashe 5

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su Sadeeq ya hana dan karsu yi hayaniya, can k'arshen aji INdo take ta duk'ufa sai satar amsa take yi cikin littafin Ayuba mati sabida ita bata da ma littafin bare tayi karatu. Tsayawa Sadeeq yayi a gaban alo domin shi bema san ta samu damar zuwa ba ya fara musu bayani. Malamin dake tsare su yana zaune a kujera Abubakar yana tsaye ya hango wata ko d'agowa ba ta yi hakan yasa shi k'arasawa gurin da take ya lek'a yaga meke faru sai yaga ta bud'e littafi sai kwafa take yi har ta kusan cika shafin farko. "Ke.....!" Taji an fad'a dai-dai kunnan ta. tsoro da razana yasa ta sakin tusa burtt ba tare da ta shiryawa hakan ba 'yan aji suka kwashe da dariya ita kuma ta zaro ido ta fara rantse-rantsen kare kai. "Malam wallahi tallahi...." Da sauri ya kifawa bakin na ta mari tayi saurin toshewa da hannun ta. matsawa yayi tare da nuna mata hanya yace. "Fito waje kafin na yayy-yaga ki a gurin nan 6arauniyar amsa.." "Wallahi mal..." Zata tsaya yi mai gaddama ya yi saurin fin ciko ta tare da tura ta gaban ajin tayi taga-taga zata fad'a kan tebur Allah ya temake ta tayi saurin sanya hannu. Kwal-kwal idanunta suka kawo ruwa zata yi kuka Abubakar ya k'arasa gurin yace. "Shanye shi, idan kika bari hawaye suka fito sai na zane ki 6arauniyar amsa." Maida hawayen tayi tana nan tsaye har Sadeeq ya gama yi musu bayani sannan ya kalli Abubakar hace, "Twinnie bar yarinyar nan ko tayi ba dubawa zan yi ba sabida ta yaye kanta ba zuwa take yi ba tayi degree yanzu sai zuwa tallah." "Ohhh! No-wonder ashe dak'ik'iya ce, amma baki yi halin asalin me sunan ba shame on you.. Kawo wannan ta hannun taki da kika sato amsar, ki d'akko sabuwar pepper kizo nan ina jiranki." Tafiya tayi tana gunguni tare da murgud'a musu baki, sabuwar takarda ta d'akko tare da biro taje ya nuna mata gaban alo yace. "Zauna kiyi anan." Kallon gurin tayi sannan ta turo baki kai da kagani kasan zai yi fitsara tace. "Toh malam ai babu abin d'orawa kuma yagewa takardar zata yi" Ba tare da ya kalleta ba dama Sadeeq ya fita yace, "ki d'ora akan cinyar ki kiyi." "Amma malam ai..." Wata uwar harara daya yi mata ne yasa ta had'iye sauran maganar, zama tayi tana zumbura mai baki yace. "Idan kika sake kira na da malam sai na fasa miki baki." Bata sake kula shi ba ganin yafi malam Sadeeq zafi da saurin kai duka, har kowa ya gama ya fita INdo tana zaune a gurin sai raba ido take yi gashi bata rubuta komai ba sai jagwal-gwalo. Ganin bata da niyar kawowa ne yasa Abubakar k'arasawa wajan tayi saurin cukwaikuye takardar ya mik'a mata hannun alamar ta bashi amma taki, "baza ki kawo ba mara kunya?" Baki ta kuma murgud'awa mai aikuwa ya sanya k'afarsa ya doke shi da takalmin sa. INdo ta kurma wani uban ihu tare da fad'uwa k'asa tana ihu tana birgima. Sunkuya wa Abubakar yayi ya d'auki takardar ya sanya cikin sauran tare da bawa invigilator d'in, ko takanta be kuma bi ba sai ma tsallake ta da yayi yabar gurin. Ihu ta kuma saki tana shure-shure har daddaud'an pant dinta ake gani sabida wandon makarantar ya yage d'alibai suka zagaye ta ana bata hakuri da kuma masu yi mata dariya amma bata fasa shure-shuren ba shima malamin yayi tafiyar Sa dan yasan INdo sarai hakan yasa be kulata ba. "Allah ya isa ban yafe ba mugaye kawai anyi satar amsar, shi dama ba malamin muba yazo yana cin zalin mutane..." "Hahaha INdo me tusa burtt..." Uba Aminu ya fad'a yana nuna ta yana dariya, ai kamar jira take yi ta mik'e tare da cakumar sa suka fara fad a. K'arfi ba d'aya ba shi namiji ya dinga gwarata da alo jikake k'um...k'um amma tak'i sakinsa sabida tsabar jaraba, can akaji Uba ya rushe da wani irin ihu mai had'e da kuka. "Kai..kai...kai! Lafiya meya faru haka.?!" Malam Zubairu daya zo wucewa yaji ihu ya tsaya yana tambaya. "Malam fad'a suke yi." "Waye da waye?!" "INdo da Uba." Ihu Uba yake yana hawaye gashi ya rik'e gaban sa, malam Zubairu ya kallesu ganin INdo na rik'e kugu yasa shi cewa "ku biyo ni ofis yanzun nan." Abokan Uba suka kamashi suka kaishi k'ofar staff room, ita kuwa tahowa tayi tana bugun cinya alamar bala'in be k'are ba taje ta tsaya malam Zubairu yakai takaddu ya ajiye sannan ya fito dan jin kanun zance, be fara bawa INdo damar magana ba yace Uba ya fara yi amma ya kasa sai shasshek'a yake yi da kuka. "Ke kuma gaya min gaskiyar abinda ya faru." Dai-dai lokacin Sadeeq da Abubakar suka fito daga cikin staff room, tsayawa suka yi Abubakar na waya ta fara baya ni. "Tonona yake yi shine muka fara fad'a." "Sai kuma aka yi yaya..?!" "Sai kazo kace mu biyo ka." "Kai Uba me yasa ka toneta gashi ta saka kuka..?!" "Malam cizo na tayi a anan." Ya fad'a yana nuna gurin, duk wad'anda ke gurin suka zaro ido Abubakar dake waya ya zare ta daga kunnansa yana kallon INdo cikin tsananin mamaki yace. "Ke mayya ce? Baki da hankali?ke wace irin yarinya ce ne da kika fitini kowa ne? Stupid,nonsense, what a fool wawuya kawai, mai wasa da maza karya.." Haushin maganar sa da kuma turancin da yake yi bata jinsa yasa ta fara murgud'a baki tana motsa lab6anta alamar magana take yi, da sauri Abubakar yayi kanta zai ham6are ta Sadeeq ya rik'osa yana kad'a masa kai alamar kar yayi yayin da zuciyar Abubakar d'in ke tafasa yanajin wani tururi cikin ransa dan yaki jinin rashin kunya da k'in gaskiya. A hankali Sadeeq ya dafa kirjinsa yana kalon INdo wadda ta makure jikin karfe tana jiran jin saukar duka yace... *HAJJA CE* [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *4* "Aisha zo ki bawa yaron hakuri." Tamkar ba taji ba sai faman wasan ta take yi da k'asar gurin da d'an yatsan ta wanda alama ce ta baza ta bayar da hakurin ba ya kuma cewa. "Aisha ba magana nake miki ba kika min shiru ko..?!" "Malam fa shine ya fara tono na kuma sai na bashi hakuri ta6di jam.." "Duk da haka ki bashi hakuri tun da kin yi mai ba dai-dai ba.." ...uhm." Ta fad'a cikin k'asan mak'oshin ta, Abubakar yayi kamar zai wuce kawai yayi wuf ya dank'e ta, nan da nan ta fara ihu har wasu malaman suna sake fitowa ya damk'eta ta 6are baki tana ihu yaji wani sumumin wari ya fito daga bakin ta yayi saurin kawar da kai tare da hankad'a ta saitin Uba ta fad'i k'asa bata San lokacin da ta furta. "Allah ya baka hakuri Uba kayi hakuri kaji ka hakura..?!" "Eh." Uba ya fad'a yana share hawaye malamai aka yi ta yiwa Indo fad'a akan karta sake yin fad'a da Namiji sannan aka sallame su. Ana tashi daga makaranta babu wanda Indo ta kula tayi wuce warta, ba gida ta wuce ba kai tsaye ofishin 'yan agaji ta nufa tana zuwa ta sami ogan ya kalleta yace, "Yarinya ya aka yi aiko ki aka yi..?!" Tace "A'a shugaba k'ara na kawo dan ance shari'ar maita bata k'arewa toh wani malamin mu ya Ce min banza maiya jaka, toh ban yafe bane shi yasa na kawo k'ararsa abi min hakkina." "Au ke cema kika kawo k'arar?" "Eh sabida ance nan ake kawowa kafin akai kotu." Sosai ya kalli INdo wadda take faman turo baki tana taunar k'asan hijabin ta da hak'ori. "Toh naji yanzu shi malamin yana ina kuma a wacce makaranta yake koya muku duk da naga inifam (uniform) d'inki na makarantar tsefawa ne...?!" "Eh Shugaba acan nake kuma ma shi ba malamin mu bane d'ayan ne malamin mu amma kaga ya mareni, yayi min kutufo da k'afarsa sannan yace min Mayya, ance shira'ar maita baya k'arewa toh yazo ya fad'a a ina nayi maitar." Shugaban 'yan agaji na k'auyan ya sake kallonta sannan yace, "Ya sunan ki...?" Tace "INdo malam Hamza." "Toh INdo yanzu abinda nake so dake nasan yanzu an tasheku ki bari gobe idan Allahu ya tahemu lafiya he muzo ki nuna mana hi malamin kin ji ko.?!" "Kai! Shugaba, ai tafiya yake yi kuma idan an gama jarabawa ba dawowa zai yi ba a hanyar gidan mu suke kayiwa Allah kayi ma ma'aiki kazo muje ayi Mai jan kunne ya dena ce min mayya da dak'ik'iya." "A'a bada ni zakuje ba bari nasa wani yabiki suje yaji abinda ke faruwa." Ya d'aga murya yana k'iran, "Awaisu! Awaisu!!, zo dan Allah kabi yarinyar nan ta kawo k'arar wani malamin su." Awaisu na zuwa suka tafi suna tafiya suna hira tamkar dama sun saba har suka k'arasa k'ofar gidan su malam Sadeeq wanda shigowar su kenan dan sai da suka tsaya suka yi juyan bak'in mai. "Kika ce nan ne gidan ko?" INdo tace "Eh nan ne suna ciki." Kwan-kwan-kwan, Awaisu ya fara buga k'ofar gidan yana kwad'a sallama. Malam Sadeeq ne ya fito sanye cikin jallabiya ya kalli INdo sannan ya kalli Awaisu cikin rashin fahimta da kuma sanin dalilin zuwansu ya fara magana. "Lafiya dai ko bawan Allah." "Eh toh lafiya ba lafiya, wannan yarinyar ce ta kai k'ara cewar kana ce mata mayya. Toh bata yafe bane yasa takai mana k'orafinta shine shugaban mu yace nazo naji dalilin da yasa kake fad'a mata wannan kalmar." Mamaki da al'ajabi suka cika Sadeeq, sai yanzu ya k'ara tabbatar da hauka da rashin hankalin 'yan garin ya kuma kallon INdo wadda itama shi take kallo yayi shiru yasan Abubakar ne dan haka ya tsaya yana tunanin abin cewa yaji INdon tace. "Awaisu ka tambaye hi idan shine idan kuma ba hi bane toh d'ayan ne ya fito dan tagwaye ne.." Kallonta Sadeeq yayi ya sake tabbatar da lallai bata da kunya, shi kuma Awaisu sai d'aga kai yake yana kallon gidan ko zai ga wani ya fito amma ba kowa hakan da sadeeq ya gani ne
Chapter 5 · 0% Book details