← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 53

Sashe 39

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. _Na baku page d'in nan kyauta danjin dad'in ku, *Home of novel, Tsakar Munay, Zauren Sadeeya, Khadija candy, Rano online, Feedohm novella, Dandalin Billy bilya, Basma elr Lele grp,* Tnxs n I really appreciate ur love's care's of d comment's_ Page *32* 'Dan zame jikin ta tayi daga nasa ta kallesa, "shin da gaske ni yake so ko kuma cikin dake jikina? Anya malam Sadeeq kana sona kuwa? Amma zamu gani idan gaske ne." "Kin yi shiru." Dariya ce ta su6uce mata ganin yadda yake kallonta tamkar wani mara lafiya, ganin tana dariya yasa shi jin wani farin ciki har cikin ransa ya kuma janyo ta cikin jikinsa yana shafarta, ba zai mata komai ba dan karma tayi tunanin dan hakan yake sonta yanzu gara ya daure ya hakura ana d'auke ruwa kawai ya gudu gurin Fateema tunda Allah ya kasa ya bashi biyu. "Kana ganin yanzu babu abinda ya samu cikina?!" "Insha Allahu karki damu, ko kina jin wani ciwon ne?" "A'ah bana jin komai ni sai yunwa." "Okay sorry bari ruwan naga ya fara d'an tsagaitawa sai na samo miki wani abun kici. Bafa ki bani amsa ta ba Aisha baki ce kin yadda zaki zauna dani ba." Dariya da kuma yi tunowa da maganar Asma'u da tace tayi hakuri wata rana sai labari, shi gani zai yi kamar an shiga rayuwarsa ne shida Fateema amma tunda had'in Allah ne wata rana sadeeq zai kulata sai so ta koda bekai na Fateema ba tunda har Allah ya kuma had'a su a bed gashi harda rabo. "Aisha me kikema dariya ne? Ko gemun dana tara kikewa dariya.?" "Kai a'ah wallahi ni ina ruwana da wani gemu." "Toh kina so kenan in barshi yamin kyau?!" "Lalalah bance ba yadda kagani kai dai, kuma tunda ka barshi ai kowa yasan so kake yi taya za ai nace beyi maka ba ni INdo." Tayi maganar tana rik'e ha6arta cikin nuna k'ask'anci dan ta san bata kai wannan matsayin ba da har zata bashi umarni yabi ba. Yatsansa yasa a goshin ta wajan billenta yana shafawa ta lumshe idanuwa tana tuno Abubakar sabida duk sanda zai ganshi sai ya ta6a mata shi, sai dai idan ta d'aura d'an kwali ta cukaro shi ya rufe shine kawai ba zai ta6a ba. "INdo malam Hamza...! Wai me yasa ake ce miki haka ne, a memakwan Aishat Hamza." Ya fad'a cikin wani irin style wanda yasa ta kalli cikin idanunsa shi kuma ya kanne mata nasa tayi murmushi tare da cewa. "Haka mutane suke kiran baban mu, toh lokacin da aka sani a makaranta dama kowa INdo yake cemin banda Inna ita sai dai tace min 'yar nan, shi kuma baba yace min uwata shine da aka kaini sai aka tambaye ni sunana baban mu yak'i fad'a ni kuma karna fad'i sunansa sai nace INdo Malam Hamza shine kawai sunan ya zama haka." "Ummm! Good, toh yanzu kuma fa a school? Ko har yanzu kina nan a INdo malam Hamzan?" "No..no..noooo, Aishat Hamza tun lokacin da Mubasheer yaje yamin registration ya saka min haka shikenan nima na cigaba da sawa." Kallonta yayi yaji wani mugun tausayinta sai dai shi kansa yasan ya makaro, tun a baya ya kamata yaji tausayinta amma beji ba ganin batada nutsuwa a memakon ya tallafa mata sai ya k'ita sam baya k'arfafa mata gwiwa akan sha'aninta amma ya zai yi da sharrin zuciya dana shed'an, yasan dai marigayi shine ya kwashe ladan gashi har yau da baya duniya ta kasa manta shi. Yana fatan shima wata rana tayi mai irin wannan abun ko yana da rai ko kuma lokacin yabi d'an uwansa. Uban ruwan daya jibgeta ne gashi kuma ya rungemata a jikinsa ta takure yasa wani daddad'an bacci ya sace ta ba tare da tasani ba. Shima sai da ya janyo ta yaji jikinta ya saki hakan yasa shi leken fuskarta kawai sai yaga ashe har tayi ya bacci, ya juya yadda zai dinga kallon fuskarta ya kura mata ido. Ya dad'e yana kallon kyawunta mai kwantar da zuciya kafin yayi murmushi tunowa da yayi sanda ta d'auke mai naira d'arinsa daya je siyayya. A hankalli yaka sanya hannunsa saman cikinta yana shafawa zuciyarsa na tsananin harba mai cikin wani masifaffan son kasancewa tare da ita ya kai lips d'insa kan nata ya sumbace shi sannan ya mik'a a hankali ya sanya mata pillow a inda ya tashi tare da rufa mata lallausan bargo ya mik'e da sauri kasan cewar an tsayar da ruwan har an fara k'iraye-kirayan sallar juma'a. Cikin sand'a ya fitar da motarsa sannan ya kulle mata gidan ya tafi gidan Fateema da zafi-zafinsa. A k'ofar gida yayi parking motar ya tura gate d'in a kulle, wayarsa ya janyo ya kirata ringing d'aya ta d'aya cikin murna da zumud'i tace. "Allah yasa dai baby haka zaka cemin ka iso cikin Kano..?!" Muryasa cikin murmushi yace. "Fito ki gani ina gate." Zaro idanuwa Fateema tayi tamkar tana gabansa cikin sanyayya murya tace. "Baby kadawo kana waje? Please I'm so sorry kaga yanzun nan muka tashi yara sabida ruwa, dan Allah baby kajira ni in k'araso." "Okey toh kiyi sauri kinga karna rasa sallahn juma'a." "Toh godiya nake baby na sai na k'araso." Sallama tayi da sauran malamai matan da suka fito tare, cikin sauri ta tari Napep kafin wani sakannin har ya kawo ta. Cikin mota ta tarar dashi ya ziro k'afarsa waje hannunsa rik'e da wayar marigayi yana kallon pic's d'insa dana INdo wanda yayi mata tun tana INdo malam Hamza ranar da taso cin atamfa Allah beyi ba, dana d'aurin aure harda wad'anda suka yi a Munjibur park da wad'anda yake mata a cikin gida sai dai duk babu hotan banza a ciki Fateema na k'arasawa wajan Motar yayi saurin zura wayan a cikin aljihunsa. "Oyo-yo baby nah, taho mushiga ciki." Ta fad'a tana kallonsa cikin murmushi tare dayin gaba ta bud'e k'ofar gate d'in shi kuma ya biyo bayan ta. A parking lot ta tsaya yana shigowa suka rungume junansu cikin nuna kewa kafin yace. "Bari nayi alwala naje nayi sallah kafin na dawo ki samar min wani abincin kiyi da d'an yawa za'a kaiwa Aisha na biya naga ashe batajin dad'i." Kallansa tayi tana dariya tace. "Wai wannan uban k'asumbar daka tara gashi hardasu gemu duk na meye." Shafar faskar yayi yana tafiya yana cewa. "Baby wannan gemun na komai ne wallahi, hmmm danma Allah ya temake ku a iya tara gemu na tsaya, bari dai naje na dawo please ki d'ora girkin." Dai-dai lokacin suka shiga cikin Falo ya shiga toilet ita kuma tayi bedroom d'insa dan k'ara masa k'amshi duk da cewar kullum tana k'amsasa shi. Yana yin alwalan ya tafi masallaci, ana idarwa ya wuce gidan su suka gaisa dasu Mama tana tayin murmushi a tunaninta be fara ganin cikin INdon ba tasan zai yi murna d'an k'aniya da ana bashi yana nuna baya sonta. **** Yana dawowa ya tarar ta gama dama already tana da miya wadda tayi jiya tasha kifi sai k'amshi takeyi. Rungume ta yayi cikin tsananin so da buk'atuwa domin da k yar yayi sallah banda ta juma'a ce da bazai yi ba sai ya fara samun nutsuwa. Sannan baya son komawa gidan INdo da wannan matsalar dan kar tayi tunanin hakan ne yasa shi cewa su shirya yanzu yana sonta, ya fison ya fara nuna mata yanzu ita d'in yake so kafin ya fara nuna mata ainihin waye shi. Bedroom suka koma hakan ya tayarwa da Fateema hankali dan tasan a wannan yanayin ita yak'e muradi gashi ita kuma tana period ya zata yi mai? Ganin yadda yake mata zafi-zafi yasa ta rik'o hannunsa tare da kwato shi saman k'irjinta murya a karye tace masa "Sorry baby.." "For what.?!" Ya tambaye ta yana matsar ta da gashin kanta, nuna mai tayi hakan ya tayar mai da hankali duk iya k'ok'arinta na ganin ya samu nutsuwa abin ya faskar sai da kawai ya nuna mata yayi normal sabida baya son damuwarta yasan da zata iya d'auke blood d'in da yanzu tayi. "Baby Ina abincin Aishan, kawo naje nakai mata zan biya can gurin Anas akwai abinda zan k'ar6o a gurinsa." Kallonsa tayi tasan k'ila yaje gurin Aisha, amma a k'a'ida yau itace dashi sai dai baxata so ta ganshi cikin matsala ba, tayi murmushin yak'e tana shafar gashin da ya lullu6e k'ewayan bakinsa tace. "Yana falo na zuba." Tashi yayi ya mayar da kayansa ta rakosa ya d'auki basket d'in k'irjinta na bugawa dan tana zargin akwai abinda zai had'asa da INdo amma tasan basa shiri zai iya sharewa ya jira har lokacin da zata samu tsarki. "Bye-bye baby ina dawowa zanci abinci nayi bacci dan agajiye nake munyi kwanan mota." "Toh sai ka dawo ayi mata sannu, kona zo muje tare?!" Kallonta yayi na 'yan dak'ik'a kafin yayi murmushi yace. "Yanzu kika dawo daga gurin aiki, sannan kice zaki fita bayan mijinki ya dawo daga tafiya me nisa. No ki zauna ki tanadar min dadd'ar hirar da zaki min idan na dawo." Fateema tayi dariya tare da d'aga mai hannu ya fita tana kallonsa kishinsa fal cikin k'ahon ziciyarta. Yana fita ya shiga mota yayi gidan INdo, yana zuwa a bud'e yaga gidan yayi parking a gefen gidan ya d'auki kayan abinci ya Shiga. Babu kowa har ya shiga cikin bedroom d'inta bayan ya ajiya abincin a falo. Tararwa yayi ta idar da sallah, ya tsaya a bayanta yau INdo ce take sallah harda su addu'a, lallai Allah buwayi mai sauyin lamari kamar yadda ya sauya salon alak'arsu daga malamin ta zuwa mijin twinnie d'insa daga nan ya sauya zuwa mijinta. "Humairah." Taji ya fad'a k'irjinta yayi tsananin bugawa tayi saurin waigawa tana kallonsa ido waje. Murmushi ya sakar mata tayi saurin d'auke kai dacta ya fad'a mata jin muryar data fara kiranta da sunan. Anya ba munafuntar ta akayi ba Sadeeq ya mutu aka raina wayonta aka ce Abubakar ne, anya shima ba yaudararta yake yi ba aka had'a baki dashi zasu raina mata hankali. Bata gama dai-dai tuwa ba taji ya zauna a kusa da ita har
Chapter 39 · 0% Book details