Sashe 21
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
k'ananun words wad'anda basu da wahalar rik'ewa. A k'ofar gate d'in gidan su ya tsaya, ba wani gidane had'add'e ba sannan kuma ba wai gajari bane dai-dai magidanci me rufin asiri da kuma kwanciyar hankali. Suna tsayawa k'irjin INdo ya fara bugawa taji kamar bazata iya shiga ba Nafeesah ta fito INdo ta kalleshi kamar zata yi kuka ya sakar mata murmushi tare da cewa. "Ya aka yi naganki haka?" "Yaya Abbakar jinake inajin tsoro." "Oh toh ai bama cinye mutane kifito mu shiga." Dakyar INdo ta iya fitowa 'yan layin sai kallansu sukeyi suka shiga parking spaces sunzo wani d'an corridor ya janyo hannunta tayi saurin kallansa ya kai fuskarsa saitin tata kamar zai yi kissing d'inta yace. "Idan kina yin haka su Halima zasu rainaki, ki saki jikinki." Yafad'a tare da sakin hannunta, Nafeesah kuwa har takusa shiga ciki sannan ta tsaya suka k'arasa sannan Abubakar yayi gaba sukuma suna bin bayansa. INdo kuwa abinda yayi mata ba k'aramin sake tsuma jikinta yayi ba hakan kuma yasa ta fara mai wata fassara domin a makaranta ana gargad'in suka akan ta6a namijin da ba aure kukayi ba. Da gudu k'annansa suka fito suna musu oyo-yo suka rungume INdo suna cewa. "Yaya Habu itace ko?!" Ya dinga d'aga musu kai yana murmushi yadda INdo da Nafeesah bazasu gani ba. A k'atan falon gidan aka sauke su an baje musu kayan abinci dana sha kala-kala INdo kuwa kamar ta nutse cikin carpet d'in da aka malale falon dashi. Su Mama da Umma suka fito su INdo suka gaidasu har k'asa sannan suka huta k'annan su Abubakar sukayi ta janta da hira suna jefo mata turanci haushinsu ya fara cika ta domin baganewa takeyi ba su kuma a tunaninsu kunya ce take hanata yin magana basu san duk taci ubansu a surutu ba. Sun jima kafin su sauka zasu ci abinci domin tunda Abubakar ya shigar dasu ya koma d'akinsu ya tarar Sadeeq sai shak'ar bacci yake yi da alama ma ko sallan la'asar beyi ba Abubkhr yace. "M twinnie ka kashi kazo mu shiga ciki gashi na kawo maka wadda zan aura kugani." Da sauri Sadeeq ya mik'e cike da mamaki yace. "Are you serious?!" "Yap tana ma ciki gurin su Mama." Sadeeq yace "wai kana nufin kace min zuwa kayi ka d'akko ta, kuma babu wani labari?!" Abubakar yace "Ya daman Ina sonayi surprising d'inka." "Ya nagani toh bari naje nayi sallah sai na shiga, nasan ko wacece wannan toh ta had'u and degree nawa gareta M twinnie?!" "Idan zaka shiga ka gani toh idan kuma labari kake so toh kaci gaba da baccinka." "A'a zanso ganin matarka mana M twinnie." Ya fad'a yana shiga toilet dan shi a tunaninsa Abubakar ya manta dawani batun INdo. Saida ya watso ruwa yayi sallah yana idarwa Abubakar na shigowa Sadeeq d'in ya zura kaya sannan suka nufi cikin gidan, tun daga kan takalma Sadeeq yasan budurwar d'an uwan nasa ta had'u suka shiga tare dayin sallama Sadeeq ya zauna kan kujera ita kuma INdo ta d'an jiya ta kallesa suka had'a ido sam Sadeeq be ganeta har ta kaidashi sannan Abubakar ya kallesa cikin sign ya cewa Sadeeq. "Ya tayi...?!" Sadeeq ya jijiga kai yana kallon gefen fuskar INdo yayiwa d'an uwan nasa alamar yana kashe mai ido d'aya. Dariya Abubakar yayi ganin be ganeta ba yace. "Aisha ce fa student d'inka ta sumaila kauyan Sani Tsefawa secondary school, idan baka gane ba toh INdo malam Hamza ce..." Sadeeq dake zaune sai gashi a tsaye yana mata kallan mamaki. Sai yanzu ya gane domin ga fashin gushinta nan sannan ya fara tuna kamanninta cikin kwakwallawarsa zuwa idanunsa cikin tsananin mamaki yace..... [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...