← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 53

Sashe 3

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuna kaunar iyayanku kuyi mana hak uri. Cewar Indo tana faman tafa hannuwa alamun rok'o,itama Maryam tsugunnawa tayi tana magiya, Dan Allah kuyi hakuri wallahi Indo ce tace muzo mugani ko aljanu ne ku, amma wallahi ni banyi niyar shigowa ba. Shhhhhhhhhhhhh..! Abubakar yayi musu bayan ya d'ora yatsan shi d'aya akan Lip's d'in shi suka had'a idanuwa da Sadeeq suka fara matsowa gurin su yayin da jikin su Indo ya hau rawa kamar an saka musu shock ai kuwa suka fara kurma musu ihu. Iiihuuu..! wayyo Allah a zo a temaka mana zasu kashe mu...!! Kafin kace mene har unguwar ta cika da mutane sai bugan gidan ake amma sunk'i bud'ewa, yaran da suka taho tare da su Indo ne suka yiwa sauran mutanen gurin bayani kan cewar ai su Indo ne suka shiga wai sai sun kallesu. wani dattijo ya kuma buga gidan jin su indo na ihu yayi magana da d'an k'arfi yace, Ku kuwa bayin Allah dan Allah kuyi hakuri ku bud'e su fito ba dan halin su ba. Sai da Abubakar yasa su kamun kunne wajan mintina goma sannan Sadeeq yaje ya bud'e su indo suka kwasa da gudu suka bar gidan,hatta wad'an da suke mak'otaka dashi Sadeeq d'in sai da suka tambaya waye Sadeeq a cikin su yace... Gani nan baba Al-hassan. Wanda aka Kira da Baba alhassan yace, Ikon Allah toh ai kud'in ne dole ku zama abin kallon jama'a sabida ba kasafai ake samun samarin matasa maza 'yan biyu masu matukar kama da juna ba. koni da Al-husain d'ina kafin ya rasu ana iya gane mu amma ko babu wata alama da zata sa a gane ku dole yara suzo kallan ku. Murmushi Sadeeq yayi tare da shafa k'eya yayin da Abubakar ya kalle su sai kuma ya juya tare da komawa cikin d'aki yana tausayin d'an uwan shi akan wannan aikin nashi daya zoyi duk babu sa'a, ba'a makarantar ba ba kuma a garin ba duk babu sauk'i haukan garin yayi yawa. Abubakar da Sadeeq 'yan biyu ne wad'an da ba zaka ta6a iya banbance Hassan ko Husaini ba mudin suna tare sabida tsabar kamannin da suka yi. Hatta tafiyar su, dariyar su, yana yin maganar su sai d'abi'un su ne kawai idan ka zauna dasu zaka iya tabbatar da cewar sun ban-banta dana juna. Engineer Alhaji Salmanu Haruna shine mahaifin su, yana da arzik'in shi dai-dai misali Matan shi na aure guda biyu ne Mama A'i itace uwar gida kuma mahaifiyar su Abubakar da Sadeeq sune yaran Alhaji Salmanu na farko sai kannan su da suke uwa d'aya su biyar Hawwa, Halima, Hamza, Amina sai Khalifa sai ta biyun Umma Fatu tana da yara uku Khaleel, Mubasshir da Rukayya. Gabaki d'ayan zuriar sun taso cikin tarbiya da ilimin boko dana addini dan Alhaji Salmanu tsayayyan mai gida ne da yake tsaye akan matan shi da yaran shi. Wannan kenan.. Indo Aisha d'iya ce a wajan Hamza mai gyaran radio da Inna Mero sai kannanta guda uku Sagiru, Shehu sai Nafeesa. Malam Hamza ya dad'e yana gyaran radio dan da sana'ar yayi aure harya hayayyafa duk da suna matukar shan wahala dan wata rana ma basa samun na abinci sai dai su kwanta haka. Indo yarinya ce k azama ainun domin wanka ma se juma a jum a take yi,shima se an tilastata agaba bayan haka kuma gagarumar fitinanniya ce ga d'an karan tonan fad'a da shiga fad'an da bana ta bane,tana da son wasa hakan yasa koda aka bud'e musu wata primary aka sanyata bata kwaso komai ba sai k'arin fitina da rashin kunya a haka harta zana jarabawar fita daga primary ta wuce secondary yanzu tana aji d'aya ko sunanta da kyar take iya rubutawa shima a karkace cikin rashin tsari, kuma kusan duk haka ajin yake monita ne kawai mai iya rubata sunan shi complete sannan ya rubuta na wasu suma ba duka ba. Gidan su na k'asa ne d'an k'arami wanda shi da kanshi Malam Hamza shi ya gina abunshi yayi d'akuna uku da makewayi katangar tasu gajeriya ce domin idan kai dogo ne to hak'ika idan kana tsaye sai an hangoka hakan yasa duk shirgin da suka kwaso suk'e iya cillashi ko su watsa shi ba tare da sanin koda mutum a wajan ba dan ansha fad'a dasu da mutanen unguwa amma sun kasa denawa har anyi shiru an zuba musu ido. Da gudun tsiya ta shiga gida tana sauke wani uban nishi Inna ta kalleta tare da cewa, Ke kuma lafiya kuwa kika shigo gida bako sallama 'yar nan..?! Inna ta fad'a kasan cewar bata iya fad'in sunan Indo sabida 'yar ta ce ta farko kuma sunan surikar ta ne wato mahaifiyar malam Hamza. cire daddauhar hijjab d'in Indo tayi me tashin hamamin wari tare da cillar dashi a tsakiyar gidan su tace, Wato inna akwai abubuwan kallo idan mutanen cikin birni suka zo nan wai...! Tah fad'a tana zaro idanuwa, kallonta inna tayi cike da takaici ta rasa gane kan Indo tunda aka kawo malam Sadeeq kullum taje makaranta ta dawo da saban labarin da zata bata akan shi dan haka tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta kok'i inna tace, Allah shi kyauta miki 'yar nan, tunda aka kaiki makarantar nan ban tab'a jin kinzo kina yin karatu ba yadda nima zanji dad'i ba sai dai tunda aka kawo sabon malamin ku toh babu ranar da zakije baki dawo da sabon labari akan shi ba sai kace shi aka ce kije ki koyo.. Kai inna ana baki kina k'in k'ar6a. Eh ba zan k'ar6a ba bana so ki rik'e kayan ki. Indo ta kuma gyara zama tare da bugun kanta da alama kwarkwata ce tayi motsi,cikin son bada labarin tace, Aikuwa inna sai na baki labarin nan dan kuwa wallahi har suma nayi aka samin ruwa na farfad'o. Jin abinda ta fad'a ne yasa inna zaro ido tana dafe k'irji tace, Na shiga uku ni Maryama meya faru dake 'yar nan?! A take Indo ta kwashe labari tun daga wanda ta sani har wanda d'alibai 'yan uwanta suka gaya mata ta k'arashe zan cen da fad'in lokacin da suka shiga gidan su shine fa ana bud'e musu ta shigo gida da gudu. Ikon Allah kenan, toh ke dai babu ruwanki dasu..ah to karkije wata rana ki basu haushi suyi miki aika-aika su cuceki Allah ya tsare ba fata ba Toh inna ai na fisu iya gudu wallahi. Yi min shiru wawiya kawai an ce miki wannan muguntar ta gudu ce, ke dai babu ruwanki dasu na gaya miki. Da haka suka dinga magana inna na son fahimtar da ita sai dai kunya da kawaici yasa ta kasa sai faman kwana-kwana take yi. Ita kuma wadda ake wa dama ba wani fahim ta ne da ita ba dan haka bata fuskanci inda maganar inna ta dosa ba. Other half gaskiya ya kamata ka nemi transfer daga wannan gajarabal d'in makarantar, ah!wannan school da kauyan ai sai kaima su maida kai kamar su dan wallahi rayuwa a irin wannan gurin tsab zasu canza ka su 6ata maka hobby d'inka. Kai twinnie God forbid wallahi sai dai ni na canza musu, ni sam basa yi min haka kawai zuwanka ne yasa dan sun ganmu mu biyu shashanci sai kace akan mu aka fara zuwa duniya mutum biyu iri d'aya... Abubakar ya kuma kallon Sadeeq shi tausayin shima yake dan ya san kawai yana zaune a garin ne ba dan yana jin dad'i ba,ta6e baki yayi tare da d'aukar laptop d'in shi ya koma cikin bedroom ya k'agara gari ya waye ya bar garin dan jin shi yake yi tamkar akan k'aya. Mik'ewa Sadeeq yayi tare da d'aukar mukullin motar Abbakar d'in, fita yayi ba tare daya sanar mai ba yayi waje. Can cikin gari ya tafi wani restaurant ya shiga inda yake zuwa cin abinci yayi musu order mai rai da lafiya sannan ya siyo musu drink's masu sanyi ya dawo gidan lokacin ya tarar da Abbakar d'in ma bacci yake kasan cewar sun kunna inji akwai iskar fanka. kallon shi yayi sannan ya fito ya dawo parlor ya fara rubuta lesson plan har wajan la'asar sannan Abubakar ya farka yana fitowa yagan shi zaune gaban shi duk takardu ne da littattafai kawai ya kalleshi yace, "Wai twinnie har yaushe ne ka koma haka? duk ka takurawa kanka ya kamata ka sauya makaranta dan kafi karfin koyar da irin wad'an nan school d'in." Sadeeq ya numfasa tare da cewa, "Meye abin fin k'arfi twinnie ? a gani na tunda teaching nake sha'awa ai be kamata nayi korafi ba." Da sauri Abubakar yace, "Ba anan ya dace da kai ba twinnie kamata yayi yanzu ace kana wata university d'in kana bada lecture's dan kafi can-canta da dacewa acan, amma nan wallahi tsaf zasu nakasa maka ilimin da kakeji dashi ya kamata ka duba magana ta." Kallonsa yayi har ya shige cikin d'aki sannan ya sauke idanun shi, dama tun ba yau ba tun suna k'anana suke da ban-bancin ra'ayi wajan zab'ar samun gurin aiki sai dai shi Abubakar ya cika burin shi yayin da shi kuma Sadeeq be samu zama pilot ba sai aikin koyarwa a university of sokoto amma yak'i tafiya sai ya tafi ya samu a wani secondary school itama d'in a kauye, sai gashi sam baya jin dad'in ta. Abubakar ne ya dawo ya zauna tare da janyo take away d'aya ya fara cin abincin shi, Sadeeq ya kalle shi tare da ture takardun gaban shi yace, "Twinnie wai ya zancen Ummi kuwa ka kuma komawa kun dai-dai ta ko?!" Abubakar yayi murmushi tare da ajiye spoon d'in hannun shi yace, "Bari kawai twinnie ban koma ba sai aikowa gida da mahaifinta yayi wai ance angan mu a tsaye toh idan na shirya na fito. kaji fa? ni ai Ummi bata cika quality's d'in da nake da burin matata ta kasan ce ba dan haka nace a'a ban shirya ba ko ya ka gani?!" Dariya Sadeeq yayi sannan yace, "Kai ma ka tsaya ruwan ido meye ai bun Ummi tsakani da Allah, yarinyar nan fa yanzu s.s 1 zata shiga kuma gata kyakyawa to meye ya rage maka.?!" "Gayu, twinnie ka san ina son mace 'yar gayu mai aji wadda koni idan ina mata magana
Chapter 3 · 0% Book details