← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 53

Sashe 18

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

abata zai had'a a cikin kud'in gyara sannan ta koma aka cire dai-dai size d'inta ta saka suka d'aure mata belt d'in sai ta koma tamkar ba wadda ta shigo d'azu ba. Tese ta sa mata veil bayan ta jera mata ribbon INdo tayi d'as da ita tamkar ba INdo malam Hamza ba. "Wowww nawawoo see this girl ooooh, you look so beautiful my daughter." Ita kanta INdo data kalleta a cikin madubi saida ta sake ta6a fuskarta dan a tunaninta ba ita bace, Madam Gloria ta fesa mata turaruka sannan ta kamo hannunta suka fito Tese sai dariya takeyi. Abubakar na ganin sun fito ya mik'e yana kallon INdo k'irjinsa na mugun bugawa, ita kuma ta kasa kallonsa domin wata irin kunya ce da nauyin sa suka dirar mata a lokaci d'aya. Da kyar Abubakar ya iya kallon madam Gloria yayi mata godiya tare da zaro 15k ya mik'a mata ta k'ar6a sai k'ara kod'a INdo takeyi shi kuma ya juya tare da bud'e mata k'ofa ta shiga ta zauna ya rufe. Cikin tsananin mamaki Nafeesa ke zuro kai tana lek'en fuskarta kafin tace. "INdo..! Koba kebace ne? Nashiga uku, wallahi kece dan ga fashin gohi nan." Banza da Nafeesa INdo tayi domin ita kanta tunda aka haifeta bata ta6ajin ta a wani irin yanayi na cikar kamala ba irin yanzu. Abubakar ya kalleta yana lek'en fuskarta shima yayi murmushi tare da cewa. "Humairah kinyi kyau sosai." K'irjin INdo ya kuma bugawa kanta ya fara sarawa jitakeyi tamkar an sauyata gabaki d'aya, bakinta kuwa ji takeyi tamkar ansa zare da allura an d'inkeshi ta kasa cewa ko uffan ta kuma kasa kallonshi. Kunna motar yayi suka fara tafiya sai magana suke mata shida Nafeesa amma tayi shiru, farin ciki takeyi yau gata cikin rigar da ko a cikin mafarki bata ta6a zaton zata sanya taba ga takalmi d'an ubansu tayi shigar da duk kauyen Sani babu wanda ya ta6ayin irinta. Shin mezata cewa dacta habubakar akan wannan abun dayayi mata, shida ba yayanta ba, ba wani nata ba a'a d'an uwane a gurin wani malamin su..! Saida ya tsaya a wani shago ya siyo musu abubuwan kwalan da makulashe sannan ya nufi kauyen Sani. Daga shi sai Nafeesa kawai suke magana amma ita batayi rigar jikinta kawai take kallo tanajin ina ma salele zaizo yau ya ganta ta zama sabuwa. A k'ofar gida ya tsaya Nafeesa ta fito ya bata ledojin INdo ma tazo zata k'ar6a ya girgiza mata kai sai da Nafeesa ta dawo ya bata harda ragowar kayanta sannan ya kalleta yace. "Humaira kina son yin karatu..?!" Shiru tayi tana faman muzurai, a zahirin gaskiya batada wani sha'awar yin karatu domin tun farko dama batasa shi a cikin tsarin rayuwar taba. Gani takeyi ma yanzu wace makarantar zatayi dan tafi k'arfin tsefawa sabida duk mate d'inta sunyi candy dan haka ma ta kuma cire san makaranta a zuciyarta. Kallonta yayi yaga yanayinta ya canza ya ciro wayarsa yana yi mata photo wannan kuwa harda su style, ya d'an matsa kusa da kujerarta tare da cewa. "Matso toh muyi photon tare." INdo ta matsa suka kusan had'e fuska yayi musu selfie kusan sau biyar yana d'aukar su gaba d'aya sunyi kyau musamman Abubakar dayasan shika-shikan iya selfe. Agogon tsintsiyar hannunsa ya kalla biyar sauran minti uku yace mata. "Humairah zan tafi sai na dawo please take care." Murmushi kawai tayi mai sabida bata san abinda ya fad'a ba bayaga (zan tafi sai na dawo). Ya zaro 5k ya mik'a mata tana kallonsu ta wutsiyar ido tana son k'ar6a tana jin wani iri ya d'ora mata a kan cinyarta ta d'auka zata bud'e k'ofar yayi saurin rufewa tare da cewa. "Humairah baki min godiya bafa zaki tafi, haka akeyi daman." Tayi saurin rufe idanu tare da cewa. "Kayi hakuri inata son yima na manta, angode Allah ya k'ara bud'i." Yace "yauwa kokefa harnaji dad'i, duk wanda yayi miki kyauta ki dinga ce mai angode kinji ko?!" Tace "Toh zanyi sai anjima yaushe xaka dawo garin mu?!" Da sauri ya kuma kallonta jin tana neman ya dawo, cikin wata irin murya yace. "Humairah kina son na kuma dawowa?!" INdo ta d'aga kai alamar eh yayi murmushin jin dad'i sannan yace. "Toh shikenan wani satin zan dawo amma ki dinga kwalliya gashi can na siyo miki kayan kinji..?!" "Toh Nagode ka kaida gida." "Zasuji amma bakice nagaida malamin kuba." Tace tana yatsina fuska. "Ai bayida kirki da kaine bakada kirki amma yanzu shine bashida kirki." "Toh kiyi hakuri ya dena kinga 'dan biyu nane." "Naji na dena kace ina gaidahi." "Zaiji a gaiheda Inna da baba." Yafad'a cikin kwaikwayon maganarsu, ta fita daga motar lokacin su Uwani halilu sunzo gulma, shi kuma yaja motarsa yabar unguwar zuciyarsa na kudurta mai son auranta. *HAJJA CE* [7/3, 10:06 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...
Chapter 18 · 0% Book details