← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 53

Sashe 11

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubakar kuwa yana matuk'ar son Mareeya har hakan ya fito fili ragowar nurses suka fuskanta, wasu suka hakura dashi yayinda wasu kuma suka d'auki tsana da takura suka d'orasa akan ita Mareeyan suna ganin itace tayi wani kulla-kullan har ya karkata wajanta ya barsu. Sosai suka shaku Abubakar har ya had'a su da Sadeeq awaya suna gaisawa hakan ya sake narkar da sonta a cikin zuciyar Abubakar d'in. Wata ranar juma'a ne Sadeeq dayaje makaranta dama duk juma'a yakewa 'yan ajinsa duban tsabta, yana duba farcensu, hak'oransu, mata ya duba kitso maza kuma aski da kuma uniform duk wanda yafi kowa tsafta zai bashi kyauta. Ashe INdo ta samu labari yau yana cikin dudduba su sai gata ta shigo askwane cikin ajin malam Sadeeq ya kalleta cikin tsananin mamaki kamar aljana uniform d'in nata sharkaf da ruwa a haka tasa su gashi tayi wata mahaukaciyar kwalliya kamar wata ifirituwa ta fara tafiya zuwa bencin su Uwani halilu suka matsa mata har ta kusa kai duwawunta k'asa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata wata razananniyar tsawa ya had'a da cewa. "Ke meya kawoki wannan ajin? Wacece ke haka? Daga wane sahun aka zakuloki..?!" INdo ta kalli kan teburinsa taga kayan kyaututtukan da zai bayar sai ta dashare mai jawur d'in hak'oranta domin tunda ta siyi brush da makilin d'in nan bata ta6a yi ba zuwa tayi ta zubesu a gida toh dama ba'a sababa ta k'arasa zama tukunna tace masa. "Haba malam Sadeeq nicefa INdo malam Hamza." "Will you shut up...Nonsence, zoki fitar min daga aji wawuya waya kawoki jss 3? Keda har yanzu kina jss 1 shine yau zaki wani shigo min zoki fita kafin na lahira ya fikijin dad'i." Yayi maganar yana nuna mata k'ofar data shigo ransa a matuk'ar had'e, sai ta fara kallon 'yan ajin d'aya bayan d'aya tare da mutsittsike idanuwa taga dai still sune dai 'yan ajin nasu na da amma ya za'ayi yace wai nan ba ajinta bane dan shi munafukine, tokuwa babu inda zata dan nan gwamnati ta tsaga mata dan haka tayi kicin-kicin da fuska wai taga ko zai kuma cewa tafita. "Ke Aisha ba magana nake yi miki ba?" Ya fad'a yana k'arasowa bencin da take, INdo tayi saurin mik'ewa tana kallonsa tace "Yo toh malam duk fa k'awayena ne kuma 'yan ajinmu ne ya zakace na fita ina zanje ni." Yace "Tallah, koba ita kika fiso ba? And bakin ce bazaki sake suwa tsefawa fa yau kuma wane munafuncin ne ya shigo dake da wasu jik'akk'un kayanki kila ma fitsarin kwance kika yi, oya zoki out kina 6ata mana lokaci." Duk cikin maganarsa babu wacce take k'ona mata rai irin yace tazo ta fita, kuma kallon kayan kyautar tayi kawai sai ta rushe da kuka tana fad'in "Kai malam.. Kai malam, sai da kaga nazo na kusa cinye kyautar nan shine zaka ce natafi ba ajina bane. Toh malam wane ajin zan koma kuma?." Tsananin mamaki ya cika Sadeeq ganin tana kuka, tunda yake be ta6a ganin hawayenta ba sai yanzu haka kurum kuma sai yaji duk ya tsani kansa domin yasan ita d'in mahaukaciya ce ya kamata ya dinga bata kulawa ta wani 6angaran ko Allah zaisa ta gyara wani abun hakan yasa shi juyawa yanaci gaba da duba 'yan ajin har ya zabo mutum shidan da zai bawa kyautar . Yana zuwa kan INdo tundaga kan uniform ya fara rankwashin ta domin haka yake yiwa duk wanda yake da gyara, INdo tayi saurin dafe gurin tana furta. "Kai...kakai...kakai..! Malam da zafifa." Yace "ha..bakin muga teeth naki." INdo da taji yace ha bakin yasa ta bud'e mai tamkar zata cinyeshi yayi saurin matsawa sabida wani hamami dayake tasowa daga ciki yana toshe hanci yace. "Such a stupid hak'oranki zaki nuna min bawai cewa nayi ki hangame min ba." Hannu tasa ta toshe bakin tunawa da tayi lokacin da sukace bakinta yayi yalo ya kalleta yace. "Bazaki bud'e ba saina mareki..?!" Ta d'aga maikai bakinta a toshe da hannunta tace "Malam gara ka marenin da na bud'e ma ballahillazi." Mtwww yaja tsaki dan yasan babu abinda za'a za6a a gurinta, ya kuma matsawa ta baje hancinta tana shak'ar k'amshin turaren jikinsa yace "muga farcenki." Tana jin haka tayi saurin zame hannunta daga baki ta cukwaikuye hannuwan acikin hijjabi tana zaro mai ido ya kuma kuluwa yace "muga kanki..?!" A hankali ta bud'e shi ya kalla tare da ta6e baki ya bar gurin, akwai kitso saidai ya tsofa sosai dan ko tsagar ba'a gani gashi gashin nata jah ne kamar gashin akuya sai dai da ka ganshi kasan zaiyi laushi domin irin me yalai-yalai d'in nan ne, ta kalli Uwani halilu tana sosa hanci tace. "Uwani kin ta6a cin gasar kuwa?!" Uwani ta harareta tare da k'in bata amsa ganin haka yasa tayi mata kallon sama da k'asa tana fad'in "ji banza kina jima ina tambayarki." Malam Sadeeq ya d'akko wani yadi na maza ya mik'awa D'ahiru Miko ya durkusa har k'asa ya kar6a sannan yayi godiya malam Sadeeq yace. "Ku tafawa D'ahiru miko ya samu wannan kyautar ne saka makon d'inkin uniform d'insa sabo ne, yayi aski sannan baya barin farce zak'o-zak'o gashi yana k'amshi babu wari a jikinsa hak'oransa ma sun fara haske.." Aka fara tafawa raf-raf-raf INdo sai k'arayi take da k'arfi har aka gama yi sau biyar yadda ya koya musu INdo bata denayi ba sai da yace "ke inji..!, ya isa haka baki ji yadda suka had'u suka yi nasu ba ne a tare?" Sai a lokacin ta dena amma fa bakin nan a wangale tamkar ita aka bawa yadin. Mace kuma Murja Ashiru ce ta samu ya bata fallen atamfa biyu itama aka tafa mata still INdo sai da ta zarce har wani dak'irewa tayi sai da Atika bawa ta bige mata hannun sannan ta denayi yace musu "Yau Atika bawa tafi ko wace mace tayi kitso harda kunshi, kayan makarantar ta harda guga babu farce ta yanke itama tayi brush." Aka sake tafawa sam INdo bata iya ba da kowa zai denayi amma ita sai ta k'ara. har ya kammala bama ragowar suka koma suka zauna yayi musu nasiha akan tsabta sannan ya kwashi littattafansa zai fita INdo tayi saurin cewa. "Malam...!" Ya tsaya cak ba tare daya juya ba tace, "nima wata juma'ar zanyi duka amma ni hadda (shadda) nakeso ruwan bula kaji ko...?!" Juyawa yayi ya kalleta sannan yace "Toh kiyo amma bake zaki gaya min abinda kike so ba sai abinda nayi niyar bayarwa kinjiko..?!" Tayi shiru bata amsa mai ba yayi tafiyarsa ta zauna tana cewa "kajishi fa, salan kawai a baka abinda bakaso mtww." Babu wanda ya kulata ta mik'e ta koma wajan Atika ta k'arbi atamfar tana gani ji take inama ta tace har ta hango irin d'inkin da zatayi dan taga wani style a jikin Rukayya amarya. Duk wanda aka bawa kyauta sai da taje ta ansa ta gani har ta fara Allah-Allah wata juma'ar tazo itama taci za6e.... *HAJJA CE* [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *9* Still hannunsa na rik'e da nata ya rik'e sai kallon fuskarta yake dan ba k'aramin kyau kwalliyarta tata tayi mai ba, INdo kuma sai k'ok'arin ture mai hannunsa take tana hawaye murya k'asa-k'asa kamar munafiki yake mata magana yace. What's your name make up artist..?! INdo tayi shiru sai tasa ka hijjab d'inta ta sharo hawayen fuskarta duk bak'in kwallin da tayi kwalliya ya wanke hijjabin daga gaba Abubakar ya kalleta sosai shi har lokacin begano taba domin be ta6a ganinta tsab-tsab kamar yau ba ya kuma cewa. "Baby ya sunanki ne.?!" Sai a lokacin INdo ta fahimta ya kalleta ya kuma cewa, "kinga kin goge kwalliyan naki da kuka ki dena kinji ko? Ya sunanki??" Ta share majina da bayan hannunta wanda be rik'e ba ai yana gani yayi saurin sakar mata d'ayan hannun ita kuma ta matsa baya tare da cewa cikin kuka. "INdo malam Hamza." Abubakar ya d'an zaro ido waje kad'an kafin yace. "Zonan gurin." Ya nuna mata inda yake son ta tsaya da k'afarsa, a hankali taje gurin ta tsaya sai dai idanunta nakan tebur din da malam Sadeeq ya ajiye kayan kyautar da zai bada. Tsaye tayi mai k'ik'am sam hankalinta baya kansa shi kuma ya kalleta yana murmushi yace. "Woww sunan Mama na gareki, toh amma ba zaki tsugunna ba kika min k'erere..?!" Da sauri ta tsuguna still fuskarta na wajan kayan, ganin bashi take kallo ba yasa shi maida kujerar sa saitin da idanta yake gurin tayi saurin kallansa ya tsuke fuska yace. "Menene baki yi ba aka fito dake?!" Ta cukwai-kuye hannunta tun kafin ta bashi ansa dan tasan mugune a hankali tana turo baki daya sha bakin kwalli a le6an tace. "Wallahi nayi komai, kawai farce na manta ban cire ba shine malam Sadeeq yace na fito kuma wallahi malam..." Ya zabga mata harara tayi saurin toshe bakinta da hijjab kafin taga ya dena tace. "Kayi hakuri dakta Habubakar mantawa na keyi kace ba sunanka malam ba, amma wallahi nayi niyyar yankewa niko dan naciyo atamfa amma duk saina manta hef (shaf).." "Ohh muga farcan naki.." Ta fito dashi yasha lalle a yatsun ta nuna mai, hannu yasa ya janyo nata yana kallah murya sanyaye INdo tace mai. "Dan Allah Dacta Habubakar kace ya bani ni yanzu ma zan iya cire farcen, dan iyayanka kace ya bani dan Allah kaji..?!" Sadeeq ne yazo gurin ya kalli d'an uwan nasa rik'e da hannun INdo hakan ya bashi matuk'ar mamaki da al ajabi cikin sauri Sadeeq ya zare hannun INdon daga na Abubakar cikin harshen turanci Sadeeq yake mai magana cewa. "Twinnie why na?am i day dreaming or are you really the one holding a village girl hands,and if you have forgotten about it then I haven t ,this villagers are cruel,I don t want them to think something else in their mind ..This is so not you Cikin ko a jikinsa abubkhr ya daga kafada sannan yafara magana, "Habba twinnie sunan Momcy gareta fa shi yasa, gashi kuma tayi kwalliya irin wadda nake so that's y kaga ina iya rik'e hand's na
Chapter 11 · 0% Book details