← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 53

Sashe 35

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. Page *29* "Aisha wannan kuma books d'in waye kike ta lalatawa haka.?!" Cikin rashin damuwa tace, "is my own." "Ooh your own?!" "Yes..!?" "Toh zane-zane kikeyi or what.?!" "Home work nake yi." Tayi maganar tana sake karkad'a biron hannunta, Sadeeq ya zaro idanuwa yana rik'e da ha6arsa kafin ya matsa kusa da ita yanan kallon littafin da take yin rubutun yana jijiga kai ganin note d'in tamkar tafiyar tsutsa wani yayi k'asa wani tsakiya wani sama ya zauna bakin gadon tare da kallon littattafan gurin ya gansu duk na turanci. Karo na farko daya fara zama kusa da ita duk da cewar ba kusa da jikinta ya zauna ba ya d'an bada gap. 'Daukar littafin kusa da ita yazo zai yi INdo tayi saurin janyewa ta 6oye k'ark'ashin cikinta tana faman harhad'e fuska dan bata son ya kushe mata rubutunta, ya ta6e baki tare da d'aga kafad a yana cewa. "Toh furniture's d'in d'akin kike drawing d'insu ko me kike yi hakan?!" "A'a ba d'aya malam Sadeeq, makaranta nake zuwa kuma acan ake koya min wannan karatu." "Ooh which school ne suka iya d'aukarki a haka Aisha..?!" Cikin jin haushin sa INdo ta tashi zaune tana kuma 6oye book d'inta tana rurufe idanuwa tace. "Dan Allah malam Sadeeq ka kyale ni haka nayi abuna ka takura min, neman ilimi naje yi sai yanzu Allah yayi zanyi, lokacin da marigayi dacta yana da rai bashi da wani buri daya wuce yaga nayi karatu amma kai sai afkin yiwa mutane gori toh nima na shiga school yanzu zan zama tauraruwa wata rana so what.?!" Sadeeq ya tsaya kallonta, sosai tayi k'iba tayi bulbul da ita tayi fresh, duk da Cewar sleeping gown ce a jikinta kuma me d'an kauri hakan be hana bayyana yadda cikar halittar k'irjinta bayyana ba, Sadeeq ya d'auke kansa tare da ta6e bakinsa yace. "Kinyiwa kanki gata kuwa Aisha, sai dai nasan zaki sha wahala tunda ba iyawa kika yi ba tun farko sai yanzu ne kika fara, shin waye ya kaiki school d'in and waye yake biya miki kud'in?!" "I am, kasan ance sa kai yafi bauta." Ta fad'a tana jin tsoran kartaje ya gwasaleta yace ba haka zata ce I am ba, sai kuma taji yace. "Good hakan ma yayi kyau, but zan cigaba da biya miki ai ilimin yana da dad'i nan gaba zakiji dad'insa idan kika yi." "No kabar abunka zanyi abuna da kaina, ko ka manta sabida rashin Ilimi na yasa kace ba zaka tafi dani inda kukaje da Fateema ba? Hmm! Allah yaji k'an dacta na, cewa yayi wallahi babu inda baxai iya shiga da niba dan har gaban Obama zai iya zuwa dani kuma yace matarsa ce. Ka tashi ka tafi ka kwanta ni bacci nakeji." Tayi maganar tana share hawayen daya fad'o mata. Kallonta yayi tsab yaga ta tsuke fuska bayan ta goge kwallar sannan yace. "Aisha ki lalla6ani, wallahi Zan iya hanaki zuwa school d'in inga ta tsiya dan dama baki gaya min ba ai kika fara zuwa." Tace "lallai malam Sadeeq, ai wallahi tallahi sai dai ka sakeni in tafi gida dama baka sona nima bana Sanka kaga sai kaje kaji da matarka Fateema nima inje inyi karatuna so what." "Wato har yanzu baki da kunya ko Aisha? Wallahi zaki sha mamaki na." Ya fad'a tare da barin d'akin cikin sauri ya koma falo yana jin wani mugun 6acin rai, ko wane munafikin ne yazo ya gaya mata wannan maganar, wannan yarinyar idan ta kuma wayewa sai tafi k'arfinsa gara ma ya togeta daga makarantar ya sanyata islamiya ko zata dinga rissinawa. Washe gari yana farkawa ya fito yayi hanyar bathroom d'in tsakar gida, yana zuwa yaga kaji gaba d'aya gurin ya zama tamkar dama dansu yayi, cikin tsananin mamaki ya fara tunanin toh kajin waye ta kar6o haka dan wulak'anci ake 6ata mai gida. A fusace ya koma ciki ya nufi bedroom d'inta, tana kwance sai shak'ar bacci take tayi d'ai-d'ai da ita books d'in wasu sun fad'i k'asa wasu kuma ta dannesu ya k'arasa kusa da ita cike da masifa zai tashe ta yaga abunda yasa shi saurin shigewa toilet d'inta yana dafe k'irjinsa. Ya dad'e a tsaye kafin yayi alwala ya fito beko kalleta ba ya fita falo yayi sallah, yarinyar akwai d'aukar hankali komai nata a wannan stage d'in ya cika yaja tsaki tunowa da yayi sanda take zuwa da yagaggun kaya ya kwanta akan doguwar kujera yana sauke numfashi. Jiyo motsinta yayi sai da ya d'an dad'e har gari ya fara wayewa sannan ya mik'e ya shiga cikin bedroom d'in nata. Tararwa yayi tana k'ok'arin fitowa suka yi karo da goshinan su INdo ta dafe gurin tare da fad'in. "Kai-kai-kai..!" Shareta yayi domin shima sauran k'iris yayi wai-wai-wai sabida tsabar zugi amma ya maze. "Ke meye wancan a bayin waje.?!" "Ina kwana?" Itama ta fad'a kafin ta bashi amsar daya tambaye ta, a ciki ya amsa bata damu ba tace. "Kaji nane." "Wai Aisha haka kikeyin duk abinda kika ga dama ne? Yanzu me kikeyi da kaji.?" "Masu kwai nefa malam, idan suka yi kwai nikuma sai na siyar, ance macen da bata sana'a aurace toh ni Ina yi kuma da kud'ad'an na shiga makaranta nayi kud'in napep. Malam tunda ka dawo baka ce INdo sau nawa kikayi rashin lafiya ba amma sai tambaya ta kakeyi abubuwan k'aruwata." Shiru yayi domin tafishi gaskiya kuma sam beyi tunanin tambayar tata ba dan haka a wannan maganar yaji kunya, amma dan ya raina ta sai cewa yayi. "Toh dama ke kina rashin lafiya ne? Naga tunda ban ta6a jin ance kinyi cuta ba, kuma da kinyi toh Abba zai gaya min." Shiru tayi ta shiga kitchen, indomie ta jik'a sannan ta jajjaga kayan miya ta ajiye tare da komawa cikin d'aki yana zaune a falo yana waya da Fateema ta sharesa dan sam batajin haushi bare ya d'aga mata hankali. Sai da ta dubi lokaci tasan indomie d'in ta jik'u sannan ta shiga kitchen ta soya ta dafa tea ta kawo kan center table ta ajiye da kofu na guda biyu ta zauna tare da cewa. "Ga abinci malam Sadeeq." Lokacin sun gama waya yana chatting ya kalleta ya kalli agogon dake kafe a falon yaga k'arfe bakwai sauran minti uku, yanzu ne za'ayi breakfast sai kace ba yanzu aka tashi daga bacci ba yace. "Tun yanzu ake yin karin kumallo.?!" "Eh ai garin ya waye malam Sadeeq me zamu jira." "Aci lafiya toh." Ya fad'a ta kallesa cikin mamaki sannan ta fara had'a tea d'inta, ta iya cin abincin kuwa kad'an kad'an harta gama ci yana satar kallon ta. Tana gamawa taje ta fara dafa zo6on ta kasan cewar ranar Monday ce batada school ta wanke ayarta tana jiran lokacin da almajirinta zai zo ya kai mata markad'e. Shima Sadeeq bacci yayi yana jiran lokaci yayi ya tafi gidan Fatima yayi wanka dan zaije lecture. Bata tashesa ba sannan duk batasan zai fita ba domin be sanar mata ba har tara da kusan kwata sannan ya farka yana duba agogo yaga har lokaci yayi da sauri ya mik'e ya d'auki mukullin motarsa, beyi mata sallama ba kawai sai tashin motarsa tajiyo taja tsaki sam malam Sadeeq bashida mutunci a jerin da ta sanya shi kenan. *** Yana zuwa gidan Fateema yayi wanka ya shirya ya tafi, around 12:30pm ya dawo, cikin murna ta tare sa tare da rungumeshi ya d'agota yana cewa. "Akwai bayani baby na zauna ki gaya min." Sakinsa tayi ta k'arasa kan TV stand ta d'akko mai wata takadda, bud'ewa yayi ya karanta tare da zaro idanuwa yana kallonta cikin murna ya kuma rungumeta yana cewa. "Woww babyna am so much happy wallahi, kin zama malama sai yau Allah yayi." "Aikuwa baby kaji yadda naji kuwa, anjima zanje gidan Aisha idan zaka tafi please zanje kaga mun jima bamu had'u ba." "Toh kinsan itama ta koma school fa." "Kai baby shine koka gaya min sai yanzu danace zani gidan? Sadeeq yace "A'afa nima sai jiya naji kuma kinga ai ban zauna ba sai yanzu, kinga bani abinci naci." Tashi tayi ta shiga kitchen yayi farin cikin samun aikinta sosai domin yana son abinda take so, yana kuma son farin cikinta. Egg into egg ta kawo mai tare da kunun gyad'a ta zuba mai yasha madara ya zauna a hankali ta dinga bashi harya cinye yasha kunnun sannan suka ci gaba da soyayyar su tamkar babu gobe har mantawa suke yi da matsayin INdo. Bayan yaje gidan Mama ya dawo sai ya d'auke ta suka tafi, gidan cike da masu siyan zo6o da kunun aya wasu na fita wasu na shiga inji yana tayi mamaki ya cika ransu sai da suka shiga sannan suka tarar da ita a zaune gaban k'atuwar kula duk wanda ya bata kud'i saita bud'e tabashi ya tafi, Sadeeq ya shiga ciki ransa a mugun 6ace shin yarinyar nan meta maidashi ne, wato ma ashe harta zama big hajiya besani ba Allah ya kaisu dare sai ya 6ata mata rai. Sosai suka yi hira da fateema ta yadda har ta gano lallai itace star a gurin Sadeeq, anayin magariba ya maida ita gida wajan k'arfe goma yazo gidan INdo lokacin tana zaune a falo tana kallon film d'in Basaja na farko. "Ke Aisha daman haka kika mayar min da gida tamkar gidan kallo? Maza da mata su dinga min strolling a ciki?!" Tayi shiru ya kuma harzuk'a ta kuma yi mai shiru ganin yana masifa yasa ta cewa. "Wai malam me yasa ka tsaneni ne? Nifa kamar yadda bakai kace kana sona ba haka nima bance Ina sonka ba. Yanzu da yake ita Fateema matarka ce ta so ai d'azu tazo ta nuna min takardar fara teaching d'inta kai da kanka ka kawo ta sai ni da nake sana'a a cikin gida da kud'ina amma ka dinga min fad'a kana Sa min ido? Toh ka sake ni dan Allah ka gani idan bazan rayuwa ba." "Ni zaki cewa na sakeki Aisha? Toh bazan sakeki ba kuma karna sake ganin wani yaro ko yarinya sun shigo min gida." Yana kaiwa nan ya
Chapter 35 · 0% Book details