← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 53

Sashe 46

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *36* Gurin d'ayar nurse d'in ta k'arasa ta bawa baby boy d'in kafin ta dawo gurin ta kalli Sadeeq dake shafar kan INdo yana hura mata iskar bakinsa ganin bata bud'e ido ba. "Angon k'arni leave us please kafin a gama shirya ta." Da kyar Sadeeq ya iya yin magana ba tare da ya kalli nurse d'in ba yace. "Ki fara duba ta tukunna naga tayi haka bata k'ifta idanuwa sosai." "Ah karka damu wannan ba wani abu bane ba, kawai wahalar haihuwa ce kad'an bamu guri tunda kaima ka bamu gudun mawa." Tashi Sadeeq yayi yana kallon INdo wadda idanunta ke a rufe sannan ya fita. Maman Sayyid mak'ociyar su da suka zo tare ta kallesa tana zaune ta mik'e duk da cewar tajiyo kukan jariri tace. "Malam Sadeeq yayi ita d'in?!" "Sun ce zasu gyara sune but ni banga ita Aishan tana wani abu ba da zai nuna min cewar komai normal ba." "Insha Allah komai lafiya lau karka damu shi yasa banso ka shiga cikin ba naso ace kawai sai dai a kiraka ace kazo ka gansu." Numfashi yaja tare da yi mata godiya sannan ya wuce masallacin dake cikin asibitin kasan cewar anata kiran sallan asuba. Kafin ya dawo daga massalacin an gama kintsa su duk da basu zo da kayan haihuwa ba, nurse d'in da ta k'arbi haihuwar tana siyar da kayan babies ta sanyawa yaron ita kuma INdo ta bata sabon zani wanda shima itake siyarwa ta d'aura tare da bata maternity pad da pant. Resting room aka maida su Maman Sayyid na zaune kusa da ita tana mata barka INdo kuwa ji take wani girim-girim ganin cewar wai yau itace ta haihu ga d'ama har tana bashi yana shi. Sadeeq kuwa sai da ya gama sharara addu'a sannan ya fito daga massallacin har gari ya d'an fara yin haske. Yana shiga reception yaga Fateema tana kalle-kalle tana juyowa kuwa ta ganshi dai-dai lokacin nurse ta fito ta nuna mai d'akin da aka kaisu. "Baby ina kwana? Ya su Aishan?!" Ta fad'a tana kallonsa kai da ka ganta kasan itama tunda ya sanar mata suna asibiti bata samu wani ishasshen bacci ba. Hannunta ya kama ganin babu mutane suka shiga cikin d'akin da su INdo ke kwance Maman sayyid na ganin su ta mik'e daga bakin gadon tana musu murna. Rufe idanuwa INdo tayi dan wata irin kunya takeji azo aga ta haihu. Yaron Fateema ta k'ar6a tana kallonsa yana ta bacci yasa yatsansa babba a cikin bakinsa, ta k'arasa wajan Sadeeq dake zaune a wajan INdo ya rik'o hannunta yana murmushi ganin yadda tak'i bud'e ido. Jaririn ya kar6a yayi mai hud'u ba sannan ya ciro wayarsa, su Mama ya kira ya sanar dasu yayin da Fateema ta kuma kar6an yaron ta zauna kusa da Maman sayyid. Yaron jawur dashi me kyau k'irjinta ya dinga bugawa tana dannewa sabida jinsa take inama daga nata cikin ya fito sai dai baza ka gane hakan ba sabida tayi nasarar fin k'arfin zuciyarta. "Wai cutie wa kikejin kunya a gurin nan da kika k'i bud'e idanuwanki.?!" Kad'a kai tayi still idanta a kulle yayi murmushi tare da mik'ewa ya fita. Gurin doctor yaje dan yana son a basu sallama su tafi gida dan kar a cika asibitin. "Mu wuce gidan Mama Fateema." Ya fad'a bayan ya dawo d'akin. Da sauri INdo ta juyo tana yin kamar zata yi kuka tace. "Gidan Mama kuma? Ni dai wannan karan baza ni gidan Mama ba can gida za'a maida ni." "Aisha wane gidan za'a maidake bayan haihuwar fari ce.?!" Sadeeq ya tambayeta bayan ya mik'ar da ita zaune. "Sani, ni dai can zan tafi gaskiya." "Au lallai gidan namu ne bazaki zauna ba?!" Shiru tayi tana tutturo baki su Fateema suka yi dariya kafin tace. "Gaskiya ranka ya dad'e a al'adance haka ake yi, a kaita gida har tayi arba'in ko sittin sannan sunyi kwari ita da baby sai a dawo dasu." "Haka ne kam." Maman sayyid ta sake gasgata zancen, Sadeeq ya shafa kai lallai akwai kwarbai kenan duk da ba zama yake yi ba ai zai so ya zauna dasu ko na d'an wani lokaci ne tayaya zai bari su wani tafi kauyan Sani. Account number d'in nurse d'in ya k'ar6a dan zai tura mata kud'in kayanta sannan ya siya magungunan me jego suka wuce can gidan INdon kasan cewar tak'i yadda ya kaita gidan Mama wannan karan da hankalinta dan haka bazata yadda taje gidan sirikai wankan jego ba. Suna komawa kuwa 'yan uwa suka fara zuwa dole tasa Sadeeq kwasar yanashi-yanashi na gidan ya tafi dasu gidan Fateema. "Allah sarki, dama rabon wannan yaron ne Allah ya d'auke Habu. Gashi daga tafiyarsa har Allah ya bada arzik'in yaro zuk'e-k'e tubarkallah." Cewar k'anwar abban su Sadeeq da tazo ganin d'ah. Hakama duk mutane suka fad'a duk wanda yaji labarin haihuwar wanda hakan sai da yasa INdo yin kuka sabida surutun mutane da tada mata da baya. Haka aka dinga zarya zuwa gidan INdo da nufin idan anyi suna za'a maida ita sani bayan Mama ta nunawa Sadeeq amfanin komawar tata tunda tafi son can. Ba k'aramin k'ok'ari Sadeeq yayi ba wajan ganin ya fita kunyar mejego da baby harma da mutane, Fateema ma be barta haka ba sai da yayi mata na fitar suna sannan itama da su Ummanta sunyi rawar gani sunyi musu kayan barka tamkar ba kishiya ce ta haihu ba. "Cutie me jego, naga alamar haihuwar nan wata wawuyar kunya ta sanya miki why?" INdo ta tura mai baki ya sanya hannunsa yajasa tayi 'yar k'ara tare da d'an dukan hannunsa. Rungumeta yayi kafin yace. "Toh me ake buk'ata na gobe wanda ba'ayi ba.?!" "Ba komai hakan ma mun gode." "Toh gobe dai nasan ganinki zai min wahala sabida mata dan ba shigowa zanyi ba, idan ma kuna son wani abun ki kira Mubasheer ko khaleefa sai ki sanar musu." INdo ta kallesa, wani irin tausayinsa takeji sabida ganin hidimar da yayi tundaga kan abincin sunan da za'aci zuwa kayan rabo na sunan da ragunan da za'a yanka ga kayan barka dayayi musu yace. "Allah yasa ayi taro lafiya cutie, please karki fushi da kowa kinga duk wanda kika gani zuwa yayi dominki domina domin marigayi infact dai kowa yazo ne dan tayamu farin cikin samun k'aruwa. Na tafi sai gobe zuwa dare zan samu mu had'u." Kai ta d'aga sannan ya juya zai tafi, da sauri tasa hannu ta rik'osa sabida wani sassanyan sonsa daya kuma shigarta a d'an tsayuwar da suka yi. Rungumesa tayi shima yasa hannu ya rik'ota yana shafar bayanta murya na rawa yaji tace. " *I love you* Sadeeq forever, I'm also wishing you all the best in your life. You are always by me, to share simple joys and each Nd every need and now with out your loving presence I'm very lonely indeed I love with all my life my husband..." A yadda yaji tana fitar da words d'in ba k'aramin tsumashi suka yi ba, a hankali ta dinga jerosu dan ba k'aramin k'ok'ari tayi ba. K'ok'arinta da kuma son ganin tayi abu yake k'ara sonya shi cikin k'aunarta, ya d'ago da fuskarta cikin lumshe ido ya zura bakinsa cikin nata. Kissing juna sukeyi cikin wani irin shauk'i har Sadeeq yaji yana neman fita a hayyacinsa sannan ya kyaleta da kyar ya shafi fuskarta sannan ya bar d'akin da sauri sabida yasan mutane na nan sun sawa d'akin ido suga mintuna nawa zaiyi a ciki. 'Yan saye duk sunje da 'yan uwan Inna daga dawakin tofa su Uwani, Sahura, Rukayya, su Maryam haka 'yan kauyan sanin nan suka yo mota guda suka zo duk da ance su bari zata dawo amma wasu suka ce ai daman basu san gidanta taba dan haka sai sunje. Washe gari suna yaro yaci sunan Abubakar dan haka ko ajikin kalandu da key holders da sauran abubuwan da akayi aka sanya mai Abubakar A (Ayman) wanda Fateema ce ta za6i lak'anin yace wa INdo yana son ta bari a sanya mai tunda dama shima uban sunansa ne dan ayi mata kara. 'Yan kauyan nan an samu shinkafa dasu zo6o lemukan jarka da sauransu suka dinga lodawa cikin jakunkunan su, gidan ya cika mak'il da al'umma su Xoxo sai nan-nan ake da little Sadeeq (ayman) duk nacin yayya Nabee ta hanata d'aukarsa sai dai ta kallesa a hannunta. 'Yan grps da fad'ar yawansu bazai musaltuba suma sai salfie suke da mejego dan a samu na sawa a status da dp, su Sis Mom s/fulani, princess meenat, Olo, aunty jidda musa, mmn ansar, ummi k.d, mmn sadeeq aunty baraka, yayya Ummi s/fulani aunty Fatee, sis Ummi A shitu, Heedah, Muhmeelat, redbutterfly, B s fari, meela adeel, ummul m, mrs splined (ko? Sunan ne na 'yan gayu Allah yasa na iya rubutawa dai-dai lol) su Sum-Q, Kaumi shaddad, matar shehi, my Halymah, (yasin da yawa kuyi hakuri dan idan nace zan jeroku ta6...) Duka masoyan INdo da Fateema duk sunje kuma sunci sunsha alhamdulillahi taro yayi sweet mejego an yi fitar suna ta kece raini. Yamma nayi 'yan sumaila suka kama hanyar komawa bayan sun jajjada ma INdo cewar ta taho musu da naman sunan su. K'arfe tara na dare Sadeeq yazo k'ofar gidan yana fitowa daga mota mutane dake wajan suka dinga mai barka fuskarsa cike da farin ciki. "Yaya Sadeeq kenan kwana biyu." Yaji an fad'a cikin nok'e murya, kallonta yayi bayan ya zare glass d'in idansa. Sanye take cikin wani fitinannan material anyi mata d'inkin riga da skirt sun d'ameta sosai, gashi kwan lantarkin k'ofar gidan ya haske su ya zabga mata harara cikin tsuke fuska yace. "Chuchu wai banace ki dena yin irin wad'annan banzayen d'in kunan ba? Wallahi Zan je na samu uncle Ahmad d'in wata k'ila baya lura da yadda kuke rayuwarku." "Kai Yaya Sadeeq yanzu nan meye na rashin dai-dai a cikin rayuwata..?!" Tayi maganar tana d'aga mayafin jikinta, tsaki yaja tare da kara wayarsa a kunne taji yana cewa. "Cutie lalla6o kizo waje ina mota." Mayar da wayar yayi cikin aljihu tare da komawa cikin mota chuchu ta
Chapter 46 · 0% Book details