← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 53

Sashe 49

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *39* Tunda Sadeeq ya koma gida be sanar da kowa zancen da suka yi da INdo ba kasan cewar baya son duk wani abinda zaija ayi mata gori akai ba. Gidan k'anwarsa Hawwa yaje suka yi magana hakan yasa duk abinda ya siyo ita yake kaiwa ga shirin gidan da ake yi mata wanda zata koma. Cikin kwana biyu ya gama had'awa washe gari ana sauran kwana biyu INdo ta dawo yasa aka kai hawwa gidan su INdon takai kayan. Sosai aka dinga murna ana yiwa INdo barkar cewar mijinta ya fitar da ita kunya da kayan da babu wacce aka ta6a yiwa kowacce mace irinsa a kauyan. Shiri tayi sosai ciki da waje Rukayya ta kawo mata kayan INdo ta sake yin wani sassanyan kyau sam bata bari a sauya mata ak'idar da take da ita dan yanzu a kauyan akwai 'yan matan da suke kwaikwayar shigarta da kwalliyarta har yafa mayafi ma. "Gaskiya Fateema kina da hakuri, ki duba ki gani a cikin shekara d'aya da auranku kishiyarki tayi zaman gidaje gashi yanzu mijinku d'aya amma zata koma wannan uban gidan na alfarma ke kina wannan duk da cewar shima yana da kyau amma nata yafi girma da kuma kyau ya kamata kema kiyi bori wallahi asan yadda za'ayi dake." Cewar wata malama da suke k'awance da Fateema tun zuwanta school d'in. Numfasawa Fateema tayi tana jin k'irjinta na bugawa zuciyarta na zafi dan ta tabbatar da zancen aunty Hafsat gaskiya ne, gashi uwa uba ita bata haihuwa duk da bata fitar da rai da rahamar ubangiji ba a kan samun ciki. "Amma ni ina ganin ba wani abun d'aga hankali bane Hafsat ganin dama tun farko a cikinsa ta fara zama, karki manta gidan mijinta ne na farko kafin tazo mu had'e. Kuma a k'ishin-k'ishin d'in da naji cewar an bashi gidan kinga dan ya mayar da ita baxan d'aga hankalina ba tunda itace ta fara zama a cikinsa." "Lallai Fateema toh ai nan gaba na san zaki gane abinda nakeso ki fahimta." Murmushi tayi kawai bata son nuna hassada akan lamarin tunda taga wanda ya narka kud'in yayi abunsa Allah be barsa yaji dad'in da ya tanadarwa rayuwarsa a cikin gidan ba. Idan ta tashi hankalinta akan abun itama Allah sai ya d'auke ta aga ta tsiya tunda kamar yadda Ummanta ta fad'a auran Sadeeq da Aisha Had'in Allah ne. Shiga yayi gidan ya tarar tayi tagumi sam ba taji shigowarsa ba sai tsayuwar sa taji Sadeeq ya zauna a gefenta yana kallonta. Murmushi tayi mai sai dai iyakarsa le6anta kasan cewar ita kanta taga yadda yake rawar k'afar dawowar matarsa dan yakan iya gaya mata zata dawo kusan sau biyar arana duk shigowa sai ya gaya mata hakan yake bata mamaki har take tunanin ko yanzu ya dena sonta ne, duk da cewar be sauya mata ba yana nuna mata soyayya fiye da tunanin me tunani. "Baby tunanin me kike yi haka?" "Babu komai baby kawai ina tunanin rayuwa ne." "Hmmm da alama dai zaman kad'aicin nan ne yasa ki shiga tunani, toh na dawo kuma bazan fita ba yau ina tare dake soyayya zamu yi." Yayi maganar yana rik'ota yana shak'ar k'amshinta, ita ma tayi k'ok'arin Kawar da abinda yake damun cikin ranta. "Kai baka gajiya da aiki ne baby?" "Ehmm kinsan ai ked'aya ce yanzu, kuma duka duka yaushe na dawo ai kinga nayi k'ok'ari baby." Dariya tayi tana shafa kanshi ya lumshe idanuwa. Wato mata biyu Lafiya ne daga nan kayi nan babu fargaba bare tashin hankali dole maza suyiwa Allah godiya daya basu wannan damar. Sai gaf da magriba ya samu ya fita bayan sallan isha'i suka yi waya da INdo sannan ya shiga gidan ba tare da Fateema ta gane sunyi ba. washe gari ya tafi Sumaila kauyan Sani yaje ya d'akko matarsa. Yana zuwa ya buga mata waya ba'a d'auka ba sai gani yayi Sagiru ya fito, gaisawa suka yi sannan ya sanar masa cewar tana wanka Sadeeq yace ba komai sannan Sagiru ya koma gidan. Tana fitowa ta buga mai ya katse ya kirata da kanshi dan shine yafi can-cantar yin hakan ba itaba. "Cutie meye nayin wanka, da kin bari idan mun koma gida sai muyi tare." "Hahaha..lallai a haka kake son na bar Sani zuwa cikin gari ko? Ban yadda ba gashi na fito kaya kurum zansa sai mutafi." "Shikenan ai tunda abun 'yar haka ne, ki turo a kawo min yaro na mu fara gaisawa nayi missing d'insa." "Okey shi zaka fara gani ba niba ma ko?shi kenan bari a kawo shi sai ku tafi ni saina zauna a gidan." "Wayyo cutie ki rufamin asiri I can die idan kika k'i bina Zuciya ta zata iya shiga rud'ani zan iya rasa nutsuwa ta. Cutie kin zamo wani jego a cikin rayuwata Ina sonki dan zan iya cewa nafi m twinnie kaunarki Ina jin zuciyata na bugawa a duk lokacin dana tuna cewar bani na fara nuna miki soyayya ba but ki yadda cewar ni d'in ina wahala a cikin raina da rayuwata idan bake a kusa dani, please kiyi sauri ki fito mu tafi dan Allah." "Gani nan fitowa barima a fara fito da kayan namu." Tana fad'a ta ajiye wayan sannan ta lek'a tsakar gida ta kira su shehu suka fitar da kayansu. Tsab INdo ta shirya Nafeesah ta shirya Ayman sannan ta fitar dashi, sai da suka gama shiryawa ta fita kallansa tayi ta glass d'in motar tare da cewa. "One minute." Mak'ota suka shisshiga suka dinga yi musu sallama har sai da suka zagaye unguwar sannan suka koma Sadeeq ya gaida Inna sannan INdo suka yi sallama da kowa na gidan suka shiga mota Sadeeq yaja zuciyarsa shar daya juya yagan su sai yaji wani farin ciki yana kuma ratsashi. "Cutie me d'ah, wai ke dan Allah bakya mamakin hakan?" "Bana yi, kai da ace fa marigayi be d'akko ni daga Saye ba da inajin yanzu 'ya'yana biyu ko uku da wani saurayi na salele." "Toh naji abar maganar waye wani salele ba ko dad'in ji. Cutie nayi missing d'inki amma ke da alama kamar bakiyi nawa ba." "Abu Ayman kenan, karka fad'i haka domin zaka zalince ni. Kawai ba yadda zanyi ne ko na nuna babu yadda zanyi tunda ko a gidan ka na zauna dole baka nan amma nayi missing dinka dan ma akwai Ayman ina kallonsa Zuciya ta na ganin kamar kaine shi yasa kaga banyi ramar rashinka ba." Dariya yayi hannunsa na ta6o k'afar Ayman, haka suka dinga hirar yadda suka yi rashin juna har suka k'arasa k'ofar gidan marigayi wanda zata ci gaba da rayuwa a cikinsa. K'irjinta ne ya dinga bugawa Sadeeq yaje ya bud'e gate ya shigar da motar duk yana ganin yadda ta sauya jikinta yayi sanyi hannunta dafe da k'irjinta idanunta a rufe. Hannunsa INdo taji a wuyanta hakan ya sake tayar mata da hankali kawai sai ta sakar masa kuka mai sauti. Ayman ya k'ar6a kafin yayi wani abun su Haleema sun fito suna musu oyo-yo kasan cewar suna ciki sune 'yan taryar su. "Cutie ya haka? Kuka? Ohh ya subahanallahi danasan zaki kuka da wallahi baxan yadda na kawoki gidannan ba, cutie bakya sona ko? Please dan Allah kiyi shiru bazan iya barin ki fita daga motar nan ba alharin kina kuka dan kinga mun shiga nan gidan ba. Ki dinga sawa a ranki nine Abubakar Sadeeq gaba d'aya ki tuna cewar kina da irinsa kamar yadda nima nake ganinki a matsayinsa please." Share mata fuska yayi sannan yasa hannu a baya ya d'akko jakarta ya zare powder da kanshi ya shafa mata ya gyara mata fuskar ya sakar mata murmushi tare da cewa. "Kinfi ma kyau yanzu da nayi miki kwalliyar kin ganki kuwa Son Sadeeq k'in wanda ya r asa zuk'i..." Dariya yaga tayi sannan yayi unlock d'in motar su Haleema suka bud'e tana kar6ar Ayman tana cewa. "Wai toh me kuke yi a motar kuka dad'e aunty Humaira." "Toh gulmammiya ina ruwanki bana son saka idofa." "Sorry broth sannun da hanya." Shareta yayi yana hararta INdo dasu Aminatu suka shiga ciki shima yabiyo bayansu. Kujerun d'ayan falon na ciki wanda ba'a shiga su aka dawo mata dashi falon farko kasan cewar da nata aka kai mata can gidan Sadeeq dining room d'inta yana nan tad'al-tad'al tayi fuskarta nason yin hawaye amma murmushi kwance a fuskarta lokacin da take tuno yadda suka yi rayuwa da marigayi,Sadeeq ya shiga tare da kama hannunta ya nufi bedroom su Haleematu suka zare idanuwa hannu rik'e da ha6a sannan suka ta6e baki. Suna shiga ya jata jikinsa suka tsaya wajan madubi yana kallonta. Hannu ya d'ora saman k'irjinta yana wasa dashi bakinsa saitin kunnanta yace. "What happen to my cutie angel ne? Aisha I love you but naga ke har yanzu akwai marigayi a cikin zuciyarki kin kasa sanyani a ranki why.? Numfashinta na sama-sama sabida yadda taji yana mata murya a sark'e tana narke mai sabida yadda k'afarta take neman kasa d'aukarta tace. "Wa yace maka baka cikin raina? Shin duk yadda nake cewa kana cikin raina kazama ni nazama Kai duk a tatsuniya kake d'aukar su?" Juyo da ita yayi yana kallonta yace. "Na kasa ganewa but prove me now." A hankali ta sanya hannu a wuyansa ta sargafo shi tare da had'e hancinsu guri guda cikin salo ta zuro bakinta cikin nasa Sadeeq yayi saurin kar6ar sakon tare da rik'ota shima. Kukan Ayman ne ya sanya suka tsaya da abinda suke yi jin kamar hanyar d'akin aka yo dashi, sadeeq na matsawa sai ga Sajida da Ayman tana cewa. "Aunty Humaira wai kuka yakeyi inji yayya Haleema." Kar6arsa tayi sannan ta fita Sadeeq ya zauna a bakin gado yana cewa. "Wallahi munafincin Haleematu ne dama naga take-taken su nasan ganin gulma." INdo tayi dariya tana k'ok'arin ba Ayman.... Sadeeq ya mik'e yana cewa. "Bari naje na maida su gida bana son kinibibin yaran nan." "A'a dan Allah ka rabu dasu kana ganinfa ko gaisawa bamu yi ba." "Yanzu cutie kin fison su zauna akan ni na zauna?!" "A'ah ba haka nake nufi
Chapter 49 · 0% Book details