← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 53

Sashe 10

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

makaranta salan yaga jirwaye ya hanaki...? A jikin hammatarki zaki fesa.!" INdo tayi yadda ta gaya mata sannan tace. "Sai nazo kawo miki kayan da zan samo Rukayya..." Tayi dariya itama cikin jin dad'i da fatan alheri tace "Toh INdo Allah ya baki sa'a sai kun dawo." Gida ta shiga yau ko karin kumallo bata tsaya yi ba sabida kar bakin yayi daud'a tayiwa Inna sallama tabar gidan yau harda littattafanta da suka yayyage tazuba a leda ta tafi burinta yau ta samu atamfar ko ya bata wani abun da zata dinga alfahari dashi, yau sai da ta riga kowa a makarantar zuwa principal ne kawai da masu kula da makarantar bata riga ba taje ta zauna kusa da farkon aji da niyar ko masu gurin sunje bazata tashi ba tafi son a fara ta kanta yau. Lokacin 8:15am yana gaf da shiga ajin aka yo mai waya hakan yasa shi tsayawa dan ya amsa. Dubawa yayi sai yaga ansa my twinnie yayi murmushi sannan ya d'anyi baya da ajin sabida hayaniyar da suke yi ya d'aga tare da karawa a kunnansa. "Twinnie me ya how far..?!" Sadeeq ya fad'a yana d'an sosa k'eyarsa da k'asan biro, daga can 6angaran Abubakar yace. "Surprise..!" Sadeeq najin haka yayi murmushi tare da cewa. "Kana gate ko..?!" Abubakar yayi dariya yace "yah kana ina yanzu.? Sadeeq ya kalli ajin sannan yace "twinnie me kashigo ciki ina aji uku jss 3c nima yanzu zan k'arasa shiga ciki." "Okay..." Suka kashe wayar Sadeeq ya shiga hannunsa d'auke da ledar viva yana shiga 'yan aji suka tashi ana gaida shi da k'arfin tsiya dan yanzu ba k'aramin so suke mishi ba, ya ajiye akan teburin sa ba tare daya kallesu ba yace su zauna nan ma suka ce "thank you Sir..." Shima da k'arfin su kamar kuma had'in baki. Waje ya lek'a ya gani ko ya k'araso yana hangosa ya d'aga mai hannu suka yiwa juna murmushi tundaga nesa har Abubakar ya k'araso suka yi musabuha sannan suka shiga cikin ajin, nan ma yaran suka sake tashi suka gaida d'ayan daya shigo amma kotakan su bebiba ya tsaya suna magana sai Sadeeq d'inne yayi musu alamar su zauna da hannu tunda shi ba yadda zaiyi d'alibansa ne dole ya kulasu. "Twinnie ga abin zama ka zauna." Avubakar ya kalli kujerar sannan ya juya yana kallon 'yan ajin sai ya gansu fes-fes dasu hakan ya bashi mamaki ya kuma rasa wadda zai kira ta goge mai kujerar dan bazai zauna a haka ba. Shi duk a tunaninsa ba wad'anda ya sani bane ya kalli Sadeeq yana shafa sajen fuskarsa yace. "Twinnie congrats an sake ma class." Sadeeq yayi murmushi tare da juyawa ya kalli 'yan ajin sannan ya kalli Abubakar yace, "twinnie sune dai wad'anda ka sani kawai canjin yanayi aka samu." "Woww good of you." "Thanks twinnie." Abubakar ya kalli 'yan matan ajin kawai ya nunu Maryam Ali ya yafitota, jikinta na rawa ta mik'e ta k'arasa inda yake tace. "Malam gani." Mtwww wai ban hanaku ce min malam vane? Ko kunga nayi kama da teacher?" "Allah baka hakuri." Maryam ta fad'a bakinta na rawa, yayi banza da ita sannan yace "daga yau kar wanda ya kuma ce min malam ko sir suna na doctor Abubakar Salman Harun, karna kuma zuwa ajin nan wata tace min malam ko wani sir ku kirani da doctor Abbakar or doctor ASH." Ajin yayi tsit babu meyin motsi yaja tsaki tare da kallonta yace "Oya tashi ki goge min kujerar da zan zauna." Da sauri Maryam ta zaro ido jin abinda yace sabida ta tuno sanda yasa INdo ta goge mai da hijjab d'inta, ya zata yi gashi ba'a duba taba yau ta shiga uku zai ja mata. "Ko baza kiyi vane.?!" Ya tambayeta ganin bataje tayi abinda ya sanyata ba, hawaye suka zobu mata shi kuma Sadeeq yak'i yin magana jiki a sanyaye tana kuka taje tasa hijabinta ta goge mai tasss sannan ta koma gurin zamanta sai kuka takeyi shi kuma yaje ya zauna tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana d'an kad'asu. Sadeeq ya kalli Abubakar yace. "Bari sai na fara yi musu inspection." Abubakar ya kallesa yace "na ina kuma..?!" Sadeeq ya d'auki rular yana cewa "na jikinsu har kyauta nake basu that's why kazo ka gansu neat." Abubakar ya ta6e baki sannan Sadeeq ya tafi farawa wanda har lokacin bemasan INdo na ajin ba, Abubakar yace "okey twinnie duk wani wanda beyi maka wani abunba ka turosa nan gurin." Ya fad'a yana d'aukar wayarsa dan kiran Qibd'iyya yace mata ya sauka lafiya kuma yaji sassanyar muryarta mai sanyi. 'Yan aji najin abinda ya fad'a kowa ya fara duba abinda beyi ba dai-dai lokacin da Sadeeq ya k'arasa gurin bencin da yake farawa kuma INdo ce a farko dan haka kafin ta gama duba abinda bata yiba har ya k'arasa. "Ohh my God..! Wacece wannan kamar Aisha?" INdo ta dashare baki kamar gonar auduga yayin da 'yan aji suka bita da kallo shi kuma malam Sadeeq ya saki wani tattausan murmushi ganinta yau tsab-tsab da ita sai dai makeup d'in da tayi ne duk ya cuceta dan duk ta cika fuskar da d'ige-d'igen baki da janbaki sai dai yaji dad'i dayaga tayi wanki yace. "Toh muga bakin." Ta bud'e mai hak'oran nata ya gani ya d'aga kai sun d'an fi na baya ya kuma cewa "muga kanki." Nan ma ta bud'e da saurinta ya kalla gashin nan yayi d'as da kitso ya kuma kad'a kai domin tayi k'ok'ari sosai lallai hakan yana nuna masa cewar ba k'aramin son a bata kyauta takeyi ba yayi murmushi yana wani sak'e-sak'e cikin ransa kafin yace. "Toh kinyi komai Aisha muga farcanki." Sai a lokacin ta tuna sam bata yanke ba sai ta 6ata rai idanunta yayi rau-rau zata yi kuka dan tasan rashin yanke farcen ba k'aramin asara zai janyo mata ba Sadeeq ya kuma cewa "muga farcan ki Aisha." A hankali ta mik'a mai hakan yasa shi saurin kallanta domin beso ta fad'i tausayinta ya kamashi ba yadda zaiyi dole yace. "Aisha baki yanke farce ba, tashi kije wajan doctor Abbakar..." Tana hawaye tace Amma malam hikadai nefa banyi ba kuma wabillahillaxi mancewa nayi dan Allah kayi hakuri kabani atamfar.." "Tashi ki fito Aisha." Tashi tayi tana kuka domin ba k'aramin haushi takeji ba ta k'arasa wajan Abubakar wanda waya take kare a kunnansa shi kuma Sadeeq ya cigaba dayi idan yaga wanda beyi wani abunba sai ya turasa wajan Abubakar, shi kuma ganin yara sun taru a gabansa yasa shi cewa Qibd'iyya. "M love bari na barki zan..." Ya kasa k'arasawa sabida ido hud'u da sukayi da INdo zuciyarsa tayi wani rass gashi idanta yayi jah sabida kuka sai kawai yaji zuciyar sa nayi mai wani irin zillo ya kashe wayar bema sani ba sannan ya mik'a hannunsa ya janyo na INdo ita kuma ta fara dak'irewa a tunaninta dukanta zaiyi ta fara ihu tana bashi hakuri shi kuma ya damk'e hannun nata sabida yadda yaji shi cikin wani irin mood akanta.... Love u m Fan's *HAJJA CE* [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _Shafin yau naki ne tawan daughter'n My Nana Hafsatu Xoxo da Nana Hafsatu Rano wato *BILLY S FARI* wannan mata Allah yayi miki abinda kikeso duniya da lahira, ya azurtaki da 'ya'ya na gari masu albarka. Hajja ce tana sonki kamar yadda take son H , Allah yabar k'auna da soyayya. Page *7* Da gudu suke bin ta suna cewa ta basu bokitan su na talla amma tamkar iska gudu kawai take har se da ta shige cikin gida sannan ta dire bokitan ta zauna tana maida numfashin wahala. Inna ta kalleta tana jimamin hali irin na 'yarta ta ganin babu ranar da zata fito ta fad'i INdo bata yi wani abun na zagi ba, wannan dalilin ne yasa tayi niyar zuwa gidan me salati ko zata samu wani temakon da za'ayi mata akan fitinar ta amma baban su ya hana yace shi 'yarsa lafiyar ta sumul. Kad'a kai kawai Inna tayi ta cigaba da mark'ad'an ta akan irin dutsen nan, INdo na gefe su kuma su Idi sai faman kumbura suke ta bud'i bokitan Ubale me d'auke da awara ta d'ibi guda biyu sannan ta tura mai bokitin nasa, ta janyo na idi shima ta d'ibi wainar rogo ta mik'a mai sauran tana cemusu. "Naci lada kuma wabillahillazi kuka sake ganina kuka fad'i wata kalmar sai na jamuku asara kuce ba suna na A isha ba." Suka d'auki bukitan su sukayi waje kowanne da irin kalar wulak'ancin da zai mata a zuciyarsa, Nafeesa k'anwarta ta shigo gidan tana ganinta tayi saurin 6oye kwanon awarar dan karta d'aukar mata. "INdo rowar jaraba." Cewar Nafeesa tare da k'arasawa wajan INdon ta zauna harda su tankwasa k'afafuwa ta mik'a mata hannu alamar ta sammata. Mtww "idan ni marowa ciya ce dalla malama kekuma mecece? Ungoni ki matsa ki bani guri." Ta juya tana kallon Inna tace "Inna ga awara idan zaki ci." Inna ta k'araso gurin tana cewa "Ni wallahi 'yar nan bana son wannan fitinar taki, inda Allah ya temaka ma kun koma makaranta zaku shiga ajin gaba ni banaci na k'oshi da abin fitina." INdo ta fara sosa kai tana kanne ido d'aya sabida jin zafin yajin bakinta tace "Inna wallahi bazan koma makarantar nan ba wata zaku sakemin, wai d'azu harni malam Sadeeq zai cewa tinkiya! Wallahi toh bazan koma ba yaje yacinye makaranta." "Yanzu kin dena zuwa 'yar nan? Toh wacce kike son a mayar dake ke ba tsayayyan saurayi ba bare ayi miki aure yau na shigesu ni Maryama." "Inna wallahi bazan koma tsefawa ba na fasa zama likitar dama temako zan dinga yi toh yanzu kuma nafasa suje sunemi wata." Inna ta kad'a kai babu abinda zata iya cewa akai koda baban su ya shigo ma bata gaya maiba bare su d'auki wani mataki haka suka barta kullum bata nan unguwar bata waccen har aka d'iba sati biyu ko hanyar makarantar bata bibare asakaran zata shiga, tsab Sadeeq ya manta da ita domin ya toshe duk wata hanya daya san suna had'uwa. A 6angaran
Chapter 10 · 0% Book details