Sashe 32
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *27* "Malam Sadeeq kenan, ai da kasani ba yanzu ba." Shareta yayi ya nuna tamkar ma bejita ba ta juya tana kallonsa ta kuma d'aukar wayarta daya cillo mata. Madubin saitin kujerarta ta bud'e tana gyara fuskarta ya girgiza kai dan shi dama yasan da wahala yarinyar tayi hankali sabida babu arabi ba boko yaja tsaki har kusan sau uku sannan INdo ta kallesa tace. "Babu kyau fa." Yace "Ni zaki cewa babu kyau? Ko kin fini sanine da zaki cemin babu kyau?!" "Allah ya baka hakuri, cewa akayi idan kaji wani ko wata sunyi abinda ba kyau ka tuna masa, toni tuna maka nayi." "Karki i sake tuna min domin tun kafin kisan hakan nasani, ke karki sake yin magana har muje inda zan kai kina jina.?!" Bata sake kula shiba har sukaje danja masu tallar abubuwa suka dinga d'ago musu taga me alawar madara da sauri ta zaro d'ari biyu ta mik'a masa ji Sadeeq kawai yayi tana cewa. "Bani ta dika." Aikuwa ransa ya kuma mugun 6aci Allah-Allah yake kafin a gama mik'o mata ya figi motar amma danja batazo kansu ba harsai da aka bata tasa a jaka sannan aka basu hannu. Leda d'aya ta mik'a masa tace. "Malam Sadeeq bisimillah." "Banasha." Maidawa tayi cikin jaka ta bud'e leda d'aya tana sha har wani kunkuni takeyi irin na zak'in nan idan ya gauraye kunne. Wayarsa ya d'auka yasa earpiece tare da kiran layin Fateema, sai da ta kusa yankewa sannan yaji ta d'aga cikin sanyin murya tayi mai sallama. "Ohh babyna har yanzu jikin ne?!" Ya fad'a cike da damuwa, can 6arin Fateema tace. "A'ah kawai dai bacci nake, kun tafi ne?" "Eh muna hanya ma yanzu zan dawo insha Allah, amma ki tashi ko tea ne kisha zaki kuma samun relief." "Toh Allah ya kiyaye hanya a gaida min ita." Tana kaiwa nan yaji ta katse, ba haka yaso ba yaso suyi hira ta d'ebe mai kewa amma tariga ta kashe ya cire earpiece d'in yana cigaba da tuk'insa ba tare daya sake kallon koda inda take ba. "Malam Sadeeq dan Allah ka kar6a kasha, wallahi tayi dad'i madara ce zallah." Yayi shiru ta kuma cewa. "Inkaji dan Allah sha d'aya kaji." A fusace ya juya yana kallonta shi har lokacin be manta yanayin ta na baya ba cikin 6acin rai yace. "Wai dole sai na Shane? Idan dole ne toh sani insha dan Allah." Ya fad'a tare da d'an kallon gabansa kafin ya juyo yana dank'ara mata harara, d'aya ta d'akko da sauri ta danna mai ita a baki ya yi saurin furzar da ita a k'asa amma duk da haka sai da zak'in ya shiga ko'ina na cikin bakinsa ya samu gefen titi ya tsaya tare da nuna ta da yatsa yace. "Wallahi tallahi Aisha ki kiyayeni karkija wata rana na 6allaki yasin. Kinga ina shiga sha'aninki ne? Toh ki kuka da kanki duk rashin kunyarki a tafin hannuna take...!" Jan bakinta tayi ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka shiga garin Sumaila, tana ganin barkono dama sund'an tsaya sabida ana bada hannu batare da tayi mai magana ba kawai yaji ta bud'e k'ofar ta fita tana cewa. "Bari na siyawa Inna barkono da gyad'a ko kwano d'aya-d'aya ne." Kafin ya harzuka yayi magana ta k'arasa wajan, Sadeeq ya kifa kansa a steering shi kam ya shiga uku wannan wace irin yarinya ce tana ganinsu a tsakiyar titi amma ta 6alle murfin motar ta fita. Idan ta dawo sai ya mareta gobe bazata sake yi mai makamancin haka ba. K'arasowa tayi wani yaro na biye da ita a baya da kaya ta bud'e gidan baya ya zuba sannan ta bashi naira hamsin ta shiga motar ta zauna tare da kallonsa tana gyara mayafi tace. "Malam muje na dawo, wallahi kuma da arha shi yasa na siyo mata kwano biyu-biy....." Bata k'arasa ba taga ya d'ago hannu tayi saurin sunkuyar da kai tare da boyeshi tana sauke a jiyar zuciya cike da tsoro da mamaki. Fad'a ya fara yi mata kamar ya samu student d'inshi har ya gama bata d'ago ba ya figi motar taji sun fara tafiya sannan ta d'ago tana kallonsa. Kasa yin magana tayi ganin yadda yayi kicin-kicin da fuskarsa dan haka ta share Sa har sukaje k'ofar gidansu. Mutane kuwa aka fara murnar ga INdo ga INdo, wad'an da suka sanshi kuma suka dinga gaidashi yana amsawa da kyar tamkar 6eyi rayuwar garin ba. Kayanta ta kwasa tare da shiga cikin gidan su bata sake fitowa ba, shiru-shiru taji babu wanda ya lek'o shi kuma jira yake su gaida koda Inna koda Malam Hamza amma babu kowa daya fito daga gidan haushi da takaici suka sa shi ya tafi ba tare daya aika ankira wani ba. A cikin gidan kuwa INdo cewa tayi musu ai ya tafi hakan yasa Inna bataje sun gaisa ba su kuma murnar zuwan INdon yasa basu fita ba bare su ganshi harya tafi. Har Sadeeq yaje gida be denajin haushin abinda INdo tayi mai ba, lokacin da yaje gidan a cike yake da 'yan uwan Fateema hakan yasa shi juyawa yayi hanyar gidan su ba tare da ya shiga ba dan yasan akwai wad'anda zasu yi mai kallon banza. Mama na ganinsa hankalinta ya kwanta tace. "Yauwa Sadeeq har ka dawo?!" "Eh suna gaida ku." Ya fad'a yana k'ok'arin zama a kujera, Mama tayi murmushi cikin jin dad'i sannan ta shiga d'aki ta kawo mai abinci, beyi musu ba yaci dan yasan Fateema ba iya yi zatayi ba sabida ciwon marar daya barta tana yi. Yana gama ci ya fita yaje can gidan marigayi ya gano sannan ya wuce gurin abokinsa har sai da aka kira magariba sannan ya koma gidan. **** Bayan sati biyu Abba ya gaji da sanya mai ido da safe ya kirasa, yana zuwa sai daya shiga suka gaisa da Umma da Mama sannan ya shiga gurin abban. Gaisawa suka yi Abba ya kallesa tare da ajiye magazine d'in hannunsa yace. "Sadeeq yaushe zaka koma kwaran ne?" "Abba nan da kwana uku insha Allahu zamu koma." "Kai dawa?" Sadeeq yace, "Abba da Fateema mana." "A'ah Sadeeq ya kamata ka farayi musu adalci tun yanzu, ina son tunda zuwan nan na k'arshe da Fateema kukayi toh wannan karan sai ku tafi da Aisha bana son ta cigaba da zama da auranka acan gidan su ina fatan ka fahimce ni.?!" Wani irin 6acin raine ya ziyarci ran Sadeeq kansa a k'asa yana danna yatsansa cikin zuciyarsa kuwa abubuwane kala-kala a cikinta. Jin yayi shiru ne yasa Abba kuma yi mai magana Sadeeq yace. "Abba ai tafiya ta da Aisha garin nan bazai yiwu ba sabida kaga su ba Hausa sukeji ba itama kuma ba yarensu takeji ba dama tanajin turanci ne da sauk'i amma gaskiya tafiya da ita matsala zai jazamin wallahi, nasanta tun kafin Abubakar yasan ta." "Toh yanzu me kake nufi?!" "Abba kawai zan samu gida na ajiyeta anan idan yaso sai ta zauna a ciki har mu dawo." Abba ya kallesa sosai kafin yace. "Kana nufin ta dinga zama anan har lokacin da zaka dinga dawowa yayi." Sadeeq yace. "Eh Abba idan ba hakan ba wallahi bansan yadda zanyi da Aisha ba idan mukaje can, gashi ta raina ni sam bata ganin girmana tun sanda na koyar dasu a makaranta." "Shikenan kafin ka tafi kaje ka d'akkota sai ta tare anan gidan Najib tunda naga ya kammalasa kuma 'yan haya zai zuba gashi dai-dai itane gidan." Sadeeq yayi shiru tunani yake yana kuma jin takaici, kawai yana zaman-zamansa an d'akko mai wani aikin, yanzu duk shekara sai ya bada kud'in gidan hayar da INdo zata zauna dubu d'ari da talatin. Mtwww yaja tsaki ba tare da yasan ya fito fili ba sai da yaji Abba yace. "Sorry ko na shiga hak'inka ne??" Da sauri Sadeeq ya hau kad'a kai alamar a'a sannan yace. "Toh Abba kuma ni zanje na d'akkota? Na d'auka kawo ta zasu yi.?!" "Eh toh kuma hakan dai yafi, amma ina son ka k'ara d'aga tafiyar ka har ta tare sannan sai kutafi." Dakyar ya iya amsawa Abba sannan ya tafi. Yau ya kuma yin Nadamar zuwa tsefawa secondary school domin zuwansa ne yasa Abubakar ya ganta harya aure ta gashi ya mutu shi anbarsa da alak'ak'ai. Yana komawa gida ya bawa Fateema labari tace Allah ya sanya alkairi, kallonta kawai yayi ya shige d'aki. Cikin kwanaki biyu tal Abba yasa Sadeeq aka kwaso kayan INdo na gidan Abubakar harda wanda duk shine ya siya aka kaisu gidan da INdon zata zauna a matsayin ta na Matar sadeeq. Su Haleema Rukayya da Amina yasa sukaje suka kwaso kayan sawarta suka kai can gidan akajera mata sai dai babu dining area gashi INdo tana matuk'ar sansa dan idan tana kai ji take tamkar tana kusa da sharukhan. Sadeeq da Umma da Hawwa suka tafi d'akko INdo, hirarsu ce duk ta sashi mance wadda zasu je su d'akko har suka k'arasa k'ofar gidansu INdo wanda yake cike da mutane wai ashe su biki suke yi wannan abun ya k'onawa Sadeeq rai sai kace wani sabon aure mtww. Sun dad'e a ciki kafin a fito da ita su Uwani sai mata murna akeyi ta baro gidan dad'i zata koma gidan dad'i INdo taja tsaki ita kad'ai tasan gidan da zata shiga dan tasan sam basanta yake ba ta kuma riga ta shirya ma zama dashi a kowane irin yanayi indai vazai hanata abinci da fita yawo ba. A kusa da Umma ta zauna yayin da Hawwah ta zauna gefensa anata yi musu fatan sauka lafiya bayan Malam Hamza yazo sun gaisa dashi Sadeeq din ya kuma bashi amanar 'yarsa sukaja mota suka tafi. Tunda suka kama hanyar komawa yaja bakinsa ya tsuke jin INdo ta zage sai subirbid'a hira take tamkar ba amarya aka d'akko ba, yaja tsaki ganin sam babu jan aji a tattare da ita. Suna zuwa a k'ofar gidanta suka sauke ta su Umma suka shigar da ita ganin amarya yasa mak'otanta suka shiga suma dan su ganta. Har kusan k'arfe shad'aya na dare Sadeeq be shigo