← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 53

Sashe 52

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nuna min bazaki shiga ba sabida bakya sona da kina sona duk abinda zan ce kiyi bazaki tsaya wani tunani ko gaddama ba sai gashi kinyi na gani shi kenan na gode Allah yaso ina da wadda ta yadda dani 100%." INdo najin haka ta saka kuka shi kuma ya tureta ya juya kan kujerar yayi kwanciyar sa duk da yanajin kukan har cikin k'ahon zuciyarsa. Tashi tayi a hankali tana kukan ta shiga bathroom, shiga tayi cikin ruwan tana ciki tana jan majina yayi murmushi ya kuma k'i bin bayanta, bata fito ba har sai dashi kansa yaga dacewar lokacin tafito yayi amma tak'i fitowa. Zaune ya ganta a ciki ta saka fuskarta tsakankanin jinyoyinta sai gunjin kuka takeyi, k'arasawa yayi ya tsugunna a gabanta tare da saka hannu ya fara k'ok'arin d'ago fuskar ta amma tak'i ta kafe. Taurin kai na INdo sai addu'a ya mik'e tare ya d'agota cikin nuna k'arfi sannan ya fito da ita suka shiga bedroom yana rungume da ita suka zauna a bakin gado. A gabanta ya zauna tare da rik'o hannunta kanta a k'asa idanuwanta a rufe sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi. Kallon fuskarta yakeyi cikin tsananin sonta da kaunarta yace. "Cutie nine fah ya kamata nayi kuka sabida kin kasa yadda dani, cutie i love you..ban san yadda zanyi na misalta miki ba duk abinda kikaga nayi dan ina sonki ne. Cutie koda kikaga na dage sai kin biyoni nan karkiyi tunanin cewar ko bana son kiyi karatune a'a ina son zuwa dake ne sabida ko bayan rai na kiyi alfaharin kema naje dake inda nake zuwa shi yasa kika ga na dage sai kin bini amma duk abinda nayi miki na rashin dad'i cikin sani ko rashinsa kiyi hakuri ki yafemin." Hawaye suka kuma zubo mata ya tashi ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinsa yana buga bayanta cikin muryar kuka take magana. "Ni ka dena bani hakuri bayan baka min komai ba, nice zan baka hakuri sabida nice nake 6ata maka rai amma dan Allah abu Ayman kayi hakuri ka dinga yafemin koda a cikin zuciyar kane nasan ina 6ata maka rai dan All..." A hankali yasa hannunsa ya toshe mata baki yana kad'a mata kai alamar tayi shiru, da sauri ta rungumesa suka k'ank'ame junansu cikin shauk'i. Basu fito ba sai da kowa yasan ya farantawa d'an uwansa sannan suka yi wanka suka ci gaba da soyayyarsu yana kuma koya mata karatunta cike da kwarewa yadda kuma zata gane ta fahimta duk da cewar tana d'an dad'ewa kafin ya zauna a kwakwalwarta danma understanding takeyi ba wai hadda ba. Bayan sati uku Lokacin sun cika wata d'aya da zuwa cikin ikon Allah kuma ya samu INdo ta fara sakarwa su blessing fuska sai dai yawanci sunfi yin wasa da Ayman kasan cewar turancin INdo ba nisa yayi ba kamar su da yazama shine yarensu na biyu da suke ji bayan inyamuranci. Itama takan d'an lek'a gidan su amma ba sosai ba dan su kan yi yarensu wanda yafi bawa INdo haushi sabida ko "zo" bata iya ba su kuma sunfi yinsa. Sosai suka sake kulla babin soyayya dan zaman su anan su biyu ya kuma kulla sabuwar alak'a dan har basa son wani yayi nisa sukanji har zazza6i amma da an had'u sai a warke zuciyar su ta riga ta zama d'aya, duk abinda d'aya yakeji wala na dad'i ko rashinsa sai duk sunji yanayin a jikinsu, ciwon kai idan d'aya yayi sai d'ayan ma yayi koda kuwa fad'uwar gaba ce wannan yanayin yana basu mamaki da al'ajabi, sun kuma sake tabbatar da cewa sunyi *MUSAYAR ZUCIYA* ya kar6i tata itama ta k'ar6i tashi suna kula da junansu sannan ta rage yi masa taurin kai musamman da yake karanto mata tarihin annabawa duk dare idan sunje bacci. Ayman yana ta wayo suna kula dashi sosai sannan koda second d'aya Sadeeq be ta6a manta Fateema ba yakan buga mata waya a rana kusan sau biyar yayi missing d'inta sosai domin ko wacce mace tana da nata matsayin a zuciyar miji musamman da ya kasan ce ita ya fara furtawa kalmar So ya kuma fara auranta ya fara saninta a matsayin matarsa. Yana jin dad'in zama da matansa su duka musamman yanzu da soyayyarsa ta kuma zama a cikin zuciyar INdo, yafi ta sonta amma yakan daure domin karya d'ora mata girman kai karta dinga d'aukar kanta a wani abun tunda yanzu ne yake d'orata akan sabuwar rayuwa dan yanzu ne take kuma sanin komai na rayuwa duk abinda ya d'orata akai zai ga shi takeyi bata ta6a k'etare duk wani abu da ya karanto mata ya fassara mata. Watansu biyu suka shirya komawa lokacin INdo ta kuma wayewa tayi kyau tayi k'iba ta zama tamkar wata k'aramar hajiya tayi dam kwanciyar hankali ya fito a jikinta da yanayinta dama yadda take gudanar da abubuwanta dan takanji zata iya gogawa da ko wacce irin mace a fad'in duniyar nan duk da cewar iliminta bema kai na Fateema ba amma yadda zata gudanar da wani abun sai mutum ya rantse ko tana kanyin master's ne. ***** Kwance take a jikinsa tana kuka domin ba k'aramin rashinsa tayi ba wata biyu ba wasa bane a gurin miji da mata musamman idan basu tare. Gashinta yake shafawa yana kuma rik'e da hannunta yana matsawa Sadeeq yace. "Baby dan Allah kiyi shiru kinga dai ba zuwa nake garin can ina yawo in dawo ba, kinsan abinda nakeyi kinfi kowa sani tun kafin kowa ya sani hatta Abba kin fishi sanin me nake zuwa inyi dan haka bana son kukan nan please yana sani cikin shakku da kokwanto." "Toh baby amma dai ka dena dad'ewa dan Allah. Ko kuma ka tattaro ka dawo nan kano shikenan kana tare damu koda yaushe." "No... Fateema bana son zaman garin nan ga sa'ido sai dai ke idan kin yadda ki ajiye aikin ki idan zan tafi sai na tafi dake na ajiyeki a can kinga na huta kina can bani da fargaba ita kuma Aisha tana nan kun hutar dani ma." "Nayi shiru baby nigara ku dinga tafiya da ita can babu kowa d'an uwa dangi duk babu sai sababbin da zaka yi na hakura zan dinga jiranka har lokacin da zaka dawo." "Ummm kaji me wayo, wato ke k'ink'i bina sabida aikin ki. Amma ni kina son na dawo nan da zama shi kenan kullum a ce mijinku yana guri d'aya baya zuwa konan da can toh na gano ki kuma nak'i wayon." Ya fad'a yana mata cakulkuli a cikinta suna ta dariya dan baya son yaji ta sako mai zancen rashin haihuwarta sabida shi be ta6ajin haushin hakan ba ko yaji sonta ya ragu a'a kullum yana jin sonta musamman da take mai biyayya da nuna soyayya. Haka Sadeeq ya cigaba da rayuwa da matansa cikin kwanciyar hankali duk da wani sa'in yakan fuskanci matsala ta kowane 6angare amma yakan warware ta cikin hikima ta yadda ya san halin kowacce a cikin su. 'Daukar su yayi su duka sukaje aka yi musu hoto ya bud'a su ko wane gida yasa d'aya guda d'aya babu kuma wadda ta nuna mai bata so. **** "Hello, Rasheedat. Okey ai zan shigo nan da 11:00 tuna sai 11:30 ko.? Okay sai na shigo." Kwance yake akan kujera INdo na k'ok'arin zuba masa fruits salad duk tana jin abinda yake fad'a ranta yayi mugun 6aci zuciyar ta na zafi kishi ya turniketa sai faman had'e gira takeyi. Tashi tayi jikinta har rawa yake yi taje takai mai fruit salad d'in ya d'ago ya kalleta ganin yanayinta yasa shi riko hannunta ta fizge ya kuma rikowa ta kuma k'ok'arin fizgewa ya janyo ta kusa dashi ta zauna kirjinta sai dokawa yake yi Sadeeq yace. "Toh yau kuma me Sadeeq sarkin 'yan masu laifi yayiwa cutien sa cikin 'yan sakanni.?!" "Ba komai kyale ni zan shiga d'aki." "Toh ki fara bani na gama sha sai kije kiyi aikin ki." INdo ta kuma yin kicin-kicin a kufule tace. "Ka kira Rasheedat ta baka mana amma ba ni ba." "Rasheedat kuma cutie? Kin santa ne ko kuma dan kinji muna waya ne zuciyar ki ta fara halin nata." Turo baki tayi tana harare-hararen gefe ta kasa cewa komai, Sadeeq ya janyo ta jikinsa yasa hannu a tsakiyar k'irjinta yaji yadda yake bugawa cikin tashin hankali ya mik'e zauna dan da a kwance yake yana rik'e da ita. "Subahanallahi cutie kishi ne haka? Rasheedat ba budurwata bace d'alibata ce yau zanyi musu lecture shine take tambaya na shin zanje nace eh su shirya shikenan fa." Sadeeq yana jin sanda ta sauke wata muguwar ajiyar zuciya sannan ta kallesa ya sakar mata murmushi tace. "Toh banda basu da kunya meye na bugo maka, su ba students bane baxasu jira har kaje ba zasu wani bugo maka waya. Ina monitor da bazai bugo ba sai ita tana mace banzar kawai." "Ta6 cutie har ina cewa zan k'ara aure sai kema na barki anan ki cigaba da karatunki Fateema tayi aikinta ita kuma amaryar na barta acan kwara gidana na Ilorin kunga an huta da zirga-zirgar fitar ku." Share sa tayi ta d'ibi fruit d'in a cokali ta sanya mai a baki, yana dariya ya kar6a har ta gama bashi sannan ya janyo ta k'irjinsa yace. "Cutie I love you zan iya mutuwa a duk sanda kika juya min baya, ki kula damu dani da yaro na dama wad'anda zaki haifamin nan gaba please cutie." Sumbatarsa tayi a goshi sannan ta kwantar da kanta a saman k'irjinsa tana shafar kansa tace. "Nima ina sonka my super glue, your my Biggest comport..my breath... My heartbeat.. Kai my everything but ka dena min zancen zaka k'ara aure, a cikin shekara d'aya kayi mata biyu sannan kace kana shekara ta biyu zaka yi ta uku ai sai ka jamana surutu. Dan Allah ka barmu mu biyu ka dena tunanin wata idan ba haka ba zanyi kuka." "Yi muga irin kukan da zaki yi idan zan k'ara au..." Tayi saurin toshe mai baki da nata kafin ta cire ta kalli cikin idanunsa daya bud'e su a hankali duk sun zama na rigima tace. "Haka zanyi uhm..uhm..uhm..ahhh..wayyoooo...!" Suka kyalkyale da dariya Sadeeq ya rungumeta akan kujerar yanajin k'aunarta har cikin
Chapter 52 · 0% Book details