← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 53

Sashe 2

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kalmar, ta zauna sai wulkita idanu take. register ya d'akko tare da bud'ewa ya mik'a mata jan biro da blue tare da cewa, "Oya started." Tayi saurin kallon shi tare da cewa, "Na'am malam.." Keya ya salle mata da hannunsa tare da cewa, "Ki fara kiran sunan idan ba haka ba zaki sha wahala dan naga alamar kin raina ni so ina son kiyi musu yadda nake yi nima na gani.." Kallon register d'in tayi sam kasa gane yadda take tayi bare aje ga karanto sunayen ciki ba zata iya ba kuma nan J.S one, kallon shi tayi tare da marairaicewa ta fara ba shi hakuri. "Malam dan Allah idan kana kaunar iyayanka kayi hakuri wallahi tallahi ba zan sake ba." "Au ba zaki fara ba sai na zane ki...?!" Ya fad'a yana gyara dorinar hannun shi, nan da nan INdo ta fara kuka dan tak'i jinin a doke ta da bulala. tayi saurin zamewa k'asa tare da sake bashi hakuri akan ya kyaleta ta tuba tabi Allah tabi shi. Ganin duk ta gigice yasa shi ce mata, "Tashi ki dawo nan kiyi naildown." "Malam baka hakura ba dan Allah?!" Ta fad'a tana matse idanuwa dan hawaye su fito amma ko d'igo, ganin yaje ya zauna ya fara kiran suna yasa INdo tashi taje tayi abinda ya sakata dan ta san ba hakura yayi ba. sai da ya kammala kiran sunan ya fara koyar dasu ya gama sannan ya kalleta yana nunata da yatsa yace, "Idan kika sake yin abinda nake yi in dai ba na karatu bane sai na 6allaki kina jina?!" "Eh malam ai baxan kuma bama." "Yafi miki.." Ya fad'a tare da kwashe kayan shi yabar ajin yana tunanin inda zai yi ya samu ayi mishi transfer ya tsani makarantar sam ba tayi mishi ba. Bayan sati biyu ranar wata Monday Sadeeq na shirin tafiya class d'in shi ya d'auki duk wani abu da yake buk'ata yana shirin fita kawai yaga Abubakar twins d'in shi tsaye cikin kananun kaya riga seegreen me dogwan hannu da wando baki sai farin eye glass wanda yayi mai matukar kyau, sosai suke matukar kama babu ta inda zaka iya bambance su sabida tsabar kamannin su. kallon shi Sadeeq yayi cikin tsananin mamaki tare da k'arasawa ya kalleshi cikin mamaki yace, "Yanzu muka gama waya da kai amma shine baka gaya min kana hanya ba why?!" Kafad'a Abubakar ya d'aga alamar ba komai sannan ya shiga ciki ya zauna tare da cewa, "Twin ko class zaka shiga ne?!" "Eh but tunda kazo sai mu wuce gida ka huta gobe na shigar musu." Yayi maganar yana k'okarin maida littattafan dake hannun shi, da sauri Abubakar ya mik'e tsaye yana tsayar dashi ta hanyar rik'e hannun shi yace, "No kazo muje sai na tsayaka ina nan tare da kai har zuwa gobe." Kafad'a Sadeeq ya d'aga sannan ya d'auka tare da juyawa yana fad'in. "Toh muje." Tafiya suke wanda ita kanta iri d'aya ce suke yi suna yi suna hira yara kuwa daga cikin tagogin ajin su sai lekowa suke suna mamaki da al'ajabi ganin malam Sadeeq guda biyu a haka suka k'arasa barandar ajin su INdo. Yauma kamar kullum cikin surutu suka gansu sam basu lura da zuwan su ba INdo suka hango a saman dest tana rik'e da kugunta sai gwada musu yadda malam Sadeeq yake tsayuwar shi take yi taji Uwani halilu ta janyota tare da nuna mata k'ofar ajin tana hango su ta shige k'ark'ashin benci cikinta sai kululululu yake sabida ta san yauma ta shiga uku. "Goody morning sirsss..!" 'Yan aji suka fad'a baki d'ayan su tare da mik'ewa tsaye. ciki suka shiga sosai Abubakar sai kallon su yake su kuma sun rasa gane waye malamin nasu a ciki. Sadeeq ya k'arasa wajan bencin da INdo ke k'ark'a shi yace. "Ke! Tashi ki fito ko na mareki.." Jikinta na rawa ta d'ago ai tana ganin still biyu take ganin shi sai ta koma tana ihu tare da cewa. "Wayyo Allah na higa uku malam nayi min fatalwa, wallahi tallahi ban yi niyar yi ba amma Maryam Aliyu tace nayi zata bani naira biyar dan Allah malam kadenayi min fatalwa wallahi ba zan sake yi ba idan na k'ara ka...." Bata k'arasa ba taji an janyo kafar ta sai ganinta tayi a gaban allo tana d'agowa still ta kuma ganin su biyu kawai a take ta sulale a wajan ta sume sabida tsabar kad'uwa da shiga cikin rud'ani. Ko gezau Abubakar beyi ba bare yayi yinkurin yin temako sai kallonta kawai da yayi yana mamakin ganin hauka irin nata, da sauri Sadeeq ya girgizata yana kiran sunanta cikin tashin hankali kar yaje ta mutu ya shiga uku 'yan aji kuma sai suka fara kuka cewar INdo ta mutu. "Aisha! Aisha!! Ke Aisha!!! Tashi mana me aka yi miki haka...?!" Sadeeq ya fara kiran sunanta ganin duk ya rud'e yasa Abubakar k'arasawa wajan ya dafa shi sannan ya kalle shi a hankali cikin rashin sonyin maganar shi yace, "Sorry my twins ba mutuwa tayi ba suma tayi da ansa mata ruwa zata farfad'o.." Shaf Sadeeq mantawa yayi da cewar d'an uwanshi likita ne sai da Abubakar ya samo ruwan wata yarinya a jarka ya shafawa INdo sannan ta farfad'o yana jin sanda d'an uwan nashi ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfen gaske na farin ciki. Tana farfad'owa idanunta suka sauka a kansu da sauri tayi baya jikinta na rawa, ganin haka yasa Abubakar dama shine wanda baya d'aukar raini ya buga mata wata uwar tsawa tare da zare mata idanuwa tsit INdo tayi jikinta sai faman rawa yake. "Ke..! Karna sake jin bakin ki yayi mana ihu, wawuya baki san ana haifar 'yan biyu ba? Ko kinga munyi miki kama da mayu ko aljanu..?!" Cewar Abubakar wanda ke tsaye akan INdo, da sauri ta girgiza mai kai cikin tsananin tsoro sannan ya ce mata, "Tashi kije ki zauna na san yanzu garau kike ba kya buk'atar wani hutu." Da sauri ta mik'a ta wuce gurin zamanta, mik'ewa Sadeeq yayi ya koma kan kujera tare da janyo d'ayar ya nunawa Abubakar alamar ya zauna. kallon kujerar yayi sannan ya kallo inda yake hango INdo cikin yatsina fuska yace mata, "Ke..! Zo nan." Da sauri ta k'arasa tare da zubewa a gurin shi tace. "Gani malam." "Karki kuma kirana da malam kinji ko? Ni ba malamin Ku bane..!" Baki na rawa INdo tace. "Toh sir." Had'e rai yayi tare da tsuke baki cikin takaici yace, "Waye sir d'in?!" INdo tace, "Kai ne sir. ." Hard'e k'afa yayi yana kallonta cikin b'acin rai yace, "Stupid...! Ya sunan namijin saniya? ya ake kiran shi da hausa?!" Cikin sauri ba tare da takawo komai a cikin zuciyar ta ba tace, "Sunan shi sah." Abubakar yace, "Ahha kin ga nayi miki kama da shi?!" Da sauri ta girgiza Kai alamar a'a tana mamakin wannan abu, toh me zata ce mishi tace malam yace baya so tace mai sir yace ta kirashi da sunan dabba toh ko sunan shi yake son ta fad'a ko tace mai baba amma ai be haifeta ba bare tace mai hakan. Jan baya yayi kad'an tare da cewa, "Zoki gogemin kujerar da zan zauna." INdo ta mik'e tana mamakin toh yau malam sadeeq mugu ya zama kokuwa ba shi bane dan har lokacin bata tantance waye malam Sadeeq ba cikin suba. kalle-kalle ta din ga yi ko zata samu wani kyallen da zata goge mai amma babu ganin haka yasa shi yin magana, "Ke..! wai ba zaki yi aikin da na saki ba kin barni a tsaye fa." "Mal.. Si.." Ta rasa me zata ce mai kawai ta kalleshi tana turo baki dan ya gundire ta tace, "Ai babu tsumma shi yasa." Cikin rashin damuwa ya kalleta daga sama har k'asa ya tab'e baki sannan yace, "Meye amfanin hijjabin jikinki ko d'ankwalin kanki su d'in ba tsumma bane?!" Da sauri INdo ta kalleshi ya d'aga mata gira guda d'aya tayi saurin kallon Sadeeq dake zaune ga mamakin ta register ma yake bud'ewa ta kalli hijjab d'inta wanda duk ruwan kashu ya dafar dashi gashi wuyan ya yage tace mai. "Ai hijjab d'ina ne bafa tsumma bane ba." "Idan baki cire kin goge min na zauna ba ranki zai 6aci yanzun nan kinji na gaya miki." Ya fad'a cikin tsawa wadda take a slow, ba yadda ta iya haka ta kama k'asan hijjab d'inta ta goge mai kujerar sannan ya zauna ita kuma ta koma wajan da malam Sadeeq d'in ya tanadar mata a gaba. Malam Sadeeq ya fara kiran sunaye sannan da ya gama yayi musu karatun da yake d'aukar su wato turanci, Abubakar dake zaune yaci dariyar zuci dan karma yayi a fili su raina shi ko idan yaji dariyar tayi mai yawa sai ya kara text book a fuskar shi yayi mai isar shi, lallai dole d'an uwan shi ya koka tab makarantun gwamnati sai addu'a yake ta fad'a a cikin ranshi har Sadeeq ya kammala musu sannan suka fita ana tashi suka wuce gidan da Sadeeq d'in yake haya a ciki..... *HAJJA CE* [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *2* Bayan an tashi daga makaranta, su Indo ta k'ofar gidan da su Sadeeq suke suka biyo. lek'en su suka din ga yi su dai suna jin hayaniya da guje-gujen yara amma basu kula ba sai can Indo da Maryam Ali suka kuma kutsa kai suka shiga suna lek'a tagar wani d'aki karaf suka hango Abubakar zaune a bakin katifa yana danna laptop wanda daga shi sai 3quarter da singlet sam beyi tunanin cewar ana lek'an su ba sai da yaji motsin yayi yawa sannan ya d'aga kai yana kallon gurin. Mamaki da al'ajabi yasa shi saurin mik'ewa tsaye su kuma suka zaro mai idanuwa kamar had'in baki su sam basu gane waye aciki ba kasan cewar kamannin iri d'aya ne. Suna k'ok'arin guduwa suka ga Sadeeq tsaye a bayan su ya rufe k'ofar gidan ya jin gina a jikin ta yana watsa musu wani mugun kallo. can Abubakar ma ya fito fuskar nan a murtuke. Wayyo Allah dan girman Allah dan annabi Muhammad s.a.w idan
Chapter 2 · 0% Book details