Sashe 4
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai taga dama zata amsa amma fa Ummi kana magana kafin kakai k'arshe ta mayar maka, no gaskiya akwai wata dai a cikin hospital din mu da suka zo sanin makamar aiki na ga kuma kamar type d'ina ce sai dai ba zan iya mata magana ba karma ta rainani." "Rai ni kuma Abbakar? toh kenan idan kayi auran ma bashi da amfani tun da dole sai wani abun raini ya shiga tsakanin ka da matar ka.." "Kasan kuwa wani sa'in ina jin tsoron yin aure, sabida wani sa'in sai naga ba shi da amfani." "Ikon Allah." Cewar Sadeeq yana yi mai kallon mamaki yayin da Abubakar d'in ya mik'e yayi waje yana son ya samu almajirin da zai wanke musu toilet d'in su. Yana fita ya samu wasu yara zaune suna wasa ya kira wanda suka had'a ido da shi. yana zuwa yaron befi 10 years ba Abubakar ya kalleshi yace. "Kai whats your name?!" Yaron ya kura mai idanuwa kunnuwan shi sai bud'ewa suke dan beji abinda yace ba nan ya fara kwakular hanci har lokacin idanun shi na kan na Abubakar ganin kamar be gane ba yasa shi cewa, "Ya sunan ka?!" Ya dashare baki hak'oran nan yalaye kamar yasha d'orawa kafin yace, "Suna na Sagiru Hamza." Abubakar ya d'auke kai tare da kallon sauran yara, gaba d'aya kaf cikin su babu na za6a har garama Sagirun dan haka ya kalle shi yace. "Zaka iya wanke mana toilet?!" Da sauri Sagiru ya d'aga kai duk kuwa da cewar be gane abinda ake nufi da toilet din ba amma yaji ance wankewa yasan koma me ye zai iya wanke shi tatass. "Toh shiga muje." Abubakar ya fad'a yana komawa ciki, Sagiru ya juyo tare da yiwa sauran abokan nashi gwalo. "Yauwa Sagir kaga ga klin da hypo shi zaka d'auka ka kwanke shi sosai." Ganin inda ya nuna ne yasa Sagiru tabbatar da cewa ban d'aki ake son ya wanke, Abubakar na gama nuna mai ya koma cikin d'aki shi kuma Sagir ya shiga yana wankewa.sai da ya kammala tasss sannan Abubakar ya fito ya bashi naira d'ari biyu ai kuwa ya dinga murna sannan ya tafi gida da gudun sa yana murna tare da burin ramuwar abinda INDO tayi mai lokacin da tana da kud'in ta naira 50 ta dinga siyan awara tana hana su. "INDO..! INDO...!! INDO..!! nima yau zoki ga kud'ina wallahi na samo.." Sagir ya shiga gidan da gudu yana k'iran ta da k'arfi, da gudu ta fito daga ban d'aki hannunta rik'e da buta tana fitowa tayi wurgi da ita tana gyara kullin pant d'inta wanda yayi mata yawa sabida bud'ewar da yayi gashi kamar rai shi kad'ai gareta ta k'arasa kusa da Sagiru tana raba idanuwa. "Wai kai dalla meye kake ta kwad'a min kira ne?!" Be yi magana ba sai kud'in daya nuna mata yana tsalle, da sauri ta ware idanuwa cikin tsananin mamaki sannan tace, "Kai Sagiru a ina ka sato ko kuma waye ya baka kud'i har d'ari biyu haka...?!" "Yarinya wankin ban d'aki nayi shine aka bani ita lada." "Ikon Allah a wane massalaci ne haka?!" Sagir yace, "Ba'a matsallaci bane a gidan malamin ku wannan mesa glass d'in nan." "Tab d'i jam! toh Sagiru nawa zaka bani a ciki?!" Wani banzan kallo yayi mata tayi kallar tausayi tare da cewa. "Dan Allah kabani ko naira hamsin ce kaji kanina wallahi nima wata rana idan na samo zan baka." "Uhh-umm yarinya ba zan bayar ba." Cewar Sagir yana danna kud'in a cikin aljihun shi, ganin haka yasa ta cewa, "Toh kuwa yaro dama Inna tana ta neman kud'in da za'a siyo daddawa da kuka sai kazo ka bayar tun da ai kaima da kai za'a ci tuwan." "Ke wallahi ba zan bayar ba, ke rannan ba da naira goma a hannunki ba Inna tace ki kawo a siyo manja da ita ba amma kikak'i sai yanzu dan kud'in ba naki bane ba zaki ce na bayar a siyo kuka toh ba zan ba da ba." Ganin bashi da niyar bata ko sisi yasa ta fara kwad'awa Inna kira, yana jin haka shi kuma ya zura da gudu yayi waje nan ya barta sai faman masifa take tamkar kud'in nata ne... *HAJJA CE* [7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Page *3* Da sauri ta fito ta biyo bayan sa amma ko kyallin sa bata hango ba,ta ciza le6anta tare da ficewa daga gidan gaba d'aya.Gidan su Maryam k'awarta ta wuce tana wak'ar ta da d'an tsalle wasa hankalinta kwance.malam Sadeeq dake k'ofar gida ya bita da kallon takaici ganin yadda tayi fururu ba wanka,sam bata kula dashi ba sai faman wak'a take tana cewa. "Indo Aisha...ta zariya mai d'an kallabi..." Har tayi kwana sai tayo baya ganin shi da tayi, shi kuwa yana ganin zata dawo yayi sauri zai koma cikin gida be kai ga k'arasa juya wa ba yaji tace. "Wil dam malam. (Well done sir).." K'in kallon ta yayi yana dan na wayar sa domin service yake nema.Ya gane abinda take son cewa so take ta gaida shi, ko me ya kawo well done a tsayuwar da yayi.dan haka Murya k'asa k'asa ya amsa mata,Indo ta washe mai baki tare da matsawa kusa da shi yayi saurin daka mata tsawa ganin yadda take shige mai.kallon sa tayi cikin mamaki ido waje ta kuma bin sa kafin tace. "Malam Sadeeq baka gane ni bane?Indo ce fa ta makarantar gwamnati ta nan unguwar d'an Awaisu. Ka gane ni? Nan tsefawa fa gwamman sakandare sukul." (Tsefawa government secondary school). "Ke! Naji me zan miki ne..?!" Ya fad'a cikin k'ufula domin ta kai shi bango. Ita ma share shi tayi da masifar tashi da yake mata domin tana son yi mai tambaya wadda take son jin amsar su daga bakin sa dan haka masifar shi ba za ta d'aga mata hankali ba. kusa da k'afar sa ta k'ara sa haushin ta ya kuma zuwar mai wuya, tsoran sa d'aya kar 'yan kauyan suyi mai muguwar fahimta sai kauce mata yake amma ta kasa ganewa ya kuma had'e rai amma ko ajikin ta tace. "Malam tsakanin ka da Allah gaskiya da gaskiya zaka gaya min, shin ku 'yan biyu ne, ko kuwa dai ni kake bawa tsoro sabida ina kwaikwayon ka a aji...?!" Wata uwar harara ya narka mata dan yaga alamar kamar zata kawo mai rai ni shi kuma bezo garin dan su raina shi ba, wato ma k'arya yake mata shine zata zo ta k'ure sa dan tsabar ba ta da kunya. Fuskar sa a murtuke ya kalleta yace, "You're very stupid." Tana dariya cikin nishad'i tace, "Sanki u malam Sadeeq, (thank you) wallahi shi yasa kake birge ni sabida ka iya turanci mai kyau da dad'i. Amma dan Allah malam ka d'an fassaramin abinda ka fad'a da hausa he nima in rik'e gurin na iya sosai..." "Zaki bar gurin nan ko sai na 6allaki... mara kunya fitsararriya kawai.." Ya fad'a cikin d'aure fuska. tayi baya-baya tana kallansa tare da kama ha6ar ta tace, "Kai malam! masifa, daga tambaya sai cibi ya zama k'ari shi kuma k'ari ya zama k'ababa. na tafi kuma ba zan je makaranta ba a-he, sai ayi kuli-kulin tara sisi dani.." Ta yi maganar tana tafiya da baya da baya har ta shige lungun gidan su Maryam. tsaki yayi ya koma cikin gida yayi kudurin sai ya gyarawa 'yan makarantar zama. kowa tayi wa dan ba ta je makaranta ba oho mata. yara sai rashin kunya basu san komai ba dak'ik'ai zai nuna musu shima bashi da mutunci. Ranar haka ya wuni yana kunci jefi-jefi yakan yi tsaki har dare yayi be fita ba sabida takaicin Indo da sanya idon 'yan gari domin fita dubu shiga dubu sai sun kalle shi gashi ya tsani saka ido cikin lamuran sa. Washe gari da yaje makaranta Indo bata je ba yaga ashe da gaske take yi, still wata washe garin tayi nan ma babu labarin Indo sai ranar juma'a yana tsaye wajan black board yana koyarwa kawai yaji ana magana a taga, juyawa yayi sai yaga babu kowa domin da taga alamar zai ganta sai tayi saurin yin k'asa, dan haka ya cigaba da abinda yake yi. Can ya kuma jiyo kus-kus yayi a hankali ya kalli gurin caraf suka had'a ido da Indo tana cillowa Sa'ade wani abu a leda, dariya ta sakar masa ya k'arasa bakin tagar yana kallonta. Sanye take cikin house wear hannunta rik'e da faranti an jera kallik'ak'au da yajin masau da alama shi ta cillawa Sa'ade ya had'e girar sa tare da cewa. "Zo nan..!" Ita yake kallo amma sai ta juya wai ko zata ga wanda yake kira amma sai taga babu kowa sai ita, dashare mai baki tayi tare da d'an matsawa kad'an ba sosai ba tace. "Gani malam." "Jeki zaga yo ta k'ofa." Ya fad'a, Indo ta tsuke fuska tare da cewa. Malam ai ba zuwa nayi ba yau d'in ma tallah nake yiwa mak'ociyar mu. Kasan idan na siyar mata mawa zata bani? Yayi mata banza ganin ita yake kallo yasa ta juyawa ta dafe abubuwan cikin farantin ta ruga da gudu dan ba zata yadda taje ya hana ta fitowa. Kai ya girgiza tare da komawa ya ci gaba da yin aikinsa kuma a kwanaki biyun alhamdulillahi suna ganewa, tamkar dama Indom ce ke hana su rashin fahimta. Yana gamawa ya fita ya koma ofis haka ya dinga ci gaba da koyar musu har aka kusa fara jarabawa wadda daga ita zasu wuce j.s 2 amma Indo bata sake zuwa ba shima har ya manta da ita har ya Saba ma idan yana kiran suna ya samata absent. Ana gobe za'a fara jarabawa Indo ta dawo makaranta. washe gari aka fara musu sai da suka yi jarabawa hud'u sannan a ta biyar d'in zasu yi English language wato subject d'in malam sadeeq. Kasan cewar tun da aka fara beje ajin ba sai yau da za'a yi tashi jarabawar kuma dole sai yabi aji-aji ya kuma yi musu bayani sannan. Tare da Abubakar suka shiga domin lokacin yazo abinsu gwanin ban sha'awa, zasu gaida