← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 53

Sashe 47

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

matsa jikin murfin ya kalleta tare da cewa. "Matsa ki bani guri." "Kai Yaya Sadeeq dan Allah, wai kana nufin kace har yau baka gane inda Zuciya ta take ba akan ka? Please Yaya Sadeeq tun kafin na mallaki hankalin kaina nake sonka amma sai wani shareni kake yi ko banyi maka ba Yaya Sadeeq?!" "Ke! Zaki matsa ki bani guri anan ko sai nayi ball dake." Turo baki tayi tana sake matsawa kusa dashi, cikin nuna izgilanci tace. "Hmmm Yaya Sadeeq duk matanka nasan tarihinsu kuma duk cikinsu babu wacce takaini komai ba kamar wannan aunty Aishan me jego, ita da ko wayewar ma anan gurinka tayi 'yar kauye da..." Kwaf... Taji ya kwad'e mata baki da phone d'in daya d'akko, dai-dai kuma lokacin INdo ta fito tayo gurin motar Sadeeq yace. "Chuchu bar gurin nan kafin raina ya kuma 6aci, k'atuwar banza sakarya kawai." Kuka tasa ganin harda jini ya fito INdo taga ta tafi tana kuka ta shiga motar shima ya kulle suka kalli juna tace. "Me kuma ya sanya chuchu kuka my super glue? Allah yasa dai ba wani abun kayi mata ba tana da kirki." "Cutie rabu da ita rashin kunya takemin. Kinga bama wannan ba ya taro hope kunyi komai cikin jin dad'i da wal-wala..?!" Hancinsa INdo taja tana murmushi jin dad'i sannan tace. "Kana sona mijina Allah ya shi albarka ya k'ara bud'a maka hanyoyin samu, mu kuma Allah ya bamu ikon yi maka biyayya kamar yadda kake iya k'ok'arin ka wajan ganin ka faranta mana." "Amin Ummi ayman ina jin dad'in yabon nan da yake fitowa daga bakinki. Ina d'ana baki taho min dashi ba, kinsan yaufa tun asuba rabona dashi." Dariya tayi sannan ta zuge jakar hannunta ta fito da kud'ad'an ciki wanda duk na barka ne. Mik'a mai tayi be kar6a ba ya kallesu tare da cewa. "Uhmm k'arin bayani tukunna cutie ai bakya mik'on Kud'i haka ba bayani ba." "Toh ka kar6a mana ai zan maka bayani, kud'in da mutane suka bani ne na barka. Ka kar6a kayi amfani dasu kaga akwai k'ananu nima sai nayi wani abun ko idan za'a nema." Dariyar shima yayi zuciyarsa fara kal, chuchu na can gefe a tsaye tana gunguni sauran 'yan uwa na mata sannu amma idanunta suna kan motar Sadeeq haushi kamar zata had'iye motar. "Cutie wannan ai naki ne, ni babu abinda zan kar6a Allah yayi miki albarka ya albarkaci yaron da kika Haifa min Ina alfahari dake Ina sonki har cikin k'ahon Zuciya ta." Kowa dad'i yake ji sun dad'e a cikin motar kafin ya duba agogo ya kalleta cikin yanayi nasan nuna rashin son abinda zai fad'a yace. "Zan tafi, gobe insha Allah ance za'ayi suyar nama acan gida kinga kar a 6atawa masu gidan idan an kammala za'a kawo jibi idan Allah ya kaimu za'a kaiku sumaila sai kuma kinyi arba'in." "Ko baka son na tafi ne..?!" Yayi murmushin yake domin harga Allah baya son suna rabuwa amma ya zai yi ko ta zauna fitina zai dinga jawa kansa gashi kuma zai koma kwara Fateema baza ta bishi ba wannan karan sabida zasuyi wani taro a makarantar da take aiki dole ya barta taje. Hannunta ya kamo tare da cewa. "Cutie karki damu kije ki dawo hmmmm zaki shaaaa." Da sauri ta bud'e motar suna dariya bata bari ya k'arasa, lek'ansa tayi sunata dariya yace. "Idan kin shiga kicewa Fateema ta fito mu tafi." Baki ta turo ya shafa kansa ganin harta mai fassara ya kashe mata ido d'aya sannan ta tafi, tasan komai shi kenan yanzu shida Fateema zasu cigaba da zama sai taji wani iri a cikin zuciyarta da kyar ta iya fad'an sakon sannan Fateema ta fita, chuchu na ganin haka ta kalli su Haleema tace. "Kuzo muje wajan Yaya Sadeeq ya rage mana hanya duk da munyi fad'a." Tashi suka yi da sauri suka k'arasa wajan motar yana kokarin tadawa suka rok'esa, sai da ya fara dank'arawa Chuchun harara kafin yace. "Ku shiga amma wallahi badan halinku ba ku dukan sakarkaru kawai." Shiga suka yi ya ya dinga jan Fateema da hira dan ya denajin muryoyinsu musamman ta Chuchun da take kamar ta gyare kyar-kyar-kyar. Yana zuwa suka fita chuchu ta kallesa shi kuma yak'i bari su had'a idanuwa sabida mugun haushinta yake ji sabida yadda yaji zata ta6a mai mutuncin matarsa uwar d'ansa. **** Washe gari bayan anyi suyar nama an kasa kowa an bashi. INdo ta kimtsa musu kaya itada ayman da Nafeesah da daddare Sadeeq yazo gidan ya kuma siyo mata wasu abubuwan da zata buk'ata na ayman sannan ya tafi. Washe gari da kanshi ya shirya zuwa kaisu sumaila tun a hanya suka fara jin kewar junan su sai dai yayi mata alk'awarin zuwa duk sanda ya dawo kano. Yana kaisu ya juyo dan INdo har kuka tamai wanda da kyar ya lalla6a ta sannan ya tafi bayan ya bata kud'i tak'i kar6a sabida akwai na barkar data samu a hannunta... *HAJJA CE* [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...
Chapter 47 · 0% Book details