Sashe 43
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* Page *35* Shirin zuwa Sumaila kauyen sani suke farin ciki ya cika zuciyar INdo har ta kasa 6oyewa, kallonta yayi bayan ta rufo d'akinta ta juyo gashi cikinta ya fito yace. "Cutie koma d'aki gaskiya mun fasa zuwa." K'irjin INdo ya shiga bugawa hankalinta duk yayi mugun tashi ta kallesa dan san tabbatar da maganarsa. Gani tayi yana dariya hakan yasa ta yin kansa zata dokesa yayi saurin guduwa cikin shagwa6ar da ta farayi wadda yanzu take neman zame mata jiki tace. "Ka tayar min da hankali Allah ya dawo damu lafiya sai na rama." Fitowa suka yi suka shiga mota Sadeeq ya d'auki hanya, wannan karan cikin hira suka ta kai da ka gansu kasan masoyane sa6anin lokacin da aka ce ya kaita garinsu ya dinga kumbura tamkar wanda aka sanyawa yeast. Cikin kwanciyar hankali suka shiga garin sumaila, suna zuwa kan kwanar da zasu shiga kauyen sani adeeq ya kalleta yana murmushi yace. "Cutie ga barkono da gyad'a bazaki siya bane?!" Juyawa tayi tana kallon gurin kafin tace. "Eh wallahi kuwa, dan Allah kaje ka siyo min kwano d'aya-d'aya." "Ke wasa nake miki ni." Ya fad'a yana tafiya, kallonsa tayi shima ya kalleta tare da d'aga mata girarsa. Hannunsa yasa ya janyo nata yana matsawa ta lumshe idanuwa tana shafar cikinta da d'ayan hannunta. A k'ofar gidan su yayi parking, gidan yana nan yadda yake tun lokacin da Abubakar ya gyara musu katangar su ya maida ita ta bulo sa6anin da datake na k'asa. INdo ta kallesa tare da Kama hannunsa tace. "Wait for me, naje na sanar ma Inna zaka shigo ku gaisa." "Hmm lalle wariyar launin fata, meyasa ni bazan shiga direct ba sai an wani yi min iso? Ban yadda ba tare zamu shiga kema ai idan mukaje gidan Mama wani sa'inma kina rigani shiga." "Hehehehe lallaima, toh ai ni macace zan iya shiga direct, kaifa sabida su Mubasheer na zuwa su shiga kai tsaye kasa duk muke kulle gidajen sai an buga munji ko waye sannan mu bud'e." "Toh ai ni har yanzu saurayi ne, su kuma su Inna sun tsufa toh meye a ciki." "Kai My super glue, wallahi Inna ta ba tsohowa bace rayuwa ce kawai ta maida su haka amma ka bari na kammala karatuna sannan cinikin zo6o ya kankama zaka sha mamakin Inna da baba wallahi. Kuma kasan dai ai abban ku dasu Mama sun girmi su Innata." "Kaiii cutie..?!" "Yanzu dai bazaka barni in shiga ba." Tayi maganar tana turo baki,janta yayi kasan cewar tinted glass ne yasa ba'a ganinsu. Sadeeq ya shafo cikinta tare da cewa. "Yau dai ina zata ga k'ok'arina, but dan Allah cutie karki bari ta ankara harsai nazo mun gaisa na fito, wallahi kuma sai naji inajin kunya." "Kunya kuma? Hahahah ta6 ai aikin gama ya riga ya gama, yanzu wannan abun taya yaya za'aiyi ya 6oyu? Dama hijabi ne ko duguwar riga shine zan iya d'anyin dabara amma ai yanzu kuwa ka makaro hakan nan zan shiga Inna ta gani kuma ka shiga ku gaisa da ita." Sadeeq ya turo bakinsa tare da dafe kuncinsa yana kallonta yace. "Toh ya zanyi? Dole na shigo tunda an banike." Tana dariya ta bud'e k'ofar yaran unguwar da suka zo gurin suka dinga kallon INdo wasu na cewa itace wasu kuma suna cewa ai k'anwar Inna ce dan ga kama nan. Gidan ta shige tana dariya jin abinda suke fad'a, tana zuwa tsab ta ajiye cewa itace 'yar fari ta d'ane Inna dake sharce gurin da tayi wanke-wanke. "Oh ni Maryamu waike yaushe ne zaki san kin girma 'yar nan.?!" Inna ta fad'a tana janye jikinta daga na INdo. Dariya kawai ita kuma takeyi tare da kallon Innar tana cewa. "Kai Inna Oyo-yo fa mukayi, nayi missing d'inku wallahi Inna dake da baba tunda aka kaini baku jeba sai su d'an rainin hankalinnan Sagiru..." "Ga INdo... Ga INdo, yeeeeee sannunku da zuwa." Nafeesah ta fad'a tana rungume INdo, murmushi tayi cikin nunawa wayewa da kuma zaman birni tare da nuna zaman teburin class ta kamo hannunta tace. "Su Feenah 'yan mata daga ina haka..?!" Ta fad'a tana jan hannunta suka nufi cikin d'akin Inna. "Kinga Feenah d'auki tabarmar baba ki shimd'a anan sabida Malam Sadeeq zai shigo su gaisa da Inna." Sabuwar tabarmar malam Hamza aka shimfid'a sannan INdo ta ciro d'ari biyar ta bawa Nafeesah cikin k'asa-k'asa da murya tace. "Mazaki siyo min lemon roba da ruwa zanba shi yasha." Kar6ar kud'in Nafeesah tayi sannan ta fita da saurinta, sai da ta kuma tsayawa wajan Sadeeq yana tsokanarta kafin ta wuce zuwa shagon da zata iya samowa mijin yayarta ta lemo da ruwan jarka. "Sannun ku da zuwa, ke d'aya kika zo ko hardashi me gidan naki?!" "Inna tare muke dashi zai shigo ku gaisa ma, wai ina baba?!" "Malam yana can gurin sana'arsa, bari wani ya shigo sai yaje ya kirasa ku gaisa." INdo dake bakin gadon Inna na k'arfe tace "toh.". 'Dan kuma gyara d'akin tayi sannan ta share shi ta ciro turare a handbag d'inta ta fesawa d'akin da kan tabarmar da Sadeeq zai sauna sannan tace. "Inna bari nace ya shigo ko? Karya ga an barshi a mota shi d'aya." "Toh kice ya shigo barina saka mayafi na nima." Fita tayi suka yi karo da k'awarta Uwani da Sahura da alama sunji labarin zuwanta. "Ahhhh kaga su hajiya INdo amaryar Malam Sadeeq oh harda su abinga." Sahura ta fad'a tana d'aga mayafin jikin INdo, kaf d'insu sunyi wani bululumu dasu Uwani ma harda tsohon ciki kai idan ka gansu bazaka ce k'awayanta bane sabida tsabar yadda kalar wayewar ta bambanta. "Kai sahura kina nan da gulmarki, ku shiga ciki ina zuwa." Ta fad'a tare da dukan bayan Uwani ganin yadda ta rik'e ha6arta tana kallonta. Cikin gidan suka shiga ita kuma ta shiga motar Sadeeq wanda ke jingine jikin kujera ya sanya hularsa a fuska yana kuma zagaye kwantaccen quarter million d'in fuskarsa. Jin an bud'e k'ofar motar ne yasa shi cire hularsa ya kalleta, zama tayi tana kallonsa da murmushi a fuskarta yace. "Uhmmm wato anzo gida harma kin manta tare muka zo ko?" Hannunsa ta kamo cikin nata cikin kalar jimami tace. "Ni na isa, tunda na shiga mafa koda Inna bamu gaisa ba kuma babu kowa duk basa nan amma ni banajin zan iya mantaka a yanzu domin ka zama ni na zama kai kadena sawa ranka cewar duk inda zan shiga wai Zan manta dakai no, idan nayi haka toh Zan iya mantawa da kaina nima." Sadeeq ya lumshe idanuwa tare da jan hannunta murya a shak'e cikin wani irin salo yace. "Kina nufin kenan munyi *MUSAYAR ZUCIYA* dani dake a yanzu? Ba kamar da ba yadda kike nuna min cewar zuciyarki ta M twinnie ce shi kad'ai yanzu zaki iya mallaka min ita...?!" "Sosai ma kuwa na baka ita ina fatan ka rik'eta amana. Anan aka d'aura mana aure dan haka anan na kuma baka amanar kaina da duk abinda ya shafeni." "Na kar6a cutie Allah kuma ya bani ikon rik'ewa gam-gam, a baya ma *Illar Zuciya* ce tasa nake ganin kamar anyi min ba dai-dai ba amma a yanzu..." Yakai bakinsa kan hannunta ya sumbace shi yana kashe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana dariya. Nafeesa ta hango hakan yasa INdo fitowa da sauri. Amsar aikenta tayi ta shiga ciki Nafeesah kuma ta tsaya a gurinsa suka dinga hira har su Shehu suka dawo suma suka gaida shi. Cikin gida kuma INdo ta gama jerawa Sadeeq abin tarba dan inna ta gama dafa wake da shinkafa Allah sarki harda yanka mai lawashin albasa kuma duk INdo bata hana ba domin ta haka ne zata iya kuma tabbatar da kaunar da yake cewa yana mata dan marigayi baya kyan-kyamin duk abinda zata bashi bare yanzu tasan kanta tasan me takeyi ta kuma san waye mijinta. "Lallai INdo wai duk malam Sadeeq d'in kikewa wannan tanadin?!" Uwani ta tambaya tana ta6e baki, gani take kamar INdo ta zurma da yawa duk miji akewa wannan hidimar. "Toh Uwani bakin ciki kikeyi ko me? Ina zan samu kifi ma dan yana son wake da shinkafa da kifi ko dafaffen kwai." "Ta6 lallai INdo Hamza, toh k'ila dai yana baki kema ba irin muba da sai dai komai kayiwa kanka." "Kwaji dashi gulmammu, Inna bari naje nace ya shigo." Tana fad'a ta kuma fita tace ya shigo. Jerawa suka yi shida Nafeesah yana kallon INdo daga baya. Gaskiya ikon Allah baya k'arewa a duniya ko kana menene sai ya nuna ikonsa akanka yau shine da INdo harda kunshin cikinsa a jikinta "Allah astagfurullah." Ya fad'a cikin ransa tare da shiga gidan yana sallama, su Sahura da Uwani suka amsa bakinsu a washe yayin da Inna ke tsaye kanta a k'asa sam bata iya kallonsu tun zamanin Abubakar. Cikin d'aki Nafeesah ta shigar dashi ya zauna yana sosa keya yana shafa wuya. Daga bak'in k'ofa Inna ta tsugunna suka gaisa da Sadeeq sannan su Uwani ma suka sake gaidashi duk da cewar sun gaidashi a cikin mota INdo ta kallesu tare da makewa Sahura hannu ganin yadda take leken sadeeq tana wangale baki. "Kedallah can malama kina da miji kina kallon mijin wasu haba." "Kai INdo bana san herri." Tashi Inna tayi ta shiga rumfar malam Hamza bayan ta tura Nafeesah tace ta kirasa. Kallonsu tayi tace. "Zan shiga daga ciki, karku ce na barku anan." "Lallai ma INdo toh ba abinci zaici ba? Toh ki zauna muyi shira mana kafin ya gama." Uwani ta fad'a tana hararta cikin jin haushin yadda take wani nan-nan da malam Sadeeq sai kace su basuda mijin. "Toh kuje ku gama muna nan hajiya INdo." "Toh hajiya Sahura." Itama ta fad'a tare da shiga cikin d'akin. Kallonta yayi ta zauna kusa dashi tare da d'akko Coca-Cola ta bud'e mai cikin halin damuwa tace. "Kayi hakuri kasha a haka da bakin jarkar, nan gidan bamu da kofuna kaji my super glue ka daure." "INdo Aisha ta zaria med'an kallabi..!" Ya fad'a tare da matsawa kusa da ita. Lek'awa yayi k'ofa aikuwa karaf suka had'a ido dasu Sahura