Sashe 50
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba, amma kaga ba dad'i ka kyalesu basu yi niyar tafiya ba toh ka kyakesu dan Allah." "Shikenan toh bari naje d'ayan gidan ai Fateema na nan." Yana fad'a ya fita INdo ta bishi da kallo, ai dole yace haka tunda ta dawo gurin sa. Tashi tayi ta koma falo wajan su haleema suka fara murnar dawowa da hirar yaushe gamo. Sai da akayi magariba sannan su Haleematu suka tafi ita kuma ta cigaba da gyara kayanta. Har kusan tara na dare Sadeeq be shigo gidan ba hakan ya 6atawa INdo rai ganin ko dai ya dawo da itane dan ya fara wulak'anta ta. Shirin bacci suka yi itada Ayman gashi ko gen ba'a kunna musu ba kuma bata damu ba domin a can gidan su ko wearing na nefa basu dashi, tana gamawa tayi kwanciyar ta zuciyarta na k'una ta janyo pillow ta rungume tare da rufe idanuwa. Sai wajan 10:15pm ya shigo hannunsa rik'e da ledoji, kayan ya ajiye a falo sannan ya fita ya tayar da injin taja tsaki tamkar yana gurin ta kuma rufe idanuwa dan ba k'aramin haushinsa takeji ba na watsar da su d'in da yayi. "Cutie..! Cutie..!" Yaji shiru sai ya shiga cikin d'akin, kwance ya gansu da alama sunyi bacci ya lalla6a ya k'arasa kusa da ita yana son juyo da ita yaji tayi tauri hakan ya tabbatar masa da cewar idanunta biyu. "Haba cutie ba Oyo-yo shine zaki zo ki wani kwanta tashi muje falo." "Sorry bacci nake ji ka koma inda kafi so." "What..?!" Banza tayi mai ya kuma komawa wajan fuskarta yana matsa hannunta yace. "Amma ki bari sai munzo kwanciya sai muyi wannan wasan but yanzu dai taho muje falo." "Nace kayi tafiyar ka wajan matarka, nasan dama can itace za6in zuciyar ka bani ba da aka lik'a maka, toh kaje katafi gurin Fateema daka fi so na bar mata kai. Banda mutuwa ma me fallasa ai da hakan bata faruba bare kamin wulak'anci harda cewa toh kaima ka tafi wajan Fateema shine sai yanzu goma da wani abun zaka ce ka dawo in tashi." Ta k'arasa maganar cikin kuka tare da tura fuskarta k'ark'ashin pillon da kanta yake kai. Ba k'aramin tashin hankali Sadeeq ya shiga ba jin abinda take fad'a, ya janyo ta yana lallashi kan ta sanar mai da abinda yayi mata amma tak'i, har zai rabu da ita yaji bazai iya ba sabida zuciyar da take tsananin sonta tak'i jin haushinta sai ma k'ara k'ask'antar da kansa da yayi yana cewa. "Kinga ba wai da gangan kika ga nayi dare haka ba no, ana yin sallahn magrib muka tafi gidan wani malami nida Abba bamu dawo ba sai bayan sallahn isha'i naje nakaisa gida sannan nayo muku siyayya naje ko dad'ewa banyi ba a gidan Fateema nayo nan amma shine zaki min wulak'anci ko? Shikenan tunda har kin fara yi min mumunan zato." Yana fad'a ya fara k'ok'arin sauka a gadon sai kuma yaji ta rik'osa, itama bazata iya fushi dashi ba ya lek'a fuskarta ta kallesa sannan ya tashi tare da d'agata suka nufi falo. "Cutie ki dena min saurin fushi bana so yana sani cikin damuwa da tashin hankali kinji?!" "Toh amma nima ka dena barmin gidan ka dad'e baka dawo ba tunda kana garin." "Insha Allahu." Ya fad'a, kitchen taje ta d'akko plate da cups ta dawo. Gashasshiyr kaza ce da aka sanya mata kwai tasha kayan lambu ga yajin tafarnuwa suka zauna suka ciyar da juna ranar sunyi kwanan farin ciki marar bayyanawa bare rubutawa. Satin INdo uku da dawowa da kyar da nuna jajircewar shine mijin ba ita ba ta yadda zata bisa zuwa kwara state sabida ta kafe ita karatunta zata koma amma yak'i har kuka tayi suka yi fad'an kwana biyu amma yaki sakkowa dole ta hakura ta bisa suka tafi aka bar Fateema... Nd Page finale is loading #love you #my fan's *HAJJA CE* [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...