← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 53

Sashe 6

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yasa shi cewa. "Naga alamar baki da kunya Aisha, toh bazai fito ba ki shiga ki fito dashi fitsararriya kawai. Kai kuma SS ne ko d'an sanda ko soja ko menene da ta d'add'ago ka kuka zo nan..?!" "A'a mu mune 'yan kungiyar agaji na wannan kauyan kuma turo ni aka yi akan naxo naji abinda yake wakana dan tace bazata yadda ba." Cewar Awaisu Sadeeq yayi tsaki cike da takaici sannan yace, "Toh kaji abinda na fad'a idan ba maita ba waye zai ciji mutum a mafitsara? Kuma ma wai fad'a mace da namiji dan iskanci." "Haka ne kam malam kana da gaskiya ke INdo baki da gaskiya dan haka zanje na sanar cewa ga abinda ya had'a dan haka sai ki tafi gida ki dena wannan halin." Awaisu na gama fad'ar haka ya bawa Sadeeq hakuri sannan ya juya ya tafi INdo na kallonsa zuciyarta fal haushin sa. Da taga yayi nisa ta juya zata yi magana sai taga ashe shima Sadeeq din ya shiga ciki ta d'aga murya saitin k'ofar tace. "Kujini da kyau ni ba mayya bace sai dai kunemi mayya, kuma an dena zuwa bokon ai ba aikin Allah bane rawawul ni INdo na dena zuwa tsefawar yo dan banje ba ai ba mutuwa zanyi ba kuje ku cinye makarantar..." Suna jinta suka yi mata banza Abubakar ya shak'a iya shak'a Allah-Allah yake ya shirya yabar garin dan takaici. Ita kuwa tana gama fad'a tayi tafiyar ta gida tana zagin su tare da d'aura aniyar baza ta sake zuwa makarantar ba tunda ai sai taje zasu ganta har suyi mata maganar banza. K'arfe 3:34pm Abubakar ya idar da alwalar la'asar yana jiran Sadeeq su wuce masallaci dan da sunyi sallah yake son dawowa ya wuce gida. Jerawa suka yi suna tafiya suna hira abinsu gwanin ban sha'awa mutane sai kallansu ake yi. Sagiru dake tsaye a k'ofar gida ya hana INdo fita ya tsaya yana kallonsu, ita kuwa INdo ganin yace baza ta fita ba yasa ta komawa cikin gida. Dai-dai katangar gidan zasu wuce kawai Abubakar yaji an cillo wani abu ya rufe mai fuska suka tsaya ya cire yana dubawa yaga hijjab ne yayi dik'il-dik'il dashi ya yarda shi, kafin ya kuma yin taku d'aya yaji an kwad'o mai wani abu a gefen wuyan sa ya kalli k'asa takalmi ne d'an madina silifas yasha d'aurin leda a wajan sanya d'an yatsa suka kalli katangar da ake yo jifan kawai sai suka ga hannu hakan yasa ran Abubakar ya kuma 6aci sai ga k'afa can sai gata ta dirgo tim...! Da sauri suka matsa inda take tana d'agowa ta gansu a tsaye a gabanta bata san lokacin da ta kuma kurma ihu ba tare da juyawa zata kuma kama katangar ta koma gida Sadeeq yayi saurin janyo rigar ta mutane suka taru yayin da INdo ke faman basu hakuri. Gabaki d'ayan ta tsami take yi da zarni Abubakar ya tsinketa da mari tare da dungure mata goshi sannan Sadeeq ya sake ta Abubakar yace. "Baki da mutunci ko?Ke mara kunya kinga abubuwan tsimmar da kika watsa min? Toh ki saita kanki idan ba haka ba kafin nabar garin nan sai na ji miki ciwo idiot kawai sai zarni kike yi mai fitsarin kwance jibe ki dan Allah da wani billanki a goshi kamar zanan one..." Yana kaiwa nan yayi gaba yayin da Sadeeq ya harare ta shima yayi tafiyar sa suka shige masallaci. Mutane kuma suka k'arasa wajan INdo da tayi shiru tana kallon jikin ta. "Kedai INdo wallahi kowa sai yace baki da kunya, suma bak'i har kin fara yi musu.." Cewar Rabi bala wadda makarantar su d'aya amma ita a js 3 take, INdo ta harareta tare da cewa. "Anyi d'in kizo kiyi kuli-kulin tara sisi dani munafuka kowa yasa dake.." "Ke INdo dan ta gaya miki gaskiya shine zaki mata rashin kunya." Wani yaro Bala ya fad'a ta kuma juyawa kanshi cikin masifa tace, "ji banza kai tunda ga kan sunanka ansan kai d'in bala'i ne banza Bala bala'i mtwww." Nan da nan gurin ya kaure ita kad'ai su kuwa wajan mutum goma amma babu wanda ta ragawa, Sagiru k'aninta ya jata suka shiga gida sai da suka kai har tsakar gida sannan ta ture shi. "Dalla can ni kyale ni banza." Ruwa ta kindima a buta ta shiga band'aki shi kuma Sagiru ya kuma fita waje yana cewa, "Dama na barki sunyi miki shegen duka masifaffiya kawai." Fitowa tayi jikinta sharkaf da ruwa wanda da alama wanka tayo amma ba a saka sabulu ba. Cikin d'aki ta shiga Inna tana sallah ita kuma taje ta sake kaya sannan ta d'an d'ibi man shanu ta shafa dama tana sato chuck ta d'auki d'aya ta daddaka tayi hoda da shi ta shafa tayi kwalliya jagirar nan har wajan kunne ta sanya kantakile a lab6anta sannan ta d'aura d'an kwali tayi waje Inna na ta faman kiranta amma ko waigowa bata yi ba. K'ofar gidan taje ta zauna tana jiran su dawo, ana idar da sallah suka dawo gida tun daga nesa suka hangota kamar aljana dariya ta kusa kama Sadeeq ya daure yak'i yi a fili yayin da yace wa Abubakar. "Twinnie ga tanan fa kayi mata gorin wanka tayo tazo ta nuna maka." Dai-dai suka je k'ofa Abubakar ya kalleta wani takaici ya kuma kamashi INdo tace. "Gani yanzu kunsan abinda yasa bana kwalliya? Sabida mazan garin nan sun fiya kallona shi yasa amma ni bana zarni." Ta fad'a tana bubbuga kanta tare da sosawa, mtwww "ke wai kinga sa'anki anan gurin ne?" Kallon shi tayi tare da kura mai ido tamkar zata cinye sa ya d'aga hannu kamar zai bugeta tayi saurin matsawa tace. "Yoo ni ina ruwa na wannan ai ba wasa bane kuma idan anyi duniya da manzo na dena zuwa makaranta wata za'a sake min irin ta 'ya'yan gidan kansilan mu." Mtwwww Abubakar ya ja tsaki tare da shigewa gidan, itama ta doka cinyarta ta kalli Sadeeq tace "Duk haka kuke babu me imani." Sadeeq ya bita da kallo yana tunanin k'ila tana da aljanu yace. "Kije kiyi brush." Abubakar daya fito da car key dinsa yace. "Bakin ta kamar kashi. Kinga yadda ake son aga hakora ba irin naki ba kamar kina shan d'orawa." Ya fad'a yana nuna mata hak'orinsa fari kal. Wucewa yayi gurin motar sa Sadeeq yabi bayan sa dan suyi sallama, suna kallon sanda ta wuce tana sanya k'asan hijabin ta tana goge hak'orin. Sallama suka yi abubakhr na sake bawa Sadeeq shawarar ya k'arbi transfer ya k'ara da cewa. "Bazan sake zuwa garin nan ba sai dai na hakura har ka dinga zuwa can gida ma dinga had'uwa amma wannan garin beyi min ba." "Insha Allahu doctor karka damu kayi min addu'ar abinda yafi alkairi." "Toh amin ni na wuce." Suka yi sallama ya tafi shima ya Shiga gida. Tunda ga ranar kuwa har aka yi hutu Sadeeq be sake ganin INdo a makaranta ba sai dai a unguwar su ya ganta suna wasa ko da farantin tallah.. *HAJJA CE* [7/1, 4:49 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. Note:- Assalamu alaikum masoya wannan labarin, dan Allah adalci d'aya zaku yi min idan kuna so toh ku ringa adanawa. Idan nayi nisa kuka ce na turo muku sai na rasa yadda zanyi gashi wayar ba lafiya gareta ba dan Allah kuyi min wannan agajin please. Page *5* Tafiya take tana dirzar hak oran ta da k'asan hijjab ko zata samu suyi fari itama, ai kuwa da ta gogo zata duba jikin hijjabin taga gurin yayi yellow ta girgiza kai tare da cewa. "Kai...! Kuma fa da gaskiyar sa wallahi, dan gahi ina kankarowa yalo na fitowa, amma shi hak'oran sa har wuta-wuta suke yi sabida kyau." Wani shago ta tsaya a nan kusa da gidan su Sahura ta kalli me shagon tace. "Idirisu kana siyar da burushi da abin matsawa...?!" Yace "A'a bana siyo shi INdo sabida ba'a siyan shi, sai dai kije kasuwa ranar laraba ki siyo." Tsaki tayi tare da fad'awa gidan su Sahura, ita dai sam ba ta son zaman gidan su domin bata ta6a yin cikakkiyar awa d'aya sai ta fita, bata taya Inna da aikin komai sai dai da taji yinwa taje taci idan ba'a gama ba ta hau sababi. Sai kusan magariba sannan ta koma gida shima dan tana son tambayar baban su kud'i zata je mahad'a wato inda 'yan mata da samari ke had'uwa suyi hira. "Baba sannu da gida." Yana jin haka ya san akwai abinda zata tambaye sa dan haka yayi mata banza, ta kuma fad'a sai ya d'aga mata kai kurum ta ciza yatsan ta cikin ranta tace, "Wallahi sai ka bani abinda nake so, kaji shi daga gani na baba yayi wani shiru." Kusa dashi ta k'arasa ta zauna shi kuma da yake a kishin gid'e yayi saurin dan ne aljihun sa me kud'in a ciki dan ya san tun da ta fara wannan shisshige mai d'in toh rok'on sa zata yi shi kuma naira d'ari da sittin ne garesa kuma goma ba zai bata ba dan yau da kyar ya samu a gurin sana'ar sa. INdo ta cire hijjab d'in jikinta sannan ta kalli mahaifin nasu duk da ya had'e rai hakan besa taji zata fasa tambayar Sa ba, cikin rashin ladabin magana ta kallesa tace. "Baba nera (naira) hamsin zaka bani anjima zanje mahad'a, daga can idan naje kaga zan siyo burushi harda abin matsawa sai kuma ka bani nera ashirin wadda zan siya abubuwa naci.." "Bani da kud'i uwata yanzu, amma ki bari gobe idan na samu zan baki." Kallonsa tayi da alama bata yadda da abinda yace ba, ganin tana kallan sa yasa shi kuma kishin gid'a kan aljihun kud'in yana k'ara volume d'in rediyon sa duk kuwa da yana jin ana k'iran sallar magriba amma ba shi da alamar ta shi yayi alwala. "..'Yar nan zo kije kiyi alwala bana jin yauma ko sallar asubahi kinyi bare kiyi sauran." Inna ta fad'a tana kashe wutar kararen da ta gama tuwo. INdo naji ta turo baki sam bata kaunar taji ance tayi wani abun a harkar
Chapter 6 · 0% Book details