← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 53

Sashe 37

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce ba. 10:35pm yana zaune a falon Fateema ya shiga cikin tunani yaji Fateema na shafar sajan sa ya kalleta yana murmushi tare da lumshe ido tamkar ya sha kwaya don sunyi wani iri tace. "Baby ya kamata ka tashi kaje gidan Aisha dare nayi maka fa." "Ai bata nan taje garin su." Ya samu kanshi da fad'ar haka yana kallonta, Fateema tana da kyau sosai domin tafi INdo haske da idanuwa ga gashi amma cikar hallitta gaba da baya INdo tafi Fateema. Ya lumshe idanuwa tare da janyo ta jikinsa yana shafar bayan ta, sai dai cikin ransa so yake yaga INdo kota halin k'a-k'ane amma ya rasa hanya. Friday morning INdo ta shirya tsab ta tattara littattafanta tasa mayafi ta fita, bud'e gidan tayi sannan ta rufeshi daga waje ta tari napep ta wuce makarantar M.M HARUNA. Submitting d'in books na Home work d'in da aka basu aka yi dan malamin ya duba yana zuwa kan na INdo yaga ba kanta hakan yasa ya kira sunanta da ya gani a jikin littafin yace idan an tashi taje ta samesa a office. Hakan kuwa aka yi ta sami M.m harunan a office d'insa ya nuna mata guri ta zauna yace. "Aisha Hamza daga wace school kika taho nan..?" INdo tace "Gaskiya malam ban gama makaranta bani, ni yanzu ne dai nake son yi sabida gaskiya kaga mijin da aka bani d'an rashin mutunci ne kuma a jami'a yake koyarwa, nidai malam dan Allah kuyi iya k'ok'arin ku wajan ganin na iya nima shida matarsa duk malamai ne shi yana min gori kar nan gaba itama tazo ta fara yi min.." M.M HARUNA yace "Toh karki damu Aisha tunda dai har kinsa a cikin ranki zaki koya toh nasan ba zaki sha wahala ba, yanzu zaki fara tun daga kan alphabets kije ki kwafe su cikin note book d'inki gobe ki kawo min ki kuma dinga k'ok'artawa wajan yin magana da turanci koda kuwa za'a yi miki dariya dan ni daga yauma ki dena min hausa da yawa understand.?!" "Toh malam yes." Ta fad'a tana rufe fuska yayi dariya shima tare da cewa "Good." Littafi ya d'akko sabo ya rubuta mata from A-Z yace taje tayi irinsu duka. Allah sarki da yake tana so ba taji wani girman kaiba ta kar6a tana komawa gida a kwance ta tarar da Sadeeq har ya shigo gidan da yake babu abinsa padlock daga waje, ta wuce cikin d'akin ta yayi saurin tashi ya bita a baya ya tsaya a wajan wardrobe ko kallansa ba tayi ba bare ta gaida shi yace. "Aisha fitsara.., wato ni kika hana shigowa gidan ko? I think nawa ne, koda yake kin ce gidan hayane amma wayake biyan kud'in gidan.?!" Ko kallansa ba tayi ba ta zare hijjab d'inta ta ninke tasa a wardrobe taje zata shiga toilet Sadeeq ya fizgota nan ma tak'i yin magana ganin haka yasa shi fita yabar gidan, yana tafiya ta kuma kullewa taje tayo fitsari ta shiga kitchen ta dafa abinda zata ci ta koma falo taci ta k'oshi sannan ta fara assignment d'in ta tana gamawa tayi bacci bata sake bud'e gidan ba sai washe gari da zataje makaranta. kullum haka take yi bata bari su had'u dashi kwata-kwata. Ranar litinin Fateema ta fara zuwa gurin aiki, damuwa da shiga tashin hankali suka taru suka yiwa Sadeeq yawa ya rasa yadda zai yi da INdo, sam ta dena bari ya kwana a gidanta sabida da anyi magariba zata 6ame gidan har Fateema ta gano suna da Matsala a tsakaninsa da Aishan sai dai bata nuna mai san jin abinda ke faruwa kasan cewar bata son shiga cikin abinda duk be shafeta ba. **** "Abba wannan karan ina son tafiya da Aisha sai dai tak'i yadda ma muyi maganar da ita." "Sadeeq kenan yanzu kai da iyalinka ka kasa shawo Kansu waye toh kake son yaje ya shawo maka kanta? Duk tsaya ai kaine kafi mu kusanci da ita ya kamata kasan yadda zaka yi ta yadda har Ku tafi tare." Shiru Sadeeq yayi ya rasa ya zai yi gashi ranar Thursday yake son komawa, ga Fateema tunda ta fara zuwa makarantar nan yasan itama ba yadda zata yi ta bishi ba kasan cewar ya mata alk'awarin idan har takardar aikinta yafito toh zai barta tayi, gashi bazai iya tafiya shi kad'ai ba tunda ya riga ya saba kasan cewa da mace. "Sadeeq ya kayi shiru? Idan ita Aishan tak'i binka ba saika tafi da wadda kuka saba tafiya tare ba." "Abba ai Fateema ta fara aiki dan tun yanzu ma ta fara nuna k'in bina wallahi." "Toh ya zaka yi da rashin iya yaren su da ita Aishan bata iya ba? Kar taje tana baka matsala fah tun da a baya haka kace." Kan Sadeeq a k'asa yana goga yatsansa a k'asan carpet d'in d'akin, shi kansa yasan ba zai iya tafiya kwara state ba sai da matarsa a kusa dashi gashi abban da zai temaka mai shima yace yaje su sasanta da d'aya a cikin su. "Shikenan Abba zanje na kuma tambayar su, sai da safe Allah ya k'ara girma." Abba ya kallesa tare da cewa "Amin Sadeeq a gaida min dasu baki d'aya. Fita yayi ya wuce gidan Fateema ranar ma anan ya kwana. Washe gari ta kasance Wednesday bayan Fateema ta tafi gurin aiki misalin k'arfe goma Sadeeq ya shirya cikin wani rantsatsan yadi mai matuk'ar taushi sky blue ya d'ora hula yasa turare sannan ya fita. Gidan INdo ya wuce yayi niyar yau kota halin k'ak'ane sai ya shiga gidan ya kuma nuna mata kuskuranta na rainin da tayi masa. Cikin sa'a ma yana zuwa ya tarar da gidan a bud'e nan da nan zuciyarsa ta sanyaya, a k'ofar gidan yayi parking sannan ya shiga gida bakinsa d'auke da sallama. Takalma ya gani a k'ofar d'akin hakan ya tabbatar masa da cewar bak'i tayi, ya shiga ciki da mamaki sai yaga su Nafeesa, Sagiru da Shehu sai wani wanda besan ko waye ba amma da alama tare suke. "Yaya Sadeeq ina kwana?!" Yaji Nafeesa ta fad'a bayan ta durkusa k'asa, murmushi yayi tare da k'arasawa ciki yana amsa mata su kuma Su Sagiru ya basu hannu suka yi musabuha. "Yasu Inna da malam Lafiya dai ko?" "Lafiya lau, sunce suna gaida kai." "Ina amsawa yaushe zaku koma..?!" Sagiru yana shafa k'eya kasan cewar yanzu duk sun girma yace. "Nan da anjima zamu wuce." "Okey tom Allah ya kaimu." Yana fad'a ya wuce d'akin INdo a tunaninsa zata biyo shi irin abin nan na tsakanin mata da miji da idan ya dawo zata bishi taji abinda yake da buk'ata ko kuma a sake yin wata special Oyo yon amma yaji shiru sai ma dariyar ta da yake jiyowa ya dafe goshi tare da rintsa idanuwa daga bisani ya mik'e yabar gidan. Tunda ya fita be sake dawowa ba sai da akayi magriba sannan ya shiga gidan lokacin bata rufe gidan ba suna zaune da 'yar mak'otansu Mansura suna kallo suna hira. Ganin ya dawo ne yasa Mansura tayiwa INdo sallama ta tafi shi kuma ya zauna a falo yana kallonta. Sanye take cikin atamfa me ratsin green, white, brown, da purple d'inkin riga da zani sun cika ta sunyi mata d'as tayi kyau sosai ya kalleta amma ita hankalinta na kan TV, sadeeq ya d'auki remote ya kashe TV d'in tare da kallonta sai yaga tana kokarin mik'ewa ta shiga d'aki yayi saurin rik'ota ta fara fisge-fizge zata kwace ya jingina ta jikin bango bayan ya rik'e mata hannuwa. Murya tamkar ta marayan daya kwana biyu be samu abin kaiwa baki ba Sadeeq yace. "Aisha what's wrong with you ne ah? Dani zaki yi gaba? Kin manta matsayi na a wajanki ne? Ko baki san wannan abin da kikeyi min ba kina cikin fushin ubangiji ba? Please Aisha ki bari mu fahimci juna I beg of you please..." Still shiru tayi Sadeeq yakai fuskarsa saitin k'irjinta yana goga fuskarsa yaji tayi magana. "Wai malam Sadeeq ya haka ne?!" "Aure ne haka if you don't know." INdo ta dinga mai-maita if you don't know cikin zuciyar amma ta kasa gane me if d'in take nufi dan tasan don't know da you dan haka tayi tunanin ko wata maganar ya gasa mata dan haka ranta ya kuma 6aci ta zabga mai harara yakai bakinsa ta kauda kai amma duk da haka sai daya laso idon rashin kunyar da harshensa yace. "Aisha you don't know me shi yasa kike min duk abinda kikaga dama ko.?!" INdo ta ta6e baki tare da yatsina fuska ta daddage tace. "Ta6 I know you're noun, ko banda malam sadeeq kana da wani sunan..?!" "I know you're noun." Ya maimaita a fili yana kallon gefen fuskarta still yana rik'e da ita a jikin bango ya rasa gane me take nufi hakan yasa shi lek'a fuskarta yace. "Mene kuma noun a cikin maganar da kika min Aisha.?" Ta murgud'a baki tare da cewa. "Sakar min hannu malam Sadeeq, kace ban sanka shine na nuna maka nikuwa na sanka, noun is a name of person, animal, place or tins (things) ko ka d'auka yanzu ma banajin abinda kake fad'a? Never past tense kenan wallahi (Da kenan)." Sadeeq ya cuno baki, so yake yayi dariya amma baya son yayi taji haushi dan so yake ya lalla6a yayi mata wayo ya samu ta bishi dan haka ya dinga gumtse dariyarsa ita kuma tana k'ok'arin kwatar jikinta yace. "Very Good Aisha you're trying, but kin san menene? Ki shirya kayanki gobe mu tafi kwara state a can wallahi zaki iya komai domin su basa Hausa sosai kafin kiga bahaushe sai kin dad'e, muje ki shirya kayan ki sai na taya kima." Ya fad'a tare da janyo ta jikinsa ya rungume ta. Cikin sauri INdo ta fisge tare da cewa.... *HAJJA CE* [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...
Chapter 37 · 0% Book details