Sashe 44
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da Uwani suna lek'owa yayi dariya tare da Kai bakinsa saitin kunnen INdo yace. "Gaskiya d'aliban nan nawa gulmammu ne, sai lek'en mu suke kamar a gidan zoo." Itama dariya tayi cikin hillata da shagalta yaci wake da shinkafar nan dan sai da suka cinye ta cikin kwanon silbar da Inna ta kawo musu. Suma su Sahura da suka kasa suka tsare aka zuba musu sukaci lokacin malam Hamza ya shigo fuskarsa kunshe da fara'a Sadeeq yayi saurin tura kwanon gaban INdo da ragowar lemonsa da ledar yajin ya maze sai wani danne-dannen waya yake shi a dole beci da yawa ba. INdo kuwa banda dariya babu abinda takeyi mai amma still ya maze su Uwani na jiyo ta sai mamakin abinda yasa ta dariyar suke yi. "Sadeequ ashe kunzo? Sannunku da zuwa. Ah kaga uwata an zama manya." Sadeeq ya fara motsi yana gyarawa malam Hamza guri dan ya shigo. Gaida shi suka yi sannan yayi ta sanyawa Sadeeq da marigayi albarka ganin yadda INdo ta canza tamkar ba 'yarsu ba. Tare da malam Hamza Sadeeq suka fita ita kuma INdo ta koma tsakar gida gurin su sahura Inna ma taje ta zauna. Suna zaune Rukayya ta shigo murna ba'a magana sabida ganin INdo da ciki, nan fa suka shiga hira baji ba gani amma duk da haka zuciyar INdo bata manta da Sadeeq a mota ba. Nafeesah ya d'auka suka shiga cikin garin har sai bayan sallan la'asar sannan ya dawo dan su tafi. "Gaskiya Inna zan baki kud'i a hannunki a samu dan Allah a gyara band'akin nan, habba wallahi za'a iya d'aukar larura tunda aka haifeni a haka yake. Ga dubu sha biyar nan ita kad'aice a hannuna nasan k'ila malam Sadeeq zai bawa baba ma wasu amma idan be bayar bama dan Allah Inna a fara da wannan kud'in ko buhu d'aya ne na siminti a siyo a malale k'asan band'akin can kosu Sagiru ne da Shehu sai suyi ai sun iya." Kwallah Inna ta share tare da yin godiya sam bata ta6a tsammanin akwai ranar da 'ya'yanta zasu yi mata wani abunba ganin itama ba tayi wa nata komai sabida rashi gashi ance sai kanayi za'ayi maka. "Inna ya kike kuka? Karki bari na tafi haka dan bazan yafewa kaina ba bayan na barki cikin kuka." Murmushi Inna tayi tare da cewa. "Allah nakewa godiya 'yar nan domin ban ta6a zata zanga irin wannan ranar ba musamman akanki, sai gashi Allah ya shirya minke ya kuma azurtaki gashi har kina tallafa mana da abinda kike dashi, Allah yayi muku albarka dukanku." "Amin Inna ta, karki damu dana gama karatu na kware insha Allah zanyi kud'i duk gidan nan sai an gyarasa." "Toh Allah ya yassare miki." "Feenah dan Allah idan ya koma kwara state zan cewa Sagiru ya kawoki mu zauna tare ko bakya so?!" "Ke! Ina so mana ai wallahi kin more gidan miji INdo." Mtwww "Ban hanaki cemin INdo ba gatsal? Ki kirani yayya Aisha ko Yaya INdo karki sake cemin wani INdo mara kunya." Kallonta Nafeesa tayi tana ta6a baki kafin ta kad'a kai tabar d'akin. Har zaure Inna ta raka ta tana yi musu fatan alkhairi bayan Sadeeq yazo sunyi sallama. Dubu d'aya ta kar6a gurin Sadeeq ta bawa su Sahura su raba d'ari biyar-biyar suka dinga godiya suna k'ara jinjina arzikin da INdo ta samu sannan ta shiga mota suka tafi cike da farin ciki. *** Kwanaki biyar yayi bayan sunje kauyan Sani sannan suka d'aga suka tafi kwara state da Fateema bayan yayi yayi da INdo ta bishi tak'i sabida karatunta. Yana tafiya da kwana biyu tasa Sagiru ya kawo Nafeesa duk ranar school d'inta zasu je tare ta zauna a barandar ajinsu INdo idan sun tashi su koma gida ta koya mata abinda ta iya itama hakan ya k'ara bud'e brain d'inta ga cikinta yana ta girma cikin kwanciyar hankali. Duk wata Sadeeq suke dawowa kuma INdo bata nuna damuwarta duk da bata son tafiyarsa amma bata son nuna mai dan karya kansile mata karatunta, gashi dama ya sanyata a makarantar dare ta islamiya ta matan aure anan unguwarsu hakan yasa ta kuma zama busy tana kuma wayewa ta fannoni da yawa a cikin rayuwarta. Cikinta har ya shiga 10months bata haihu ba sai dai yayi girma har bata iya zuwa ko'ina. Ranar wata laraba cikin dare ta farka lokacin Sadeeq na mak'ale da ita duk da girman cikin jikinta hakan baya hanashi nanik'arta. Kallonsa tayi tana faman rintsa ido cikin wani irin mugun rik'o yaji ta rik'e mai hannu hakan yasa shi saurin farkawa. "Cutie what happen?" Shiru sai cizon lips d'inta takeyi tana matse idanuwa ya mik'e tsaye ya sakko yace. "Cutie kodai haihuwa ce? Bari nazo muje asibiti." A gigice ya sanya jallabiya ya zari mukulli yayi parking lot. Motar ya fitar da ita shiru garin babu kowa ya kuma komawa gidan da kyar ya kimtsata ya fito da ita mota lokacin mak'ocinsa ya leko sabida yaji k'arar mota. Ganin halin da ake ciki ne yasa shi taso matarsa ta bisu zuwa asibitin. Duk ya rud'e ya bugawa Fateema ya gaya mata itama hankalinta ya tashi gashi babu abin hawa bare tabisu gata mace. Ganin abun yayi yawa ne yasa suka kira Sadeeq d'in ciki INdo tana ta kuka ya rik'e hannunta zuciyarsa na bugawa da k'arfi da k'arfi tace. "Dama a makaranta malama tace idan mace zata haihu k'afarta d'aya a duniya d'aya kuma a k'abari. Malam Sadeeq kayi hakuri nasan nima yau dacta zan..." Sadeeq yayi saurin rufe mata baki yana kad'a kai, da k'arfi ta fizge kanta ta juyar da kai tana ci gaba da magana. "Sai na fad'a d'in ka bari in gaya maka mana, dacta zanbi nima yau amma dan Allah tunda ance namiji zan haifa dan Allah koda na tafi malam Sadeeq ka sawa d'an suna Abubakar Sadeeq kar kuma a 6oye mai suna dan Allah." Jikin sadeeq ya dinga rawa gumi gaba d'aya ya gama jik'asa, tana gama yin magana kawai nurse d'in dake gurin tasa hannun zureren jariri ya santalo kan hannun nurse d'in INdo na kwance tayi shiru yayin da Sadeeq ya bud'e baki yana kallon fuskarta gumi na d'iga akan hannunta na jikin fuskarsa.... *Fatan alkairi gareku masoya, a koda yaushe Ina alfahari daku cikin labarin MUSAYAR ZUCIYA. Hajja ce take muku fatan alkairi tare da d'in bin godiya marar adadi* *HAJJA CE* [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...