← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 53

Sashe 17

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki?!" "Eh wallahi Inna ai Rukayya mutuniya tace kinga tunda na tahi ban mance da ita ba." Tashi tayi ta suri takalma tayi waje, a k'ofar gida taga su malam Sadeeq da baban ta amma ta wuce sai tsayawa take suna gaisawa da mutane. Lokacin da su Abubakar suka gama magana da malam Hamza abubakar kasa tafiya yayi domin yana son suyi sallama, k'ofar gidan Rukayyar ya k'arasa ya tura yaro ya kirata ya kalleta sai faman dashare baki takeyi tana rufe ido yace mata. "Humaira zan tafi gida, Zan dawo jibi insha Allahu karki dinga tafiya yawo idan ba haka ba bazan baki komai ba." "Ai bazan yiba dacta, ammafa karkak'i zuwa kaji?!" Yace "Toh Humaira Zan tafi amma fa kiyi wanka ranar dazan zo." Tace "Toh dacta Ina jiranka." Yana tafiya ta koma gidan Rukayya shi kuma ya shiga mota bayan sunyi sallama da malam Hamza da baba iro. Sadeeq yaja mota suka nufi gida. Da daddare suna zaune abin duk ya damu Sadeeq ya kalleshi yana danna laptop yace mai. "M twinnie can you tell me why cared Nd protect her? I know bawai dan wancen dalilin bane tunda gashi har kana cemin zuciyar kace please tell me." Ture laptop d'in yayi tare da kwanciya ya sanya hannuwansa ya tallafo kanshi yana kallon fankar sama yace. "Twinnie bazan 6oye maka ba hakan yasa naje tare dakai muka dawo da ita gida, twinnie I'm in love with her, I can not do anything with out her. Ina son ta zama matata, ina son na mallaka mata ragamar rayuwata koda kuwa bata zama wayayyar da nake da burin aura ba." Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Sadeeq yake kallon Abubakar jin abinda ya fad'a. Ganin Sadeeq na niyar yin magana yasa shi saurin cewa. "M twinnie kayi min fatan alkairi, ka kuma taya ni yak'in neman yarda da soyayyar Humaira please n please twinnie." "Allah ya k'ara dankwan soyayya Allah yasa ayi komai muna nan." Cewar Sadeeq yana kallonsa, Abubakar yayi murmushi tare da cewa. "Amin m twinnie thank you." Kowa ya cigaba da abinda yakeyi zuciyar Sadeeq fal mamaki, shi kuma Abubakar tashi kaddarar kenan auran INdo Allah kadiran alaman yasha. Washe gari Sadeeq ya tafi k'wara state, a day after Abubakar ya shirya tafiya sumaila yayi sallama dasu Mama, sannan ya d'auki k'anwarsu Hawwah ya kaita wani shago yace ta had'a mai kayan kwalliya, tayi-tayi ya gaya mata na meye yak'i tana dariya ta had'a mai komai sannan ya bata kud'i yace tahau napep. Ya wuce a hanya ya tsaya ya shiga wani Boutique ya siyawa INdo wasu tsala-tsalan dogwayan riguna guda biyar da takalma guda uku ya had'asu da kayan kwalliyar sannan ya wuce sani... *HAJJA CE* [7/2, 6:33 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* _Ina ganinku dearest comments d'inku na k'ayatar danifa_ *K'anwata Stylish, my Xoxo, Faxyfation, phartzarah, Nuceeyluv, khady, Mmn gausiya, UmmuMuhammad, Khady M/kano, Mmn nuceey, sumeey Q, Meela adeel, Mummy, Hafsat A Fulani buchi, Hafsat A shitu, aunty Ag, Ummul Meenal, Habeeba M, aunty baraka, Mmn Nazir * gaskiya bazan iya duka ba kuyi hakuri naga nakusa yin rabin wani paragraphs d'in Page *14* Yana zuwa unguwar ya ganta a k'ofar gida a zaune tayi wanka tayi kwalliya irinta zamani lokacin ba'a gama sanin su concealer ba, amma tasa eyeshado red janbaki tayi kuma jagira.Tana ganin mota a k'ofar gidan su ta shek a da gudu tana gayawa su Inna yazo kafin ta kuma fita kamar wata saban kamu lokacin harya fito yana rik'e da murfin ya kalleta itama ta kallesa. Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda getzner light blue anyi mata dinki na dark blue ya d'ora hula fuskarsa har wani kyali-kyali takeyi kawai INdo ta saki baki da hanci tana kallansa kallo na kurrullah tamkar tana son ganin wani abu ya mik'a hannunsa yana zagaya shi a saitin fuskarta tayi firgigita tare da yin dariya tace. "Dacta Habubakar wallahi kanada kyau ta6 heyau na ta6a ganin haka." Murmushi yayi tare da rufe k'ofar ga yara sun fara mai dandazo ya ciro 2k yabasu sannan ya shiga zauran gidan su ta bishi ya tsaya yana kallonta ganin tayi mai wankan dayace tayi harda kwalli sai ya ce. "Humaira babu gaisuwa? Bafa ki gaida niba." INdo tace "Au hakane fa ina yini ya gida ya iyaye..?!" "Lafiya lau baki tambaye ni malam Sadeeq ba why..?!" "Ta6 narasa wanda zan tambaya hewani malam Sadeeq Allah ya tsare ni wallahi." Kyaleta yayi ganin bilhakk'i bata son Sadeeq tun lokacin daya hanata atamfa, kallonta yayi yace. "Ina baba yake? Tace "Baya nan." Abubakar yace "Toh Inna fa?" INdo tace "tana ciki." "Toh jekiki ce zanzo mu gaisa da ita." "Kai dacta Habubakar, kawai kashiga meye na tsayawa ai bazata hanaka ba." "A'a Humaira ba'ayin haka a musulinci dole sai kinje kin gaya mata." "Toh hikenan tunda baka yadda dani ba." Tana magana tana shiga gida, yana jiyo sanda take gayawa Inna sak'on duk maganar da sukeyi yana jiyo su. "Kai Inna toh meye na saka hijjabi dan nace miki dacta habubakar zai shigo. Lallai saban salo." Rintsa ido yayi jin yadda INdon keyin magana da mahaifiyarta, lallai yarinyar nan indai yana sonta yadda yake so toh akwai jan aiki a gabansa. Dawowarta kawai ya gani beji motsinta ba, tana dariya tare da wasa da gefen mayafinta tace. "Tace ka higo an hinfid'a maka tabarma a k'ofar d'aki." Tana gaba yana bayanta har suka k'arasa ya zauna, daga bakin k'ofar d'akin Inna ta tsuguna suka fara gaisawa. Shiru babu wanda ya sake magana sai gasu Nafeesa sun shigo itada k'awarta suka gaidashi, Abubakar yace ma Inna. "Inna dan Allah idan babu damuwa ina son ki bani aron su Humaira suyi min rakiya nan cikin gari." Shiru yaji Inna tayi kafin can kuma yaji tace. "Toh gata nan ai Nafeesah sai tazo kuje tare harda ita." "Toh Inna na gode." Tashi yayi yafita su kuma suka bi bayansa. A baya Nafeesa ta zauna yayin daya kwashe ledojin kayan yasa a k'asa wajan dazata saka k'afa tace ta shiga ta zauna sannan shima ya zagaya drive seat ya zauna tare da tayar da motar suka tafi 'yan kauyan sai gulmarsu akeyi. Cikin garin Sumaila suka shiga INdo badai surutu ba sai labari takeyi musu sanyin A.c yana ratsata ga k'amshi a cikin motar ta kalli Abubakar tace. "Dacta Habubakar wannan motar taka akwai sanyi karmuyi mura a bud'e gilahin." Dariya yayi sannan ya mik'a hannu ya rage A.c ya juya yana kallanta itama shi take kallo yace. "Humaira ya akayi ne?!" INdo tayi dariya tana tafa hannuwa tace. "Meye kuwa, wai Ina zaka kaimu ne hefanan tafiya muke..?" Parking yayi a bakin titi wajan wani shagon saloon ya kalleta yaga sai kallon window take ya juya bayansa Nafeesa sai bacci take a hankali ya mik'a hannu zai ta6a kafad'un INdo sai kuma yayi saurin janyewa tare da bud'e k'ofar yafita. Zagayawa yayi ya bud'e mata ta fito yace su shiga cikin shagon abar Nafeesah tunda tana bacci suka nufi shagon ya tsaya ta glass inyamurar ta hango su ta fito cikin azama. "Hey!good evening sir how are you.?!" "Fine madam how is your business." "Fine..fine oooh." INdo tabisu da kallo sai faman tabe baki takeyi ta samu sumintin gurin ta zauna tana kallon titi. Saidai Sadeeq ya gama gayawa madam Gloria abinda za'ayiwa INdo sannan ya kalleta yace. "Yauwa toh Humaira tashi ku shiga ciki." INdo ta kalli madam gloria cikin mamaki ta maida kallonta gurin Abubakar tace. "Mezai kaini wajan arniya dacta Habubakar? Arniya cefa kake cewa naje gurinta, me zata min...?!" Ganin yadda takeyi ne yasa hankalin Abubakar tashi har mutane sun fara taruwa da k yar ya satayi shiru yace mata. "Kayanki zata baki amma tunda bakya so zomu tafi gida." Da sauri ta nufi madam guloriya tana cemai. "Yo toh ai kaine bakayi min bayani ba."Gloria na gaba tana bin bayanta Abubakar ya girgiza kai sannan ya koma wajan mota yana jiran fitowar Gloria . INdo kuwa suna shiga gurin taga abubuwa birjic ga manyan madubai ta kalli fuskarta sosai sannan ta fara gyara kwallin daya zazzago mata wajan kumatu Tese yarinyar Gloria ta cewa INdo. "Sister come and seat here." Sam INdo batasan da ita ake ba Tese ta kuma yi mata magana still INdo bata juyo ba Tese taja tsaki tare da zuwa ta janyo hannun INdo tare da zaunar da ita a wajan wankin kan sai masifa take da turanci ita kuma INdo tana Hausa. Cige d'ankwalin Tese tayi taja wani uban tsaki ganin ko tsefewa batayi ba, gashi Mommy d'inta tace tabita a hankali dan wanda ya kawota yace zata iya guduwa. Kibiya tad'auka ta tsefe mata gashi akwai laushi da tsayi saidai babu cika gashi kuma jah ne. Mayukan wanke gashi ta d'ebo sannan ta janyo kan INdo ta malala mata sai mita takeyi har aka gama Madam guloriya ta kuma shigowa hannunta d'auke da riga da takalmi wanda Abubakar ya bata yace abata tasa ayi mata kwalliya. Lokacin da aka saka kan INdo a dryer taji zafi sai ta saki wani uban ihu wai zafi, Madam Gloria tazo tana d'anyi mata wasa tare da takura mata har aka gama kannan yayi kyau gashi an tura mata shi yayi baki Tese ta nuna mata bathroom a shagwan ta nuna mata tace tayi wanka, INdo tayi da sabulai masu k'amshi gashi ruwan d'umi sannan ta fito sanya da kayan data cire babu wanda ya kulata Tese tayi mata kwalliya sannan aka bata doguwar rigar suka ce ta saka. Duk bayanin da sukeyi mata toh da hannun suke nuna mata tamkar wasu bebaye. Wata irin had'add'iyar abaya ce pink da belt black sai kwalliyan ma black ta jikin rigan, fitowa tayi daga d'akin bayan tasa saidai jikinta babu bra madam Gloria ta tambaye ta bayan ta nuna mata ta jikinta kasan cewar itama INdo akwa breast d'in ta turo baki tana k'unk'una da alamar dai batada ita. Babu kunya madam Gloria tafita wajan Abubakar yana zaune suna hira da Nafeesa tace k'anwarsa batada bra amma suna siyarwa ya bada kud'in. Abubakar kunya ta lullu6esa yace toh
Chapter 17 · 0% Book details