← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 53

Sashe 16

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. *VOTE me on wattpad @Hajjac* _page 13 na kune 'yan candidate d'in government girl secondary school Kwah, hope zakuji dad'in shi sannan kuma ina muku fatan alkairi a cikin rayuwarku kamar yadda kuke bin labarin nan_ Page *13* "Amman dai baka min adalci ba kasani ko m twinnie? A k'a'ida yau zanje gidan su fatma sabida gobe nakeson wucewa amma kayi min haka, wallahi danasan gurin wannan wayuwayar zamuzo bazan rakoka ba mtww "Sanin idan na gaya maka bazaka yadda ba yasani k'in gaya maka sabida ina son muzo tare dakai." Sadeeq yayi mai banza har suka shiga cikin rugar fulanin, suna zuwa suka ga 'yan mata yara da manya sunzo zasu wuce. Ra6awa Abubakar yayi da motar gefe kasan cewar bazata wuce canciki ba sannan suka fito Sadeeq sai faman cin uban magani yake yi idonsa sanye cikin dark shade shi kuma Abubakar d'an siriri ne nashi fari kal kamar k'ank'ara. Suna fitowa INdo dake tsakiyar 'yan matan zasu tafi kasuwar badume tana ganinsu ta ganesu cikin karad'i tace. "Jakar uban nan,sun biyo ni masifaffun malamn nan." Kallon sauran abokan tafiyarta ta tayi tana gyara mayafinta tace. "Kowa ya samu sanda zamu k'arasa wajan wad'an can malaman, kawai danace muku kulle kukuma sai ku jibgesu." Suka ce toh kowa ya juya ya samu sanda harda ita sannan suka nufi gurin suma su Abubakar lokacin sun k'araso ciki sam basu ganeta ba sabida tayi girma ta zama 'yan mata, lokacin da ta baro sani tana 12years yanzu kuma tana 15years gashi tayi 'yar k'iba ta kuma canza. Abubakar shine ya taresu yana kallansu yace. "K'annena dan Allah muna neman gidan da INdo malam Hamza take, wadda tazo daga kauyen sani." Caraf ta cafe bayan ta rik'e kugu tace, "ga wata nan lafiya kuka zo inda nake..?!" Duk suka zuba mata ido Sadeeq dariya da takaici suka kusan kamashi ya kalleta kallo irinna raini sannan ya juya zai koma cikin mota yaji tace. "Wannene kaid'in dacta Habubakar ko kuma malam Sadeeq? Na ganeku rasai." Ko waigowa beyi ba sabida haushi ita kuma ta kalli Abubakar dake tsaye yana kallonta, sam bega wani aibu a tattare da ita ba yaji zuciyarsa ta sanyaya yanajin tamkar ya rungumeta amma bahali gashi ya gansu da sandina kuma su ba shanu a taredasu bareyayi tunanin cewar kiwo zasuje. Cikin sanyin murya yace. "Humaira inason muyi magana dake, naje munyi magana da mahaifinki sauran ke." "Allahu akubar kabiran, malam Sadeeq ni ba'a renamin hankali wallahi nan garin yanzu sai nasa su rakaku da duka wallahi." Ido ya zaro jin abinda take cewa ya fara bin hannayen yaran tare da tuna wata kalma ta bahaushe da yake cewa sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, ya d'an kalleta cikin ransa yana tunano ko harsai yaushe ne zata yi hankali. Ya rasa ya zaiyi da su sai yayi murmushi tare da zura hannu cikin suit d'insa ya zaro wallet suka bishi da kallo ya ciro 2k ya mik'awa wata yarinya yace ga wannan kusha alawa. Kallon kud'in suka yi sai kuma sukayi baya-baya suna zaro idanuwa, ganin dalla-dallan kud'i yasa INdo tayi saurin k'arasawa zata fisge Abubakar yayi saurin janye hannunsa tare da kad'a mata kai yace. "A'a wannan ba naki bane, naki yana gurin Sadeeq sai kin yadda da abinda zan gaya miki sannan zamu baki su suna can dubu ashirin." INdo ta dafe k'irji tare da jan baya tace, "Dubu ahirin? Toh kaine dacta Habubakar kenan, meyasa kabari aka bawa malam Sadeeq kud'ina kuma alhalin mugune ba bani zai yi ba..?!" "Zai baki amma sai kin yadda da maganar da zamu gaya miki." Tana jin haka tace "kaltume ku kar6i kud'inku, kuyi gaba zan taho daga baya idan na kar6i kud'ina." Kar6a suka yi sannan suka tafi ita kuma ta yarda icen hannunta tare da goge hannun jikin zaninta, shi kuma sai kallanta yake yi, sam ya rasa abinda ya gani a jikinta yaji zuciyarsa na azabtar dashi, yace. "Toh kinga wani dutse can muje mu zauna in gaya miki abinda muka zo sanar miki." Ba musu suka tafi sai juyawa take tana kallon Sadeeq a cikin motar, suna zuwa Abubakar ya zauna ita kuma ta tsaya yace. "Humaira zauna mana." "Karkafa kuma cemin wani humaira hekace wata yarinya e'heee." "Sunan Mamana gareki shima humairan na fad'a ne sabida babu yadda zanyi, ki zauna kijini dakyau abinda zan sanar miki, idan baki yadda ba zamu d'auki wata yarinyar anan kauyan mu bata kud'in." Da sauri ta zauna ya kalleta yama rasa ta Ina zai fara mata bayani yadda zata faminta ta gane manufarsa karta yi mai hayaniya. Zare glass d'insa yayi sannan ya kalli fuskarta sai faman wasa take da k'ananun duwatsu yace. "Humairah kina son yin karatu?" Kai tsaye INdo tace mai, "A'a aradu nida zanyi aure." Abubakar ya kuma kallanta, ganin tayi maganar har cikin ranta yasa shi mik'ewa tsaye yace. "Eh ai zakiyi auran amma ki gaya min idan kinason yin karatu kema wata ran ki zama kamar matar gwamna ko shugaban k'asa kuma kema wata ran ki amfanar da bayin Allah da kuma 'ya'yanki wanda zaki haifa idan kinyi aure." Rufe ido tayi da tafin hannunta wai kunya sannan tace. "Eh toh bank'i ta bakinka ba amma ni bazan yi wani karatu ba haka kurum naje malamai su dinga jibgata ba a'hh jikina bana banza bane, kuma ma yazan yi da auran saleleh tunda shaura 'yan makwanni.." Mtwww Abubakar yaja tsaki jin ta kira salele cikin d'an 6acin rai yace. "Waye shi salelen? Me gareshi? Ana son fito dake daga cikin duhun kai kina wani sake dulmiya kanki? Kinga humaira ki yadda yanzu mu koma sumaila dake akwai kayan da na tanadar miki sababbi tindaga kan, atamfofi, shaddoji, materials, mayafai takalma, jakunkuna da kayan kwalliya, amma sai kin yadda zaki bimu mu koma can gidan ku..." Shiru INdo tayi ta fad'a cikin tunani, kallonta yayi ganin tayi shiru ya fara addu'ar karta ce mai bazata ba murya a raunane yace mata. "Please Humaira talk to me mana." Kallansa tayi jin yayi mata turanci tace "sake gaya min abinda ka fad'a yanzu da hausa ko da fulatanci sune yarena." "Oh cewa nayi kiyi magana mana, inason jin matsa yarki I told you zaki samu komai idan muka maida ke sani." "Kai dacta habubakar kun saba cewa zaku yi amma ni bakwa bani bare ma kuma malam Sadeeq hmmmm. "Humaira wannan karan nine zan d'auki duk wani nauyin abunda kike so, fatana da burina ki yadda mu koma nayi miki alk'awarin yi miki duk abinda kike so indai befi k'arfina ba." "Harda kayan d'aki idan mun tashi yin aure da salele?!" Ta tambayesa duk da yaji haushi amma be nuna mata ba sai ma eh daya ce mata. "Toh kuwa zan biku amma hemunje mun gayawa baba iro dasu yakumbo talatu." Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Abubakar yace mata. "Toh muje." Jerawa suka yi INdo sai d'an tsince-tsince takeyi yana hanata da haka har suka k'arasa. Tun a bak'in k'ofa ta fara k'iran yakambo talatu tafito da d'aurin k'irji tana tambayar. "Lahiya mai sunan uwa.?" "Anzo tahiya dani gida, ina lawisa da kande suzo muyi bankwana A gindin bishiya Abubakar ya tsaya yana kallon inda suke rayuwa ya kuma tuno cikin garin kano kafin ya tunano garin abuja zuciyarsa ta dira a k'asar Spain. Lallai Allah beyi ko ina dai-dai ba, wannan yafika kaima kafi wani sannan ya furta kalmar "Alhamdulillah." "Ina wanda yazo tahiya dake d'in, karki ce mini wannan ne?" "Aradu baba iro shine, d'an uwan malamin mune a sani." Tabarmar kaba aka shimfid'awa Abubakar ya zauna tare da baba iro k'arin bayani da kuma sanar dashi cewar da izinin malam Hamza yazo d'aukarta. Abinciccika aka kawo mai saidai beci ko d'aya ba sannan baba iro yace. "Toh gaskiya bazan baku yarinyar nan ku tafi da itaba, hedai muje tare har garin, idan kuma ka yankamu kaida Allah domin hine mesakayya." Babu gaddama Abubakar ya amince, aka sanar da mutanan gari INdo taje ta harhad'a kayanta akayi mata tsaraba da yawa sannan mutane mata da maza suka tafi raka ta gurin mota. "Yakumbo dan Allah idan salele ya dawo kice mihi na tafi amma ya dinga zuwa sumaila muna gaisawa kafin bikin mu kinji.?!" INdo ta fad'a Abubakar dake gaba ya dinga jan tsaki yana jin yadda take k'ara jajjada sak'on da za'a gayawa salele suka k'arasa wajan mota dama tundaga nesa Sadeeq ya hangosu ya dinga kwasar dariya ganin yadda sukayo gungo guda sai tada kura sukeyi, suna zuwa ya had'e rai sukuma mutanen suka dinga fad'in ahe 'yan biyu ne. INdo da baba iro suka shiga gidan baya sannan Abubakar ya zauna a driver seat Sadeeq na kusa dashi ya data motar suka dinga d'aga musu hannu anayiwa baba iro adawo lafiya. Har suka fito daga surkullen babu me magana sai INdo datake lissafo wad'anda zata yi kewa, suna hawa babban titi iska ta fara hurata ta A.C ta mirgina kai sai bacci har rawar sanyi take yi. ***** Sani...Suna zuwa har k'ofar gidan malam Hamza suka tsaya baba Iro ya tashi INdo duk ta cika su da munshari wanda hakan be damu Abubakar ba amma Sadeeq iya kuluwa ya kulu, ta bud'e k'ofar da sauri tana fitowa 'yan unguwa suka fara cewa. "Ga INdo... Ga INdo...!" Ta bud'e ido tare da kuma mistsike shi tana dariya, duk wanda ta gani saita fad'i sunansa kafin ta shige cikin gida da gudu tana k'iran Innar su. "Kai INdo yaushe kika dawo?!" Cewar k'aninta shehu yana wankin kayansa, bata kulasa ba Inna ta fito INdo ta d'areta cikin murna tana washe mata baki. "Oh 'yarnan kina nan da halinki ko??" "Ta6 Inna kenan Ina zeje, yana nan aradu wai ina Nafeesah da Sagiru duk bangansu ba..?!" "Suna waje k'ila dai suntai wani gurin ne, ahe yau zaya d'aukoki jiya malam ke gaya min yadda sukayi da malam Saddiqun." Cewar Inna INdo tayi dariya bata ma bata amsa ba tace, "Inna ina Rukayya kuwa, oh ni INdo tana nan kuwa?!" "Tana nan yanzu ma 'ya'yanta uku sai kuma wanda zata kuma haihuwa." "Kai Inna yanzu cikin wani gareta kama d'ahare ta saye? Bari naje gidan naganta nikam." "Haba 'yar nan daga dawowar
Chapter 16 · 0% Book details